Free chapter · Read without an account

THE MAN DADDY TRUSTED

by Jiddaah Barkum · KADDARAR ZUCIYA

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER SEVEN: 7*

*THE MAN DADDY TRUSTED*

*JIDDAAH BARKUM*

—————

SIX MONTHS AFTER AHMAD’S DEATH, ganin yadda Inteesar ta koma tamkar inuwar kanta tun bayan mutuwar Ahmad ya zame wa gidan Alhaji Kabeeru babban ciwon kai, ta daina walwala, dariyarta da ke cika gidan a da ta ɓace, kuma mafi yawan lokutanta tana shafe su ne cikin tunani da kaɗaici, the once cheerful Inteesar was no longer the same girl, a wasu lokutan ma, idan ana hira a gabanta, sai ta yi murmushi na dole kawai domin kada a lura da halin da take ciki, amma duk wanda ya san ta sosai zai fahimci cewa murmushin nata ba ya kaiwa idanunta, Yaya Umar, ɗaya daga cikin yayyenta da ke zaune a Abuja tare da matarsa, ya zo Katsina musamman domin duba halin da ake ciki, tun lokacin da ya shiga gidan, ya kasa ɓoye damuwarsa, ya ga yadda ƙanwarsa ta rame, ta yi shiru, ta rasa walwalarta, kuma har yanzu tana rayuwa cikin wani irin baƙin ciki da ya kasa barin zuciyarta, bayan ya zauna ya ɗan tattauna da iyayensu, sai ya nemi Alhaji Kabeeru a sirri, “Daddy,” Umar ya fara magana cikin girmamawa, fuskarsa cike da damuwa, “Ina ganin idan aka bar Inteesar a Katsina, abubuwan da suka faru ba za su gushe daga zuciyarta da wuri ba, kusan duk abin da ke cikin gidan nan yana tunasar da ita da Ahmad,” Alhaji Kabeeru ya ɗago kansa a hankali, yana sauraron ɗansa, Umar ya ɗan ja numfashi kafin ya ci gaba, “Me zai hana ta dawo Abuja wajena? At least, ta canza muhalli, ta samu sabon environment, sannan ta ci gaba da karatunta a jami’ar Nile University, ta fara Level Three ɗinta, ta samu abubuwan da za su ɗauke mata hankali, maybe, with time, Allah Ya sa ta saki ranta ta fara murmushi kamar da,” Alhaji Kabeeru ya yi shiru na ɗan lokaci, maganar Umar ta taɓa zuciyarsa sosai, ba ya son yin nesa da ƙwayar idonsa, musamman a wannan lokacin da yake ganin yadda take taɓewa a hankali a gabansa, a matsayinsa na uba, burinsa kawai shi ne ya ga ’yarsa ta dawo da walwalarta, amma a wani ɓangaren kuma, ya san cewa ci gaba da zama a Katsina na iya ƙara tsananta mata tunanin abubuwan da suka faru, ya sauke numfashi a hankali, “You may be right,” ya faɗa cikin murya mai ɗauke da rauni, “Maybe she needs a change of environment,” Umar ya gyada kai, “In Shaa Allah, Daddy, I’ll take good care of her, ba zan bari ta ji kamar ba ta da gida a can ba, she’s my sister, and I want to see her happy again,” Alhaji Kabeeru ya kalli ɗansa na wasu daƙiƙu kafin ya ɗan gyada kai, “Allah Ya taimake ka, Umar,” a wannan daren, Daddy ya kira Inteesar ɗakinsa, ta shigo cikin nutsuwa, sanye da doguwar riga mai sauƙi, fuskarta babu walƙiyar da aka saba gani a da, ta zauna kusa da shi lokacin da ya nuna mata wurin zama, Daddy ya kama hannunta cikin tausasawa, yana shafa bayan hannunta a hankali, “Inteesar, ɗiyata…” Ta ɗago idanunta ta kalle shi, “Na’am, Daddy,” ya yi murmushi a hankali, amma a cikin murmushin akwai damuwa mai yawa, “Ina so ki yi mini biyayya ki tafi Abuja, gidan Yayanki Umar,” Inteesar ta yi shiru, da farko, kamar ba ta fahimci abin da ya faɗa ba, sai ta ɗan juya fuskarta tana kallonsa, “Abuja, Daddy?” “Eh, ɗiyata,” ya matse hannunta a hankali, “Ba don ina son yin nesa da ke ba, a’a, you know you’re my little girl, and nothing will ever change that, amma ina so ki samu nutsuwa, ina so ki canza muhalli, ki ci gaba da karatunki, ki fara sabon abu da zai taimaka miki wajen mantawa da abin da ya wuce,” ya ɗan dakata, yana kallon fuskarta, “Ki koma can ki yi Level Three ɗinki a jami’ar Nile University, Yaya Umar zai kula da ke, kuma duk lokacin da kika ji kina son dawowa gida, gidan nan naki ne, no one is sending you away, my daughter,” a wannan karon, hawaye suka fara taruwa a idanun Inteesar, ba ta son barin Katsina, duk da cewa abubuwa da yawa suna tunasar da ita da Ahmad, nan ne gidanta, nan ne Daddy da Mommy suke, nan ne yayyenta suke, kuma ko da yake Ahmad ya tafi, wani ɓangare na zuciyarta yana jin kamar ta bar shi a baya idan ta bar garin, amma ta kalli mahaifinta, ta ga irin ƙaunar da ke cikin idanunsa, ta ga damuwar da yake ƙoƙarin ɓoyewa domin kada ya ƙara mata ciwo, ta kasa cewa a’a, a hankali ta gyada kai, “To, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya ja ta jikinsa, ya rungume ta sosai, “Allah Ya yi miki albarka, ɗiyata,” Inteesar ta lumshe idanunta, tana jin yadda hannayen mahaifinta suka kewaye ta, a wannan lokacin, ba ta buƙatar wata doguwar nasiha, ba ta buƙatar a gaya mata cewa komai zai daidaita, abin da take buƙata kawai shi ne ta samu damar yin kuka a hannun mutumin da ya kasance mafakata tun lokacin da nake ƙarama, bayan Daddy ya gama yi mata lallashin tafiya Abuja domin ta canza muhalli, ta koma ɗakinta, ta zauna a gefen gado, tana kallon akwatunan da aka riga aka shirya mata, a hankali ta miƙa hannu ta taɓa ɗaya daga cikin akwatunan, sannan ta sauke hannunta kamar ta tuna wani abu mai raɗaɗi, so this is it? I’m really leaving Katsina? Ta ɗago kanta ta kalli tagar ɗakinta, iskar daren Katsina tana kaɗawa a hankali, labulen tagar yana motsi lokaci-lokaci, ta yi shiru, amma tunaninta ya fara komawa watanni da suka shuɗe, watannin da suka gabata, lokacin da gidan Alhaji Kabeeru yake cike da dariya, annashuwa da farin ciki, lokacin da har yanzu tana da dalilin murmushi, lokacin da har yanzu tana da Heartbeat ɗinta, ta lumshe idanunta, sai waiwayen abubuwan da suka wuce ya fara bayyana a zuciyarta, (WA IWAYE) ruwan sama yana sauka a hankali a harabar gidan Alhaji Kabeeru, iskar yammacin ranar tana kaɗawa, tana girgiza rassan bishiyoyin da aka ƙawata da su a cikin katafaren gidan, ƙamshin ƙasa bayan ruwan sama ya mamaye ko’ina, yayin da giragizai masu duhu suka lulluɓe sararin samaniya, amma duk da yanayin ruwan sama, babban falon gidan yana cike da annashuwa, dariya ce ta mamaye wajen, “Wallahi, Mommy, ki gaya mata ta dawo min da wayata!” Khalil ya faɗa, yana ƙoƙarin ƙwace wata farar waya daga hannuna, na yi saurin komawa bayan kujera, ina riƙe wayar a hannuna, dariya ta ƙi barina, “Ba zan ba ka ba!” “Me ya sa?” “Saboda kai mugunta kake mini!” Khalil ya zaro ido, kamar na yi masa wani babban laifi, “Ni? Mugunta? Ke ce kika ɗauki wayata ba tare da izinina ba!” Na ƙara matsa wayar a ƙirjina, “So what? Ka kama ni mana!” “Ke dai yau za ki ga abin da zai same ki!” Na fashe da dariya, “Come and get it!” Dariya ta sake tashi a falon, Mommy Haleema ta girgiza kai, tana kallonmu da murmushin da ya nuna cewa ta saba da irin wannan hayaniyar tamu, “Ni dai ku biyu, Allah Ya shirye ku, wallahi, wani lokacin ina tunanin ko shekarunku sun tsaya ne a ƙuruciya,” na yi saurin juya mata, “Mommy, ni fa ba ni na fara ba!” Khalil ya nuna ni da yatsa, “Kin ji ta? Kullum ita ce innocent one karki saurareta ” na turo baki, Mommy ta yi dariya, ta girgiza kai, “Kai ne ba zan saurara ba, Khalil, ka bar ta da wayarka mana ba ta yayanta bace,” “Mommy!” “Ko kana so in kwace taka ma?” Nan take Khalil ya yi shiru, na fashe da dariya, har sai da na riƙe cikina, “Serve you right!” “Ke kuwa, Inteesar, sai kin ga ƙarshen wannan magana!” ya faɗa yana nuna ni, amma shi ma yana murmushi, a ɗayan gefen falon kuwa, Daddy yana zaune yana kallonmu, wani irin murmushi na nutsuwa ya kwanta a fuskarsa, murmushin mutumin da yake kallon farin cikin ’yarsa, mutumin da dukiya, matsayi da duk abin da yake mallaka ba su kai masa muhimmancin ganin Inteesar tana dariya ba, a gare shi, wannan hayaniyar tamu ni’ima ce, domin gidan da dariyar ’ya’ya ke cikinsa, gida ne mai rai, wayata ta yi ƙara a hannuna, na ɗan tsaya, na duba screen ɗin, Heartbeat Calling…, gabana ya yi wani irin bugawa, kamar yadda yake faruwa a duk lokacin da na ga sunansa a wayata, sai na ji wani irin farin ciki ya mamaye zuciyata, ba tare da na sani ba, murmushi ya bayyana a fuskata, Khalil ya lura, nan take ya ɗaga gira, “Toh, ga shi nan!” Na zaro ido, “Khalil!” Ya haɗe hannayensa a ƙirjinsa, yana kallona da murmushin wanda ya san ya gano wani sirri, “Duk lokacin da Ahmad ya kira, sai ki canza, kamar an saka miki sabon battery!” “Shut up!” Mommy Haleema ta yi dariya, “Ke dai je ki ɗauki wayarki, Angelic,” na juya mata da sauri, “Mommy!” Ta yi murmushi kawai, ban jira su sake cewa komai ba, na miƙe da sauri, na bar falon ina murmushi, yayin da dariyarsu ke biyo bayana har lokacin da na isa balcony, na tsaya na ɗan gyara hijab ɗina kafin na ɗaga wayar, “Assalamu Alaikum, Heartbeat,” muryarsa ta fito cikin sanyi, “Wa Alaikum Salaam, Angelic,” kamar kullum, muryarsa tana da wani irin tasiri a kaina, ko da ina cikin fushi, idan na ji muryarsa, sai na ji zuciyata tana samun nutsuwa, “Me kake yi?” na tambaye shi, ina jingina da jikin balcony, “Ke nake tunani,” na yi shiru, ya yi wata ƙaramar dariya, “Kullum sai ki yi shiru idan na faɗa miki gaskiya,” na yi murmushi ina kallon yadda ruwan sama yake sauka, “Saboda kana yawan faɗa,” “Saboda gaskiya ce,” “Hmm,” “See? Kin sake yin shiru,” na yi dariya, “Heartbeat, you talk too much,” “Really? Amma duk lokacin da na yi shiru, ke ce kike tambayata abin da ya faru,” na buɗe baki zan ba shi amsa, amma sai na kasa samun abin cewa, ya yi dariya, “Exactly,” na girgiza kai, duk da cewa ba ya ganina, “Yaushe za ka zo Katsina?” “Jibi, In Shaa Allah,” na ɗago kai da sauri, murmushi ya faɗaɗa a fuskata, “Da gaske?” “Da gaske, Angelic,” “Kar ka fasa fa,” “Me ya sa zan fasa?” “Just asking,” ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin murya mai cike da tabbaci, “Ko duniya za ta taru, ba zan fasa ganinki ba, In Shaa Allah,” wani irin nishaɗi ya mamaye zuciyata, na jingina da balcony ɗin, ina kallon ruwan sama, murmushi bai bar fuskata ba, ban san dalilin da ya sa duk lokacin da Ahmad yake magana nake jin kamar komai zai yi kyau ba, kamar duk wani abu mai wahala zai zama mai sauƙi muddin yana kusa da ni, he was my peace, mutumin da ko da ba ya kusa da ni, muryarsa kaɗai tana iya sa na manta da damuwata, na yi nisa a tunani, sai na ji ya kira sunana, “Inteesar,” “Na’am?” “Kin taɓa tunanin rayuwa bayan aure?” Na yi dariya, ina jin kunya duk da cewa ba ya ganina, “Kullum,” “To, ni ma,” na yi shiru ina jiran ya ci gaba, “Ina son gida mai cike da dariya,” ya faɗa a hankali, “Gida inda mutane za su zauna tare su ci abinci, su yi hira, su yi dariya, a place where everyone feels loved,” na yi murmushi, “Like our home?” “Exactly,” “Ina son yara,” na ɗan rufe idanuna, murmushi yana ƙara faɗaɗa a fuskata, “Nawa?” “Da yawa,” na buɗe ido da sauri, “Da yawa kuma? Heartbeat!” Ya fashe da dariya, “What? You don’t want children?” “Ina so, amma ba ka faɗi min yawan da kake nufi ba!” “Za mu tattauna da zarar mun yi aure,” na ji kunya, na sunkuyar da kaina duk da cewa yana can gefe guda na waya, “Ka yi shiru mana!” “Why? Kin fara jin kunya ne?” “Ahmad!” Ya sake yin dariya, dariyar da ta kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi sanyaya min zuciya a duniya, sai kuma muryarsa ta canza a hankali, ya yi shiru, shiru mai ɗan nauyi, wanda ya sa na cire murmushin da ke fuskata na ɗan daidaita tsayuwata, “Inteesar,” “Na’am?” “Ki yi min alkawari,” na ɗan daure fuska, “Wane alkawari kuma?” “Ko da wani abu ya taɓa faruwa…” Gabana ya faɗi, ban san dalilin da ya sa kalamansa suka sa na ji wani irin fargaba ba, na matsa wayar a kunnena sosai, ina ƙoƙarin fahimtar abin da yake nufi, “Me ya sa kake magana haka?” Ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya ce cikin wata murya mai laushi, “Answer me, Angelic,” na haɗiye yawu, “Heartbeat…” “Ki yi min alkawarin za ki ci gaba da rayuwa,” na ji zuciyata ta ɗan kaɗu, me yake nufi da hakan? Me ya sa yake tambayata irin wannan tambayar? Na yi saurin yin dariya domin in kore fargabar da ta fara tasowa a raina, “Ba zan yi irin wannan alkawarin ba,” “Me ya sa?” “Saboda babu inda za ka je,” shiru ya biyo baya, na tsaya ina kallon ruwan sama, ba tare da na san cewa waɗannan kalaman za su zama ɗaya daga cikin abubuwan da zan fi tunawa da su a rayuwata ba, sai na ji ya yi magana cikin murya mai cike da ƙauna, “In Shaa Allah,” ban sake tambayarsa komai ba, ban kuma san cewa wannan tattaunawar za ta kasance cikin abubuwan da za su riƙa dawowa min a zuciya a duk lokacin da na tuna da shi ba, ban san cewa wata rana zan tuna da wannan alkawarin ina kuka ba, ina fatan da ace lokaci zai dawo baya, ina fatan da ace zan iya komawa wannan ranar, in riƙe wayar da kyau, in saurari muryarsa na tsawon lokaci, in gaya masa abubuwan da ban taɓa tunanin zan rasa damar gaya masa ba, amma lokaci baya dawowa, kuma wasu alkawura… sai bayan an rasa mutum ake fahimtar dalilin da ya sa ya nemi a yi su, (WASU KWANAKI KAFIN HATSARIN AHMAD) ranar Asabar ce mai cike da annashuwa a gidan Alhaji Kabeeru, tun da sassafe gidan ya fara cika da hayaniya saboda baƙi da ’yan uwa da suka zo gaisuwa, kamar yadda suka saba duk ƙarshen mako, a irin gidan Daddy, ba a rasa mutane, wasu suna zuwa neman shawara, wasu neman taimako, wasu kuma saboda kawai suna son ganin fuskar mutumin da Allah Ya yi wa baiwar arziki da karamci, kowa yana samun kyakkyawar tarba a gidan, a babban falo kuwa, Daddy yana zaune tare da wasu manyan baƙinsa suna tattaunawa, Adam yana kusa da shi, yayin da Abubakar ke duba wasu takardu da aka kawo masa daga kamfani, ni kuma ina kitchen tare da Mommy Haleema, na ɗaure apron a jikina, ina ƙoƙarin nuna mata cewa na san abin da nake yi, duk da cewa ita kanta tana kallona da wani irin shakku, “Mommy, wai na ce miki yau zan yi girki da kaina,” ta ɗago kai daga abin da take yi, ta kalle ni na wasu daƙiƙu kafin ta girgiza kai, “Ke?” Na turo baki, “Eh, ni mana!” Ta yi murmushi, “To, Allah Ya kiyaye,” na zaro ido, “Mommy!” Ta fashe da dariya, “Me na faɗa? Ko na yi ƙarya ne? Ba ke ba ce wadda ta taɓa ƙona taliya saboda waya ta yi ƙara?” Na rufe idanuna saboda kunya, “Mommy, kin ce ba za ki sake tuna min da wannan abin ba!” “Ni na ce? Ai ba zan iya mantawa ba, har yanzu ina mamakin yadda kika iya ƙona taliya da ruwa a ciki,” “Mommy, please!” Ta ƙara dariya, ni kuma na ɗauki cokali na nuna mata, “Yau za ki ci abincin da na dafa ne, sai ki yi min rating,” “Rating?” “Eh mana, out of ten,” ta girgiza kai, tana murmushi, “To, bari mu gani, amma idan kin ƙona komai fa?” Na turo baki, “Mommy, you don’t believe in me!” Ta taɓa kumatuna cikin wasa, “Ina yarda da ke, ɗiyata, amma kitchen ɗin nan yana buƙatar addu’a,” na yi dariya, ita ma ta yi, a wannan lokacin, komai yana da sauƙi, ban san cewa akwai wasu ranakun da mutum zai tuna da su daga baya har zuciyarsa ta riƙa masa ciwo ba, kafin Mommy ta sake magana, sai muka ji muryar Khalil daga falo, “Ahmad ya zo!” Gabana ya yi wata irin bugawa, da sauri na ɗago kai, na manta da komai da ke gabana, Mommy Haleema ta lura da yadda fuskata ta canza, murmushi ya bayyana a fuskarta nan take, “Je ki gaishe da bakonki,” na juya mata da sauri, “Mommy!” Ta daga hannu tana kore ni, “Je mana, kafin ya tafi,” ban jira ta sake cewa komai ba, na juya da sauri na bar kitchen, zuciyata tana bugawa kamar zan yi tsere, da na isa falon, idanuna suka sauka kansa, sanye yake cikin farar shadda mai sauƙi, babu wata kwalliya ta musamman, amma a gare ni, duk lokacin da na gan shi, sai na ji kamar shi ne mutumin da ya fi kyau a duniya, ba don tufafinsa ba, ba don kuɗinsa ko matsayinsa ba, sai don yadda kasancewarsa take sa zuciyata ta ji daɗi, ya hango ni, murmushi ya bayyana a fuskarsa, murmushin da nake ganin sa a matsayin wani abu na musamman da yake da ni kaɗai, ni kuma na sunkuyar da kai kamar yadda na saba, “Assalamu Alaikum,” “Wa Alaikum Salaam,” muryarsa ta kasance cikin natsuwa, amma idanunsa suna kallona da wani irin kulawa da ya sa na kasa ɗaga kaina sosai, Daddy ya kalli mu, sai ya yi murmushin da ban gane ma’anarsa ba a lokacin, “Ahmad, zo ka zauna,” “To, Daddy,” Daddy, wannan sunan da Ahmad yake kiransa kenan, ba Alhaji ba, ba Sir ba, ba Alhaji Kabeeru ba, Daddy, kuma abin mamaki, Daddy ma yana son yadda yake kiransa da wannan sunan, bai taɓa nuna masa cewa ya wuce gona da iri ba, a maimakon haka, sai ya riƙa amsa masa da wani irin farin ciki da yake nuna cewa ya riga ya karɓe shi a zuciyarsa, Ahmad ya zauna kusa da shi, suka fara hira, ni kuma na zauna nesa kaɗan, ina sauraron tattaunawarsu yayin da nake ƙoƙarin kada na riƙa kallon Ahmad fiye da kima, da farko, maganar kasuwanci ce, sai Daddy ya tambaye shi, “Yaya shagon Kano?” Alamar mamaki ta bayyana a fuskata, Daddy ya san komai game da Ahmad, har harkokinsa da yadda kasuwancinsa yake tafiya, Ahmad ya gyara zamansa, sannan ya amsa cikin girmamawa, “Alhamdulillah, Daddy, Allah yana taimako,” Daddy ya gyada kai, “Na ji daɗi, Allah Ya ƙara albarka,” “Amin, Daddy,” sai Daddy ya yi shiru na ɗan lokaci, ya kalli Ahmad kai tsaye, sannan ya ce, “Wani abu nake so na gaya maka,” nan take hankalin mutanen da ke falon ya koma kansu, Adam ya ɗago kai daga wayarsa, Abubakar ya ajiye takardun da yake dubawa, ni kuma na daina tunanin komai na mai da hankalina ga Daddy, Ahmad ma ya gyara zamansa, “Ina sauraronka, Daddy,” Daddy ya ɗan jingina da kujera, yana kallon Ahmad da wata irin nutsuwa, “Na yi rayuwa mai tsawo,” kowa ya yi shiru, ya ci gaba da magana cikin natsuwa, “Na ga mutane iri-iri a rayuwata, na yi mu’amala da masu gaskiya, na kuma haɗu da waɗanda ba su da gaskiya, na koyi cewa mutum yana iya ɓoye abubuwa da yawa a fuskarsa,” ya ɗan nuna zuciyarsa, sannan ya ɗaga yatsansa zuwa idanunsa, “Amma idan ka yi shekaru da yawa a duniya, wani lokaci za ka iya gane mutumin kirki daga yadda yake mu’amala da mutane,” falon ya sake yin tsit, sai Daddy ya juya kansa ya kalli Ahmad kai tsaye, “Ni ina ganin kana daga cikin mutanen kirki,” wani irin yanayi ya mamaye falon, har Adam ya ɗago kai sosai, yana kallon Daddy, Abubakar ma ya daina kallon takardun hannunsa, yayin da Ahmad ya kasa magana na wasu daƙiƙu, na lura da yadda yanayin fuskarsa ya sauya, kamar bai yi tsammanin jin waɗannan kalaman daga bakin Daddy ba, ya haɗiye yawu a hankali kafin ya yi magana, “Na gode, Daddy,” muryarsa ta kasance cikin sanyin murya, amma a idanunsa akwai wani irin girmamawa da godiya da ya kasa ɓoyewa, Daddy ya gyada kai, sai kuma ya ƙara da cewa, “Inteesar amanata ce,” gabana ya buga, na ɗago kaina a hankali, ina kallon mahaifina, “Ina son duk wanda zai zo rayuwarta ya fahimci hakan, ba ni da abin da ya fi min muhimmanci kamar ganin ta cikin farin ciki, na raina ta, na kula da ita, kuma ina son duk wanda zai kasance a rayuwarta ya san darajarta,” Ahmad ya gyara zamansa, yana sauraron Daddy ba tare da ya katse shi ba, “Na fahimta, Daddy,” Daddy ya ɗan karkatar da kansa, “Ka fahimta da gaske?” Ahmad ya kalli Daddy da cikakkiyar nutsuwa, “Eh, Daddy, na fahimta, kuma zan kula da ita fiye da yadda nake kula da kaina, ba zan ɗauki amanarka a matsayin ƙaramin abu ba,” na ji zuciyata ta yi wani irin dumi, ba zan iya bayyana yadda na ji a wannan lokacin ba, wani ɓangare na zuciyata yana cike da farin ciki, wani kuma yana jin wani irin kunya saboda ana magana a kaina a gaban kowa, na sunkuyar da kai, ina wasa da yatsuna, sai na ji Khalil ya ɗan yi gyaran murya daga gefensa, kamar yana son yin magana amma ya yanke shawara ya yi shiru, Daddy ya kalli Ahmad na wasu daƙiƙu, sannan ya gyada kai a hankali, “Allah Ya tabbatar da alheri,” “Amin, Daddy,” Ahmad ya amsa, sai Daddy ya yi murmushi, “Allah Ya ba ku zaman lafiya da fahimtar juna,” “Amin,” muka amsa a hankali, ni kuma na ji kunya ta ƙara mamaye ni, a wannan ranar, na fahimci cewa Ahmad ya wuce matsayin baƙo a gidanmu, ya zama ɗan gida, mutumin da Daddy ya fara yarda da shi, mutumin da Mommy Haleema take yi wa addu’a, mutumin da yayyena suka karɓa da zuciya ɗaya, duk da irin zolayar da suke yi min a duk lokacin da ya kira, kuma mutumin da na fara ganin rayuwata gaba ɗaya tare da shi, na kalli Ahmad a hankali, yana murmushi, yana sauraron Daddy yayin da suke ci gaba da tattaunawa, a zuciyata kuwa, na fara tunanin irin rayuwar da za mu gina tare, gida mai cike da dariya, yara, zaman lafiya, soyayya, our own little world, amma wasu lokuta, Allah yana nuna mana farin ciki ne domin mu gode Masa, ba wai domin Ya yi mana alkawarin zai dawwama ba, a lokacin da nake zaune ina kallon Ahmad yana hira da Daddy cikin annashuwa, ban san cewa watanni kaɗan ne suka rage mana ba, ban san cewa wata rana zan yi kewar wannan muryar har ta zama kamar ciwon da ba ya da magani ba, ban san cewa wata rana zan riƙa tuna yadda yake zaune a wannan falon, ina fatan da ace zai sake shigowa ta ƙofar gidanmu, ban san cewa kujerar da yake zaune a kai za ta taɓa zama abin tunawa a gare ni ba, ban san cewa zan taɓa kallon mutane suna dariya a wannan gidan, ina mamakin yadda duniya ta ci gaba da tafiya duk da cewa tawa ta tsaya a ranar da ya tafi ba tare da ya dawo ba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol