Free chapter · Read without an account
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
WASHEGARI DA safe aka shiga da Zaid a OT za'a yi fixing ribs ɗin shi da suka samu fracture. Abba yana zaune waje a waiting area. Muhammad yana tsaye ya kasa zama damuwa na nunawa a fuskar shi ya zama very quiet fuskar shi tayi sullen. Ina tsaye na ɗaura jikina a bango harda kaina bana iya zama. Wannan feeling na tsoro na tattare dani. Ina jin tsoron abinda ze je ya dawo. Ina jin tsoron rashi. Kun san yadda mutum ke jin tsoro idan yana tunanin ze rasa wani masoyin shi? Zuciyar ka ce take zama very quiet ga mutanen waje amma a ciki, kai kasan irin dukan da take ka rasa dukkanin natsuwar ka koda ana ganin ka natsu.
Muhammad ne yayi waya tukunna ya fita. Ba da jimawa ba se gashi ya dawo tare da Mummy da Yaya Hauwa.
Tun lokacin da Yaya Hauwa ta faɗa min maganganu bamu ƙara haɗuwa ba se yau. Nasan na gaida ta a yanzu da na ganta ko bayan irin abubuwan da suke min yawo a cikin zuciya kuma nasan ta ji gaisuwar da na mata amma kuma bata amsa ni ba. Ko kallo bata sparing min ba. Munyi magana da Mummy har take ce min ya jikin shi na amsa mata da sauƙi. Ita da Yaya Hauwa suka samu wuri su biyu a wuri ɗaya suka zauna ba gefen Abba ba.
“Hadiza” Abba ya faɗa. Idanuna na maida a wurin shi nace “Abba?” cikin muryar da bata fitowa sosai.
“Tsayin nan be ishe ki ba? Taho nan kusa dani ki zauna” ya faɗa min tare da nuna kusa dashi. Dawowa wurin shi nayi a gefen shi na zauna se na ɗaura kaina akan laps ɗina. Kamar wacce dama jira take a mata magana ta fitar da wani abu da take riƙewa na fara kuka.
“Subhanallah Hadiza!” Abba yace cikin rashin jin daɗi “Ba kuka zaki yi ba, Hadiza. Yanzu se kiga an mishi aikin nan successfully. Dan Allah ki dena kuka ki mishi addu'a”
Kasa shiru nayi duk da inason kuka na ya tsaya bana son yin shi a gaban mutane. Hannun Abba naji a kafaɗa ta kamar yadda mahaifina ze min idan ina cikin damuwa “Kiyi haƙuri, Hadiza, kinji?” Abba yace, se nake ganin kamar yana bani haƙurin rashin Zaid da zanyi ne “Ki yiwa Zaid addu'a Allah ya fito dashi lafiya. Shima ba ze ji daɗi ba idan yasan kuka kike yi”
Gyaɗa mishi kai nayi ina ƙoƙarin dena kuka. Hannun shi ya cire a kafaɗa ta yace “Ko zaki koma masaukin mu har a fito dashi ki dawo?”
Da sauri na girgiza kaina. Nafi so ina nan insan duk abinda ze faruwa na gani da idona da ace na koma hotel zuciya ta da dukkanin tunanina ya dawo nan bani da sukuni.
Bayan har na dena kuka hawaye basu dena fito min a idanu ba. Ban ɗago kaina daga laps ɗina ba ina jiran doctor ya fito yace an gama aikin da ake yiwa Zaid kuma successful.
Ji nake jiran da muke is getting long and long and long. Zan iya cewa ban taɓa jira irin wannan ba, da zuciya ta me duka tana son sauke wani relief da take ɗauke dashi tare da tsoro.
Muna nan zaune a waiting area muna jiran a fito a faɗa mana halin da ake ciki. Ƙofar OT aka buɗe, likitan Zaid ya fito. He looks a little tired Abba ya tashi tsaye suna tafiya in the direction of each other. Ban tashi tsaye ba ina zaune akan kujerar da nake na sunkuyar da kaina ina jiran sauraren the inevitable. Ina jin yadda zuciya ta ta zama calm ta dena duka kamar ta tsaya da bugawa.
