Free chapter · Read without an account
BABI NA ASHIRIN DA UKU
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
GIDANA YA zame min kamar na shiga wurin da bansan kowa ba kuma bana so kowa ya sanni da abinda yake faruwa dani. Ya zame min wani irin wuri da bana so nayi magana kuma bana neman farin ciki a cikin shi. Ya kasance, a wurina, bana so nayi hulɗa da kowa kuma bana so kowa yayi hulɗa dani. Baffa ya koma makarantar da ya dawo hutu ba tare da ya sanar dani ba kuma nasan be sanar da mahaifin shi ba saboda naji a washegari yana tambayar Farida be ga Baffa ba ko ina ya shiga. Tace ya wuce makaranta. Nima a wurin ta nake jin ya tafi. Bayan tafiyar shi kuma be kira ni ya min magana ba. Ban san abinda ya dame shi ba. Nasan duk rashin nuna damuwar shi, Baffa baya wucewa makaranta be min magana ba. Kuma naga babu ɗaya daga abinda ya ɗauka na duk irin abinda muke dashi a gida. Nan na ƙara shiga mamaki saboda nasan yana buƙatar abinci. Kiran shi nayi a waya domin naji dalilin wucewar shi makaranta be faɗa min ba. “Babu komai Umma” itace amsar da ya bani. Na faɗa mishi ya kira mahaifin shi ya tura mishi kuɗi tunda akwai buƙatocin rayuwar da yake so ya biya. Flatly ya amsa ni wanda ya bani tabbacin ba ze yi ba. Tunani na babu inda ya kaini se me yake faruwa dashi irin haka ko yana jin atmosphere gidansu ya chanja mishi ne ko kuma yasan abinda yake faruwa tsakanina da mahaifin shi. Da sauri na kawar da wannan tunanin a raina saboda ban san ta ya ze san abinda mahaifin su ya aikata ba kuma bana son wani daga cikin ƴaƴanmu yasan abinda yake faruwa.
Wannan mutunci da daraja da suke ganin mahaifin su dashi, bana son ya taɓa gogewa a idanun su.
Yaya ta da na faɗawa sirrina ta kan kira ni akai akai domin taji yadda nake. Na kasa yin walwala a gidana. A duk inda naga Ibrahim, a duk tunanin da nake yi a rayuwa ta, be wuce wannan abu da naji a kunne na ba. Na kasa cire abinda naji da kunnuwana. Wani lokaci har gani nake a cikin idanuwa irin abinda Ibrahim ya aikata da wata mace wacce ba matar shi ba da kuma yadda ta tambaye shi ba ze taho su yi wanka tare ba.
Zuciya ta a kodayaushe zafi take min. Na rasa sukuni na. Ina ta duban inda na kasawa Ibrahim ba ta hanyar shimfiɗa a wurin shi ba, ta hanyar komai na rayuwa wanda ya kama da wannan wacce ke tare dashi a kowane yanayi na rayuwa. Ya haɗa da wannan wacce take encouraging nashi a duk abubuwan da yasa ma gaba ko ma abinda be sa ma gaba ba wanda nasan ze samu cigaba a tattare dashi. Nayi haƙuri da duk wani abu da ya kawo min a gida yace gashi koda bana son shi ko kuma ɗanɗanon shi be min ba. Nayi haƙuri na zauna da irin kalar rayuwar da yake iya affording ban taɓa tilasta mishi yi min abinda yafi ƙarfin shi ba. Na kasance me tarbiyya me kare kaina da duk wani abu me alamar tambaya a dabi'u ko kuma ta hanyar kasancewa tare da wasu maza duk da irin tafiyar da yake yi yana barina. Ba saboda bani da sha'awa ba, saboda tsoron Allah da mutunta kaina da mutunta shi da kuma mutunta auren dake tsakaninmu dashi. Ina kan kokari iya ƙoƙarina akan yaranmu. Na tsaya akansu a wurin tarbiyyar su da ilimin su se idan yaro ya bi wata hanyar daban na ɓata wacce ba ni na koya mishi ba saboda ba zaka iya haifar dabi'un yaro ba, shine kawai kake iya haifa. Na kasance matar da yake samun natsuwa a wurinta da tausayi da jin ƙai haɗi da ƙauna. Shin menene namiji yake buƙata idan ba waɗannan abubuwan ba?
Zaune nake a ɗakin su Baffa, Yaya ta ta kira ni. Murmushi nayi tukunna na ɗauki wayar ta.
“Yaya Barka da wuni”
“Barka kade, Maryam. In jin kina lahiya da ɗiya ta Farida da sauran ɗiya na Ahmad da Babana?”
“Lafiya ƙalau Yaya. Su Ahmad suna makaranta har yanzu basu yi hutu ba amma dai sun kusa”
“To ma sha Allah. Lahiya dai ko Maryam?”
Ban san lokacin da hawaye suka fara fitowa daga idanuna ba. Na kasa bawa kaina da kuma zuciyata haƙuri akan irin wannan abu da mijina ya aikata. Shin kun gane irin abinda nake ji kuwa? Kun gane daga inda nake fitowa da duka waɗannan abubuwan?
“Yaya wallahi na kasa yin haƙuri da wannan abu da Ibrahim ya min, Yaya”
“Ba zaki dawo gida ba, Maryam? Dama akwai wani abu da kike a garin can na Inyamurai”
“Yaya idan na dawo gida nayi me Yaya? Kin san maganar kashe aurena be tashi ba Yaya. Idan na kashe aure na yaya zanyi? Da wane ido mutane zasu dinga kallona? Da girmana da shekaruna na zama bazawara Yaya? Ta ina zan fara kamawa? Kin san yadda society mu yake da duk irin pressure da ake ɗaurawa mutum. Yaya na wuce zama bazawara yanzu ta dalilin kashe aure ba mutuwar miji ba. Ya zan bar su Ahmad da Farida? Ina jin tsoron sa musu trauma na rabuwar iyaye Yaya. Da wane ido zasu kalla mahaifin su idan suka san abinda yayi? Bana son mutuncin shi ya zube a idanun ƴaƴan shi Yaya”
“To wannan zama wane iri ne kuke yi yanzu Maryam? Da irin wannan auren irin haka yanzu naki, ai gwara ki dawo gida ki huta. Yana da mutunci ze je ya aikata abinda ze zubar mishi da mutuncin nashi, Maryam? Idan ba zaki iya rabuwa dashi ba, nima bana baki shawarar rabuwa da mijinki na shekara da shekaru Maryam, ki duba zuciyar ki ki yiwa kanki karatu ki ba zuciyar ki haƙuri akan abinda ya faru. Dukkanin mu masu laifi ne, Maryam. Ki duba alhairan shi kiyi haƙuri ki ba zuciyar ki haƙuri. Amma idan kika ji ba zaki iya ba, ba zan tilasta miki yafe mishi ba. Dukkannin mu muna da dalilai mabanbanta na aikata abubuwan da muke aikatawa”
Ina kuka nace “Yaya ya zanyi dan Allah Yaya? Ki bani shawara wacce ba zata cutar dani ba. Yanzu haka ko Ibrahim bana son gani. Nasan Farida zata iya fahimtar ba ma zaman lafiya tare dashi kin san yadda nake dashi Yaya. Yaya fisabilillah kinsan wani hali nawa wanda bashi da kyau a wurin miji? Kina iya faɗan inda zan iya kuskurewa ga Ibrahim ko kuma inda na kasa mishi?”
Shiru Yaya ta tayi ba tace komai ba.
“Yaya?”
“Maryam” ta kira sunana tare da sauke ajiyar zuciya “Idan kika gane maza kin huta Maryam. Nasan abinda Ibrahim ya miki be kyauta ba ko zan ce be kyautawa kanshi ba be kuma girmama auren dake tsakaninku ba. Amma inaso ki sani, zaki iya zama komai na kirki ga namiji, amma ze tafi yayi abinda yake so ba tare da ya duba halin da zaki shiga ciki ba. Ban ce duka maza ba, Maryam, amma wasu daga cikin su haka suke. Abinda Ibrahim yayi, ina so ki duba ƴaƴan ki ki yafe mishi. Ki dube shi a matsayin wani babban kuskure da ya miki ki yafe mishi. Kiyi haƙuri Maryam. Kiyi haƙuri. Kiyi haƙuri Maryam. Nasan wannan abun da ciwo yake amma kiyi haƙuri”
Jin abinda Yaya ta ke faɗa ina kuka na kashe waya ta na aje akan gado na cigaba da kuka saboda irin zafin da nake ji a cikin zuciyata. Haƙuri ya kasance wani abu me zafi ga duk wanda aka ce yayi. An fiya bada haƙuri ne ga wanda aka zalunta ko kuma wanda yake cikin jarabawa marar daɗin gani da sauraro.
Se ana kiran Maghrib na fito daga ɗakin su Baffa. Bana kwanciya a ko wane ɗaki saboda bana son tunanin Farida yayi zurfi akaina da mahaifinta.
Sallah Maghrib nayi a ɗakin mu ina zaune har Isha. Bayan nayi Sallah Isha ne na kwanta nan akan carpet da na gama sallah da ita tunanin duniya ya min yawa. Ina so na samu wani abu da zan riƙe na daidaita kaina kafin sauran manyan yara na su dawo hutu daga makaranta.
Sallamar mutum naji ina nan kwance. Ibrahim ne ya shigo yayi sallama kamar wanda baya son yayi magana saboda wata damuwa da ta dame shi. Ban amsa ba saboda bana son wani abu ya haɗa ni dashi.
A wurin kaina naji yayi min tsaye se na rufe idanuna ina roƙar Allah yasa ba magana ze min ba.
“Maryam” ya kira sunana
Shiru nayi ban amsa mishi ba.
“Maryam” ya ƙara kiran sunana. Nan ma ban amsa mishi ba.
“Maryam kiyi haƙuri muyi magana dan Allah”
“Ibrahim, ba zaka ƙyale ni ba?”
“Ya zan ƙyale ki, Maryam? Dan Allah kiyi haƙuri muyi magana dan Allah”
Shiru nayi ban sake cewa wani abu ba se wane irin zafi da nake ji a cikin zuciyata kamar na fashe da kuka.
Gabana ya dawo ya tsugunna yana kallona “Maryam”
“Dan girman Allah ka wuce daga wurin nan Ibrahim. Wallahi bana son ganin ka”
“Ni kike cewa baki son gani Maryam?”
Daga kwancen da nake na tashi na haɗe hannuwana wuri ɗaya nace “Dan Allah ka rabu dani Ibrahim. I need space”
“Wane irin space Maryam? Dan Allah kiyi haƙuri da abinda ya faru”
Idanuna ne suka cika da hawaye “Bana son haƙurin ka Ibrahim. Bana kuma buƙatar shi. Kuma bana so idan kana min magana. Duk abinda kake so kaje ka cigaba da yi Ibrahim. Wallahi Allah ze saka min a cikin wannan auren namu tsakanina da kai”
Kneeling down yayi ina kallon shi. Hannuwana yaje ya roƙo nayi saurin janye hannuwa na.
“Kiyi haƙuri Maryam”
A cikin tsawar da ban taɓa yiwa Ibrahim ba nace “Ba zan yi haƙuri ba Ibrahim. Ba zan yi ba”
Sunkuyar da kai yayi hawayen da suke idanuna suka fara zubowa. “Wallahi kayi min cin amanar da ba zan iya misalta zafin ta ba, Ibrahim. Kanka ka zalunta amma irin wannan zaluncin ba kai kaɗai yake illatawa ba, dani da duka iyalanka yake illatawa”
Ibrahim kallona yake idanun shi sun cika da hawaye suna ƙoƙarin fara zubowa. Hawayen shi na fara zuba na sunkuyar da kaina.
“Ban san wani irin abu ne yazo min a kai har na aikata abinda nayi ba, Maryam. Roƙo na kawai shine ki bani dama na gyara kuskure na a wurin ki”
Ɗago da kaina nayi jin abinda yace “Ta ya zaka gyara kuskuren ka Ibrahim? Zan ƙara yadda da kai? Zan ƙara aminta da kai? Waɗannan abubuwan duk kasa ƙafa ka watsar dasu bayan kasan ba lokaci ɗaya suke samuwa ba, Ibrahim. Ka zaluncen mu, nida ƴaƴana”
“Maryam dan girman Allah kiyi haƙuri. Nasan na zalunce kaina kuma nasan bani kaɗai na zalunta ba har wanda nake jagoranta amma dan Allah kiyi haƙuri. Ba zan ce rashin Nasir ne ya janyo min matsala a rayuwa ba amma rashin sa na ɗaya daga cikin manyan abinda yasa na aikata abinda na aikata. Bana justifying laifina dan Allah kiyi haƙuri ki bani wani chance a rayuwarmu”
“Kasan kuwa ka sanya reza me kaifi ka datse wannan zaren dake riƙe da rayuwarmu, Ibrahim? Ta ya zan kallon ka yadda nake kallon ka bayan ka zubarwa kanka mutunci kuma ka zubar min da mutunci? Me yasa baka yi tunanin iyalanka ba se de Kai kanka? Dan Allah ka ƙyale ni dan Allah”
Kanshi na sunkuye yana zubar da hawaye be tashi ba kuma be ce komai ba. Tashi nayi na bar mishi wurin na zauna a kujerar ɗaya dake cikin ɗakinmu. Kaina na ɗaura akan laps ɗina ban ɗago ba hawaye na cigaba da zubo min.