Free chapter · Read without an account

PIECES OF A BROKEN HEART

by Jiddaah Barkum · KADDARAR ZUCIYA

*ƘADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SIX: 6*

*PIECES OF A BROKEN HEART*

*JIDDAAH BARKUM*

———

Ƙarfe kusan tara na dare aka maido da Daddy ɗakin da Inteesar take bayan an sake bincika lafiyarsa, da aka buɗe ƙofar ɗakin, Inteesar ta ɗago kai, ganin an shigo da Daddy ya sa ta yi saurin miƙewa, duk da raunin da jikinta yake ciki, “Daddy…” Ta kira shi cikin kuka, muryarta tana rawa, Alhaji Kabeeru ya ɗago hannu, yana nuna mata da alamar ta zauna, “Ah-ah, Princess, ki zauna mana,” amma Inteesar ta kasa zama nan take, ta tsaya tana kallonsa, hawaye suna taruwa a idanunta, har sai da aka taimaka aka kawo Daddy kusa da gadonta, da ya zauna, sai ya miƙa hannu ya kamo hannunta, hannun nata ya yi sanyi, ya ɗan matse shi cikin nasa, sannan ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, “Zo nan, Princess,” Inteesar ta matsa kusa da shi, Daddy ya yi mata murmushi, murmushin da a wasu lokuta yake sa ta ji cewa babu wani abu a duniya da zai iya cutar da ita muddin yana kusa da ita, amma a wannan karon, murmushin ya ƙara karya mata zuciya, ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin danne kukan da ke son ƙwace mata, Daddy ya shafa bayan hannunta a hankali, “Princess, ki saurare ni,” ta ɗago idanunta masu hawaye ta kalle shi, “Ba kowane abu ne da muke so a rayuwa Allah yake rubuta mana ba, wani lokaci za mu yi buri, mu yi shiri, mu yi tunanin yadda rayuwarmu za ta kasance, amma ƙaddarar Allah ta kasance daban da abin da muka tsara,” ya ɗan yi shiru, yana kallon fuskarta, “Ahmad ya tafi, kuma na san kina cikin babban baƙin ciki, na san kina son shi, kuma na san ba abu ne mai sauƙi ba ki karɓi wannan rashi,” idanun Inteesar suka sake cika da hawaye, Daddy ya matse hannunta a hankali, “Amma ki tuna da abu ɗaya, ƴata, mutuwa ba ita ce ƙarshen rayuwar waɗanda aka bari a baya ba, rayuwa za ta ci gaba, ko da zuciyarmu tana jin kamar ta tsaya,” ya ɗan sauke numfashi, “Ki yi wa Ahmad addu’a, ki roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sa Aljanna ce makomarsa, wannan shi ne abin da zai fi amfanar da shi yanzu,” Inteesar ta sunkuyar da kanta, “In Shaa Allah, Daddy…” Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa, Daddy ya sake shafa hannunta, “Ki kuma kula da kanki, Princess, ba na son ganin kina cutar da kanki saboda baƙin ciki, your life matters too, my daughter,” ta ɗaga idanunta ta kalle shi, Daddy ya yi murmushi mai rauni, “Kuma akwai wasu abubuwa da nake son sanar da ke kafin lokaci ya kure min…” Kalaman suka fito cikin nutsuwa, amma akwai wani abu a cikin muryarsa da ya sa Inteesar ta ɗago kanta da sauri, “Waɗanne abubuwa, Daddy?” Daddy ya yi shiru, ya kalli fuskarta, sannan ya sauke idanunsa kan hannunta da yake riƙe da shi, “Ba yanzu ba, Princess,” ya ɗan yi murmushi, “Lokacin da ya dace, zan gaya miki,” Inteesar ta zuba masa idanu kawai, amma ba ta matsa masa da tambayoyi ba, a gefe guda, Mommy Haleema da Abubakar suka yi musayar kallo, kalaman Daddy sun ba su mamaki, sun san cewa tun bayan hatsarin Ahmad, Daddy yana ta ƙoƙarin faɗa musu wani abu, amma duk lokacin da yake shirin yin hakan, sai ya yi shiru ko kuma ya sauya zance, yanzu kuma ga shi yana son sanar da Inteesar wani abu kafin lokaci ya kure masa, Mommy Haleema ta kalli mijinta cikin damuwa, amma ba ta ce komai ba, Abubakar ma ya sunkuyar da kansa, babu wanda yake son matsa wa Daddy, musamman saboda halin jikinsa da kuma yadda likita yake ta jaddada musu cewa su kula da shi sosai, amma kalaman Daddy sun bar wata tambaya a zukatansu, wane irin abu ne yake son sanar da Inteesar? Kuma me ya sa yake magana kamar lokaci yana ƙoƙarin ƙwace masa wani abu? KWANA UKU BAYAN RASUWAR AHMAD, bayan an sallame su daga asibiti, gidan Alhaji Kabeeru ya koma kamar ba shi da rai, ba wai mutanen gidan sun daina rayuwa ba ne, amma farin cikin da aka saba ji a cikinsa ya yi nisa, kowa yana ƙoƙarin ci gaba da harkokinsa, amma tunanin Ahmad da halin da Inteesar take ciki yana damunsu, a wannan rana, Inteesar ta shiga ɗakin Daddy, ta same shi zaune a gefen gadonsa, yana kallon wani tsohon album na hotuna, da ya ji motsinta, sai ya ɗago kai, “Princess, zo nan,” Inteesar ta ƙarasa ta zauna kusa da shi, Daddy ya buɗe album ɗin sosai, sannan ya juya shi ya nuna mata wani hoto, a hoton, Inteesar tana ƙarama, tana zaune a kafaɗarsa, hannayenta a wuyansa yayin da shi kuma yake murmushi cike da farin ciki, Inteesar ta tsaya tana kallon hoton, a hankali, murmushi mai rauni ya bayyana a fuskarta, “Daddy…” Ta taɓa hoton da yatsunta, “Look at me, I was so tiny!” Daddy ya yi dariya ƙasa-ƙasa, “Kin manta da yadda kika kasance?” Inteesar ta girgiza kai, murmushin nata yana faɗuwa a hankali, “Ka riƙa ɗauka na a haka?” “Of course!” Daddy ya ɗaga gira, “Ke dai ba kya son tafiya da ƙafafunki, kullum sai na ɗauke ki,” Inteesar ta yi wata ƙaramar dariya, amma ba da daɗewa ba hawayen da take ƙoƙarin riƙewa suka taru a idanunta, Daddy ya kalle ta, “Me ya faru, Princess?” Ta girgiza kai, tana share hawayen da bayan hannunta, “Nothing, Daddy…” Amma muryarta ta nuna cewa akwai abin da ke damunta, Daddy ya rufe album ɗin a hankali, sannan ya juyo ya fuskance ta, “Princess…” Ya kamo hannunta, “Kin san wani abu?” Ta ɗago kai, “Me, Daddy?” Ya yi mata murmushi mai cike da ƙauna, “Na yi ƙoƙarin zama uba nagari a gare ki, ko?” Tambayar ta karya mata zuciya, Inteesar ta buɗe baki, amma kalma ta ƙi fitowa, sai ta fashe da kuka, “Daddy…” Ta rungume shi da ƙarfi, kamar tana tsoron kada shi ma ya ɓace mata, “Kai ne mafi alherin uba a duniya!” Ta girgiza kai a jikinsa, “Please, don’t ever think otherwise, you have always been the best father to me,” Daddy ya rungume ta, yana shafa bayanta a hankali, “Shhh… Princess, ki yi haƙuri,” amma Inteesar ta ƙara matse shi, “Kai ne komai nawa, Daddy…” Muryarta ta karye, “Kai ne kullum kake sa ni farin ciki, kai ne kake kula da ni, kai ne…” Ta kasa ƙarasa maganar, kuka ya ƙwace mata, Daddy ya lumshe idanunsa, Allah kaɗai Ya san abin da ke ransa a wannan lokacin, ya ci gaba da rungume ta, yana ƙoƙarin ɓoye irin nauyin da ke zuciyarsa, domin ganin ƴarsa cikin wannan hali ya fi masa ciwo fiye da yadda zai iya bayyanawa, ya shafa kanta a hankali, “Allah Ya ba ki haƙuri, ƴata, Allah Ya sa ki zama mai ƙarfin zuciya,” Inteesar ta ɗaga kanta ta kalle shi, Daddy ya share mata hawaye da babban yatsansa, “Kuma ki sani, duk abin da ya faru a rayuwarki, ba za ki taɓa rasa addu’ata ba,” ta