Free chapter · Read without an account

Chapter 4: The girl who tested his patience

by Hauwa Jibrin Sulaiman · FADIANA

Bayan kamar mintuna ashirin da tashin jirgin, sai wata flight attendant ta fara sanar da fasinjoji cewa za a fara raba musu abincin. Wasu daga cikin fasinjojin da suke bacci suka fara farkawa, yayin da wasu kuma suka ajiye wayoyinsu suna jiran a kawo musu


Ba da daɗewa ba, wasu ma’aikatan jirgin sanye da uniform masu kyau suka fara tura trolley ɗin abinci a tsakiyar hanyar da ke tsakanin kujerun. Ɗaya daga cikinsu tana tambayar fasinjoji irin abin da suke so, yayin da ɗayar take rarraba abincin a kan trays tare da murmushi a fuskanta


“Chicken or beef, sir?”


“Chicken” Rayyan ya amsa a taƙaice ba tare da ya ɗago kansa bat


“Chicken, please,” Rahama ma ta faɗa, tana murmushi ga matar da ta kawo mata abincin


“Enjoy your meal,” matar ta faɗa kafin ta wuce zuwa ga fasinjojin da ke bayansu


Rahama ta gyara zama, tana kallon tray ɗin abincinta cike da sha’awa. Tun da safe take mafarkin lokacin da za ta samu ta zauna cikin nutsuwa ta ci abinci, kuma yanzu ga shi ta samu. Ta ɗauki cokali, ta ɗanɗana abincin, sannan ta jinjina kai cikin gamsuwa


“Hmm, not bad at all” ta faɗa a hankali


Rayyan ya juyo ya kalle ta da gefen ido, sai dai bai ce komai ba. Ya buɗe nasa abincin, ya fara ci cikin nutsuwa, yana kallon wayarsa lokaci-lokaci


Rahama kuwa, bayan ta ɗan ci, sai ta lura da tissue da  aka ajiye a gefen trolley ɗin da ma’aikaciyar jirgin take amfani da shi wajen rarraba abubuwa. Ta miƙa hannunta domin ta ɗauka, unfortunately a daidai lokacin ne hannunta ya taɓa gefen tray ɗin Rayyan


Komai ya faru ne within secs, tray ɗin ya karkata, abincin da ke ciki ya zube


Miyar abincin ta watsu a kan farar shirt ɗin Rayyan, ta bazu daga kirjinsa har zuwa ƙasan cikinsa


Rahama ta daskare nan take


Cokalin da ke hannunta ya zame, idanunta ta zaro kamar wadda ta ga wani abu da ba ta taɓa tsammanin gani ba. Ta sauke idanunta daga kan abincin da ya zube zuwa kan shirt ɗin, sannan ta ɗago ta kalli fuskar Rayyan


Ya Allah!


Ba ta ma san abin da ya fi firgita ta ba, zubewar abincin ko kuma yanayin fuskar mutumin da ke zaune kusa da ita


Rayyan ya yi tsit na ɗan lokaci, ya kalli shirt ɗinsa ya kalli tray ɗin


Sannan a hankali ya ɗago kansa ya kalli Rahama “ARE YOU FUCKING SERIOUS RIGHT NOW?”


Muryarsa ta fito da ƙarfi har wasu fasinjojin da ke kujerun gaba suka juya suna kallonsu


Rahama ta firgita matuƙa. Zuciyarta ta bugawa da sauri, hannunta ya yi sanyi, ta kasa ko motsa baki ta ce uffan. Wannan karon, ba kamar karo na farko da suka haɗu ba ne da ta iya mayar masa da magana. A yanzu ta ga ainihin fushinsa, kuma yadda ya yi maganar ya sa ta ji kamar an zuba mata ruwan sanyi a jiki ne


Ma’aikaciyar jirgin da ta kawo musu abincin ta yi saurin dawowa


“I’m so sorry, sir. She didn’t mean to do that. It was an accident,” ta faɗa, tana neman tissue a cikin trolley ɗin


“An accident?” Rayyan ya maimaita, yana nuna kirjinsa da hannu “ki kalla fah! Just look at what she has done to my shirt!”


“I’m really sorry, sir. Let me help you clean it up”


Ta miƙa masa tissue, sannan ta yi ƙoƙarin taimaka masa ya goge rigar, amma ya ɗaga hannu ya dakatar da ita


“Don’t! Just give me some space”


Ya janye jikinsa daga hannunta, sannan ya miƙe da sauri, yana kallon rigarsa cike da takaici


Rahama ta buɗe baki a hankali “I… I’m sorry”


Amma muryarta ta yi ƙasa sosai har sai da ita kanta ta kusa kasa jin abin da ta faɗa da kanta


Rayyan ya juyo ya kalle ta “You’re sorry?” Ya yi dariyar banza, yana nuna mata rigarsa “Do you even know how expensive this shirt is? Do you have any idea how much it costs?”


Rahama ta haɗiye yawu, idanunta suka fara cika da hawaye. Ta so ta ce masa ba da gangan ta yi ba, ta so ta bayyana cewa tissue kawai take son ɗauka, amma ganin yadda yake mata magana ya sa ta kasa samun ƙarfin halin yin hakan


Ma’aikaciyar jirgin ta sake shiga tsakaninsu

“Sir, there’s a lavatory at the back. You can go and clean up there, kayi hakuri da abun daya faru”


Rayyan ya ja dogon numfashi, ya karbi tissue ɗin daga hannunta, sannan ya juya ya nufi bayan jirgin


Yayin da yake tafiya, ya ci gaba da kallon rigarsa cikin fushi, yana girgiza kai kamar har yanzu bai yarda da abin da ya faru ba


Rahama ta bi shi da kallo har sai da ya ɓace a bayan labulen da ke kusa da lavatory ɗin


Sai ta sauke numfashi da ta daɗe tana riƙewa

“Oh my God!” ta rada, tana dora tafin hannunta a kirjinta “Wannan mutumin zai sa na kamu da hawan jini before I even get home”


Ta ɗauki tissue ta goge gefen kujerarta, sannan ta gyara tray ɗinta. Duk da tsoron da ta ji, wani ɓangare na zuciyarta ya fara tunanin yadda abin ya faru


Ba ta yi niyyar zubar masa da abinci ba fa! Wai ita ce ta lalata masa rigar saboda tissue?


Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin hana kanta dariya. Amma da ta tuna yadda ya yi tsawa, sai ta sake buɗe su da sauri


“A’a Rahama, ki yi shiru kawai, wannan mutumin fa kamar zai iya cinye mutum ne idan ya yi fushi”


A can bayan jirgin kuwa, Rayyan yana tsaye a cikin ƙaramin lavatory, yana kallon kansa a madubi. Ya ɗauki tissue ya fara goge rigarsa a hankali, amma duk yadda ya yi, tabon bai fita gaba ɗaya ba


Daga ƙarshe ya sauke tissue ɗin, ya ɗora hannayensa biyu a gefen sink, yana kallon kansa a madubi


“Unbelievable!” ya furta, yana girgiza kai


Tafiyar da ya yi tsammanin zai yi cikin kwanciyar hankali, amma tun kafin jirgin ya sauka, the fucking girl ta riga ta mayar masa da shi abin takaici


Kuma abin da ya fi ba shi haushi shi ne, ba wannan ne karon farko da ta jefa shi cikin yanayin da bai so ba


“First the phone, now this,” ya faɗa a hankali “What is wrong with that girl?”


Ya sake gwada goge tabon, amma da ya ga bai fita sosai ba, sai ya daina. Ya wanke hannunsa, ya gyara cuff ɗin shirt ɗinsa, sannan ya fito daga lavatory ɗin yana jan numfashi a fusace


Da ya dawo kujerarsa, sai ya tarar Rahama ta koma kallon windown jirgin, ba ta ma ɗago ta kalle shi ba


Ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta, yana jiran ko za ta ce wani abu, ko aƙalla ta sake ba shi haƙuri. Amma sai ta ci gaba da kallon waje kamar ba ta san ya dawo ba


Wannan ya ƙara fusata shi, ya zauna da ƙarfi, ya ɗaure seat belt ɗinsa, sannan ya juyo gare ta


“Amma ke, kanki nawa ne?”


Rahama ba ta amsa ba, ta ci gaba da kallon windown, tana kallon farin gajimaren da ke shawagi a ƙarƙashin jirgin. A zahiri, hankalinta ba ya kan gajimaren gaba ɗaya. Tana jin duk wata kalma da yake furtawa, amma ta yanke shawarar cewa ba za ta sake ba shi damar cin mutuncinta ba


“I’m talking to you,” ya faɗa, yana ɗan karkatar da jikinsa gare ta


Still taki juyo wa, hakan ya sake hatsalasa 


“Hey! Are you deaf?”


Rahama ta lumshe idanunta a hankali. Ta san idan ta buɗe baki, akwai yiwuwar hawaye su zubo, kuma ba ta son wannan mutumin ya ga ta yi kuka saboda shi


Rayyan ya ƙara matso da kansa kaɗan yana leka fuskanta ya ce


“Next time, ki sake yin irin wannan kuskuren, ki ga abin da zan yi miki. I swear, zan kakkaryaki, idiot!”


Ta ji kalmomin nasa sun bugeta sosai, ta juya a hankali, idanunta har yanzu cike da ruwa, amma a wannan karon ta yi ƙoƙarin riƙe kanta


“Enough,” ta faɗa cikin ƙaramin murya


Rayyan ya ɗan ɗago gira sabar mamakinta “What?”


Rahama ta juyo gaba ɗaya, ta kalle shi na wasu secs, sannan ta sake cewa “I said enough”


Wani kallo ya watsa mata “Don’t you dare raise your voice at me”


Ta yi mamakin yadda ya juya abin kamar ita ce ta fara masa magana da ihu, ta so ta tambaye shi ko da gaske yana ganin kansa a matsayin wanda ya isa ya riƙa yi mata barazana a cikin jirgi, amma ta tuna da halinsa, ta kuma tuna cewa ba ta son ta sake jawo hankalin sauran fasinjoji, saboda haka sai ta juya ta koma kallon tagarta


Rayyan ya yi tsaki “Stupid girl”


Rahama ta cije leɓenta na ƙasa, ta dafe hannayenta a kan cinyarta


“Allah Ya ba ni haƙuri” ta furta a hankali, tana kallon gajimaren da ke waje


Ya kalle ya ce “Ke! Me kika ce?”


Ta yi kamar ba ta ji shi ba


Rayyan ya karkatar da kansa domin ya kalle ta sosai “Look at me when I’m talking to you”


A hankali Rahama ta juya tana kallonsa


Sai kawai ya ce, “If you don’t stop looking at me like that, I’ll pluck your eyes out, stupid”


Ta zaro idanunta, sannan ta juya da sauri tana girgiza kai “Wannan mutumin fa…” ta rada, muryarta na rawa saboda fushi da tsoro a haɗe “Kai dai Allah Ya shirye ka” Bayan haka ta daina magana gaba ɗaya


Ta jingina kanta da kujerar, ta gyara mayafinta, sannan ta juya tagar ta zama abin da za ta mai da hankali a kai. A hankali, gajimaren da ke waje ya fara ɗaukar hankalinta, yayin da sanyin iska daga na’urar sanyaya iska suka fara kwantar mata da hankali


Ta rufe idanunta na ɗan lokaci


Da farko, ta yi niyyar hutawa ne kawai, amma gajiya da damuwar da ta tara tun kafin tafiyarta suka fara rinjayar ta. Ba ta ankara ba, baccin ya ɗauke ta


Rayyan kuwa, ya ɗauki wayarsa ya fara duba saƙonnin da suka shigo masa. Duk da haka, lokaci-lokaci yana kallon Rahama da gefen ido, musamman idan ya tuna tabon da ke kan shirt ɗinsa


“Unbelievable” ya sake rada, kafin ya girgiza kai ya mayar da hankalinsa ga wayarsa


Ba su sake magana ba har sai da aka fara sanar da fasinjoji cewa jirgin zai fara sauka


Muryar flight attendant ta cika cikin jirgin, tana sanar da su cewa su tabbatar sun ɗaure seat belt ɗinsu, sun mayar da kujerunsu yadda ya kamata, sannan su ajiye dukkan kayan da ke gabansu


Rahama ta buɗe idanunta a hankali, ta ɗan rikice na ƴan secs , tana ƙoƙarin tuna inda take, kafin ta waiwaya ta ga tagar jirgin da filayen ƙasa suka fara bayyana a ƙarƙashinsu


“Oh, mun kusa sauka?” ta tambayi kanta a hankali, tana gyara zama


Ta kalli Rayyan ta gefen idonta, amma ya riga ya mai da kansa other side


Rahama ta ja ƙaramin numfashi

“Thank God” ta rada, tana danna kanta da kujerar


Bayan wasu mintuna, jirgin ya sauka a filin jirgin sama, suna jin motsin ƙafafun jirgin a kan titin sauka, sannan ya fara rage gudu har sai da ya tsaya gaba ɗaya


Wasu fasinjoji suka fara motsi a kujerunsu, wasu suna buɗe wayoyinsu, wasu kuma suna cire seat belt ɗinsu bayan an ba su izini


Rahama ta ɗauki wayarta da jakar hannunta, sannan ta gyara mayafinta. Ta yi farin ciki da ta kusa isa gida, duk da cewa tafiyar ta zo da wani ɗan abin takaici da ba ta taɓa tsammani ba


Rayyan ya miƙe da aka ba su izinin fita. Ya ɗauki kayansa, ya fita daga kujerar ba tare da ya kalli Rahama ba


Ta bi shi da kallo, ta ɗan girgiza kai

“Alhamdulillah, na rabu da kai” ta rada, tana sauke numfashi


Ta jira fasinjojin da ke gabanta suka fara tafiya kafin ta miƙe ita ma. Da suka isa hanyar fita, sai ta bi alamomin da ke nuna hanyar zuwa wurin karɓar kaya, ta ɗauki trolley, sannan ta tsaya tana jiran akwatunanta su fito


Bayan an kawo kayanta, ta tabbatar da cewa duk sun cika, ta ɗora su a kan trolley, sannan ta bi hanyar fita zuwa inda ake jiran fasinjoji


Da ta fito daga cikin ginin filin jirgin, iska ta bugi fuskarta. Ta ɗan tsaya, tana kallon wurin da mutane ke taruwa domin karɓar ƴan uwansu. Wasu suna rungumar juna, wasu suna ɗaga hannu suna kiran sunaye, wasu kuma suna jan akwatunansu zuwa motocin da ke jiransu


Rahama ta yi murmushi, a ƙarshe, ta dawo gida.


Ta zaro wayarta daga cikin jakarta, ta kira direbansu. Ba da daɗewa ba, ta ga motar t ta shigo wurin da ake tsayawa. Direban ya fito da sauri, yana leƙen mutane har sai da ya hango ta


“Yar gidanmu!” ya kira da fara’a, yana ɗaga hannu


Rahama ta yi dariya, ta ɗaga masa hannu ita ma “Malam Habu! Gani anan!”


Direban ya zo gare ta, ya karɓi trolley ɗin da ke ɗauke da akwatunanta, yana murmushi


“Yauwa, sannu da zuwa, Alhamdulillah! kin dawo lafiya”


“Alhamdulilah fah!”


“Su Mammy suna ta jiran ki. Tun safe suke ta hirar yaushe za ki iso”


Murmushin Rahama ya ƙara faɗaɗa. Ta ɗauki jakar hannunta, ta bi shi zuwa motar. Ya buɗe boot ɗin, ya sanya akwatunan, sannan ya buɗe mata ƙofar baya


Ta shiga ta zauna, ta jingina kanta da kujerar cikin gamsuwa. Da motar ta fara tafiya, sai ta fitar da wayarta ta kira mahaifiyarta


“Mammy!”


“Rahama ta?” Muryar mahaifiyarta ta fito cikin farin ciki “Kin sauka knn, ɗiyata?”


“Eh, Mammy! Na sauka lafiya, yanzu muna hanya zuwa gida”


“Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah Ya ƙara kiyaye ki. Kin ga yadda kika sa ni zaman jira? Tun safe nake kallon waya”


Rahama ta yi dariya, tana kallon gine-ginen da suke wucewa a gefen titi


“Sorry Mammy! But I’m home now, and I’m not going anywhere again”


“Sai kin Kara so, nasan kina Jin yunwa?”


“Mammy, don Allah kada ki tambaye ni wannan tambayar. I’m starving! Ki tabbata kin yi tuwon shinkafa da miyar kuka, kuma kar ki manta da nama da busasshen kifi. Ina so miya ta yi kauri sosai, idan kuma ban samu ba na canza gida”


Mahaifiyarta ta fashe da dariya

“Wai ke tun a jirgin kike tunanin tuwo?”


“Mammy, please! Tun safe ban ci abincin da ya gamsar da ni ba. Sannan ban manta da jollof rice dina ba, da kayan lambu da soyayyen kaza. I deserve a welcome-home feast!”


“Allah Ya ba ki haƙuri da wannan cikinki, sai me kuma kika ce?”


Rahama ta yi dariya, tana jin zuciyarta ta cika da wani irin farin ciki da ba za ta iya bayyana shi da kalmomi ba


Ta fara ba mahaifiyarta labarin tafiyarta, amma ba ta ambaci mutumin da ta haɗu da shi a jirgi ba. Ba ta son ta ɓata wannan farin cikin da ta dawo da shi gida da labarin wani mutum mai mugun hali


Bayan sun gama waya, ta ajiye wayar a cinyarta, ta kalli hanyar da motar ke bi


A zuciyarta, ta riga ta manta da Rayyan, ko kuwa ta ce tana ƙoƙarin mantawa da shi


“Allah Ya sa kada na sake ganin fuskar wannan mutumin” ta furta, tana girgiza kai


Meanwhile, Rayyan ya fito daga cikin filin jirgin da matuƙar sauri, yana jan ƙaramin akwatinsa da hannunsa ɗaya. Ya tsaya a wurin da aka ware domin motocin da ke jiran fasinjoji, sannan ya zaro wayarsa ya kira ɗan uwansa


“Where are you?”


“Na iso tun ɗazu. Ina inda na saba tsayawa, kai fa?”


“I’m outside. Come and get me” Bai jira amsar da Rameez zai ba shi ba, ya katse wayar, sannan ya fara duban motocin da ke wucewa. Ba da daɗewa ba, sai wata mota ta tsaya a gabansa, gilashin gefen direba ya sauka


“Your Highness!” wata murya ta kira shi cikin zolaya


Rayyan ya ɗaga kansa, ya ga babban ɗan uwansa Rameez zaune, yana murmushi


“Get out of my face,” Rayyan ya faɗa, yana buɗe ƙofar gaba domin shiga


Rameez ya fashe da dariya “Subhanallah! Waye ya ɓata maka rai haka? Ka fito daga jirgi kamar wanda aka kora daga fada”


“Just drive”


Rameez ya kalle shi da gefen ido, ya lura da yadda yake gyara hannun shirt ɗinsa, sannan ya ga tabon da ya rage a jikin farar rigar


Ya yi shiru na secs biyu, sannan murmushinsa ya faɗaɗa “Wait a minute. What happened to your shirt?”


Rayyan ya sauke numfashi mai nauyi, ya jingina kansa da kujerar, sannan ya rufe idanunsa “Don’t even ask”


“To yanzu kuma ka sa na so tambayar nawa, Kai ne fa ka fi son komai ya kasance perfect, waye ya yi maka wannan?”


Rayyan ya buɗe ido ya kalle shi “A girl”


Rameez ya ɗan yi shiru, sannan ya juya gaba daya garesa “A girl?”


“Yes, a girl! Wata yarinya mara hankali da ba ta san yadda ake tafiya a airport ba. Ta fara cin karo da ni, ta sa wayata ta faɗi ta fashe, sannan a cikin jirgi ta zubar min da abinci a kan shirt ɗina”


Rameez ya buɗe baki yana kallonsa

“Wait, wait, wait. Ta sa wayarka ta faɗi kuma ta zubar maka da abinci? Same girl?”


“Unfortunately, yes”


Rameez ya fashe da dariya har sai da ya jingina da sitarin motar“Wallahi wannan yarinyar ta yi maka aikin da ni ma ban taɓa iya yi maka ba!”


Rayyan ya juya ya kalle shi cikin mamaki “Are you seriously laughing?”


“Of course I am! Ka san tsawon shekarun da muka yi tare, ban taɓa ganin mutum ya samu damar ɓata maka rai sau biyu cikin rana ɗaya ba. This is impressive!”


Rayyan ya yi tsaki, ya juya ya kalli windown mota “She’s so annoying, wallahi saura kadan da na dake ta”


Rameez ya daina dariyar da yake yi na ɗan lokaci, ya kalle shi da wani irin kallo mai nuna rashin yarda “Ba ruwanka da dukan wani, balle ma mace. Me ya same ka ne? Yaushe ka zama ɗan daba kuma?”


Rayyan ya yi gyara zamansa a kujerarsa, yana jin haushin yadda ɗan uwansa ya maida abin kamar wasa


“Ba za ka gane ba, Rameez”


“Of course I won’t. Domin ni ban taɓa samun wata yarinya da ta fasa min waya, sannan ta zubar min da abinci a jikina cikin tafiya ɗaya ba” Rameez ya sake fashewa da dariya


Rayyan ya ɗauki wayarsa, ya fara duba saƙonninsa, amma Rameez bai daina zolayarsa ba “Ka san me? Ina ganin ya kamata ka gode mata”


Rayyan ya juyo da sauri “Gode mata? For what?”


“Ta koya maka cewa akwai mutanen da ba sa tsoron ɓata maka rai. You need that kind of experience sometimes”


“Rameez!”


“To na yi shiru mana!” ya faɗa, yana ɗaga hannunsa ɗaya alamar miƙa wuya, duk da murmushin da bai bar fuskarsa ba


Motar ta hau kan babban titi, ta fara tafiya cikin sauri. Rameez ya kunna rediyo, wata waƙa mai daɗin sauraro ta fara tashi a hankali, amma Rayyan bai kula sa ba, har sannan yana tunanin abin da ya faru a jirgi


Ya tuna yadda Rahama ta kasa magana lokacin da ya yi mata tsawa, da yadda ta yi shiru ta juya kanta window kamar ba ta jin shi


Ya ɗan daure fuska “She didn’t even have the decency to apologize properly” ya faɗa a hankali


Rameez daya ji shi ya ce “Amma ka ce ta ce maka sorry”


“Not properly”


“Ah, yanzu ka zama ƙwararren mai tantance haƙuri? Ka san cewa wani lokacin mutum yana tsorata ne idan aka yi masa tsawa?”


Rayyan ya yi shiru


Rameez ya ɗan kalle shi, sannan ya ci gaba da magana cikin raha “Maybe you scared her”


“I didn’t scare her”


“Okay, sir. You didn’t scare her. Ita ce kawai ta yi shiru saboda ta ji daɗin muryarka mai daɗi”


Rayyan ya juya masa da wani kallo “Can you shut up?”


Rameez ya fashe da dariya “Yanzu na tabbatar akwai wani abu da wannan yarinyar ta yi maka. Har ka manta da yadda kake magana da ni”


Rayyan ya yi tsaki, ya jingina kansa da kujerar, ya rufe idanunsa “Just take me home”


“Your wish is my command, Your Highness”


Duk da cewa Rameez ya daina yi masa magana na ɗan lokaci, murmushin da ke fuskarsa ya nuna cewa ba zai manta da wannan labarin da wuri haka nan ba. A ganinsa, abin ya fi ban dariya ganin yadda Rayyan, wanda ba ya son wani abu ya ɓata masa rai, ya samu wata yarinya da ta iya yin hakan sau biyu cikin rana ɗaya


While Rayyan kuwa, yana jin haushin kansa saboda har yanzu yana tunanin fuskar yarinyar


Ya buɗe idanunsa, ya kalli hanya ta tagar mota, sannan ya furta a hankali, “I hope I never see that girl again”


Rameez bai ji maganar ba. Ko kuma ya ji amma ya yi kamar bai ji ba, domin a zuciyarsa, wannan labarin ya fara zama mai ban sha’awa fiye da yadda Rayyan yake zato…


Da motar Rahama ta isa gida, sai ta fara murmushi tun kafin direban ya tsaya gaba ɗaya. Gidan ya yi kyau kamar yadda ta saba gani, ƙofar gidan a buɗe take, furannin da ke gefen hanyar shiga suna sheƙi a ƙarƙashin hasken rana


Da motar ta tsaya, ta buɗe ƙofar ta fito


“Mammy!” Ta kira da ƙarfi, tana tafiya da sauri zuwa cikin gidan


Mahaifiyarta ta fito daga cikin falon, da ta hango Rahama sai fuskarta ta washe da farin ciki. Ta buɗe hannayenta, Rahama ta ruga ta rungume ta, ta matse ta a jikinta kamar wadda ta daɗe take son wanga hug


“Alhamdulillah ɗiyata. Alhamdulillah, kin dawo lafiya” Mammy ta faɗa, tana shafa bayanta


Rahama ta lumshe idanunta, ta matse mahaifiyarta sosai “Na yi kewarki Mammy. Wallahi na yi kewarki sosai”


“Ni ma na yi kewarki, zo ki bari in kalle ki”


Ta ja Rahama kaɗan daga jikinta, tana kallon fuskarta, sannan ta shafa mata kumatu cikin ƙauna “Kin ƙara kyau fa. Kin zama babbar yarinya yanzu”


Rahama ta yi dariya “Mammy please. Kada ki fara, ni dai abinci nake so”


Mahaifiyarta ta girgiza kai tana dariya

“Wannan cikinki! To, ki shiga ki canja kaya, an riga an shirya abinci a dining”


Rahama ta yi ihu na cike farin ciki “Really? I love you, Mammy!”


Ta sake rungumarta kafin ta juya da sauri zuwa cikin gida, tana jin kamar duk wata gajiya ta tafiyar ta ɓace. A yau ta dawo gida, ta dawo wajen mutanen da suke ƙaunarta, wajen wanda ba sai ta yi bayani ba kafin su fahimci abin da ke zuciyarta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol