Free chapter · Read without an account

THE MAN DADDY TRUSTED II

by Jiddaah Barkum · KADDARAR ZUCIYA

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER EIGHT*

*THE MAN DADDY TRUSTED II*

*JIDDAAH BARKUM*

———

Yammacin ranar ya kasance mai cike da natsuwa, iskar harmattan tana kaɗawa a hankali cikin harabar gidan Alhaji Kabeeru, tana girgiza ganyayen bishiyoyin da suka ƙawata compound ɗin, wani irin sanyi ne ke ratsawa cikin iska, amma a zuciyata kuwa, akwai wani zazzafan tashin hankali da nake ƙoƙarin ɓoyewa, a babban falon gidan, Daddy yana zaune tare da Adam da Abubakar suna duba wasu takardu na kasuwanci, lokaci-lokaci, ɗaya daga cikinsu zai yi magana kan wani abu da ke cikin takardun, Daddy kuma ya ba da amsa cikin natsuwarsa ta kullum, Mommy Haleema tana zaune kusa da su tana gyaran wasu kayan da aka kawo daga Lagos, lokaci-lokaci tana ɗaga kai ta shiga hirar da suke yi, ni kuwa, ina zaune a gefe ina pretending kamar ina karanta wani handout na makaranta, amma gaskiyar magana? Babu ko kalma ɗaya da nake gani, idanuna suna kan takardar, amma hankalina yana wani wuri dabam, na ma karanta layi ɗaya har sau uku ba tare da na fahimci abin da aka rubuta ba, saboda zuciyata gaba ɗaya tana kan Ahmad, tun safe ya gaya min, “Angelic, yau ina da magana da Daddy,” tun daga lokacin, zuciyata take bugawa kamar wadda ta san wani babban abu yana shirin faruwa, what exactly does he want to tell Daddy? Shin abin da nake tunani ne? Shin yau ne zai faɗa wa Daddy abin da yake yawan yi min alƙawarin cewa zai faɗa masa? Na sauke numfashi a hankali, ina ƙoƙarin kwantar da hankalina, Inteesar, calm down, whatever it is, you’ll find out soon, kamar dai zuciyata tana jiran wata alama ce, ba zato ba tsammani, ƙarar horn ta tashi a harabar gidan, gabana ya faɗi, na ɗago kai da sauri, kusan handout ɗin ya zame daga hannuna, Khalil ne ya miƙe ya leƙa ta taga, da zarar ya ga motar, sai ya juya da murmushi, “Ahmad ya zo,” ya faɗa cikin wata murya mai ɗauke da ɗan tsokana, nan take zuciyata ta yi wani irin juyi, na ji wani daddadan farin ciki yana yaɗuwa a jikina, har na kasa hana murmushin da ya bayyana a fuskata, Mommy Haleema ta ɗago kai daga kayan da take gyarawa, da zarar ta hango yanayin fuskata, sai ta yi murmushi mai cike da fahimta, “Allah Ya shirya ki,” “Mommy!” Na faɗa a hankali, ina sunkuyar da kai saboda kunya, ta yi ƙaramar dariya, “Me na ce kuma? Ai ban ce komai ba,” Khalil ya yi murmushi yana kallona, “Wallahi, da zarar an ambaci sunan Ahmad, sai ka ga kamar an kunna wani light a fuskarki,” “Please, Khalil, just shut up!” Na faɗa ina ƙoƙarin haɗe fuska, amma hakan bai hana shi dariya ba, “Okay, madam, I don talk again,” ya ɗaga hannuwansa alamar ya miƙa wuya, sannan ya koma wurin zama, ban samu damar ƙara ce masa komai ba, domin a lokacin ne Ahmad ya shigo falon, sanye yake da wata haɗaɗɗiyar shadda mai launin cream wadda ta zauna a jikinsa cikin tsari, fuskarsa cike take da nutsuwa, kamar yadda na saba ganinsa, ya gaishe da kowa cikin ladabi da girmamawa, sannan ya tsaya a gaban Daddy, “Barka da yamma, Daddy,” “Barka da yamma, Ahmad, ya hanya?” “Lafiya lau, Alhamdulillah,” daga ƙarshe, idanunmu suka haɗu, ya yi min wani ɗan ƙaramin murmushi wanda ni kaɗai na san ma’anarsa, na ji zuciyata ta yi wani irin tsalle, sai na sunkuyar da kai da sauri, ina ƙoƙarin ɓoye murmushin da ya ƙi barin fuskata, ya Allah, why does he have to look at me like that? Daddy ya ɗan gyara zamansa, sannan ya nuna masa wurin zama, “Ahmad, zo ka zauna,” ya zauna cikin natsuwa, ya gyara zamansa, sannan ya ɗora hannayensa a kan cinyoyinsa, bayan ya zauna, sai falon ya yi tsit, ba irin shirun da ake yi idan babu abin cewa ba ne, a’a, wani irin shiru ne mai ɗauke da tsammani, kamar kowa ya fahimci cewa akwai wata magana mai muhimmanci da ke shirin gudana, Daddy ya ɗan dube shi na wasu daƙiƙu kafin ya yi magana, “Na lura yau kana da wata magana,” Ahmad ya yi murmushi kaɗan, sannan ya gyara zamansa, “Haka ne, Daddy, na zo ne domin neman izininka,” falon ya ƙara yin shiru, Adam ya ɗago kai daga takardun da yake dubawa, Abubakar kuma ya ajiye nasa a hankali, Mommy Haleema ma ta dakata da aikin hannunta, ta ɗago kai tana kallon Ahmad, ni kuwa, sai na ji kamar zuciyata ta manta yadda ake bugawa, Ahmad ya sauke numfashi a hankali, sannan ya ɗaga idanunsa ya kalli Daddy kai tsaye, “Daddy… ina son Inteesar,” ya Allah! Na ji kamar numfashina ya tsaya cak, ƙirjina ya matse, kunnuwana suka fara yin zafi, yayin da na sunkuyar da kaina sosai don kada wani ya lura da yanayin da nake ciki, ya faɗa, a ƙarshe, ya faɗa wa Daddy, Ahmad ya ci gaba da magana cikin nutsuwa, duk da cewa na lura da yadda ya haɗe hannayensa, alamar shi ma maganar ba ƙaramin abu ba ce a gare shi, “Na daɗe ina nazarin rayuwa da addu’a, Daddy, na yi tunani sosai kafin na yanke wannan shawarar, kuma a duk tsawon wannan lokacin, ban taɓa samun mace da ta kwantar min da hankali kamar Inteesar ba,” ya ɗan dakata, sannan ya ci gaba, “Ba don dukiyar gidan nan ba, ba don matsayinku ba, ba don abin da zan samu ta wurinta ba… sai don ita kanta, I love her for who she is,” hawaye suka fara taruwa a idanuna, na cije leɓena a hankali, ina ƙoƙarin hana su zubowa, amma duk yadda na yi, zuciyata ta ƙi yin shiru, he really means it, wannan ba magana ce ta soyayya da yake yi min a waya ba, ba alƙawari ba ne da zai yi min cikin dare idan muna hira, a gaban iyalina yake tsaye, yana bayyana abin da ke cikin zuciyarsa ba tare da ɓoye komai ba, Daddy ya daɗe bai ce komai ba, ya jingina da kujerarsa, yana kallon Ahmad da wani irin kallo mai zurfi, kamar yana ƙoƙarin fahimtar abin da ke cikin zuciyarsa, daga ƙarshe, ya ɗan gyara zama, sannan ya tambaye shi, “Idan na ba ka Inteesar, me za ka ba ni a madadinta?” Na ɗago kai kaɗan, zuciyata tana bugawa da sauri, Ahmad bai ɗauki lokaci mai tsawo yana tunani ba, ya yi murmushi, amma wannan karon murmushin ya fito ne daga wani wuri mai zurfi a zuciyarsa, “Rayuwata, Daddy,” falon ya yi tsit, har Adam ya ɗaga gira, yayin da Abubakar ya ɗan karkatar da kansa yana kallon Ahmad, Daddy ya jingina da kujerarsa, ya zuba masa ido na wasu daƙiƙu, sannan ya yi murmushi, “Rayuwarka kenan? Idan ta yi kuskure fa?” “Zan gyara,” “Idan ta fusata ka fa?” “Zan yi haƙuri,” “Idan ta sa ka kuka fa?” A wannan karon, Ahmad ya yi wata ƙaramar dariya, ya girgiza kansa a hankali, sannan ya amsa cikin wata murya mai cike da ƙauna, “Zan ɓoye kukana saboda kada ita ta yi kuka,” na kasa riƙe hawayena, sun zubo a hankali, ɗaya bayan ɗaya, yayin da na sunkuyar da kai ina murmushi cikin hawaye, ya Allah, wannan mutumin fa? Wannan ne mutumin da na zaɓa da zuciyata, mutumin