Free chapter · Read without an account
Chapter 35
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
https://www.arewapen.com/book?id=6ab251c3cb0cfb2373811a7f
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 35.
"Za ki bini imbaki ruwan." Jay ya faɗa kamar me tambayarta, sai de kuma ba ainahin tambayar yake son yi ba, so yake ya ce maya ta bishi ya bata ruwan, sai maganar ta fito da siffar tambaya.
Idonta na tsiyayyar hawayen data kasa tsayarwa ta zame hannayenta daga cikin na shi sannan ta ɗaga ma shi kai.
Sake kama hannayenta ya yi tare da matsawa da ita kusa da motar ya buɗe mata back sit tare da juyawa ya lumshe idon shi akanta sannan ya ce.
"Bisimillah."
Yana matsawa kaɗan donta samu ta shiga.
Wani iri zuƙa tayiwa daddaɗan sassanyan ƙamshin turaren shi daya wuce mata kai tsaye cikin ciki.
Karkata miron yayi a saitinta yana tuƙi yana kallonta ta cikin madubin yana jin wani abu na yawona ƙirjinsa.
Daidai wajen gidan man Asha shayi ya hangi wani table da aka cike shi da goruna da ledojin ruwa, dan haka kan shi tsaye ya nufi wajen tare da yin parking a saitin me siyar da ruwan sannan ya fita yaje wajen shi.
Da siyen ruwan da buɗe mata motar da damƙa mata luwan a lallausan hannunta da kuma tada motar da yayi duka sun faru ne cikin abin da bai wuce mintuna biyar ba.
A yanzun da yake yin nesa da wajen yana barin wajen cikin gudun da yake sheƙawa da motar, sai yake jin kamar yana tafiya da iya gangar jikin shi ne banda zuciyar shi, yana jin kamar ya yi mantuwar abu me muhimmanci daya gagara gane ko minene.
Kallon shi Uncle ya yi sanda yake karya hancin motar yana isa wajenda aka tanada don yin parking ɗin motocin gidan.
"Ammadai wannan ba ita bace haɗuwarku ta farko ba ko?." ya tambaya da muryar zolaya lokaci ɗaya yana buɗe murfin motar fuskar shi ƙunshe da murmushi....
****
ALHAJI AHMAD.
Ba ƙaramin ɓaci ran shi yayi ba lokacin da Mommah ta buɗe ɗakin ya taradda idon Afnan yayi jazur alamar tasha kuka ta ƙoshi, saɓarta ya yi a kafaɗa tare da soma takawa ya nufi sama.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un Alhaji muna cikin tashin hankali banga Mujaheed ba ya fita tun marice kuma wallahi shi kaɗai ya fita wayar shi a akashe kuma." Mommah ta faɗi tana bin bayan shi tana magana.
A mugun fusace ya juyo tare da daka mata tsawar data firgitata sannan ya ce a kausashe.
"Halima ki shiba hankalinki da ni tun gabanin in aikata abin da baki tsammata ba." ya faɗa yana huci tare da hayewa a zafafe saɓe da Afnan a hannun shi ya shige ɗakin shi ya murza key.
A jiyar zuciya Mommah ta sauke lokacin da ta shige yabarta saroro bakinta ɗauke da magana.
Sauka ƙasa ta yi tare da soma laluben layin Hajiya Zainab, sai data jera kira wajen bakwai amma no anser gaba ɗaya a rikice ta ke da ɓacewar Mujaheed kamar wani yaron goye.
"Ya Allah kaci gaba da bani juriyar zama da wannan baiwar taka ba tare da na aikata abin da zuciyata ke umurtata akai ba."
Daddy ya faɗa yana shimfiɗar da Afnan akan lafiyayyen bed ɗin shi, ya zauna tare da dafe kan shi da yayu ma shi nauyi sosai.
"Allah na tuba ka yafe min abisa laifin cin amanar ɗan uwana da nayi na ha'ince shi akan dukiya, Allah kada ka jarabe da sake aikata kwatankwacin hakan, idan abin da nike shirin aikatawa daidai ne Allah kaci gaba da baki zumma da ƙwarin gwuiwar aikata hakan." ya faɗa yana share kwallar data zubo a idon shi.
Kwanciya ya yi kusa da Afnan wasu ƙananun firarrakinsu shi da marigayi Abdul na dawowa kan shi yana jin kamar Abdul yasan abin da zai faru yanzu yayi maganganun.
"Abdul ka yafe min akan cin amana da yaudarar dana aikata maka, tabbas ban cika amini na ƙwaraiba da ban samu damar kula maka da amanarka ba, niɗin butulu ne."
Yana irin waɗanan maganaganun kamar wanda ya taɓu barci ne nauyi yayi awon gaba da shi.
A ranar Momma sai de barci ɓarawo ne yayi awon gaba da ita amma sam ta kasa rintsawa tunanin Mujaheed da halinda yake ciki kawai take yi, tun yana yaron shi daya gama bodin bayajin ya sake zuwa wani waje ya kwana shi kaɗai, duk rintsi yana gida tare da su, bai zuwa ko nan da can sai da izininta.
Washe gari.
Da kuka Mommah ta nufi ɗakin Daddy gaba ɗaya ta firkice ko isashen barci bata samu ba, a can kuma ta tadda wata damuwar, domin kuwa ta same shi yana sallah sai ta nufi bakin bed ta zauna akan sit ɗin gaba, nan take idonta ya sauka akan takardun data gani ranar can, a kiɗime ta ɗauke su ta shiga duddubawa.
A nutse ya linke sallayar batare da ya kalli koda inda take ba ya nufi kan bed ɗin da zummar ya tada Afnan ta yi sallah.
"Wait Alhaji Ahmad wai dama da gaske kake? miye hakan kake shirin aikatawa anya kuwa kana amfani da tunaninka." Mommah ta faɗa a ɗan tsawace, ɓacin rai da firgice na kuma bayyana a kan fuskarta.
Daddy bai kulata ba ya shiga tada Afnan.
"Allah ka tsinewa wannan shegiyar Zunainar da take neman haukata lissafin gidana, ta raba ni da ɗana sannan kuma tana ƙoƙarin rabani da dukiyar mijina, na rantse da Allah idona idonta saina salwantar da rayuwarta."
A bazata kalama Mommah suka daki dodo kunnen Daddy wanda hakan ya saka shi tsayawa daga ƙoƙarin sauko Afnan da ya ke yi, ya ɗago a fusace tare da isa wajen Mommah ya tsinke fuskarta da lafiyayyen marin daya tsaida ji da ganinta na yan sakanni.
Can sama sama ta tsinkayo muryarsa yana faɗin.
"Ke butulu ce wallahi, makira annamimiya me fuska biyu, zanyi mummunan saɓa miki idan har kika ƙara kuskuren zagar min ya."
"Sakina zaka yi akanta ko?" ta tambaya idanuwanta a bushe.
"Akan Zunaina zaka sake ni ko Ahmad, ita Zunainar dana raineta tun yarinta, karfa ka manta na raineta ne kamar yanda na raini Mujaheed da Afnan ban rageta da komi ba, kenan sakayyar da zaka yi min kenan dan na riƙi ɗiyar amininka wanda baku haɗa komi da shi ba, sam bakada adalci wallahi Ahmad." ya faɗa zuciyarta na tafarfasa.
A fusace Daddy ya ce. "Akan Zunaina zan iya saɓawa kowa Halima, kuma ki daina cika baki akan kin raineta, idan ke kin manta bara intuna miki, abaya kin ƙyamaci Zunaina bayan mahaifanta sun rasu, saboda kina ganin babu wanda za baki abin duniya, baki rungumi Zunaina ba har saida kika ji labarin dukiyarda take da ita, wacce ke hannuna, kin raineta bisa son zuciya sannan kuma kina fakewa da soyayyar ƙarya a bayan idona kina cutar da ita, bugu da ƙari kina ganin kin sami dukiya kika manta da maraicinta, kika rushe soyayyar dake ginuwa tsakaninta da Mujaheed, ko kin manta ina sane da halin matsi da takurawar da kike yi mata ne a gidan nan kawai ina kawar da kaine bana tanka miki."
Ya faɗa zuciyar shi na ƙuna.
"Ya isa Ahmad ya isheka haka, bangane batu akan dukiyar da kake nufin na ci ba, ni naci dukiya ko kai kaci, ina ce kaine kazo da batunta ni kuma na goya maka baya tare da baka shawara shine kuma zaka juya abin kaina."
"Kika bani shawara ko kuma kika cutar da ni kika kaini ga halaka?." ya faɗa a fusace.
"Na faɗa Ahmad, na faɗa kaci dukiya kaine kaci ba ni ba, sannan kuma ka sani banyarda ba ban lamunce maka ba akan wannan ɗanyan aikin da kake shirin aikatawa na bayarda dukiyarka wa Zunaina, ban lamunce maka ba Ahmad domin kuwa ni keda kai da kuma ƴaƴana baka isa ka aikata abu kai tsaye ba tare da shawarata ba."
Wani baƙin fusatacen kallo Daddy ya watsa mata a harziƙe ya ce da ita.
"Arw you mat? ya zaki ji if nace maki ina da another women, and inada wasu yaran bayan naki, ya zaki ji idan nace miki ina da yara masu yawa ba guda biyu ba kika haifamin???.".....✍🏻
Nikam nace Ummumm fa Daddy kar ɓacin rai yasa ka faɗin abin da nan gaba zai dame ka.
Kai Mommah ko ciwon kai, ai ni Mujaheed yayi min daidai daya gudu ya barki wallahi ina dalili wannan rashin sanin daidai naki.
Masu karatu mu kasance tare da ku a next chapter.
Please like and share my yan amana.
MARYAM STAR CE