Free chapter · Read without an account
THE ECHO OF SILENCE
*ƘADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER TWO (2)*
*THE ECHO OF SILENCE*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Wayar tana manne a kunnana, na lumshe idanuwana a hankali yayin da daddadan muryar Ahmad ke ratsa kunnuwana, muryarsa tana da wani irin salo da kullum yake sa zuciyata yin laushi, murya ce mai sanyaya zuciya, wadda ko da ina cikin damuwa, jin ta kaɗai yana iya sauya yanayin fuskata, “Angelic…” Ya kira sunana cikin wannan murya tasa mai sanyi, na kasa hana murmushin da ya bayyana a fuskata, na sauke idanuwana ƙasa, ina wasa da gefen mayafina, duk da cewa babu wanda yake kallona, “Yes, Heartbeat?” Na amsa cikin wata murya mai ɗauke da shauƙi, “Yanzu haka na baro cikin garin Kano, ina kan hanyar Katsina, na kasa jurewa ne, shi ya sa na kira ki kafin hanyar ta ɗauke muryar,” ya ɗan yi dariya a hankali, “Tsakaninki da Allah, kin shirya kuwa? Ko kuwa har yanzu kina nan kina faɗa da Khalil?” Na turo baki gaba, ina girgiza kai duk da na san ba ya ganina, “Wane irin faɗa kuma, Heartbeat?” Na yi ƙaramar dariya, sannan na gyara zamana a kan gadon, “Shiri na fa ya daɗe da tsaf, kai nake ta jira tun dazu,” na ɗan yi shiru, murmushin da ke fuskata ya lafa kaɗan yayin da na tuna cewa yana kan hanya, sai muryata ta sauya zuwa ta damuwa, “Amma don Allah, ka tuka motar a hankali, ka san hanyar nan akwai ababen hawa da yawa yanzu,” a ɗaya ɓangaren, sai na ji dariyarsa mai sanyaya zuciya, “Karki damu, my love, I am driving very carefully,” na ji zuciyata ta yi wani irin tsalle, na lumshe idanuwana, ina ƙoƙarin danne murmushin da ya ƙara bazuwa a fuskata, “Tunaninki kaɗai ma da nake yi ya isa ya sa ni cikin natsuwa,” na kasa magana na ƴan seconds, wannan ba sabon abu ba ne a gare ni, amma duk lokacin da Ahmad ya furta irin waɗannan kalaman, sai na ji kamar zuciyata tana sake koyon yadda ake soyayya, “Heartbeat…” Na kira shi cikin wata murya mai ɗauke da kunya, “Hmm, Angelic?” “Ka daina faɗin irin waɗannan kalaman,” “Why?” Na turo baki, ina kallon bango, “Because…” Na tsaya cak, na rasa abin da zan ce masa, ya yi dariya a hankali, “Because what, my love?” Na rufe idanuwana, “Just leave me alone!” Na faɗa cikin raha, abin da ya sa ya ƙara dariya, “Okay, okay, I won’t disturb you again,” sai ya yi ɗan shiru kafin ya ƙara da cewa, “Zan riƙa kiranki idan na kusa shiga Katsina, okay?” “Okay…” Muryata ta fito a hankali, bayan mun yi sallama, na sauke wayar daga kunnana, na tsaya ina kallon screen ɗin na ɗan lokaci, murmushi kawai nake yi, murmushin da ko wani mutum ya gan ni a lokacin, zai iya tunanin na haukace, na matse wayar a ƙirjina, na sauke numfashi mai cike da shauƙi, sannan na jingina da filo, Ahmad yana zuwa, na maimaita maganar a cikin zuciyata, kuma ban san me ya sa kawai wannan tunanin yake sa zuciyata rawa ba, na rufe idanuwana, ina tunanin yadda zan tarbe shi idan ya iso, wane irin murmushi zan yi masa? Me zan fara ce masa? Ko kuwa zan iya kallon fuskarsa ba tare da na ji kunya ba? Na buɗe idanuwana da sauri, na girgiza kai, “Ya Allah, look at me!” Na faɗa ni kaɗai, ina dariya, “Wai saboda saurayi zan zauna ina murmushi ni kaɗai kamar wata mahaukaciya?” Amma duk da maganar da na yi, murmushin bai bar fuskata ba, saboda a gare ni, Ahmad ba saurayi ba ne kawai, shi ne mutumin da zuciyata ta zaɓa, shi ne wanda nake ganin zai zama abokin rayuwata, kuma a wannan lokacin, babu abin da nake fata kamar ganin sa a gabana, kusan awa biyu da rabi bayan haka… sautin engine wata mota ya fara ratsawa cikin tsakar gidanmu, na ɗago kai daga inda nake zaune, idanuna suka karkata zuwa ga taga, na saurara na ɗan lokaci, sautin ya ƙara bayyana, nan take zuciyata ta fara bugawa da sauri, na miƙe daga kan gadon, “Ahmad…” Sunansa ya kubuce daga bakina cikin farin ciki, na nufi ƙofar ɗakina da sauri, ina gyara zaman doguwar rigar abaya ta a jikina, hannuna ya tafi kan mayafina, na sake gyara shi kafin na sauko ƙasa, ina saukowa, na ji muryoyin wasu daga cikin mutanen gidan suna fitowa daga falon, amma hankalina yana wani wuri ne, he’s here, Ahmad is finally here! Da na isa harabar gidan, motar ta riga ta tsaya, na ɗan rage gudu saboda Daddy yana nan, sai na hango Ahmad, ya fito daga motar cikin nutsuwa, sannan ya durƙusa har ƙasa a gaban Daddy yana gaishe shi cikin ladabi da girmamawa, a jikinsa akwai wata haɗaɗɗiyar shadda sky blue, wadda ta ƙara fito da kyawun fuskarsa da kamalarsa, na tsaya daga nesa ina kallonsa, zuciyata ta cika da farin ciki, shi ne, mutumin da na shafe kwanaki ina jiran ganinsa, na kasa kawar da idanuna daga kansa, har sai da Daddy ya ɗago kai ya kalle ni, sai murmushi ya bayyana a fuskarsa, kamar ya riga ya fahimci abin da ke faruwa a zuciyata, “Ah, Inteesar,” ya kira ni cikin raha, “Ga baƙon naki ya iso,” na sunkuyar da kaina ƙasa saboda kunya, ina ƙoƙarin ɓoye murmushin da ya ƙi barin fuskata, “Daddy…” Na kira shi a hankali, ina jin yadda kunya ke kokarin yadda ni a wajen, Daddy ya yi dariya kaɗan, sannan ya mayar da hankalinsa ga Ahmad, “Ahmad, kun zo lafiya? Fatan ba ku sha wahalar hanya ba?” Ahmad ya ɗago kansa, ya yi murmushi cikin ladabi, “Lafiya lau, Daddy, hanya babu matsala, sai dai ɗan cunkoson ababen hawa da ba a rasa ba,” ya sake sunkuyar da kansa cikin girmamawa, Daddy ya gyada kai, “Alhamdulillah,” bayan ƴan mintuna na gaisuwa, Daddy ya tashi a hankali, “Ku zauna ku yi hira, ni zan shiga ciki,” na ji zuciyata ta yi wani irin tsalle, finally! Amma na yi saurin danne farin cikin da ke neman bayyana a fuskata, Ahmad ya kalle ni, sai na kau da kai cikin kunya, Daddy ya yi tafiyarsa, ya bar mu a wajen, shiru ya ɗan mamaye wurin, na tsaya ina wasa da yatsuna, ban san ko ya kamata in zauna ko in yi magana ba, sai Ahmad ya juyo gaba ɗaya ya kalle ni, idanunsa suka tsaya a fuskata na tsawon wasu seconds, ya yi murmushi, murmushin da ya sa ni jin kamar ina son ɓoye fuskata, “You look breathtakingly beautiful, Inteesar,” na lumshe idanuwana cikin kunya, ya ɗan karkatar da kansa, yana ci gaba da kallona, “Kullum ƙara kyau kike yi,” na ɗaga ido na kalle shi, “Da gaske?” Ya gyada kai ba tare da jinkiri ba, “Da gaske,” na yi ƙaramar dariya, na kau da kai gefe, “Allah ya sa ba dai kana faɗin haka ne kawai don ka faranta min rai ba,” ya ɗan matsa kusa da ni, murmushi yana nan a fuskarsa, “Angelic, do I look like someone who would lie about something like that?” Na kalle shi da gefen ido, “Sometimes,” ya buɗe baki cikin mamaki, “Sometimes?!” Na fashe da dariya, ya girgiza kai, yana murmushi, “Okay, fine, I will remember that,” na ɗan yi shiru, sannan na nuna cikin gidan da hannuna, “Toh, mu shiga ciki kar mu tsaya a nan,” bai yi musu ba, na shige gaba, ya biyo ni a baya har muka isa falon ƙasa, bayan mun zauna a kan kujerun falon, sai na ɗan gyara zaman mayafina, ina kallonsa a hankali, shi kuma ya jingina da bayan kujera, yana kallona da wani irin natsuwa, ban san abin da ya sa nake jin kunya haka ba, ai ba yau ne karo na farko da muka haɗu ba, amma duk lokacin da na haɗu da shi bayan wani lokaci, sai na ji kamar sabuwar soyayya ce take tasowa a zuciyata, na ɗan kau da kai, ina ƙoƙarin mayar da hankalina ga wani abu daban, sai ya ɗan sunkuya, ya ɗauko wani babban box da aka naɗe shi da takarda mai sheƙi daga kusa da kujerarsa, ya turo min shi, “Ga wannan,” na kalle shi, sannan na kalli akwatin, “Kyauta kuma, Heartbeat?” Na karɓa da mamaki, ina juya akwatin a hannuna, “Me ke cikin wannan katon akwatin haka?” Ya jingina bayansa da kujerar, ya naɗe hannayensa yana kallona cikin nutsuwa, “Buɗe ki gani mana, Angelic,” ya ɗan yi murmushi, “Duk abin da ke ciki naki ne, na zaɓe su ne musamman saboda ke,” na buɗe baki cikin mamaki, “Duk abin da ke ciki nawa?” Ya gyada kai, “Yes, my love, yours,” na kasa ɓoye farin cikin da ya mamaye fuskata, cikin sauri na fara cire takardar da ke jikin box ɗin, amma sai na lura hannuwana suna ɗan rawa saboda farin ciki, Ahmad ya kalle ni, ya yi murmushi, “Easy, Angelic, it’s not going anywhere,” na ɗago na kalle shi, “Ka yi shiru mana! Bari na gani,” ya fashe da dariya, na ci gaba da buɗe akwatin, da na ɗaga murfinsa… na yi shiru, idanuwana suka buɗe sosai, “Subhanallah!” Na faɗa a hankali, a ciki akwai wani daddadan super wax mai tsada, mai kalar sky blue, wanda ya yi daidai da shaddar da ke jikinsa, a gefensa akwai kwalaben turare masu ƙamshi mai daɗi, sai wasu sarƙoƙin gwal masu kyalli, na ɗauki gefen leshin a hankali, ina shafa kyawun kayan da hannuna, sai na ɗago ido na kalle shi cikin mamaki, “Wannan ai ya yi yawa, Heartbeat!” Na girgiza kai ina murmushi, “Gaskiya ka kashe kuɗi sosai, why would you buy all these things for me?” Ya kalle ni da wani irin murmushi mai cike da taushi, “Babu abin da ya yi yawa ga Angelic dina,” muryarsa ta yi ƙasa, “Burina kawai shi ne na ga kina farin ciki a kowane lokaci,” na ji zuciyata ta yi laushi, na sake kallon kayan, sannan na kalle shi, “Amma Heartbeat, wannan leshin fa…” Na ɗan daga shi sama, “Ya yi kyau sosai!” Ya yi murmushi, yana kallon yadda nake ta duba kayan cikin farin ciki, sai ya nuna leshin da yatsansa, “Kuma ina so ki yi amfani da wannan ranar da zan dawo da magabatana wajen Daddy,” kalaman nasa suka sa na yi shiru, hannuna ya tsaya a kan leshin, na ɗago kai a hankali, na kalle shi, “Da gaske?” Ya gyada kai, yana kallona kai tsaye, “Of course, Angelic, na gaya miki abin da nake so, kuma yanzu ina ƙara tabbatar miki da cewa ni da gaske nake,” na ji wani irin ɗumi ya ratsa zuciyata, na sunkuyar da kai, murmushi ya bayyana a leɓɓena, “Heartbeat…” Na kasa cewa komai, a wannan lokacin, na ji kamar zuciyata ta cika fiye da yadda za ta iya ɗauka, ya yi dariya a hankali, “Me ya sa kika yi shiru?” Na ɗan girgiza kai kaɗan, “Ba komai,” “Kin ji kunya ne?” Na kalle shi da gefen ido, “Ka yi shiru mana!” Ya fashe da dariya, ni ma na kasa hana kaina murmushina, na sake duba kayan, ina tunanin ranar da zai dawo da magabatansa wajen Daddy, ranar da za a fara ɗaukar shirye-shiryen aurena da gaske, ranar da zan iya cewa Ahmad ba saurayina kawai ba ne, zai zama mijina, my husband, tunani kaɗai ya sa na lumshe idanuwana cikin kunya, na ji kamar in yi dariya, amma a lokaci guda zuciyata ta cika da wani irin farin ciki mai zurfi, a wannan lokacin, komai ya yi kyau, kamar babu wata matsala a duniya, kamar rayuwarmu ta riga ta kasance a rubuce, mun shafe kusan awa biyu muna zaune a falon, muna magana kan abubuwan da za mu yi bayan aure, ya ba ni labarin irin gidan da yake son mu zauna, ya yi min bayani kan yadda yake son mu tsara rayuwarmu, abubuwan da yake son mu cim ma tare, da irin zaman da yake fatan za mu yi, ni kuma na faɗa masa irin abubuwan da nake mafarkin yi, wani lokaci sai ya yi magana, ni kuma in yi dariya, wani lokaci ni nake magana, shi kuma ya zauna yana kallona kamar babu wani abu a duniya da ya fi ba shi sha’awa fiye da ni, “Heartbeat, ka san ina son babban kitchen?” Na faɗa masa cikin murmushi, ya ɗan ɗaga gira, “Really? Is that your biggest dream?” Na yi saurin girgiza kai, “A’a mana! Amma ina son kitchen mai kyau, I want to cook for you,” ya ɗan yi shiru yana kallona, sai murmushi ya bayyana a fuskarsa, “You want to cook for me?” Na gyada kai, “Eh mana,” ya jingina da bayan kujera, yana kallona cikin raha, “Then I guess I’m going to be the luckiest man alive,” na yi dariya, “Of course!” Ya yi kamar yana nazari, “Okay, then, I will make sure your kitchen is exactly how you want it,” na buɗe baki cikin mamaki, “Da gaske?” Ya gyada kai, “Da gaske, Angelic,” na yi murmushi, ina kallonsa, a gare ni, irin waɗannan ƙananan kalaman suna da muhimmanci fiye da yadda zai iya tsammani, domin ba gidan kawai nake mafarkin samu ba, ina mafarkin rayuwa tare da shi, ina mafarkin komawa gida in same shi yana nan, ina mafarkin mu yi dariya a kan abubuwan da ba su da wani muhimmanci ga sauran mutane, ina mafarkin mu kasance tare a lokacin farin ciki da lokacin damuwa, ina mafarkin samun wanda zan kira my person, kuma a lokacin, Ahmad ne nake ganin zai cika wannan gurbi a rayuwata, “Angelic?” Muryarsa ta dawo da ni daga tunanina, na ɗago kai, “Hmm?” “Where did you go?” Na yi murmushi, na girgiza kai, “Nowhere,” ya matso kaɗan, yana kallona da shakku, “Really?” Na gyada kai, “Yes, Heartbeat,” ya yi murmushi, “Okay, I believe you,” sai ya sake jingina da kujerarsa, mun ci gaba da hira, har sai da na tuna cewa bai ci komai ba tun zuwansa, na miƙe da sauri, “Subhanallah ka ga ka sa ban kawo maka abinci ba,” ya ɗago kai, “Ba sai kin wahala ba, Angelic,” na girgiza kai, “Ba wahala ba ce,” na nufi kitchen ina murmushi, a hanya na haɗu da Rabi, wadda ta tambaye ni ko ina buƙatar taimako, na gaya mata ta taimaka min da wasu abubuwan, sannan muka shirya kayan ciye-ciye tare, bayan ɗan lokaci na fito ɗauke da babban tire a hannuna, tiren ya cika da ruwan ‘ya’yan itatuwa mai sanyi, soyayyen naman kaza mai ƙamshi da sauran kayan ciye-ciye, Rabi ta biyo ni, tana ɗauke da wasu abubuwan, na ajiye tiren a kan ƙaramin table ɗin da ke gabansa, sannan na zuba masa juice a cikin kofi, na miƙa masa, “Bismillah, Heartbeat,” ya karɓa, yana kallon kayan da na kawo masa, “Wow, Angelic, you prepared all this?” Na ɗan yi murmushi, “Eh mana, ka sha ka ɗan huta, ka yi sallah sai ka ci abinci,” ya ɗan kalle ni, sannan ya yi murmushi, “Thank you, my love,” yayin da yake karɓar kofin, yatsunsa suka ɗan taɓa nawa, na ji wani irin sanyi ya ratsa jikina, na ɗan janye hannuna cikin kunya, ina sauke idanuwana ƙasa, ya lura da hakan, sai murmushi ya faɗaɗa a fuskarsa, “Na gode, Angelic dina,” ya ɗan sha ruwan, sannan ya lumshe idanu a hankali, “Hmm…” Na kalle shi, “Me?” Ya yi murmushi, yana kallon abincin, “Kamshin naman nan kaɗai ya nuna min cewa kece kika shirya komai,” na yi ƙaramar dariya, “Ka ci kawai,” ya ɗauki ɗan naman, ya ɗanɗana, sannan ya gyada kai kamar wanda ya tabbatar da wani abu, “Delicious!” Na yi murmushi, “Really?” Ya ɗago kai ya kalle ni, “Really, you should cook for me every day after we get married,” na buɗe baki cikin mamaki, “Every day?!” Ya gyada kai da gaske, “Yes, every single day,” na danyi dariya inaso na tsokana shi, “Ah, Heartbeat! So you want to turn me into your personal chef?” Ya yi dariya tare da ɗaga hannayensa, “Okay, okay! Maybe not every day,” “Better!” Ya sake dariya, sannan ya ci gaba da cin abincinsa, muna cikin hira mai daɗi, ya ba ni labarin shagon sarinsa a Kano da yadda yake son faɗaɗa shi, ya yi magana kan sabbin shirye-shiryen da yake da su, da yadda yake son ƙara bunƙasa kasuwancinsa kafin mu yi aure, na saurare shi cikin kulawa, ina jin daɗin yadda yake magana kan makomarsa, a gare ni, ganin yadda yake da buri da ƙoƙari yana ƙara sa ni alfahari da shi, ya kuma yi magana kan yadda yake son idan mun yi aure, ya dawo da ni kusa da shi, “Ba na son ki yi nisa da ni,” ya faɗa cikin nutsuwa, na kalle shi, “Ni ma,” ya ɗan yi murmushi, “Kin san ke ce farin cikina?” Na sauke idanuwana, ina wasa da yatsuna, “Ka daina…” “Me?” “Yawan faɗin irin waɗannan maganganun,” ya ɗan karkatar da kansa, “Me ya sa?” Na ɗan yi murmushi, “Saboda suna sa ni jin kunya,” ya yi dariya, “Ni kuma ina son ganin kina jin kunya,” na ɗaga kai da sauri, “Ahmad!” Ya fashe da dariya, “Okay, okay, I’m sorry,” amma har yanzu murmushin bai bar fuskarsa ba, ni ma na kasa hana kaina dariya, dariya ta sake cika falon, komai ya kasance cikin nishaɗi, cikin farin ciki, cikin ƙauna, a wannan lokacin, ban taɓa tunanin akwai wani abu da zai iya sauya wannan farin cikin ba, a zuciyata, na riga na zana hoton makomarmu, ni da Ahmad, gida ɗaya, rayuwa ɗaya, mafarkai iri ɗaya, ban san cewa wani lokaci, mutum yana iya yin shiri mai kyau ga rayuwarsa, amma bai san abin da ƙaddara ta tanada masa ba, har sai da agogon hannunsa ya tunasar da shi cewa lokaci yana tafiya, da misalin ƙarfe huɗu na yamma, ya ɗaga hannunsa ya kalli agogon azurfarsa, murmushin fuskarsa ya sauya kaɗan, ya sauke numfashi a hankali, sannan ya kalli ni, “Angelic…” Na ɗago kai daga inda nake zaune, “Hmm?” Ya sake kallon agogon, “Lokaci ya tafi da sauri haka?” Na ɗan yi shiru, ya girgiza kai a hankali, “Kamar yanzu na shigo gidan nan,” sai ya miƙe a hankali, yana gyara zaman shaddarsa, “Gaskiya ya kamata na kama hanya yanzu kafin yamma ta yi nisa,” na ji zuciyata ta buga, murmushin da ke fuskata ya fara lafa a hankali, “Yanzu tafiya za ka yi?” Muryata ta fito da rauni fiye da yadda na yi tsammani, Ahmad ya tsaya yana kallona, fuskarsa ta nuna tausayi, ya matso kusa da ni, “Angelic…” Na ɗaga ido na kalle shi, ya yi murmushi kaɗan, yana ƙoƙarin kwantar min da hankali, “Kin ga dare ya yi, kuma ba na son na makara a hanya, zan dawo satin sama idan Allah Ya nufa,” na sauke idanuwana, “Amma…” Na tsaya, ban san abin da zan ce ba, ba wai ban fahimci dalilin tafiyarsa ba ne, na san tafiya ce mai nisa, kuma ba zai iya zama har dare ya yi ba, amma zuciyata ba ta son ya tafi, na so ya ƙara zama, ko da na wasu mintuna ne, ko da kuwa ba za mu yi komai ba, kawai ina son ya kasance a gabana, Ahmad ya ɗan ɗago fuskata da kallonsa, “Ki kula da kanki, kin ji?” Na gyada kai a hankali, sai na kasa jurewa, na ɗan kau da kai gefe, “Allah ya kiyaye hanya,” ya yi murmushi, “Ameen, thank you, my love,” na ɗan share idanuwana, ina ƙoƙarin hana ƙwallar da ta fara taruwa bayyana, sai ya ce, “Mu je na yi wa Daddy sallama,” ban iya magana ba, na gyada kai kawai, sannan na bi shi zuwa falon Daddy, da muka isa, Daddy ya tarbe shi cikin fara’a, Ahmad ya yi masa sallama, sannan ya tsaya yana sauraron addu’ar da Daddy ya yi masa, “Allah Ya kiyaye hanya Ahmad, Allah Ya kai ka lafiya,” Ahmad ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa, “Ameen, Daddy, na gode sosai,” Daddy ya ɗan taɓa kafadarsa, “Ka yi hankali a hanya,” “In shaa Allah,” na tsaya a gefe ina kallonsu, zuciyata cike da wani irin yanayi da ban iya bayyana shi ba, bayan sun gama sallama, Ahmad ya juya gare ni, “Ready, Angelic?” Na ɗan yi murmushi mai rauni, “Yes…” Muka nufi wajen motarsa tare, na raka Ahmad har wajen motarsa, ya buɗe ƙofar motar ya shiga, ni kuma na tsaya a gefe ina kallonsa, ya zauna, ya kunna motar, sannan ya kalle ni ta taga, “Angelic…” Na matso kaɗan, “Hmm?” Ya yi murmushi, “Why do you look like you’re about to cry?” Na buɗe baki zan musanta, amma sai na ji maƙogwarona ya ɗan ɗaure, na yi saurin girgiza kai, “I’m not crying,” ya ɗaga gira, “Really?” Na kau da kai gefe, “Yes, really,” ya yi ƙaramar dariya, “Okay, my love, I believe you,” amma kallon da yake yi mini ya nuna cewa bai yarda da maganata ba, ya ɗan kalli harabar gidan, kamar yana tabbatar da cewa babu wanda yake kallonmu, sai ya miƙo hannunsa, na yi mamaki, na ɗan tsaya kafin in miƙa masa nawa hannun, ya kama hannuna cikin nashi, zuciyata ta buga da ƙarfi, ya kalli hannunmu na ƴan seconds, sannan ya ɗago idanunsa ya kalle ni, “Ki kula da kanki, Angelic,” na gyada kai a hankali, “Kaima ka kula da kanka, Heartbeat,” ya ɗan matse hannuna, “Ki yi min addu’a,” muryarsa ta yi ƙasa, “Sai mun yi aure, in Shaa Allah, kin ji?” Kalaman nasa suka sa ƙwallar da nake ƙoƙarin riƙewa ta zubo, na yi saurin sunkuyar da kai, ina share ta da bayan hannuna, Ahmad ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya ce a hankali, “Hey… don’t cry, okay?” Na yi ƙoƙarin murmushi, amma leɓɓena suka ƙi yin yadda nake so, “I’m not crying…” Na maimaita maganar cikin wata murya mai rauni, abin da ya sa shi yin murmushi mai taushi, “Okay, Angelic, you’re not crying,” ya ɗan matse hannuna kafin ya sake shi a hankali, sai ya ɗaga hannuna… ya sumbaci bayan hannuna cikin ladabi, na kasa motsi, na zaro idanuwana kaɗan, ina kallonsa cikin mamaki, wannan shi ne karo na farko tun da na san shi da ya taɓa yin haka, na ji wani irin sanyi ya ratsa jikina, yayin da zuciyata ta fara bugawa da ƙarfi, ya kalle ni kai tsaye, “Bye, Angelic,” na buɗe baki zan ce masa sai anjima, amma muryata ta ƙi fitowa, sai na ɗaga masa hannu kawai, ina kallonsa da idanun da suka cika da ƙwalla, ya yi murmushi na ƙarshe, sannan ya mayar da hankalinsa ga hanya, motar ta yi reverse, na ɗan ja baya domin in ba shi hanya, kafin ya fita, ya yi horn, gate ɗin ya buɗe, na tsaya a wurin ina kallon motarsa tana barin harabar gidan, mota ta ci gaba da tafiya… ta ƙara nisa… har sai da ta ɓace daga ganina, amma duk da haka, ban motsa daga wurin ba, na ci gaba da kallon hanyar da ya bi, kamar zuciyata tana tsammanin zai dawo a kowane lokaci, sai da na fahimci cewa motar ta daɗe da ɓacewa sannan na sauke numfashi mai nauyi, hawaye suka zubo min a hankali, na share su da bayan hannuna, na yi murmushi mai rauni, “Allah Ya tsare ka…” Na faɗa cikin raɗa, na ɗan juya na kalli gate ɗin da aka rufe, sai na sake kallon hanyar, ban san dalilin da ya sa zuciyata ta ji wani irin nauyi ba, ban san dalilin da ya sa rabuwar yau ta yi min zafi fiye da sauran lokuta ba, ai zan sake ganinsa, ya ce zai dawo, mun yi magana kan makomarmu, ya kawo min kyaututtuka, ya tabbatar mini da cewa yana sona, so why does my heart feel this way? Na ɗora hannuna a ƙirji, ina ƙoƙarin kwantar da bugun zuciyata, wataƙila zuciyata ce kawai take tsoron rasa abin da ta fi so, wataƙila saboda na daɗe ina jiran ganinsa ne, shi ya sa ban so lokacinmu tare ya ƙare da wuri ba, ko kuma… wani wuri can cikin ƙaddara… an riga an rubuta abin da zai faru, na sake share fuskata, na yi ƙoƙarin gyara yanayina kafin in koma cikin gidan, ban so kowa ya tambaye ni dalilin da ya sa nake kuka ba, ban so a yi mini dariya saboda na yi kewar mutumin da zan sake gani nan ba da jimawa ba, amma kafin in juya, na sake wa hanyar kallon ƙarshe, “See you soon, Heartbeat…” Na raɗa cikin murmushi mai ɗauke da ƙwalla, ban san cewa wannan ƙaramin bankwana da na yi masa ba zai taɓa zama wani abu da zan tuna da shi da wani irin yanayi dabam ba, ban san cewa akwai wasu bankwana da mutum yake yi ba tare da ya san muhimmancin lokacin ba, domin wani lokaci… shiru ba yana nufin babu komai ba, wani lokaci, shiru yana ɗauke da amsar da zuciya ba ta shirya ji ba, kuma wani lokaci, abin da muke ganin zai zama farkon kyakkyawar rayuwa… shi ne farkon gwajin da ba mu taɓa shirin fuskanta ba.