Free chapter · Read without an account

Chapter 36

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

https://www.arewapen.com/book?id=6ab251c3cb0cfb2373811a7f
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
    
Chapter 36.
Nan take kanta ya sara da wani irin ƙarfi, wani hazo ya soma lulluɓe idanuwanta, kamar me lalube haka ta dinga  yawo da hannayenta, bakinta na buɗewa da zummar yin magana amma kuma maganar ta ƙi fitowa.
     "Daddy!!!!, Ahmad kama hannuna dan Allah, faɗuwa zan yi, kaina ciwo ya ke yi min please Ahmad ɗina." ta faɗa cikn karyewar zuciya.

"Mtwssss aikin banza." Daddy ya faɗi tare da wucewa ya kama hannuwan Afnan  ya nufi toilet da ita ya tunna mata tap yace ya yi alwala, sarai ya lura da kallon da yarinyar ke yi ma shi amma kuma ya share.
    "Daddy!." ta faɗa da sanyin murya tana riƙe rigar shi.
   Kallonta yayi baice komi ba.
   "Mommah bata da kirki ko Daddy! kuma ai bata son Anty Zunaina shiyasa ta ɓace na daina ganinta, kuma ita ce ta kulleni ni kaɗai jiya a room nayi kuka amma bata buɗe ni ba, Daddy  amma ai tace maka zata faɗi ka kamata, ka manta Anty Zunaina ta ce mu dinga yafiya."

Kalaman Afnan ne suka daskarar da wani abu a zuciyar shi, wani abu da yake ji yanada danganeda Zunainah, Zunainah yarinyar da ta taso tare da su, take bin dukanin umarninsu, take kuma biyayya agare su.
    Kwalla ce ta gangaro a idanuwan shi, nan take ya fice daga toilet ɗin, ko bi takan Mommah wacce ke yashe a ƙasa bai yi ba ya fice daga gidan gaba ɗaya.

***
MUJAHEED

Kallon fuskar matashin ya ke yi ƙurrrr babu ko ƙyaftawa, yayinda wani abu me nauyi ya narke a ƙasan zuciyar shi, wani fata na sake yunƙuro ma shi.

Tari yayi wanda ke tafe tare da jini guda-guda, da sauri Mujaheed ya tashi ya goge ma shi tare da furta.
   "Sannu Muhammad, zaka  samu lafiya soon."

Ɗago rinanu kuma jemamrun idanuwan shi Muhammad ya yi tare da kallon fuskar Muhammad, memories ɗin da suka shuɗe na gilma masa ta cikin kan shi.
    "Mujaheed!." Ya furta  sunan a hankali kamar me son tantancewa.

Mujaheed wanda daɗi ya baibaye shi jin cewa Muhammad ya gane shi ya murmusa tare da faɗin.
   "Kwarai kuwa Muhammad, ni ne Mujaheed yayan Zunaina ashe baka manta da ni ba?."
    Wani busashen murmushi Muhammad ya yi, yana jin ƙasan zuciyar shi na zugi da raɗaɗin rabuwarsa da Zunaina.
    "Taya bazan ganekanba ɗan Mommah."
   Muhammad ɗin ya faɗa wani tari haɗe da jini na taso manshi.
   Ɗan takune fuska Mujaheed ya yi jin abin da Muhammad ɗin ya ce, har ya buɗe baki da zummar yayi magana sai kuma ya rufe ya sake ɗaukar wata tissue ɗin ya goge ma shi jinin daya zibo.

   "Kana da zuciya me kyau, koba yanzu ba zanyi alfahari da wannan." Muhammad ya faɗa yana dafa kafaɗun Mujaheed da hannayensa masu kyarma.
    "Ka daina magana kaga kana zubda jini." Mujaheed ya faɗa tana kuma goge ma shi wani jinin daya zubo ma shi.
    "Ina da muhimmanaci har haka, ko dan ita ne wannan ɗin?." Ya kuma faɗa yana kaiwa kwance saboda jirin da yake ji.

"Ba saboda ita ba, saboda  Allah ne kuka saboda zuminci na ƴan uwantaka da musulinci ya haɗa."

Guntun murmushi Muhammad ya yi, sannan ya ce.
   "Baka tambaye ni ya take ba?."

Ras gaban Mujaheed ya yanke ya faɗi, wata iriyar fargaba ta baibaye shi, tun ɗazu yake kokowa da bakin shi kar ya tambayeta, ji yake kamar ya dakatar da Muhammad ɗin yace masa ba yanzu ba, yana jin kamar bai shiryawa hakan ba, sai de kafin yace wani abu tuni maganar Muhammad ɗin ta yi dirar mikiya a kunnuwan shi.

    "Wataƙila tana makamacin yanayin da nike, wataƙila kuma fiye da haka, amma dai ko yaya ne tana cikin hatsari, ina jin motsinta a can ƙarƙashin zuciyata alamar tana raye sai de bansaniba a ina, mi kuma ya faru, waye yanayine?." ya faɗa wani ƙaƙƙarfan tari na ƙwace ma shi, yayinda jini ya dinga bulbulowa daga bakin shi kamar an buɗe fanfo, lamarin daya sake kiɗimar da Mujaheed kenan.

   "Nooo! not now please Muhammad." ya faɗa da siffar roƙo kamar zai iya riƙe ran Muhammad ɗin ya hana shi fita a sanda Ubangiji ya ƙaddara hakan.

Wani irin wahalallen numfashin Muhammad ke saki, ga jinin da ke fitowa ta baki da hancin shi sai ƙara zubowa ya ke.
     A daburce Mujaheed ya danna ƙaraurawar shaida akwai matsala, cikin minta ɗaya norse da Doctor suka hallar, aka fitar da Muhajeed waje suka cigaba da aikin su.

Gaba ɗaya Mujaheed baya cikin nutsuwar shi in banda shesheka da zarya babu abin da yake yi ga zuciyar shi sai luguden duka take a ƙirjin shi kamar zata tsaga allon ƙirjinsa ta fito waje, tambayoyi ne fal zuciyar shi dake son sanin inda Zunaina ta ke da kuma abin da ya raba ta da Muhammad ɗin....

****
Rimsha
     Tsaye ta yi tana kalon wawakekiyar hanyar data samu da ɓula da dabara, tana tunanin aikata ƙudurinta cikin nasara ba tare da samun tangarɗa ko ba.
    A hankali ta shafi tabon yankar wuƙar da ke hannunta, wanda ya ɗauki tsarin shekaru ashirin da ƴan kai amma bai ɓace ba, idonta ya cika tab da kwalla a sanyaye ta ce.
   "Ka yi haƙuri yarona Junaid ban tafi na barka ba da son raina, ƙaddara da son zuciya ne suka saka rabani da kai, ka shirya gani nan zuwa gareka, ba gudu ba ja da baya, na roƙi Ubangiji ya ƙaddara saduwarmu, da alama ya amshi roƙona tunda har ya bani ikon fasa wannan ginin ba tare da azzalumai sun ganni ba, gani nan zuwa da izinin Ubangiji." ta faɗa tare da ɗaga ƙafarta ɗaya tana jeranto addu'o'i daga bakinta taci gaba da kawa sannu a hankali har saita da fice daga ɓular.
    Wata iriyar harbawa zuciyarta ta yi, ta zare duka girman idanuwanta tana kallon abin da ya gigita kwanya da tunaninta harya saka ta jin kamar ta juya ta koma da baya ta fasa tafiyar.
   Wani irin ƙungurmin baƙin daji ne, da alama babu wani mahaluƙi da ke rayuwa a cikinsa idan aka cire dabbobu masu tsoratarwa da kuma Aljannu.

Saide wani sashi mafi rinjaye daga zuciyarta na gargaɗarta akan komawa baya, gara ta fuskanci gaba koda ace zata mutu gara ta mutu a hannun namun daji, data mutu inda tasan za'a tsaface gawarta, da wannan tunanin ne ta soma takawa sannu a hankali idonta a rufe tunaninta na haska mata yaronta yaron da take kwana kuma take tashi da tunanin shi a can ƙasan zuciyarya.

Ta yi tafiya me tsayi sosai, wacce har saida gaɓɓan jikinta suka yi mata kafiya wajen cigaba da taimaka mata sannan ta nemi kan wani tudu da ciyayi suka firfito ta zauna a daddafe tana ƙarewa dajin me duhuwa kallo, gabanta na luguden suka....

   Hamzalul ne ya fito cika umarnin ɗan uwan shi, shigowar shi kenan baƙin dajin yayi tozali da ita, kan shi tsaye ya haske goshinta a nan ne yaga dukanin abubuwan da suka faru da rayuwarta, baiyi jinkiriba wajen saka hasken shi ya nisantata da wannan dajin me hatsari, sai da ya tabbatar da ta fita daga hatsari sannan ya yi abin da ya kai shi ya ɓace ta cikin iska zuwa can ƙasan teku....



MARYAM
Zaune ta ke a gefen hanya tana kallon tsirarun mutanen da ke wucewa da kuma ababen hawa, sam bata damu da kasancewarta a wajen ita ɗaya ba, kuma bata tsoron faruwar komi, domin kuwa tariga da tayi imanin da Allah zai tsareta adu inda take, tanada yaƙini akan yanda take kashe wuni tana ambarta sunayen shi tare da tsarkake shi da tazbihi, haka shima bazai manta da ita ba, zai tallafe ako ina take da shi kaɗai ta dogara a yanzu ta maida dukkanin lamuranta gare shi.
    Saka sirarran yatsun hannayenta ta yi ta soma zagaye zoben da ke a yatsarta ta tsakiya wanda ya zauna ɗas yana fitar da wani irin haske da walwali kamar fitila.
    Kallon zoben ta ke tana jin inama ace zata samu damar ganin me zoben a yanzu da tayi ma shi wata tambaya guda ɗaya dake cin zuciyarta, kuma data sanar da shi tsananin kewarsa da yake yi iya wannan wunin da tayi ba tare da shi ba.
   Kamar daga sama taji sautin shi cikin muryarsa ta tsofi da yake amfani da ita kafin tasan shi ɗin ko asalin waye.
    "Noorin kakanta, muna kewarki."
    Da sauri ta ɗaga zoben saitin fuskarta tana kallon yanda lokaci ɗaya ya ke sauya kala hasken shi na ƙaruwa.
    "Kaka." ta furta a takaice.
   "Aminci su tabbatar agareki baiwar Allah, yake Maryam kiyi sani cewa a ƴan mintocin da suka shuɗe bana tare da ke a duniyarku na yi kewarki fiye da misali."
   Kanzul ya faɗa siffar hasken shi na bayyana a tafukan hannayenta.
    "Ka dawo ka ɗauke ni mu koma duniyarku Kaka, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba, mutane basa da tausayi, ni wajenka nike son in zauna." ta faɗa da muryarta da take rawa alamar daf takr da fashewa da kuka.

    Wani sauti fa ji me cike da sanyi me haɗe da wani irin iska dake hurowa har inda take.
   "Kiyi haƙuri ki karɓi abin da rayuwa ta zo miki da shi, haƙiƙa halitarku ba zata iya rayuwa a inda muke ba kamar yanda muma muke cutuwa a yayin rayuwa tare da ku."
   Cikin katse shi ta ce. "Du tsanani zan jure rayuwa tare da kai nasan ba zaka bari wani abu ya cutar da ni ba, karka manta saboda ni kuka baro rayuwa da ƴan uwanku kuka rayu a duniyarmu, ni mi zai hana nayi tawa rayuwar a tare da ku."
   Murmushi ya yi irin nasu wanda har tsakiyar kanta sai da ta jishi sannan yace da ita.
    "Noor bamu sanki da musu ko gardama ba, Maryama me bin dukanin umarni da hukuncin da muka zartar  mata ne mi yasa zaki sauya a rana ɗaya."
    Saboda rayuwa a cikin mutane a kwai wahala, kasan abin da ya faru da ni kuwa yau, a ɗazu?."
   "Na sani kuma na gani karki damu haka wasu daga cikin ƴan Adam suke amma kuma ai kin samu wanda ya baki ruwan, kuma me yawa nima bara in ɗauki nawa rabon ai bakinsha ke kaɗaiba."
   Ya faɗa wasu daga cikin robobin ruwan na ɓacewa.

   "Karki damu ɗan uwana Hamzalul ya samo miki abokiyar rayuwa wacce ƙaddararku ta yi shige, tana nan zuwa gare ki, ki rungume hannu bibiyu ita ce zata haska ma ki hanya ta kuma daidai maki rayuwarki, kuma wannan ruhin daya mamaya da naki ruhin yana da kusanci me girma da ita, ki kula da kanki sai wani lokacin."  ya disashe bayan ya gama faɗa mata maganganun da suka ɗaure kanta tamau.
   

Daga can nesa sosai ta soma jiyo wani sauti, sauti ne me kama da na amai ko kakkarin yin aman.
   Da farko ta share kamar yanda ta ke ɗauke kai akan tarin abubuwanda ta gani yau da suka bata mamaki, amma daga baya sai ta kasa daurewa jin tsigar jikinta na tashi, ga nutsuwarta da tayi ƙaura daga gareta.
    Miƙewa tayi tsaye tare da soma taka ƙafafuwanta dake saye cikin takalmin fatar damisa masu laushi.
    Da hasken zobenta ta yi amfani wajen nausa wajen dake kama da gona ko juji, ta soma haskawa don son sanin daga inda sautin yake da kuma abin da ke kakarin......✍🏻

MARYAM STAR CE

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol