Free chapter · Read without an account

Unexpected encounter

by Rabi'ah Shariff · Soyayya Ta

Chapter One 
unexpected encounter 
by 
Rabi'ah Muhammad Shariff Aka Ramsha Tales.

Latif Abdurrahman!

Sunan da idan ya shiga kunnen mutane da yawa a duniyar kasuwanci, ba abin da zai fara zuwa musu a rai face kuɗi, iko da nasara.

Shi ne mamallakin L.A Imperial Group of Companies, wani katafaren kamfani da ya shahara wajen gina manyan gine-gine, karɓar manyan kwangiloli da kuma hulɗa da manyan kamfanoni na cikin gida da ƙasashen waje.

Daga cikin kwangilolin da kamfaninsa ya samu akwai manyan ayyukan gine-gine a ƙasar Amurka. Duk da cewa yana da wasu manyan 'yan kasuwa da yake hulɗa da su, Latif ya kasance mutum ne da yake son komai ya tafi yadda ya tsara.

A wajen kuɗi kuwa, ba ƙaramin attajiri ba ne. Yana da manyan motoci na alfarma, gidaje masu kayatarwa da kuma kadarori da suka sa sunansa ya zama abin girmamawa a duniyar kasuwanci.

Amma duk da wannan nasarar da ya samu, akwai wani abu da Latif ya kasa fahimta.

Soyayya!

A ganinsa, kuɗi su ne ginshiƙin rayuwa. Da su ake samun iko, mutunci da jin daɗi. Don haka, bai ganin dalilin da zai sa ya ɓata lokacinsa wajen neman abin da yake ganin ba shi da amfani.

Girman kansa kuwa, sai wanda ya san shi.

Latif ba ya son a yi masa gardama, ba ya yarda da uzurin da bai gamsu da shi ba, kuma ba ya yawan nuna tausayinsa ga kowa. Idan mutum ya yi kuskure a wajen aikinsa, ko da kuwa ƙaramin kuskure ne, zai iya rasa aikinsa ba tare da Latif ya damu da abin da hakan zai haifar masa ba.

Fuskarsa kuwa, da wuya ka ga murmushi a kanta. Kullum cikin ɗaure fuska yake, kamar wanda duniya ta yi masa laifi.

Amma duk da wannan halin nasa, akwai wani abu da ya sa mata da dama suke sha'awar sa.

Kyawunsa!

Latif dogo ne, mai faɗin ƙirji da kyakkyawan sura. Gashinsa baƙi ne, mai yawa, kuma kullum ana gyara shi yadda zai zauna cikin tsari. Idan ya sa kayan alfarma, musamman baƙar kwat ɗinsa, yana ƙara bayyana irin kyawun da Allah ya yi masa.

Kuɗinsa kuwa, ba ƙaramin ƙarin jan hankali suke yi ba.

Matan da suke aiki a kamfaninsa da dama suna mafarkin samun kulawarsa. Wasu suna neman hanyar da za su kusance shi, yayin da wasu suke jiran ranar da zai nuna wa ɗayansu wata alamar soyayya.

Amma abin takaici, Latif bai taɓa nuna cewa akwai macen da ta isa ta ɗauke masa hankali ba.

Ko da yake mata da dama suna sha'awar sa, su kansu suna tsoronsa. Idan ya shigo ofis, kowa sai ya gyara zamansa. Wasu ma sai dai su saci kallonsa daga nesa, domin babu wanda yake son ya kama idonsa ba tare da wani dalili ba.

Latif ba ya wasa da aikinsa.

Kuma ba ya wasa da kuskure.

Wannan shi ne mutumin da ya kasance yana ganin kuɗi a matsayin komai a rayuwa.

Amma bai san cewa wata rana za a kawo shi gaban wata jarabawa da kuɗinsa ba za su iya warware masa komai ba.

Wata safiya da sassafe, a cikin wani katafaren gida mai kayatarwa, Latif ya farka da niyyar shirya kansa domin wata muhimmiyar ganawa da wasu manyan 'yan kasuwa daga ƙasar Amurka.

Waɗannan mutanen ne suka ba kamfaninsa kwangilar gina wani katafaren banki. Latif ya riga ya kammala tsara aikin, kuma abin da ya rage shi ne tattaunawar ƙarshe da kuma amincewa da sharuddan kwangilar.

Wannan ganawar tana da matuƙar muhimmanci a gare shi.

Don haka, ba ya son wani abu ya jawo masa jinkiri.

Ya miƙe daga kan gadonsa ya nufi babban banɗakinsa.

Banɗakin kuwa, sai wanda ya gani!

An tsara shi cikin salo na zamani, da manyan tayal masu sheƙi a ƙasa da bango. A gefe guda akwai babban madubin bango da kuma wurin ajiye kayan gyaran jiki. A tsakiyar banɗakin kuwa akwai wani katafaren wurin wanka mai gilashi, inda aka tsara kayan wankan cikin tsari mai kayatarwa.

A ɗaya gefen akwai kabad ɗin da aka tanada domin kayan wanka da tawuloli masu laushi. Akwai kuma wani sashe na musamman da aka ware domin bayan gida, wanda aka raba shi da sauran wurin ta hanyar ƙofar gilashi mai duhu.

Hasken fitilun da aka saka a saman madubin ya sa dukkan wurin ya ƙara haskakawa.

Latif ya shiga wurin wankan, ya yi wanka, sannan ya fito yana ɗaure da babban tawul a ƙugunsa.

Ya tsaya a gaban madubi yana gyara gashinsa.

Ya shafa masa abin gyara, sannan ya tsefe shi har ya kwanta cikin tsari. Ya ɗan karkatar da kansa yana kallon fuskarsa a madubin, kafin ya juya zuwa inda kayansa suke.

Bayan ɗan lokaci, ya fito cikin baƙar kwat ɗinsa mai tsada, baƙar riga da kuma necktie da ya dace da kayan. Ya zauna a gefen gadonsa, ya saka takalmansa na alfarma, sannan ya fesa turarensa mai daɗin ƙamshi.

Ya ɗauki madubi ƙarami ya sake kallon kansa, yana tabbatar da cewa komai yana cikin tsari.

Da ya gamsu, sai ya miƙa hannu ya ɗauki file ɗin da yake ɗauke da takardun da suka shafi kwangilar bankin.

Ya duba takardun a taƙaice, sannan ya rufe file ɗin.

Everything is in order, ya faɗa a hankali.

Ya ɗauki wayarsa da agogonsa, sannan ya nufi ƙofar ɗakin.

Bayan ya fito, ya fara saukowa daga matakalar benen da ke kaiwa zuwa babban falon gidan.

Tafiyarsa cike take da izza da kwarin gwiwa. Yana tafiya ne kamar wanda ya riga ya san cewa babu wani abu da zai iya hana shi cimma burinsa.

Da ya isa falon, sai ya hangi mahaifiyarsa zaune a kan kujera mai laushi.

Hajiya Aisha tana shan kayan marmari, kamar yadda ta saba yi kowace safiya kafin ta ci wani abinci.

Tana son kula da lafiyarta, kuma ba ta son ta fara cin abinci ba tare da ta sha kayan marmarinta ba.

Da Latif ya ƙaraso, sai ya tsaya a gabanta yace Good morning, Mummy. Ina kwana?
Ya faɗa cikin ladabi, yana ɗan sunkuyar da kansa.

Domin duk da halinsa na girman kai a wajen mutane, yana da wani irin girmamawa ta musamman ga mahaifiyarsa.

Hajiya Aisha ta ɗago kai tana kallonsa sannan tace Lafiya ƙalau, Latif. Amma ina za ka da wannan shirin haka tun da sassafe?

Latif ya gyara tsayuwarsa yace Eh, Mummy. Yau ne muke da ganawar da na ba ki labari. Waɗancan mutanen daga Amurka za su zo domin mu kammala tattaunawar kwangilar ginin bankin.

Ya ɗan ɗaga fayil ɗin da ke hannunsa. ya ce Na shirya komai. Ina so kawai in isa wurin da wuri kafin su ƙaraso.
Hajiya Aisha ta yi murmushi. tace nasha Allah, Allah ya ba ka sa'a, ɗana. Allah ya sa ka yi nasara.

latif yayi murmushi yace Amin, Mummy.
Ta ajiye kofin da ke hannunta, sannan ta ƙara da cewa Amma ka tsaya ka karya mana. Bai kamata ka fita haka ba tare da ka ci komai ba.”

Da jin haka, Latif ya ɗan yi saurin duban agogonsa. Ya san halin mahaifiyarsa, Idan ta ce ya tsaya ya ci abinci, to lallai za ta iya ɗaukar lokaci kafin ta sake shi. latif yayi saurin cewa A'a, Mummy, Yanzu na makara, Waɗannan mutanen suna da muhimmanci sosai a gare ni, kuma ba na son su jira.

Hajiya Aisha ta ɗan murtuke fuska, sannan tace To, yanzu kenan aikinka ya fi muhimmanci fiye da lafiyarka?

Latif ya yi murmushi kaɗan ya kalli mummy yace Mummy, kin san halin da nake ciki, Zan je in yi aikina, daga baya kuma zan nemi abin da zan ci, Na yi miki alkawari.”

Ta girgiza kai, amma murmushin bai bar fuskarta ba tace To, Allah ya kiyaye hanya Ka dai tabbatar ka ci abinci idan ka samu dama.”

Latif ya sunkuya ya sumbaci goshinta sai yace To, Mummy, Zan je in duba Layal kafin in fita.”

Ya juya da sauri ya nufi ɗakin ƙanwarsa yana tafi latif yayi murmushi yace mummy kenan har yanzu kallon yaro take min.

Layal Abdurrahman, ƙaramar kanwar Latif, ta kasance yarinya mai kyakkyawar zuciya da hankali. Ba ta da girman kan da ɗan'uwanta yake da shi, kuma tana da sauƙin mu'amala da mutane.
Duk da cewa ita ma ta taso cikin wadata, ba ta ɗaukar mutane da darajar kuɗinsu.
A wajen Layal, mutum shi ne mutum, komai matsayinsa.
Da Latif ya shiga ɗakinta, sai ya same ta tana shirya wasu kayanta.

Da ta gan shi, sai ta yi saurin zuwa gare shi ta rungume shi tace Good morning, Yaya

Latif ya amsa rungumar, yana murmushi yace nata Good morning, my baby, kin tashi lafiya?

Lafiya ƙalau, Amma Yaya, ina za ka haka da sassafe? Kuma me ya sa ba za ka tsaya ka yi breakfast ba?

Latif ya yi murmushi, sannan ya riƙe fuskarta a hankali yace wato kema kin zama kamar Mummy yanzu, Kowa sai ya damu da abin da zan ci!”

Layal ta yi dariya, tace To, ai dole mu damu da kai, Ba za ka tafi aiki kullum kana gudu ba tare da ka ci abinci ba.

Latif ya girgiza kai, latif ya e cikin sanyin murya Today is a very important day, Layal. I have a meeting, and I don't want to miss it.
Ya sumbaci goshinta, sannan ya sake ta.

latif ya dauki files din sa yace Ina sauri, Sai na dawo, okay?

Layal ta ɗaga kai tana murmushi.

Okay, Yaya. Allah ya taimaka.

latif yace Amin, Ya juya ya fita daga ɗakin, sannan ya nufi inda motarsa take.

Bayan ya shiga motar, ya kunna injin ɗin, ya ɗora fayil ɗin a kujerar gefensa, sannan ya fice daga gidan.
Ba ya da wani tunani a zuciyarsa sai yadda zai tabbatar da cewa ganawar ta yi nasara.
Bai san cewa wannan safiyar da yake ganin za ta zama wata rana ta musamman a harkar kasuwancinsa ba, za ta zama safiyar da rayuwarsa za ta fara sauyawa ba.

A wani ɓangaren kuwa, Hibba tana shirin fita daga gida tare da goggon ta Aunty, wadda ta kasance tana kula da ita.
Aunty ɗin tana buƙatar zuwa asibitin gwamnati domin duba lafiyarta. Saboda sun san irin cunkoson da ake samu a asibitin, suka yanke shawarar fita da wuri domin su isa kafin mutane su yi yawa. Hubba sun fito suka karasa bakin titi.
Da suka isa bakin titi, sai suka tsaya domin samun abun hawa, sabida yanayin safiyar yasa babu abun hawa sosai.
Hibba suna tsaye suna jiran mota, Ba ta san cewa a cikin 'yan mintuna masu zuwa, rayuwarta za ta shiga wani yanayi da ba ta taɓa zato ba.

A gefe guda kuwa, Latif yana tuƙi cikin sauri.

Agogonsa yana nuna cewa lokaci yana tafiya, kuma ba ya son ya makara zuwa ganawar da yake da ita. Yana mai da hankali kan hanya, amma cikin gaggawar da yake ciki, bai lura da Aunty da Hibba da suke bakin titi ba.

Nan take!

KASH!

Motarsa ta bugi Aunty.

Ta faɗi ƙasa ba tare da ta sake cewa komai ba.

“AUNTY!”

Hibba ta yi ihu da ƙarfi, tana rugawa zuwa gare ta. Aunty! Aunty, ki tashi! Don Allah ki tashi!
Ta durƙusa a gefenta, tana girgiza ta a hankali, amma Aunty ba ta amsawa.
Hankalin Hibba ya tashi matuƙa. Hawaye suka fara zuba daga idanunta yayin da take ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru.

Latif kuwa, duk da saurin da yake yi, ya kasa ci gaba da tafiya. Ya taka birki, ya yi parking, sannan ya fito daga motar. Da ya ƙaraso, sai ya ga matar a kwance, sai Ya kalli agogonsa, sannan ya sake kallon matar.
A fili yake cewa Subhanallahi, amma ba wai saboda halin da matar take ciki kaɗai ba. Ganawar da yake da ita ce a gabansa, kuma bai san yadda zai warware lamarin ba tare da ya makara ba.
Ya koma motarsa, ya buɗe inda yake ajiye kuɗinsa, sannan ya ɗauko wasu takardun kuɗi. Da ya dawo, ya tsaya a gaban Hibba, ya ce mata Excuse me.
Hibba ba ta ɗago kai ba, Tana nan tana ƙoƙarin tayar da Aunty, hawaye na zuba daga idanunta.
Latif ya sake magana, Ke, saurara, Na san abin da ya faru, amma ina da wani muhimmin al'amari da ya kamata in je. Ga waɗannan kuɗin, ki ɗauke ta zuwa asibiti. Ya miƙa mata kuɗin.

Hibba ta ɗago kai a hankali, Da farko, ta kalli Latif, sannan ta kalli kuɗin da yake miƙa mata, Ba ta iya gaskata abin da kunnuwanta suka ji ba.
Mutumin da ya bugi Aunty ɗinta ne yake tsaye a gabanta, kuma maimakon ya taimaka mata ko ya nuna damuwa, sai ya miƙa mata kuɗi kamar yana biyan bashin wani abu da ya saya.
Latif ya lura cewa ba ta karɓi kuɗin ba, Sai ya sake cewa, Me ya faru? Kuɗin ba za su isa ba ne? Idan ba su isa ba, zan ƙara, Amma yanzu ina cikin gaggawa. Ya juya zai koma motarsa, yana shirin ɗauko wasu kuɗin.

Amma kafin ya kai ga motar, sai Hibba ta miƙe tsaye cikin fushi. Ta tsaya a gabansa, tana kallonsa kai tsaye, Hawaye suna zuba daga idanunta, amma a wannan karon ba tsoro ne kawai a cikinsu ba, Akwai fushi, Akwai ɓacin rai, Kuma akwai wata ƙiyayya da ta fara tasowa a zuciyarta, Ta kalli kuɗin da yake hannunsa, sannan ta mayar da dubanta gare shi, Hubba tace cikin fushi Ka tsaya.

Latif ya tsaya cak. A hankali ya juya ya kalle ta, fuskarsa cike da mamaki da ɓacin rai. Domin a duk rayuwarsa, ba kasafai wani yake tsayar da shi haka ba.
Hibba ta nuna masa Aunty da take kwance a ƙasa, tace wai saboda ka bugi mutum, abin da za ka yi kawai shi ne ka miƙa kuɗi ka tafi?
Ta share hawayenta da bayan hannunta, hibba tace Mutum ce fa a kasa, Ba kaya ka bugo ka lalata ba, Mutum ce mai rai, mai iyali, mai daraja.

Latif ya ɗan zaro ido.
Ba don maganganunta sun girgiza shi ba, sai don bai saba da irin wannan magana daga bakin wani da bai sani ba.
Ya ɗan matso kusa da ita. latif ya fada cikin izza Listen, young lady, Na ce ina da  aiki me muhimmanci ne, Na ba ki kuɗi domin ki taimaka mata, kuma na ce zan ƙara idan ba su isa ba. Me kuma kike so in yi?”

Hibba ta kalle shi cikin mamakin sa
Ta nuna Aunty ta fada Wannan matar da kake gani a ƙasa tana buƙatar taimako. Ba wai kawai kuɗi za ka jefa mata ba ka wuce ba, ka mata yayi ka dauke ra ka sata a mota mu kaita asibiti.

Latif ya bata rai sannan yace kinga ni bani da lokaci idan zaki dauki kudin nan ki dauka idan kuma ba zaki dauka ba to fine wannan damuwar kice.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol