Free chapter · Read without an account
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
ZAID NA Port Harcourt wurin aikin shi amma gaba-ɗaya tunanin shi baya jikin shi saboda abinda Hadiza ta mishi, most especially wannan cikin nashi da ta zubar har sau biyu. Ya kasa gane wane irin abu ne take ji a cikin zuciyar ta wa shi. Ya kasa gane dukkanin ta. Be san ko ƙiyayya ce take ji game dashi ba. Amma ze 'iya cewa ƙiyayya ce bayan wani lokaci ba haka take ba?!
A cikin jirgin ruwa Zaid yake lokacin da iska ya fara bugowa da ƙarfi da ruwan da suke motsawa violently. Babban kayan da suke ɗagawa suka fara jujjuya. Ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin, ganin Zaid ne kawai be riƙe rope da kyau ba yace “Hold the rope tightly, Zaid. The machine is swinging”
“Yes, I'm holding it” Zaid ya amsa yana riƙe da rope.
Cigaba da iskan ake jirgin na cikin ruwa yana motsawa babu sassauta wa. Ruwan teku na kara karfin motsawa kai kace rai ne dasu. Abokin aikin su yace “Everybody should stand clear and well. The load is moving too much”
Zaid yayi stressing idanun shi ya zama very quiet and he stood still and well saboda sosai ake iskan jirgin yana motsawa violently. Suddenly , the ship rolled hard. Ƙarfe me nauyi yayi swinging sideways ya buge Zaid a hannun hagun kirjin shi. Kanshi ya buge bango se ya faɗi ƙasa. Zafi ne ya cika mishi kirji haɗi da kanshi. Zaid na ƙoƙari yayi steadying numfashin shi amma ya kasa baya iya yin shi da kyau. Duhu ya fara gani yana ƙoƙarin buɗe idanun shi amma ya kasa, idanun shi suka rufe baya ganin komai. Abokanan aikin shi ya ji suna kiran sunan shi amma baya iya amsawa har yaji kamar daga nesa ne ake kiran shi.
Da sauri abokanan aikin nashi suka yo kanshi.
“He's not breathing well” ɗaya daga cikin su ya faɗa.
A radio ɗayan su yayi magana “Zaid Liman got injured on deck. He needs the helicopter immediately it's an emergency. Send medevac to our location”
A gefen Zaid suka tsaya suna mishi magana kafin helicopter ya iso. Ɗayan su yayi tsaye yana kallon Zaid hannun shi a wurin kuncin shi be iya yayi komai ba saboda tsoro da kuma tunanin yanzu suke tsaye nan wurin bada jimawa ba amma gashi cikin ƙanƙanin lokaci Zaid a kwance da kyar yake iya numfashi.
Bayan helicopter ya iso aka ɗauke shi zuwa coastal base inda ambulance ke jira aka ƙara ɗaukar shi zuwa University of Port Harcourt Teaching Hospital.
Isar su a asibitin aka wuce da Zaid trauma bay. Daga nan suka tafi CT scans aka wuce dashi ICU saboda irin abinda ya faru dashi.
Zaid baya iya numfashi da kanshi saboda ƙwaƙwalwar shi ta kumbura da kuma chest trauma da ya samu yasa Doctors suka hooking nashi up to a mechanical ventilator via a tube down his throat domin yayi pumping oxygen a cikin lungs ɗin shi. Suka yi administering IV medications domin kumburin ya rage kuma zasu cigaba da monitoring nashi akan wannan swelling so it doesn't get worse.
A chan gefen wurin aikin shi, HR na companyn su ya kira next of kin nashi ya faɗa Zaid ya samu ciwo while at work.
Tun lokacin da yayi aure Hadiza ta zama next of kin nashi kuma number ta ce akan emergency contact ɗin shi.
Tsaye nayi bayan an faɗa min abinda ya faru da Zaid wayar dake hannuna tana son zamewa daga gare ni. Zuciya ta ce naji kamar wacce ta dasqare na kasa jin komai a cikinta. Wayata da ta faɗi akan carpet ne ya dawo dani daga duniyar wani tunani da na shiga. Da sauri na bi wayar na ɗauko na fara dubawa ko zan samu jirgin zuwa Port Harcourt yanzu. Ina dubawa naga da akwai jirgin da ze tashi ƙarfe biyu.
Ɗaki na koma na ɗauko mayafi na na wuce Nnamdi Azikiwe Int'l Airport. Ina chan har ƙarfe biyu babu alamar tashin jirgi anyi sanarwa ba ze tashi yanzu ba se ƙarfe biyar. Tsaye na tashi na kasa zama ina to and fro da tunanin da ya dameni na halin da Zaid ke ciki. Waya ta na jawo na kira mahaifin shi na sanar dashi da kuma duk abinda yake faruwa a filin jirgin Abuja.
Bayan na faɗa mishi yace na fito daga wurin ze sa akawo private jet mu tafi. Fitowa nayi ina jira se gashi ya kira muka wuce. Naga Muhammad a cikin jirgin, daga shi se Abba se ni.
Isar mu asibitin koyarwa na Port Harcourt muka haɗu da abokan aikin Zaid. Inda aka ajiye Zaid suka kai mu.
Mutane mabanbanta ne a cikin asibitin wasu na gyara wuri wasu kuma malaman asibitin ne doctors da nurses.
Gabana naji yana duka kamar wacce zata faɗi ƙasa ɗakin da yake kallon mu an rubuta mishi ICU. Tsaye nayi ban isa kofar ICU ba ina kallon Abba ya shiga. Windown da yake wurin nake kallo amma bana ganin komai a ciki se machines da wayoyi na cikin ɗakin. Bayan Abba ya fito ne, Muhammad ya shiga. Shima be jima ba ya fito.
“Hadiza. Ba zaki shiga ki gan shi ba?” Abba ya faɗa min fuskar shi bata ɗauke da damuwa ko kaɗan kamar ba yaron shi ne ke cikin ICU ba.
Shiru nayi ban ce mishi komai ba. Muhammad ya kalle ni shima be ce komai ba shine me damuwa akan fuskar shi ya sunkuye kan shi ban san abinda yake tunani ba. Ko yana tunanin zamu yi rashi ne?!
“Ki shiga ki gan shi”
Ahankali na taka ina jin nauyin tafiyar da nake na shiga ICU. Idanun Zaid na rufe, tube a bakin Zaid anyi connecting da ventilators da monitors. Babu wani sound da yake tashi a cikin ICU se na'urorin dake aiki. Kenan Zaid baya ma iya numfashi da kyau se da oxygen?! Zuciyata naji na min zafi ganin shi irin haka da nayi. He looks helpless babu wani abu da yake iya yi yana de kwance wayasani be ma san abinda yake faruwa ba.
Fitowa nayi daga cikin ɗakin saboda ba'a jimawa a ciki suna controlling infection. Doctor ne yazo duba Zaid muna jira ya fito muyi magana dashi.
Bayan fitowar likita muka tafi office ɗin shi tare dashi. Anan yake mana bayanin Zaid ya samu traumatic brain injury da chest injury. Gobe zasu mishi aiki and fix his ribs.
Shiru Abba yayi se a lokacin naga damuwa akan fuskar shi. Da sauri kuma yayi brushing nata off yace “Will he have problem with his brain?”
“The brain swelling is not worse. We're monitoring it” Doctor ya bada amsa
Inaso nayi tambaya akan mantuwa idan ya tashi amma ban ce komai ba ina sauraren duk bayanan likita.
“Will he have problem recognizing people, things, or even remembrance?” Abba ya tambaya abinda nake son tambaya
“It might occur during the early stages of his recovery but it'll not be long term. Or it might not happen at all”
“Is that his wife?” likitan yace tare da nuna ni
Abba ya amsa da eh. Likitan yace “We need you to talk to him even though he's unconscious because familiar voices can help with orientation after a brain injury”
Nodding Kai nayi nace “They don't allow visitors to stay for long”
“Yes, that's for infection control rules. You should talk to him even for 5minutes. It does help our patient. I'll talk to the nurse on shift”
Nodding mishi kai nayi bayan mun gama magana dashi muka fito.
Abba yace mu je mu dawo. A hotel muka tafi. Sallah muka yi ina chan ɗakina aka kawo min abinci. Kallon abincin nake har lokacin da yayi sanyi. Ƙarfe tara Muhammad ya kira ni muka koma asibitin nida shi. Bayan an aje mu ni na wuce inda Zaid amma be biyo ni ba. Nasan dalilin da yasa be biyo ni ba ko Abba. They're giving me space with my husband har dai saboda abinda likita yace.
Har na kawo Kofar ICU gabana duka yake ina jin tsoron duk wani abu da ze iya faruwa da Zaid. Ina jin tsoro kar damuwa ce dalilin kasa focusing wurin aikin shi har ya samu irin wannan matsalar me girman gaske.
Shiga ciki ne a karo na biyu yasa na fara jin hawaye suna zubowa a idanuna. Nan take na fara jin wani sabon tsoron rashin Zaid ya mamaye dukkanina. Ina jin tsoro kar ace wucewar shi da yayi wurin aiki shine lokaci na ƙarshe da zan gan shi lafiya. Oxygen dake hancin shi nake kallo da idanun shi da suke rufe kamar jira kawai yake a rufe shi da ƙyalle.
Kirjin shi na kalla da yake da chest drain likita yace suna tsoron pneumonia ko kuma wasu matsaloli da suka dangance respiration.
“Zaid” na kira sunan shi wanda nasan ni kaɗai nake ji
Wurin shi na matsa na kai hannuna a nashi. Hannun shi yayi sanyi ina so ya zama clingy kamar yadda yake amma Zaid be riƙe hannuna ba.
“Zaid, yaushe zaka tashi?”
“Dan Allah kayi haƙuri Zaid. Duk wani abu da baka so kuma nasan bashi da kyau kayi wa wani ɗan uwanka, ba zan sake maka ba, Zaid. Kayi haƙuri mu cigaba da zama tare da juna. Duk ƙuncin rayuwa ina tare da kai Zaid saboda tun lokacin da na yarda muyi aure, zaren rayuwa ta da naka ya haɗu kuma yanzu bana son ya taɓa gaucewa, Zaid. Kayi haƙuri ka tashi i would want you to make me pregnant again I promise I'll give birth to our baby I won't abort our baby Zaid. I'm so sorry”