“Weldone, Doctor. How was the surgery?” Abba yace muryar shi bata ɗauke da damuwa
“It was successful Sir” ya amsa
Rufe idanuna nayi se ga hawaye sun fara zubowa ina jin sassauci a cikin zuciyata haɗi da wani relief wanda yake da wahalar misaltawa.
“Alhamdulillah! Can we see him?”
“Yes, but you have to wait for some minutes. He's still unconscious tho”
“When will he wake up?”
“Soon, Sir. Soon. His wife or anyone of you should keep on talking to him anytime you go to see him”
“We will. Thank you Doctor”
Daga haka, likitan ya wuce.
Dawowa Abba yayi ya zauna gefe na. Abu na farko da Abba yace shine “Hadiza kukan ya isa mana. Ba ki ji yace aikin Zaid ya zama successful ba? Kuma in sha Allah ze farka”
Nodding mishi kaina nayi, nayi ƙoƙari na na dena kuka tare da ɗago kaina. Wasu hawaye ne suka ƙara zubo min, nasa hannuna na goge.
Bayan sun gama shirye-shiryen su aka sake komawa da Zaid a ICU. Anan ne aka fara shiga ana duba Zaid. Fitowar Yaya Hauwa daga ɗakin ta min wani irin kallo tana nuna ni ce sanadiyyar duk wani abu da ya faru da Zaid.
A ICU na shiga, ko yanzu babu wani abu wanda yake motsi a jikin Zaid se numfashin da yake da taimakon oxygen. Fuskar shi tayi haske, hannuwan shi su ma sun yi haske sun zama wani iri kamar wanda yayi sati ɗaya baya amfani dasu. Kallon shi nake ko magana bana iya yi jikina duk ya saki ina gane ba aikin ba, Zaid de ya tashi shi. Fitowa nayi daga ciki bana so na tsaya na cigaba da kallon Zaid a yadda yake.
Gabaɗayan mu hotel muka wuce Abba yace mu huta mu ci abinci ayi sallah tukuna wasu su koma.
Na jima a ɗakina kafin na shiga banɗaki nayi wanka. Bayan na fito na shirya, abinci na na cikin ɗakin amma ba zan iya ci ba. Ruwan Lipton na haɗa na sha ina jiran ace na fito mu tafi inda Zaid.
Ina ta jiran su basu ce a fito ba. Ji nake kamar na tashi na wuce da kaina tunda nasan wuri amma nasan haka ba ze yiwu ba. Komai abinda nake ji, waɗannan ƴan uwan shi ne na jini kuma sun san shi kafin ni na san shi.
A waya Muhammad ya kira ni yace na fito mu tafi. Tashi nayi na fito muka wuce. Daga ni se Yaya Hauwa zamu koma tare da Muhammad. A cikin mota babu wanda yace wani abu har muka isa asibiti.
Bayan mun isa asibitin, Muhammad ya fara shiga ya ƙara duba Zaid kafin ya fito yace mana ze je ya dawo. Bata shiga inda Zaid ba yasa nima nayi tsaye ban shiga ba. Bana so nayi wani abu wanda ze sa tayi magana saboda nasan duk maganar da zata min yanzu, ba zan ji daɗin ta ba. Idanuna na sunkuye ta shiga inda yake kwance.
Yaya Hauwa kallon Zaid take tunda ta shiga ɗakin har ta kawo daidai wurin shi. Mamakin ta na farko wanda take ciki shine Zaid ne kwance akan gadon asibiti be ma san inda yake ba kuma be san abinda yake faruwa dashi ba kuma baya cikin hankalin shi.
“Ƙanin Hauwa” Yaya Hauwa tace tare da kai hannun ta a nashi “Bani da wani wanda ya kai ka duk faɗin duniyar nan, Zaid. Idan ka tafi haka Zaid, me kake so na riƙe? What will I hold onto Zaid?” fuskar shi ta shafa da hannun ta daidai goshin shi. “Wannan shine ƙaddarar ka, Zaid” ta faɗa tayi murmushi me zafi tana son cewa ka rabu da wannan mata taka saboda ba abokiyar zama ce ba amma bata so tayi wata magana wacce zata fama mishi ciwon da yake ciki. Bata so ta bashi umarnin sakin Hadiza amma ita ta yankewa rayuwar ta bata ra'ayin Hadiza kuma bata son zaman da Zaid yake da ita duk saboda dalilin abinda tayi wa Zaid. Itace ma silar wannan abu da ya faru dashi. Yaya Hauwa ta sani.
“Mamanmu ta bar ni da kai kana ɗan shekara biyu, Zaid. A hannuna ka girma. Nasan komai naka. Nasan farin cikinka na kuma san duk wani abu wanda ze dame ka kuma bana son wani abu ya dame ka amma bani da iko akan wasu abubuwa na rayuwar ka saboda shi ciwo, wani abu ne daban wanda kowa ze ɗauke nashi. Ba wani mahaluki da ze bawa wani burden nashi, we all have to carry our burden, Zaid. Ina so ka dawo mu cigaba da zama tare da juna mu cigaba da zumuntar mu wacce Allah ne ya haɗa mana ita. Bani da wani kamar ka Zaid. Zaid ƙanin Hauwa. Allah ya baka lafiya ya tada mana kai a cikinmu”
Yaya Hauwa ta jima sosai a cikin ɗakin, Zaid harda yatsun shi ya motsa. Daga nan kuma be ƙara motsa komai ba. Tashi tayi ta fito ta zauna duk abubuwa sun dame rayuwar ta sun ishe ta.
Tsaye nayi ko bayan ta fito ban shiga ba. Akan irin damuwar da nake ciki akan halin da Zaid yake ciki, ji nake kamar a dawo da hannun agogo baya na ban taɓa sanin Zaid ba, rayuwar mu bata taɓa haɗuwa ba.
Shiga ɗakin Zaid nayi. Yanzu ma ba zan iya mishi magana ba saboda ban san abinda zan cewa Zaid ba.
Hannuna nasa a cikin nashi amma Zaid be ma san abinda yake faruwa ba bale ya kama hannuna a cikin nashi. So nake na ɗaura mishi jikina a nashi flatly naji warmth na jikin shi amma kuma haka ba ze yiwu ba. Goshina na haɗa da nashi. Hawayen dake cikin idanuna suka zubo akan fuskar shi. Ban ɗauke goshina a nashi ba ina jin yadda zuciyata ke duka da sauri. Hannuna na haɗe da nashi na riƙe nayi intertwining yatsun mu ina jin yanda ni ce kaɗai nake sa ƙarfi babu wani ƙoƙari a wurin Zaid. Na ɗan jima haka dashi ina sauke mishi dukan da zuciyata ke yi as tears continue cascading down my cheeks. Goshin shi nayi pecking nace “I love you, Zaid. All of these beats you heard my heart beating, my heart is beating for you and it'll never stop beating for you and only you. Get well soon my good man, my dear Zaid.” Ƙara pecking forehead nashi nayi na fito.
Ina jin idanun Yaya Hauwa akaina. Hawayen da suke idona bana so su zuba amma gasu se zuba suke sun ƙi denawa.
“Ban taɓa ganin mace me kamar irin ki ba. Kukan mene kike yi? Na munafurci? Saboda duk abinda ya faru da Zaid, da wani abu da ze faru dashi nan gaba marar kyau, kece sila kuma kece zaki zama sila. Na kasa gane abinda yake dake har yanzu a gidanshi. Be sake ki ba kuma be ce ki tafi gida ba se ya neme ki. Na kasa gane wannan wace irin jarabar banzar soyayya ce yake miki. To me amfanin yiwa irin ki wannan soyayyar? Dake da masu kisan mutane basu da bambanci ai. You're a serial killer, Hadiza. Kuma da kika gama da babyn shi biyu da suka zauna a mahaifar ki, shine yanzu kika dawo kan shi ko? Listen then and listen well. Duk wani abu ya faru da Zaid a wurin recoveryn shi ko bayan recoveryn shi, wanda ze nuna tawaya a yadda yake ko kuma wannan abun da ya faru dashi yayi sanadiyar mutuwar shi, wallahi Shari'a ce zata raba mu dake. Zan yi amfani da duk wani abu da na mallaka a duniyar nan domin ki fuskanci abinda kika aikata. It'll serve as a deterrent to any woman that has similar behaviors as you, Hadiza. So when you pray, pray hard that Zaid gets well and healthy” Yaya Hauwa na gama magana hawaye suka biyo a idanun ta zuwa kuncin ta. Hannun ta tasa ta share, wasu hawayen basu ƙara zubowa ba.
Fita nayi daga wurin duka na samu wuri away from people na zauna. Itace ne shukoki a wurin da nake zaune. Iska yana kaɗawa ahankali duhu na sauka. Kaina na ɗaga ina kallon taurarin dake sama da wata da yake ya kai rabi. Ba ina tsoron ayi Shari'a dani akan wani abu da ze faruwa da Zaid ba, saboda ma idan babu Zaid yanzu, Ya zanyi rayuwa? Se yafiye min tayi Shari'a dani idan babu Zaid da na zauna laifi ya gama cin rayuwa ta. Amma meyasa zata yi irin wannan magana? Ko tana tunanin Zaid ba ze tashi ba? Hannu na kai a wurin zuciya ta na shafa saboda irin abinda nake ji. Kaina na ɗaura a kusa da ginin da nake, wayata dake hannuna nayi dialling number Abba na. Ringing ɗaya biyu zuwa na uku ya ɗauka.
“Abba” na kira shi yadda nake kiran shi “Abba Zaid bayi da lafiya yau kwana biyu ko magana baya iya yi be san inda yake ba, Abba” daga nan se kuka
“Subhanallah Hadiza! Subhanallah, ashsha” Abba na ya faɗa “Dena kuka. Share hawayen ki, dena kuka Hadiza”
“Abba baka gan shi bane ba, Abba. Baya magana baya motsi. Abba, Zaid baya iya numfashi da kanshi se da taimakon oxygen. Ban san ya zanyi ba. Ji nake kamar likitocin nan are not giving us their best. I'm so sad and angry. I want Zaid to wake up. I just want him to live. And what if he leaves, Abba?”
“Ashsha Hadiza! Ki dena magana irin haka mana. Zaid ze tashi ki cire kanki a cikin damuwa. Ze tashi ku cigaba da zaman ku. Ki mishi addu'a kuma ki cigaba da mishi addu'a in sha Allah Zaid ze samu sauki. Yanzu kuna Abuja? Wane asibiti kuke?”
“A Port Harcourt. Muna asibitin koyarwa na Port Harcourt”
“In Sha Allah gobe zamu shigo mu duba ku kinji? Ki tashi idan kina da dama kiyi raka'a biyu Allah ya bashi lafiya. Allah yana sauraron ki”
Gyaɗa kai nayi yace “Ki dena kuka ya isa. Ciwon kai kawai zaki jawowa kanki. Allah ya bashi lafiya”
“Amin Abba. Nagode”
Gobe da safe Abba na da Umma suka taho har Port Harcourt duba Zaid. Abba yana bani baki akan Zaid ze samu lafiya kar na damu. Basu wuce ba se ƙarfe biyar Abban su Zaid ya musu rakiya har airport.
Kwana biyu Zaid yana motsa yatsun hannuwan shi. Abokanan Abba da ƴan uwan su sun zo duba shi da abokanan aikin Zaid. Naga ƙoƙarin duk wanda ya taho daga ko ina ne har Port Harcourt zuwa duban Zaid.
Zaid ya fara buɗe idanun shi. Abban su na tare dashi lokacin da ya fara buɗe idanun nashi. Ya gane Abba. Zaid ya gane duk wani wanda yake tare dashi. Se de ana magana dashi kuma ze zama confused ko ya fara bacci. Da muka yiwa likitan shi magana akai, yace it happens and it'll stop eventually he just needs some rest. Aka chanjawa Zaid ɗaki. Anan ne hankali na ya fara dawowa jikina.
Wata magana bata haɗa ni dashi se de kallo. Yaya Hauwa kuma suna jimawa suna magana dashi. Da ya fara samun sauki ana ganin improvement sosai a tattare dashi, Abba yace yana so a dawo dashi Abuja a Cedacrest.