sake rungume shi, “Ameen, Daddy,” a lokacin ne kuma, a falo, Abubakar da sauran yayyenta maza suke tattauna halin Daddy, Adam, Khalil, Faruq, Salim, Abdul, Jaafar, Alamin da Umar duk suna zaune cikin damuwa, Abubakar ya jingina bayansa da sofa, yana kallon sauran, “Kun lura da Daddy?” Adam ya ɗago kai, “Me kuma?” Abubakar ya sauke numfashi, “Tun bayan hatsarin Ahmad, yana ta ƙoƙarin faɗa mana wani abu, amma duk lokacin da yake shirin yin magana, sai ya yi shiru,” Khalil ya gyara zama, “Na lura da hakan ma,” ya ɗan daure fuska, “Har ma yau da safe, na shiga ɗakinsa, yana son fara magana da ni, amma da na tambaye shi abin da yake son faɗa, sai ya ce ba komai,” Faruq ya kalli Adam, “Do you think something is bothering him?” Adam ya yi shiru na ɗan lokaci, “Wataƙila, amma bana son mu matsa masa,” Salim ya jinjina kai, “Likita ya yi mana gargaɗi sosai cewa mu kula da shi, ba ma son wani abu ya sake tayar masa da hankali,” Abubakar ya sauke kansa, “Haka ne, amma duk da haka, akwai wani abu a zuciyata da yake gaya min cewa abin da Daddy yake son faɗa ba ƙaramin abu ba ne,” Khalil ya kalli ɗakin Daddy, “Whatever it is, I hope he tells us when he’s ready,” Adam ya gyada kai, “Mu ba shi lokaci, abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne lafiyarsa da ta Inteesar,” bayan sun yi shiru na ɗan lokaci, Abubakar ya yi magana a hankali, “Maganar Inteesar ma fa…” Duk suka juyo suka kalle shi, ya haɗiye yawu, “Ban san yadda za mu taimaka mata ba,” babu wanda ya amsa nan take, domin duk suna da wannan damuwar a zukatansu, Inteesar ba ƙanwarsu kawai ba ce, ita ce farin cikin gidan tun tana jaririya, kuma tun bayan rasuwar Ahmad, babu wanda ya sake ganin cikakkiyar fara’arta, SATI GUDA BAYAN RASUWAR AHMAD, sati guda kenan tun bayan rasuwar Ahmad, tun daga ranar da aka sallame su daga asibiti, Inteesar ba ta sake fitowa falon gidan ba, ba ta zuwa kitchen, ba ta zama tare da iyalinta, ba ta shiga hirar da ta saba yi da ƴan uwanta, ta ware kanta daga kowa, abincin da take ci ya yi kaɗan sosai, wani lokaci tea kawai take sha, sannan ta sha ruwa da ƙyar, kamar maƙogwaronta ya ƙi karɓar komai, idan wani ya shigo ɗakinta ya yi ƙoƙarin yi mata magana, takan amsa da kalmomi kaɗan kafin ta sake komawa cikin shirunta, ta daina dariya, ta daina yin barkwanci, ta daina kasancewa waccan yarinyar da gidan yake cika da muryarta, kamar wani ɓangare na ita ya ɓace tare da Ahmad, a wannan daren, zaune take a gefen gadonta, tana rungume da babban akwatin da Ahmad ya kawo mata ranar ƙarshe da suka haɗu, akwatin nan, kyautar nan, leshin nan, turarukan nan, da sarƙar nan, duk suna nan yadda ya kawo su, ba ta buɗe akwatin ba, ta dai riƙe shi a jikinta, tana kallonsa lokaci-lokaci kamar wata rana zai zama abin da zai tabbatar mata cewa Ahmad ya taɓa kasancewa a rayuwarta da gaske, a hankali, ta ɗaga hannunta ta shafa murfin akwatin, ta tuna ranar da ya shigo gidansu da murmushi, yana sanye da shadda mai launin sky blue, ta tuna yadda ya kalle ta, ya yi murmushi sannan ya kira ta da sunan da ya saba kiranta da shi, “Angelic…” Wani sabon hawaye ya zubo mata, ta matse akwatin a ƙirjinta, “Heartbeat…” Ta furta sunan a hankali, sai ta runtse idanunta, tana ƙoƙarin danne kukan da ya sake tasowa daga can cikin zuciyarta, amma ta kasa, kuka ya ƙwace mata, kukan da tun ranar da aka kira wayarta aka sanar mata da hatsarin Ahmad take yi, har idanunta suka canja yanayi gaba ɗaya saboda yawan zubar hawaye, ta ɗaga kanta, tana kallon ƙofar ɗakin, wani ɓangare na zuciyarta har yanzu yana jiran ta ji an buɗe ƙofar, har yanzu tana tunanin wataƙila Ahmad zai shigo da murmushinsa, ya zauna kusa da ita, sannan ya ce, “Angelic, what happened? Why are you crying?” Sai ta yi masa murmushi, ta gaya masa cewa ta yi kewarsa, amma babu wanda ya buɗe ƙofar, babu wanda ya kira ta da sunan da ta saba ji daga gare shi, sai shiru, shiru mai ciwo, shiru da ke tunasar da ita cewa babu wanda take jira zai dawo, ta sunkuyar da kanta a kan akwatin, hawaye suna zuba a hankali, “Why did you leave me, Heartbeat?” Muryarta ta fito cikin rauni, “Why?” Babu amsa, sai kukan da ke ci gaba da fitowa daga zuciyarta, ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali, Mommy Haleema ce ta shigo, sanye da doguwar rigar atamfa mai launin ruwan kasa, fuskarta cike take da damuwa, a hannunta tana riƙe da tray mai ɗauke da tea mai ɗumi, bread da wasu fruits, ta rufe ƙofar a hankali, sannan ta kalli Inteesar, ganin yadda take rungume da akwatin ya sa zuciyarta ta yi wani irin ciwo, ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a kan ƙaramin table, sannan ta zauna kusa da Inteesar, shiru ya ratsa tsakaninsu, sai sautin kukan Inteesar kaɗai ke tashi, Mommy Haleema ta ɗan kalli akwatin, sannan ta ɗaga hannu ta shafa kan ƴarta, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…” Ta furta cikin sanyin murya, Inteesar ta ƙara rungume akwatin, “Mommy…” Ta kira ta cikin rauni, Mommy Haleema ta juyo gare ta, “Na’am, ƴata?” Inteesar ta ɗaga idanunta masu hawaye, “Me ya sa Allah ya ɗauke shi?” Tambayar ta fito ne daga can cikin zuciyarta, tambayar da ta daɗe tana neman amsarta, amma duk lokacin da ta yi tunani, sai ta ƙara jin cewa ba za ta taɓa samun amsar da za ta gamsar da zuciyarta ba, Mommy Haleema ta lumshe idanu, “Allah kaɗai Ya sani, ƴata,” ta ɗan shafa kanta, “Mu dai bayin Allah ne, abin da Ya ƙaddara mana, dole ne mu karɓa, ko da kuwa zuciyarmu tana jin zafi,” Inteesar ta girgiza kai, hawayenta suna ƙaruwa, “Mommy, ya yi min alkawari…” Ta fashe da kuka, “Ya ce zai dawo, ya ce zai kira ni idan ya kusa Kano, ya ce zai zo da iyayensa,” ta ɗaga akwatin sama kaɗan, “Look at this, Mommy, ya kawo min waɗannan ne saboda yana son mu yi aure…” Muryarta ta karye, “Ya yi shirin komai, ya gaya min irin gidan da yake son mu zauna a ciki, ya gaya min yadda yake son rayuwarmu ta kasance…” Ta haɗiye yawu, tana ƙoƙarin ɗaukar numfashi, “Yanzu ina zan je da duk waɗannan abubuwan?” Mommy Haleema ta ji zuciyarta ta karye, hawaye suka taru a idanunta, amma da sauri ta goge su, domin ba ta son Inteesar ta ga tana kuka, ta kama hannunta cikin rarrashi, “Ki yi haƙuri, ƴata,” Inteesar ta jingina kanta a kafaɗarta, “Mommy, zuciyata na min ciwo…” Ta matse hannunta, “Ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba,” Mommy Haleema ta rungume ta sosai, kamar yadda take yi tun tana yarinya, ta sumbaci kanta, tana shafa bayanta a hankali, “Ki saurare ni, Intee,” ta ɗan ja da baya kaɗan domin ta kalli fuskarta, “Na san kina jin zafi, na san kina tunanin cewa ba za ki iya rayuwa ba tare da shi ba, saboda kin yi masa wuri mai girma a cikin zuciyarki,” ta share mata hawaye, “Amma rayuwarki ma tana da muhimmanci, ƴata, Allah Ya ba ki wannan rayuwar ne, kuma har yanzu akwai abubuwa da ba ki san abin da Ya tanadar miki ba,” Inteesar ta yi shiru, Mommy Haleema ta ci gaba da magana cikin nutsuwa, “Ba na ce miki ki manta da Ahmad ba, ba na ce miki kada ki yi kuka ba, ki yi kuka idan zuciyarki tana buƙatar hakan, amma kada ki bari baƙin ciki ya hana ki kula da kanki,” ta matse hannunta, “Ki ci abinci, ki sha ruwa, ki yi addu’a, ki ba jikinki damar samun ƙarfi,” ta ɗan yi murmushi mai rauni, “Kaddara ce, ƴata, kuma da yardar Allah, za ki iya sake tsayawa da ƙafafunki,” Inteesar ta lumshe idanu, ta jingina kanta a kafaɗar Mommy, tana kuka a hankali, Mommy Haleema ta ci gaba da rungume ta, a wannan lokacin, ba ta da wata kalma da za ta iya goge mata zafin da take ji, abin da kawai za ta iya yi shi ne kasancewa kusa da ita, ta bar ta ta yi kuka, ta bar ta ta tuna, ta bar ta ta furta sunan Ahmad sau nawa take so, domin wani lokacin, abin da zuciya ke buƙata ba nasiha ba ce, abin da take buƙata shi ne wanda zai zauna kusa da ita har sai ta samu ƙarfin ɗaukar numfashi ba tare da jin kamar zuciyarta za ta tsage ba, a can falo kuwa, su Adam, Abubakar, Khalil, Faruq, Salim, Abdul, Jaafar, Alamin da Umar duk suna zaune cikin shiru da damuwa, Abubakar ya dafe kansa, yana kallon ƙasa, “Ta ci wani abu yau?” Adam ya girgiza kai, “A’a, tun jiya ba ta ci abinci yadda ya kamata ba,” Khalil ya sauke numfashi, sannan ya jingina bayansa da sofa, “Wallahi, ba zan iya ganinta haka ba,” ya ɗaga kansa ya kalli sauran, “Inteesar ba ƙanwarmu kawai ba ce, ita ce farin cikin gidan nan tun tana jaririya,” ya yi shiru na ɗan lokaci, “Har yanzu ina tuna yadda take gudu tana neman Daddy idan ta yi fushi da ɗayanmu, yanzu kuwa ta kulle kanta a ɗaki, ba ta son ganin kowa,” fuskarsa ta nuna irin damuwar da yake ciki, “It’s really painful to watch her suffer like this,” Faruq ya gyada kai, “Gaskiya ne, amma me za mu yi? Ba za mu iya tilasta mata ta daina baƙin ciki ba,” Salim ya ɗaga kai, “Abin da ya fi muhimmanci shi ne kada mu bar ta ta ji kamar ita kaɗai ce,” Abdul ya amsa da sauri, “Haka ne, dole ne mu riƙa shiga mu duba ta, ko da kuwa ba ta son magana,” Abubakar ya ɗaga kansa, “Amma kar mu matsa mata da tambayoyi, a hankali za mu riƙa ƙarfafa ta,” Adam ya jinjina kai, “Exactly, we need to be patient with her,” ya yi shiru, sannan ya ƙara da cewa, “Kuma mu tabbatar Daddy bai damu da ita har ya manta da lafiyarsa ba,” da aka ambaci Daddy, sai kowa ya yi shiru, domin su ma sun lura cewa halin da Inteesar take ciki yana ƙara damun mahaifinsu, a ɗakinsa kuwa, Alhaji Kabeeru yana zaune a kan gadonsa, fuskarsa ta ƙara ramewa saboda rashin lafiyar da yake fama da ita ta sake tsananta, ya jingina bayansa da matashin kai, idanunsa a rufe, yayin da yake ƙoƙarin samun nutsuwa, ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali, Mommy Haleema ta shigo, da ya ji motsinta, sai ya buɗe idanunsa, “Haleema…” Ta ƙaraso kusa da shi, “Na’am, Alhaji,” ya kalleta na ɗan lokaci, sannan ya tambaya, “Yaya take?” Mommy Haleema ta yi shiru, Daddy ya lura da hakan, “Ta ci abinci?” Mommy ta sauke idanunta ƙasa, amsar ta bayyana a fuskarta tun kafin ta yi magana, Daddy ya lumshe idanu, ya juya kansa gefe, yana ƙoƙarin danne wani irin baƙin ciki da ya taso masa, ba don ciwon jikinsa ba ne ya dafe ƙirjinsa, sai don ciwon da yake ji saboda ƴarsa, ƴar da ya raina, ƴar da ya riƙa ɗauka a hannunsa tun tana jaririya, ƴar da yake son ya ga farin cikinta har ƙarshen rayuwarsa, yanzu kuma yana kallonta tana fama da wani ciwo da ba zai iya warkar mata da shi da hannunsa ba, “Haleema…” Muryarsa ta fito a hankali, ta matso kusa, “Na’am?” Ya buɗe idanunsa ya kalleta, “Ki kira min Abubakar,” Mommy Haleema ta gyada kai, “To, Alhaji,” ta juya ta fita, tana ƙoƙarin ɓoye damuwar da ke fuskarta, bayan mintuna kaɗan, Abubakar ya shigo ɗakin, Alhaji Kabeeru ya ɗaga masa hannu, “Zo nan, ɗana,” Abubakar ya ƙarasa ya zauna kusa da shi, Daddy ya kalle shi da ƙyar, “Ku kula da ita,” Abubakar ya gyada kai, “In Shaa Allah, Daddy,” Daddy ya matse hannunsa, “Kar ku bari ta ji cewa ita kaɗai ce, ko da ta ƙi magana, ku riƙa kasancewa kusa da ita, ko da ta kulle kanta a ɗaki, ku tabbatar tana da wanda za ta iya kira idan ta buƙaci taimako,” Abubakar ya sunkuyar da kansa, “Za mu kula da ita, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya sauke numfashi, “Ahmad yaro ne na kirki,” ya ɗan yi shiru, kamar yana ƙoƙarin haɗiye wani abu da ya makale masa a zuciya, “Na so shi, na yi fatan zan ga aurensu,” Abubakar ya kalli mahaifinsa, yana jin wani irin tausayi, Daddy ya ci gaba da magana, “Na yi fatan zan ga Princess ɗina cikin farin ciki a ranar aurenta, na yi fatan zan ga yadda za ta yi murmushi idan aka kawo ta gidan mijinta,” ya ɗan yi murmushi mai rauni, “Amma Allah Ya fi mu sanin abin da yake mafi alheri a gare mu,” Abubakar ya sunkuyar da kai cikin sanyin jiki, “In Shaa Allah, Daddy,” Daddy ya matse hannunsa kaɗan, “Kuma Abubakar…” “Na’am, Daddy?” Ya kalli ɗansa cikin wata irin damuwa da ba ta bayyana sosai a fuskarsa ba, “Ka tuna, akwai wasu abubuwa da mutum ba ya iya faɗa cikin sauƙi, amma idan lokaci ya yi, dole ne a faɗe su,” Abubakar ya dago fuskarshi kaɗan, “Daddy, akwai wani abu da kake son ka gaya mana?” Alhaji Kabeeru ya yi shiru, ya kalli ɗansa na ƴan daƙiƙu, sannan ya sauke idanunsa, “Ba yanzu ba, ɗana,” Abubakar bai matsa masa ba, ya san halin da Daddy yake ciki, kuma bai son ya ƙara tayar masa da hankali, “Allah Ya ba ka lafiya, Daddy,” Daddy ya gyada kai, “Ameen,” Abubakar ya zauna kusa da shi na ɗan lokaci, yana yi masa hira a hankali kafin ya miƙe ya nufi ƙofar fita, amma kafin ya fita, ya sake juyowa ya kalli mahaifinsa, Daddy yana zaune shiru, idanunsa a kan tsohon album ɗin hotunan da ke gefen gadonsa, Abubakar ya tsaya na ɗan lokaci, sai ya fice a hankali, a ɗakin kuwa, Alhaji Kabeeru ya ɗauki album ɗin ya buɗe shi, hoton Inteesar tana ƙarama ya bayyana a gabansa, ya shafa hoton da yatsunsa, “Princess…” Ya furta cikin raɗa, “Allah Ya kiyaye min ke,” ya rufe idanunsa, yana addu’a a cikin zuciyarsa, domin duk da cewa bai faɗa wa kowa ba… akwai wani abu da yake son ya bayyana, wani abu da yake ta neman lokacin da ya dace domin faɗa, kuma a duk lokacin da yake kallon Inteesar, sai ya ji cewa lokacin nan yana ƙara kusantowa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol