Free chapter · Read without an account
75
Boɗejo ta ƙara ɗaure fuska a lokacin da take isowa ta tsaya kan Turaki.
Tsananin jin takaicinsa na bayyana ɓaro ɓaro akan fuskarta, ji take tamkar ta kai hannu ta wanke masa fuska da marukan da zai saka shi ganin walƙiya.
"Mara mutuncin banza da wofi, kai har nawa kake da zaka raina ni? Ina maka magana ka yi banza da ni ka ƙaro gaba, wato ga ƙatuwar shashasha na yi maka magana ko? Ko da yake babu komai, ba ni ka raina ba, ubanka ka raina".
Ta gyara zaman gilashinta tana saka hannu ta ɗago fuskarsa da ke ƙasa,"Wallahi bari ka ji na faɗa maka, ka yi kaɗan ka ce zaka wulaƙanta min Ilham, sanin kanka ne kaf jikokina na fi ƙaunarta, ba'a haifeka ba, ba'a haifi uwar da zata haifeka ba, ɗan iskan banza. Yaushe ne ma kaciyarka ta girma har da kake jin kafi ƙarfin ka bi umarnina da na ubanka."
Ta numfasa, tana watsawa Hajiya Madina da Hajiya Ramla wani kallon jin haushi. Sannan ta ci gaba da magana, bakinta kamar zai yi kumfa.
"Kai ka san Ilham ta fi ƙarfin wulaƙancinka, domin kuwa ta fika gata. Ita ɗaya a wajen uwarta bata ta so ta san wata aba damuwa ba, don haka ƙaryarka ka zame mata damuwa. Kishiya! Kishiyar ma mara aji ƙasƙantacciya wadda ta yi aiki a gidanku. Duk wannan rashin mutuncin da ka ke yi ba kowa ke saka ba, illa waɗannan munfukan marasa yafiya da haƙuri".
Ta faɗa tana nuna Hajiya Ramla da Hajiya Madina da baki, tana bin su da harara.
"Kuskure uban waye ba ya yinsa, haka laifi uban waye ba ya yinsa."
Sai kuma ta koma kan su Maama ɗin.
"Ku waye ya san adadin laifin da ku ka yiwa ubangiji. Saboda kawai uwar yarinya ta yi masa laifi sai ace akanta za a yi hukunci... Shekara nawa da faruwar lamarin, shine ba a tashi ramako ba sai yanzu da ubangiji ya haɗa tsakaninsu da aure, saboda son tada husuma. Sunnar ma'aikin zaku lalata saboda rashin neman albarkar rayuwa. Kuma ke Madina ba cewa kika yi kun yafe ba, amma saboda dai zuciyarki baƙa ce sai yanzu za ki wani fa-ke da abin da aka riga aka manta da shi. Dama na san kina baƙin ciki da gatan da Allah ya yiwa Ilham, wanda ƴaƴanki ba su samu ba, to kuwa sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu, domin gata da mulki da jin daɗi da ilimi da tarbiyya, Ilham ta yiwa ƴaƴanki zarra, har a naɗe duniya ba zasu samu abin da ta samu ba".
Hajiya Ramla ta ji kamar ta miƙe ta bar wajen. Hajiya Madina kuwa ko a gefen silifas ɗinta. Ranta fess, hasalima ma fakar idon Boɗejo ta yi ta kyaɓe baki, tare da kawar da kanta gefe.
Jira take ta gama tijarar sannan a bata takardar sakin Jikartata, da ta zo tana tijara akan an yi mata kishiya, ta san da hujjar ita ƴar aikin da suka raina ta fi Ƴar sarkin matsayi.
Boɗejo ta ƙara ƙuluwa ganin duk sun mayar da ita kamar wata mahaukaciya.
Ta sake gyara zaman gilashin da tsabar masifa yake zamowa.
Ta dubi Turaki da sabon takaicinsa ta ci gaba da cewa,"Idan ba ka sa ni ba ka sa ni, akan Ilham ina iya ɓatawa da uban kowa, idan na ce uban kowa har da nata uban kuwa, ka ga kenan naka uban ba komai ba ne a idona. Saboda haka yanzu tun muna ta lafiya lafiya, ban ja abin da zai hana kowa kwanciyar hankali ba, to ka miƙe ka wuce mu je ka kaita asibiti. Ɗan banza ka samu ka ɗirkawa yarinya ciki shine za ka watsar da ita, to miƙe mu tafi, alhakin kulawa da ita ai akanka ya ke yanzu ba'a kan iyayenta ba".
Shi dai kansa har lokacin na ƙasa yana ta kallon rubutun sakin da ya yi, ya rasa gaba ɗaya me ma yake ji a tare da shi, tsabar bala'in ciwon da kansa ke yi masa ji yake kamar zai bar jikinsa.
Da yana da dama, da ya yiwa Boɗejo abin da ba zata sake zuwa kansa ta masa ihu haka ba, balle har ta faɗa masa maganganun banza.
Ganin alamar dai ko zata shekara a wurin tana sababi, cikinsu babu mai cewa ci kanki. Hakan ya ƙara ƙular da ita, ta ja dogon tsaki ta wuce.
Sai da Boɗejo ta kai bakin ƙofa tukunna ta waigo tana ƙara cewa,"Wai kuwa ba zaka taso ba? Ka san Allah in har wani mummunan abu ya sami Ilham, sai nasa an ɗaureka".
Ta yi ƙwafa tana bin su Hajiya Madina da wani kallo na ban haushi ta ce,"Ba ku da aiki sai saka yaro a gaba kuna kimtsa masa yanda zai bijirewa umarnin ubansa, yau zan gani sai dai ko ni ko ku a cikin gidan nan. Zan nuna muku na isa, zan nuna muku kaf a ƙasana ku ke, munafukai biyu masu son raba zumuncin ƴan'uwa, abokan sheɗ...".
Ba ta ƙarasa ba Turaki ya dakatar da ita a fusace,"Ya ishe ki Boɗejo, zan lamunci duk kalar rashin mutunci akaina, amma banda cin zarafin iyayena. Haba don Allah don Annabi, duk kin bi kin hana kowa kwanciyar hankali akan wata banzar yarinya can, idan tafi ƙarfin a wulaƙantata me yasa kika na ce aka aurawa wanda ba ya sonta, ba kuma zai taɓa sonta ba".
Bai san lokacin da ɓacin rai ya kaisa ɗaga ɗan yatsa ya na nuna ta da shi ba.
"Kina cin darajar kin kawo mahaifina duniya ne, shiyasa na ke ɗaga miki ƙafa akan irin cin kashin da kike yiwa Maama da Mum. Darajarsa kike ci nake yi miki duk kalar wata biyayya da girmamawa, banda haka wallahi da comon inuwarsu aka ce ki yiwa kallon banza ba za ki yi ba. Saboda haka yau ta zama rana ta ƙarshe da za ki ƙara ɗaga muryarki akansu, in ba haka ba zan baki mamaki".
Ba Boɗejo ba, hatta Hajiya Madina ta yi matuƙar mamaki, gami da tsorata da yanayinsa. Abu ne sabo a wurinta, sabon yanayi ne a tare da shi na ƙololuwar ɓacin rai da bata taɓa ganinsa a ciki ba, wata murya ce da ya fitar, wadda ba don tana kallonsa ba, tare da tabbacin cewa shi ɗin ne, zata rantse cewa ba muryar Ɗanta ba ne.
Kai da ganin yanda yake maganar ka san ya kai ƙarshen fusata, yadda yake kyarma kamar ma zai kai wa Boɗejo hannu.
Hajiya Madina ta kallesa ta sauke idonta ƙasa leɓenta na talewa da murmushi, alamun ta ji daɗin abin da ya yi. Ya biyata yau, ya nuna mata rainonta ne shi.
Hajiya Ramla ta yi saurin miƙewa tana sauke hannunsa da yake nuna Boɗejo da shi, murya a sanyaye ta ce,"Mene haka Babana? Kar fushi yasa ka aikata ba daidai ba, yi haƙuri komai ya yi zafi maganinsa Allah...".
Yana kallon Bodejo da ta saki baki tana kallonsa da tsananin mamaki, ta taho gare shi ya ce,"Ai komai ɗin ma ya zo ƙarshe Mum, ba zan iya ci gaba da ɗauka ba".
Ya faɗa yana barin kusa da Mum, ya ƙarasa gaban Boɗejo kafin ta iso gare shi, ya miƙa mata farar takardar da ke hannunsa yana cewa,"Na gaji, Na gaji da masifarki da neman tashin hankalinki, gaba ɗaya kin hana kowa sakat. To ina buƙatar Mum da Maama su sami nutsuwa, hankalinsu ya kwanta su huta da fitinarki, nima kuma ina da buƙatar nawa hankalin ya kwanta".
Ya manna mata takardar a jikinta. "Ga shi nan ki samawa Iyayena lafiya".
Boɗejo ta yi mutuwar tsaye ta kasa ko motsi, bin sa kawai take da ido, ta ji ƙirjinta na bugawa kafin ta iya ɗaukar takardar tana duddubawa, ta yi masa kallon tsab sannan ta ce,"Wannan kuma na menene?".
Bai ce da ita komai ba ya nemi kujera ya zauna yana dafe kansa, Khalil ya shigo a lokacin, ta yi saurin dakatar da shi daga hawa upstairs da yake shirin yi. Don shi ma kamar wani abun na damunsa, bai kula ma da su Maama ɗin ba a zaune.
"Zo, zo nan Khalil".
Ya dawo ya tsaya gabanta, ta miƙa masa takardar hannu na rawa,"Duba min mene aka rubuta a ciki".
Ya warware takardar, kalmar NI da ya fara cin karo da ita, tasa shi ɗago ido ya kalli Mum, sannan ya kalli Maama, sannan ya juya bayansa ya kalla Turaki.
Boɗejo ta doke shi,"Na ce ka karanto min abin da aka rubuta, ba wai ka bi su da idanu ba, saninsu ne baka yi ba ko me".
Ya sauke gwauron numfashi yana murza idonsa da kyau, sannan ya shiga karanto ma ta abin da ke jiki tiryan tiryan.
Boɗejo ta lailayo wata uwar ashar ta yarfa a sanda ya gama karantawa, ta fizgi takardar da ga hannunsa ta isa gaban Turaki ta wurga masa.
"Kai ka isa ma, ka isa ka saki Ilham, to bilahillazi samun kwanciyar hankalinka da na iyayenka shi ne ka mayar da auren nan".
Maama ta miƙe zata bar wajen, ta yi saurin dakatar da ita cikin hargowa,"Tsaya baƙar munafuka, gidan uwar wa za ki je da kika miƙe sim sim za ki tafi? Ai na san ba kowa yasa ya yi sakin nan ba sai ke algunguma, wallahi ban san Dikko annoba ya kawo cikin gidansa ba sai yanzu, Madina! Baƙin kaidin ki har ya kai ki raba aure? To kuwa tun da kika sa ya saki Ilham, sai kin sa ya saki ɗayar, ko kuma ke ma in sa a sake ki".
Hajiya Madina ta ji wani abu ya taso mata, ta yi saurin haɗiye shi da ambaton Allah.
Boɗejo ta miƙo mata takardar tana faɗin,"Yanda kika sa ya saketa haka za ki sa ya mayar da ita, ungo nan ba shi".
Maama na kallonta ta ce,"Na san ina da babban matsayin da zan iya sawa ya saketa, amma ban yi hakan ba tun farko, da na so da ba za azo wannan gaɓar ba ma. Ki daina alaƙanta sakin jikarki da ni, ba ni na saka shi ba, wadda take ganin ta isa da shi kaf duniya ita ce ta ba shi wannan umarnin. Kuma saboda gujewa fushin ubangijinsa da kuma taɓewar duniya yasa ya bi umarnin dole, don kowanne Ɗa na gari so ya ke ya rabu da mahaifiyarsa lafiya".
Boɗejo ta bi Mum da kallo kafin ta yi ƙarfin halin ce mata,"Ramla kika sa ya saki Ilham?".
Mum ta kawar da kanta gefe tana jan yatsunta ta ce,"Ki yi haƙuri, amma abin da nake ganin ya dace shi na sa shi ya aiwatar, hakan shi kaɗai zai sa hankalin kowa ya kwanta, da ga mu har ke, har kuma ita yarinyar".
Mayafin Boɗejo ya zame ya faɗi.
"Haka kike Ramla?".
Ta tambaya da tsananin mamakin Mum ɗin, wanda take tantamar da ƙyar idan ita ce tasa Turaki ya yi wannan sakin.
Mum ta fuskanceta tace,"Ba zance haka nake ba ko ba haka nake ba, amma idan hakan bai yi miki daɗi ba Allah ya huci zuciyarki. Na ga masalaha ake ta nema tuntuni, wanda kuma ta hakan ne kaɗai za'a samar da ita. Ki yi haƙuri da abin da zan faɗa, ina son farin cikin ɗana, ina so ya sami kwanciyar hankali da nutsuwar da ya rasa tun daga ranar da ya auri Ilham...".
"Dakata! Me kike so ki faɗa min? So kike ki ce an aura masa annoba da har kike faɗar ya rasa kwanciyar hankali. To cikin ku biyun kar wadda ta ƙara ambatar min kalmar tashin hankali anan, tashin hankali na can wurin shegiyar yarinyar da yaje ya aura a titi, kuma tun da kika sa ya saki Ilham, to ya zama dole kisa shi ya saki waccan yarinyar da ban yarda da asalinta ba, ba zan taɓa yarda a kawo mana gurɓatacce cikin zuria'armu ba, ku san da wannan, dan haka ba shi umarni ya saketa".
Mum ta rufe ido ta buɗe sannan tace,"Ina son rayuwar ɗana, kamar yanda na ke tsananin son farin cikinsa, hakan yasa ba zan taɓa raba shi da abin da yake farin cikinsa ba. Idan kika ce lallai sai ya saketa hakan zai zama barazana ga rayuwarsa, domin kuwa uwar gidansa ita ce rayuwarsa, rabuwa da ita dai-dai yake da taɓa rayuwarsa, saboda haka ni ba zan sa ya saketa ba, don Allah ki yi haƙuri a bar min yaro ya huta haka".
Boɗejo ta nemi kujera ta zauna tana salati, ta dafe kai tana girgiza shi,"Yau na ga abin da ban taɓa gani da ji ba a tarihin rayuwata, ni yau ake bijirewa umarni na, ni yau ake ja-inja da ni. Ramla da Madina me ku ka taka? Me Azima ta yi muku da ku ka tsani ƴarta haka? Zumuncin da ubangiji ya ce a yi shi ku ke so ku rushe yau? Babu komai bari Dikkon ya shigo".
Ta miƙa hannu ta ɗauko jakarta, da ta tangarar a ƙasa ta ɗauko wayarta, da ƙyar ta iya lalubo lambar Baffa, dan ta san duk wanda ta sa ya nemo mata a yanzu ba zai nemo ba.
Ringing biyu ya ɗaga, ta amsa sallamar tana cewa da shi,"Kana ina?".
"Ina gida Boɗejo".
"Kana cikin gidan naka ka barni da matanka su ke min rashin mutunci, suna gaggaya min maganganun da suka ga dama? Dikko kana so ka gama da duniya lafiya kuwa? To ka bar duk wani abu da kake ka zo ɓangaren Mandina yanzu dan babu lafiya".
Tana faɗar hakan ta kashe wayarta, idonta akan Turaki da har yanzu yake dafe da kansa, danasanin amincewa auren Ilham da ya yi kawai yake.
Mintunan da ba su wuce biyar ba, Baffa ya shiga parlon Hajiya Madina, tun daga baƙin ƙofa ya ke kallon Hajiya Madina da Kuma Hajiya Ramla, waɗanda ke tsaye sun kasa zama, ya ƙaraso ciki da sauri wajen mahaifiyarsa ya zauna a ƙasa yana cewa,"Ranki ya daɗe gani, lafiya dai?".
"Ina kuwa lafiya Dikko".
Ta faɗa tana ɗauke ido daga kansa, ta mayar kan su Hajiya Madina ta ce,"Waɗannan marasa mutuncin Matan naka, sun sa yaron nan ya saki Ilham, sun raba zumuncin da na ke so ya ɗorewa har tashin ƙiyama".
With shock Baffa ya ɗago yana kallon Maama, Boɗejo ta yi saurin cewa da shi,"A'a ai ba ita ce ta sa ya yi sakin ba, gata nan ita ta saka shi ya saki matarsa, saboda bata tsoron Allah bata gudun girgizar al'arshin ubangiji".
Ran Baffa a ɓace ya miƙe yana kallon Hajiya Ramla. "Kika sa ya saki Ilham? A bisa wanne dalili Ramla? Kina cikin hankalinki kuwa? Matsayinki na wa??".
Mum ta yi murmushin takaici ta ce,"Matsayina na wadda ta ɗauki cikinsa tsawon wata tara, na raini cikin da wuya ba ta daɗi ba, na kuma haife shi a cikin mawuyacin halin da kai kanka kake tunanin ba lallai na rayu ba. Sannan na shayar da shi tsawon shekaru biyu, na ci kashinsa na sha fitsarinsa. Ka tuna wacece ni ko kuma dai still kana buƙatar ƙarin bayani? Ni ce mahaifiyarsa, ni ce wannan uwar da ubangiji ya faɗeta sau uku kafin ya faɗi uba sau ɗaya tal. Ina da ikon sawa ina kuma da ikon hanawa, muddin ana so a gama da duniya lafiya. Banga dalilin da zai sa abi a takura rayuwar yarona ba, ya yi biyayyar amma hakan duk bai yi muku ba, ya kuke so ya yi da ransa? So kuke sai ya kamu da wani mugun ciwon a ƙanan shekarunsa? Tun da har ya yi biyayya ya auri zaɓinku, ku barsa ya auri zaɓinsa mana, amma son rai duk ya hanaku ku yi masa adalci."
Ta yi shiru kamar ba zata iya ƙara cewa komai ba. Amma sai ta ji Hajiya Madina ta zungurota, alamun ta ɗora kar ta ba kowa cikinsu damar tofa magana.
Hajiya Ramla ta rumtse ido sosai, kafin ta buɗe ta dubi Baffa, wanda ya saki baki yana kallonta da mamaki sosai. Ƙwayar idonsa kuma na hasko masa tarin ɓacin ran da yake cikin na ta idon, haɗe da damuwar da take neman agaji.
"Ni nasa ya saki amaryarsa, zai kuma tare da uwar gidansa kamar yanda zuciyarsa take so, kamar yanda hakan ne zai zama farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa, kamar yadda hakan ne zai zama maslahar da aka kasa samu".
Ta ƙara kallon Baffa da kyau tace,"Don Allah ka samawa yaron nan lafiya haka nan, iyakar biyayya ya yi maka, wadda tun da ka haife shi yake yi maka, har kawo yau bai taɓa bijirewa umarninka ba".
Baffa ya ɗaga muryarsa,"Shutup Ramla".
Ya juya yana kallon Turaki ya ce,"Ban goyi bayan ka rabu da kowacce a cikin su ba, amma ka mayar da matarka yanzu anan, idan ba haka ba na yi mugun saɓa maka".
Har yanzu kan Turaki na ƙasa bai ɗago ba, Baffa na ƙoƙarin yin wata magana Mum ta tari numfashinsa.
"Wallahi tallahi sai dai idan bana numfashi, amma ba zai mayar da ita a yanzu ba, yanda kake bin umarnin mahaifiyarka saboda ka gama da duniya lafiya, shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar saboda ya gama da duniya lafiya, yanda kake gudun fushin taka mahaifiyar haka shima, yanda kake so ka haɗu da ubangijinka lafiya shima haka yake so. Haba Alƙali, ka bar yaro ya huta mana..".
Ta mayar da idonta kan Turaki da tsananin tausayinsa ta ce,"Babana ta shi ka je".
Ya miƙe jiki ba ƙwari zai wuce, Baffa ya ce,"Daga yau na haramta maka shigowa gidana, kar in sake ganin ƙafarka a ƙofar gidana, idan kuma ba haka zaka sha mamakin abin da zan maka, fitaaa a gabana".
Ya ƙarasa maganar a tsawace, wadda har sai da ta tsorata kowa na wajen.
Turaki ya yi saurin ɗago kai yana dubansa, zai yi magana Mum ta tari numfashinsa da cewa,"Je ka Babana, Allah ya yi maka albarka".
Turaki ya fice yana jan ƙafafunsa da yake jin kamar ba zasu ɗauke shi ba.
Yana fita Hajiya Ramla ta dubi Boejo ta ce,"Ina ƙara baki haƙuri, Allah ya huci zuciyarki".
Sannan ta kalli Baffa tace da shi,"Ka yi haƙuri your highness".
Bai ko kalleta ba ya durƙusa gaban mahaifiyarsa, yana bata haƙuri tare da ban baki. Shi dama bai ƙi auren nan ba, ba don rigimarta ba wannan tashin hankalin duk ba za a yi shi ba, auren mata biyun ai ba haramun ba ne. Har zuciyarsa yana tausayawa Ɗan nasa, na yadda mahaifiyar tasa ta sako shi gaba. To amma bai da wani zaɓi face na bin umarninta da son faranta mata, don su rabu da ita lafiya.
Hajiya Madina ta ɗauki wayarta ta bar wajen ranta fess, sai murmushi take yi. Ai tun farkon auren ta sha alwashin sai Turaki ya rabu da Ilham, kuma Allah ya cika mata burinta.
Ta haye sama tana danna kiran lambar Ummi, tana yin picking bayan sun gaisa take shaida mata cewa,"Ummin Fullo in sha Allahu ranar litinin zamu kawo lefe".
Ummi ta amsa da,"Allah ya kaimu".
Daga haka suka yi sallama. Ɓangaren Turaki kuwa yana zuwa compound kiran wayar Daada ya shigo wayarsa, kamar ba zai yi picking ba sai kuma ya ɗaga, abin da ya tsammata shi ɗin ne ya faru, dan yana sakawa a dodon kunnensa ya ji tana da masifa tana cewa,"Ka sakar min jika ko kuwa? Ka san Allah kar ka bari in muku ɗanyen kai".
Muryarsa ta fito kamar ta mara lafiya da cewa,"Daada in tana kusa ki bani ita sai na faɗa mata".
A harzuƙe tace,"Ka faɗa mata me?".
Yace,"Shi abin da kika ce".
Ta ce,"Wai sakin?".
Ya ce,"Ehh".
Ta ce,"Haba yaro. Ai ni ba ƴar yau ba ce, saboda ka raina ni zaka min wannan furucin na wasa da hankali? To Saki a rubuce nake so ka yi shi, a cikin farar takarda ka yo min aikensa".
A hankali yace,"Shikenan Daada, ina kan hanya yanzu zuwa gida, idan na je zan rubuta".
Ta ce,"Ya dai fi, a sakar min jika, in ba haka ba kotu ta rabamu da mutum."
Ta kashe wayarta tana ta jaraba, kamar ta zane Fullo da ke kwance kan gado tana aikin kuka tun ɗazu. Tambayar duniya ta faɗi mai yake damunta taƙi magana. Sai haɗiyar zuciya kawai take yi. Daada takaici yasa ta watsar da lamarin nata.
Ilham na kwance a ɗaki, hadimarta na matsa mata ƙafa. Turaki ya shigo kamar an hankaɗo shi, ɗaya bayan ɗaya hadiman suka miƙe suka fita da azama.
Ya yi tsaye bakin ƙofa yana kallon Ilham, wacce ganinsa yasa ta ɗauke idonta gefe, tamkar bata ga shigowar tasa ba, shiru ya ratsa ɗakin na ƴan sakanni, sannan muryarsa na shaida ɓacin rai yace da ita,"Ki fito waje ki same ni".
Har ya yi bakin ƙofa zai fita, sai yaga kamar bata ji me yace ba. Hakan yasa ya dawo ya tsaya, ta ji shi sarai, bata yi niyyar fa ta saurare shi ba sam, amma mugun kallon da ya watso mata na alamar rashin son raini, yasa ba shiri ta ce,"Bani da lafiya fa."
Ya yi ƙyam yana ta kallonta from head to toe da son gano wani abu, sai dai hakan ya gagara, ba ya son wata sabuwar damuwar, dan haka bai ƙara cewa da ita komai ba, ya juya zai fita.
Da matuƙar mamaki, yaji tana cewa,"Na faɗa maka zan kuma ƙara nanata maka. Ba zan zauna da kishiya a cikin gida ɗaya ba, in har kuma ka aikata wannan kuskuren, to ina mai tabbatar maka da cewa ka yi bankwana da zaman lafiya da kwanciyar hankali kenan, sonka da na ke ba shi yake nufin ka ɗebo duk yayin da ka ga dama ka watsa min ba, Wallahi! Wallahi! Wallahi! Muddin wata ta tare a cikin gidan nan, sai dai ko ni, ko kuma ita".
Ta yi shiru tana fashewa da kuka, tana miƙewa zaune ta kifa kanta da gwiwa, sosai take kuka tana faɗin,"Me nayi maka a rayuwa ka yi min wannan tsanar. Kai ko tausayina ma baka ji, ina cikin tashin hankali na irin mawuyacin halin da mahaifiyata ke ciki, kai baka zauna ka rarrasheni ba ka kwantar min da hankali, sai ka zo min da batun ka auri wata tun kafin ni, wanna kalar rainin hankali ne wannan? To wallahi duk wacce ta shigo gidan nan sai na ga bayanta, ka rubuta ka ajiye".
Turaki ya yi murmushin takaici ya fice ya bar ɗakin, ba tare da yace da ita ƙala ba, bedroom ɗinsa ya wuce kai tsaye, yana shiga ya yi kiran lambar Bello.
Bello na ɗagawa yace da shi,"Kai MT you should have call me ka faɗa min bama baman da suke tashi a gida. Kawai kasa na ɗau ƙafa na tafi zance, Boss ya ce kar in ƙara zuwar masa gida, in ba haka ba sai ya ɓalla ni. Boɗejo kuwa kamar zata bankawa motata wuta, to ni dai yace in ƙara jadadda maka inuwarka ma kar ya sake gani. You thank God kana da gidanka har da mata, ni yanzu fisabilillah ta ya zan jure rashin ganin Zaytun har tsawon lokacin da zai sauko daga dokin fushinsa? MT please ban shawara, dan wallah jin zuciyata na ke kamar ana ɗinketa da zare da allura, AC ce fa a motata amma uban gumi kawai na ke haɗawa".
A lokacin da Turaki ke ɗaura towel a ƙugunsa yace,"Kana jina?".
Ya faɗa cike da takaicin rashin hankalin abokin nasa.
Bello yace,"Yo MT ko ban da kunnen jinka, ai ya zama dole ma na aro na saurareka, balle kuma akwai, maza ka faɗi duk wata kalar shawara da kake ganin zata zama mafita".
Turaki ya cika bakinsa da iska ya fesar, yana kama ƙugu sannan ya ce da Bello,"Plss kar ka min hauka, i want ask you something and be serious about it ka bani amsa, ta ya ake gane Mace na da ciki?".
Bello ya lailayo wata ashar yace,"Dan ubanka dama har haka ka yi babban aiki? Shege wooo, ka ce baka sonta?"
Ya yi shiru, kafin ya bushe da wata muguwar dariya ta ƙularwa, wanda har sai da Turaki ya dunƙule hannu yana janye wayar daga kunnensa.
Yana jin Bellon cikin dariya yana cewa,"To da kake tambayata ya ake gane mace na da ciki waka taɓa gani na yiwa? Ni ba ɗan iska ba MT karka ƙara min wannan tambayar, ka ɗauketa ku je asibiti ka tambayi waɗanda suka karanci abun. Ni dai ka ban shawarar kawai da na nema, ta ya zan ke ganin Zaytun?".
Turaki ya ja tsaki da cewa,"Useless".
Sannan ya kashe wayar. Ya ƙara lalubo lambar Dr Hasheer, sai da kiran ya yanke sannan Dr Hasheer ya kira shi, bayan sun gaisa yake ce masa.
"Dr kana gida?".
Dr Hasheer yace da shi,"Ehh lafiya dai?".
Turaki yace,"In ba damuwa don Allah ka leƙo gidana".
Dr Hasheer ya ce,"Ok babu damuwa, on my way right now".
Ya dire wayar yana shiga toilet ya sakarwa kansa shower, bai jima ba a ciki ya fito, ya zo ya tayar da sallar azahar don ba ya jin zai iya fita masallaci, duk da already ma an riga an idar. Idarwarsa kenan Dr Hasheer ya kira shi, yake shaida masa yana ƙofar gida, yace da shi alright ga shi nan fitowa.
Jallabiya ya zura ya sauka ya fita ya shigo da Dr Hasheer, suka ɗan zanta a parlo na ƴan mituna, sannan Dr Hasheer ya ba shi urine container.
Da ya shiga ɗakin Ilham tana toilet, har zai tsaya jiranta, sai kawai ya isa bakin toilet ɗin ya yi knocking.
Ta kashe shower ɗin tana tambayar waye, yace,"Ni ne, are you coming out now?".
Ta yi masa shiru bata yi magana ba har tsawon minti uku, bai ji ta amsa mishi ba, kuma bai ji ta kunna shower ɗin ba.
Ransa ya ɓaci, kawai ya murɗa handle ɗin ya faɗa ciki, ya ɗaure fuska ya haɗe girar sama da ƙasa, ya miƙa mata robar,"Yi fitsari ki bani".
"Ban gane ba".
Ta faɗa tana kallonsa nata ran itama a ɓace, tana ɗaure tata fuskar. Da ya yi mata jan ido ya sakar mata tsawa, bata san lokacin da ta miƙa hannu ta karɓa roban ba, zuciyarta kamar zata fito waje dan baƙin ciki, ta durƙusa ta yi fitsarin dole ta miƙa masa.
Ya karɓa yana ƙare mata kallo tsab a naked ɗin da take, don gano wasu alamomi da Dr Hasheer ya faɗa masa, ya watsa mata banzan kallo da zai fice, irin kallon da ke tabbatarwa da mutum ba zai taɓa samun zuciyarka ba, ko ƙofar bai rufe mata ba, ya bar ɗakin kamar iskar guguwa.
Dr Hasheer ya miƙe ganin ya fito, Turaki ya bashi container ɗin da yake riƙe da ita kamar ya riƙe kashi, yace,"please Dr kar ya wuce yau".
Dr. Hasheer yace, "Just give me one hour, shima saboda ba hospital zan wuce direct ba. But once we'hve completed the test, I'll call you and let you know the result."
Turaki ya basa hannu su kai shaking yana faɗin,"Thank you so much for your time".
Su ka yi sallama ya wuce. Shi kuma ya haura upstairs ɗakinsa. Yana shiga ya buɗe locker ya ɗauko jotter da biro, ya hau kan gado ya zauna.
Ba ya son tashin hankali, ba ya son abin da zai zama silar rugujewar farin ciki a tsakanin iyayensa, dan haka dole ya yi abin da yake ganin ya dace, kowa da kowa ma ya huta.
Amma a lokacin da ya ɗora biron akan takardar, sai ya ji ya kasa rubuta abin da yake ganin zai zama mafita ta ƙarshe, ya ji zuciyarsa ta yi wani irin matsewa, ya jinginar da kansa jikin gadon, yana tunani tsawon wucewar daƙiƙu masu yawa.
Daga bisani ya ɗauko wayarsa ya kira wayar Mum, ko da ta ɗaga ta tambaye shi lafiya, sai ya ji ya kasa faɗa mata hukuncin da yake shirin yankewa, hakan yasa ya ce mata ya kira ta ne kawai.
Tace da shi,"Babana karka sake ka sawa kanka damuwa ka ji ko, ba komai ya sa Baffa faɗa maka haka ba illa ɓacin rai, ka yi haƙuri ka ba shi space zuwa wani lokaci. Allah ya yi maka albarka".
Bayan sun yi sallama ya kira lambar Hajiya Madina, tana ɗagawa ko amsa sallamar tasa bata yi ba, balle ta ji abinda zai ce mata tace da shi,"Ya aka yi?".
Ya kira sunanta kamar yaron da ke buƙatar shan nono.
Ta ce,"Ka ga Mai babban suna, in ka ce zaka biyewa wannan uban na ka da shima tsufa ya fara rikitar da shi, to zaka dawwamar da kanka a cikin damuwa ne. Ka rabu da shi, ka ba shi space zuwa ranar da zai nemeka da kansa, kai ɗin ai na daban ne, mahaifinka ba ya iya fushi da kai mai tsawo. Na ji fitinanniyar Kakarka na cewa za su zo su ɗauki kayarsu yanzu, to da zarar sun zo sun ɗauketa ka rufe gidanka ka huta abinka, ko office karka dinƙa zuwa har matarka ta tare, ka ji ni ko?".
Ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya sauke numfashi ya ce,"Tom Maama".
Ta ce,"Yauwa Allah ya yi maka albarka, zamu kai lefe monday in Allah ya kaimu. Za su fara biki ranar wednesday, but Ummi bata faɗa min ranar da za su gama ba, sun ce sai Daada ta dawo ita zata yanke wannan".
Magana take ta yi, ta hana shi faɗar abin da yake so ya ce, har ta gama sannan ta yi masa sallama.
Ya kasa sauke wayar daga kunnensa, sai sulalewa ta yi daga hannunsa.
Ya maida hannunsa kan takardar da har yanzu ke hannunsa, ya shiga rubutu, yana jin zuciyarsa na bala'in matsewa.
Rubutun yake yi kamar ɗan koyo, muryar Fullo na amsakuwwa a cikin kansa, kamar yanda hotonta ke haska masa a cikin idanuwansa, tun daga ranar da ya fara ganinta, har zuwa ranar ƙarshe na rabon da ya sanyata a idonsa.
Zai yi kewarta! Tabbas zai yi kewarta sosai.
Ya rumtse idonsa gam bayan ya kammala rubutun, kuma ba tare da ya iya buɗe idonsa ba, ya nannaɗe takarda ya ɗaga ƙasan pillow ya saka. Zai aika kamar yadda Daada ta buƙata, fatansa a samu daidaito a tsakani, a samu wanzuwar zaman lafiya a Familynsa.
Ya ja wata doguwar a jiyar zuciya, yana kwanciya ko zai sami sassaucin abin da yake ji a ƙasan ransa.
Amma zuciyarsa zafi take masa sosai, Fullo kawai yake buƙata a tare da shi, ita ce maganin ciwon da yake ji. Amma a haka yake jin wani ɓari na zuciyarsa na faɗa masa,"Kul! Ta zama haramiyarka a yanzu."
Babu shiru ya rumtse ido gam, kamar ba ya so ya ƙara ganin komai a duniya. Ya ɗora hannu ya toshe dukka kunnuwa biyu, kamar ba ya so ya ake jin sautin komai a duniya.
So! Dama haka Son ya ke? Yaushe ya fara yi mata irin wannan son da zai iya hallaka shi? Nooooo!
Ya yi zancen zucin, yana cusa fuskarsa a cikin pillow.