da ko da yake bai riga ya zama mijina ba, tuni ya sa na fara ganin makomar rayuwata tare da shi, Daddy ya ɗan lumshe idanunsa, kamar amsar Ahmad ta taɓa wani wuri a zuciyarsa, lokacin da ya sake buɗe su, akwai wani irin natsuwa a fuskarsa, “Allah Ya sanya alheri, na amince,” na ɗago kai da sauri, he agreed, na kalli Mommy Haleema, wadda ta yi murmushi tana goge gefen idonta, Adam ya yi murmushi ya girgiza kansa, Abubakar kuma ya kalli Ahmad kamar yana son ya ce masa, you better keep your promise, young man, Daddy ya ci gaba da magana, “Wanda ya kula da amanata… Allah zai kula da shi,” Ahmad ya sunkuyar da kansa ƙasa, a karon farko tun lokacin da ya shigo falon, na ga yadda idanunsa suka cika da hawaye, “Na gode, Daddy,” muryarsa ta ɗan yi rauni, amma ya yi ƙoƙarin riƙe nutsuwarsa, Daddy ya ɗaga hannunsa ya yi masa addu’a, sauran iyalin suka amsa da Ameen, ni kuwa, na kasa yin komai sai murmushi ta cikin hawaye, a ranar, na ji kamar an buɗe min ƙofar sabuwar rayuwa, rayuwar da zan kasance tare da mutumin da nake so, ba tare da ɓoye soyayyarmu ko jiran ranar da zai zo ya nemi izinina daga wurin iyalina ba, amma ban sani ba… ban san cewa mutumin da ya tsaya a gaban Daddy ya ce zai ba shi rayuwarsa domin ni ba, shi ne zai fara tafiya ya bar ni ina rayuwa da tunaninsa kaɗai ba, ban san cewa wata rana, waɗannan kalaman za su koma abubuwan da zan riƙa tunawa ina kuka ba, domin a lokacin, ni kawai farin ciki nake ji, ban san cewa rayuwa tana iya ɗaukar abin da ta ba ka ba tare da ta nemi izininka ba, na tsaya a wajen gate har sai da baƙar Camry ɗinsa ta ɓace daga ganina gaba ɗaya, na daɗe ina kallon hanyar da ya bi, hannuwana a haɗe a gabana, yayin da iskar harmattan ke kaɗawa a hankali, ban san dalilin da ya sa zuciyata ta yi nauyi haka a ranar ba, ba sabon abu ba ne Ahmad ya zo Katsina ya koma Kano, ya saba zuwa, mu yi hira, sannan ya kama hanya ya koma harkokinsa, amma ranar… wani abu daban nake ji, kamar akwai wata murya a cikin zuciyata da take roƙona in hana shi tafiya, kada ya tafi, kada ya shiga motar, kada ya kama hanyar Kano, na girgiza kaina a hankali, ina ƙoƙarin kawar da wannan tunanin, what is wrong with me today? Na sauke numfashi, sannan na ɗan yi murmushi da kaina, wataƙila saboda farin cikin da nake ciki ne, wataƙila saboda yanzu na san cewa Ahmad ya nemi izinina daga wurin Daddy, kuma komai yana shirin zama kamar yadda muka daɗe muna fata, amma duk da haka, zuciyata ta ƙi samun nutsuwa, sai na ji muryar Daddy daga bayana, “Inteesar,” na juya a hankali, Daddy yana tsaye a ƙofar falon, hannunsa ɗaya a bayan ƙugunsa, yana kallona da irin wannan murmushin da kullum yake yi idan ya fahimci abin da ke zuciyata kafin ma in faɗa, “Ki shigo ciki mana,” na gyaɗa kai, “To, Daddy,” amma kafin in juya, sai na sake kallon hanyar da Ahmad ya bi, kamar ina fatan zai dawo, kamar ina fatan baƙar Camry ɗinsa za ta sake bayyana a can nesa, ya fito daga cikinta yana murmushi, sannan ya ce, “Angelic, na fasa tafiya yau, zan zauna da ke,” amma hakan bai faru ba, hanyar ta kasance babu kowa, na juyo a hankali, na shiga gidan ina jan ƙafafuna kamar zuciyata ta tsaya a wajen gate tare da shi, na shiga falon na tarar da Daddy yana zaune a kan sallayarsa, carbi a hannunsa, ya ɗago kai ya kalle ni, sannan ya ɗan matsa gefe yana nuna min wurin zama kusa da shi, “Zo nan, ’yata,” na ƙarasa na zauna a kusa da shi, ya zuba min ido na wasu daƙiƙu, sannan ya ɗan karkatar da kansa, “Kin yi kuka?” Na buɗe baki zan yi magana, amma sai na goge gefen idona da sauri, “A’a, Daddy,” ya ɗaga gira, “A’a?” Na girgiza kai, ina ƙoƙarin hana murmushin kunya da ke neman bayyana a fuskata, ya yi wata ƙaramar dariya, sannan ya ce, “Maza ba sa son ganin matansu suna kuka,” nan take na rufe fuskata da hannuwana, “Daddy!” Dariya ya yi, irin dariyar da take sa mutum ya manta da damuwarsa na ɗan lokaci, “Me na ce kuma? Ai gaskiya na faɗa,” na sauke hannuwana a hankali, ina kallonsa da wani irin murmushi mai haɗe da kunya, “Ka daina mana,” “To, na daina,” ya yi kamar zai koma ga carbin hannunsa, amma kafin ya yi hakan sai ya ƙara da cewa, “Ahmad yaro ne na kirki, kuma yana son ki da gaske,” murmushin da ke fuskata ya ɗan lafa, na kalli Daddy, ina son in fahimci abin da ke cikin zuciyarsa, ya ci gaba da jujjuya carbin hannunsa a hankali, “Ba kowa nake yaba wa ba, Inteesar kin san haka,” na gyaɗa kai, na san haka, kowa a gidanmu ya san haka, Daddy mutum ne mai lura da mutane, ba ya saurin yanke hukunci, kuma ba ya yawan yabon mutum saboda kawai yana son jin daɗinsa, idan ya amince da kai, to ya amince da kai ne daga zuciya, shi ya sa kalamansa suka ƙara tabbatar min da abin da na daɗe ina ji a zuciyata, Ahmad mutumin kirki ne, mutumin da zan iya miƙa masa makomata ba tare da tsoro ba, Daddy ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ɗaga hannunsa ya ɗan taɓa kaina cikin ƙauna, “Allah Ya tabbatar muku da alkhairi, ya sa aurenku ya zama sanadin farin ciki da kwanciyar hankali a gare ku duka,” “Ameen,” na amsa cikin murmushi, sannan na ɗan jingina da kafadarsa, Daddy ya shafa bayana a hankali, a lokacin, ban san cewa wannan addu’ar za ta zama ɗaya daga cikin addu’o’in ƙarshe da zai yi wa Ahmad ba, ban sani ba cewa wata rana, zan zauna ina tuna wannan lokacin, ina mamakin yadda rayuwa ta iya sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci, a lokacin, ina da fata, ina da mafarki, kuma ina da mutumin da nake tunanin zai kasance tare da ni har ƙarshen rayuwata, ban san cewa nan gaba kaɗan, zan fara koyon yadda ake rayuwa da zuciya mai ciwo ba, da dare ma, Ahmad ya sake kira, ina kwance a kan gadona, na jingina da matashin kai, wayata a hannuna, da zarar na ga sunansa ya bayyana a allon wayar, sai murmushi ya zame min ba tare da na shirya ba, Heartbeat Calling…, na ɗaga wayar nan take, “Hello, Heartbeat,” “Angelic,” muryarsa ta fito a hankali daga ɗayan gefen wayar, mai ɗauke da wannan sanyin da kullum yake sa ni jin kamar yana kusa da ni, “Har yanzu ba ki yi barci ba?” ya tambaya, na yi murmushi, ina kallon ceiling ɗin ɗakina, “Kai ma fa? Me ya sa ba ka yi barci ba?” “Saboda ina tunaninki,” na turo baki, duk da cewa ba ya ganina, “Kullum magana ɗaya, ba ka da wani sabon abu ne?” Ya yi dariya, “Sabon abu kuma? Bayan yau na samu amincewar Daddy, me kuma zan nema?” Na yi dariya cikin kunya, na juya gefe ina rungume da matashin kai, “Heartbeat, please,” “Me na yi?” “Ka daina magana haka,” “Ta yaya zan yi? My fiancée is shy,” na buɗe baki ina son in mayar masa da magana, amma sai na kasa, na ji fuskata ta yi zafi, na runtse idanuna ina murmushi, this man will be the death of me, mun yi ƴan mintuna muna wasa da juna kamar yadda muka saba, har sai da muryarsa ta sauya, ya yi shiru, ba irin shirun da yake yi idan yana tunanin abin da zai faɗa ba, wannan karon, akwai wani abu mai nauyi a cikinsa, “Inteesar,” na daina murmushin da nake yi, “Na’am, Heartbeat?” Ya yi shiru na ɗan lokaci, “Ki sani…” Ya dakata, kamar yana neman kalmomin da suka dace, sai ya ce a hankali, “Ina son ki sosai,” zuciyata ta yi wani irin bugawa, na lumshe idanuna, ina jin kalamansa suna ratsawa ta cikin zuciyata, na saba jin yana gaya min yana sona, sau da yawa yakan faɗa min haka har na saba mayar masa da wasa, amma a wannan daren… ban san dalilin da ya sa kalmar ta bambanta da sauran ranaku ba, kamar yana faɗa min wani abu da nake buƙatar riƙewa a zuciyata, kamar yau ne karon farko da ya faɗa, kamar yau ne kuma karo na ƙarshe, na yi murmushi a hankali, na matse wayar a kunnena, “Nima, Heartbeat,” ya sauke numfashi, “Jibi zan dawo, zan je Malumfashi in ƙarasa wani abu, amma wajenki zan fara zuwa, daga nan kuma, ba zan sake zuwa ba sai bayan na dawo da magabatana wajen Daddy domin a karɓa min auranki,” murmushi mai faɗi ya bayyana a fuskata, “Da gaske?” “Da gaske, Angelic, na gaji da jira, ina so komai ya zama a hukumance,” na rungume matashin kai sosai, ina jin wani irin farin ciki da ya kusan hana ni magana, “Allah Ya kai mu,” “Ameen, Allah Ya sa mu dace,” na ɗan yi shiru, sannan na ce cikin wasa, “To, yanzu ka kwanta, ka gaji saboda tafiyar hanyar da ka yi,” ya yi dariya a hankali, “Ni kika damu da shi kenan?” “Eh mana, ko ba ka gaji ba?” “Na gaji kaɗan, amma yanzu da na ji muryarki, na samu ƙarfi,” na girgiza kaina ina murmushi, “Lallai kai ma kana da baki,” “Baki ne na gaskiya, Angelic,” na yi dariya, sannan na ce, “To, sai da safe, ka kwanta ka huta sosai,” ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya amsa, “Ina son ki, kin ji?” Murmushina ya lafa, zuciyata ta cika da wani irin daddadan yanayi, “Nima haka, ina son ka,” “Good night, my love,” “Good night, Heartbeat,” na kashe wayar, sannan na ɗora ta a kan bedside table, na kwanta ina murmushi, zuciyata cike da tunanin ranar da za mu zama miji da mata, a raina, na fara tunanin yadda zan ji idan na gan shi sanye da shaddarsa a ranar da zai zo da magabatansa, na yi tunanin yadda Mommy Haleema za ta yi murna, yadda Khalil zai yi min tsokana, da yadda Daddy zai yi addu’a a ranar da zai ba ni auren Ahmad, ban san cewa waɗannan mafarkan za su kasance cikin abubuwan da zan riƙa tunawa ina kuka ba, ban san cewa wasu lokuta, mutum yana iya yin barci cikin farin ciki, amma ya farka cikin wata sabuwar rayuwa da bai taɓa shiryawa ba, a wannan daren, na yi barci da murmushi a fuskata, saboda a raina, kwanaki biyu ne kawai suka rage kafin in sake ganinsa, ban san cewa zan sake ganinsa ba… amma ba yadda na yi tsammani ba, DAYS OF LOVE, YEARS OF SILENCE (Bayan Kwanaki Biyu — Ranar Hatsarin) a ranar da Ahmad ya ce zai zo, ya zo, shi ne zuwan da ya kawo min kyaututtuka cikin wani babban box, yana murmushi yana min alƙawarin makoma mai cike da farin ciki, amma ban sani ba cewa zuwan nan shi ne zuwan da zai bar min kyaututtuka da tunawa kawai, ban sani ba cewa ranar da ya tafi, tana nan a matsayin ranar da na gan shi a karo na ƙarshe, domin bayan tafiyar nan… ban sake ganin Ahmad ba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol