Free chapter · Read without an account
THE WATCHFUL EYES
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER ELEVEN: 11*
*THE WATCHFUL EYES*
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Washegarin ranar ya kasance cikin natsuwa a gidan Yaya Umar, tun da safe Umar ya fita aiki, don haka gidan ya rage da wani irin annashuwa da Inteesar ta daɗe ba ta ji ba, a babban falon gidan, Nana da Inteesar suna zaune suna kallon wani Indian series a TV, yayin da plate mai ɗauke da apples da grapes yake a gabansu, lokaci zuwa lokaci, ɗayarsu za ta yi wata magana game da abin da ke faruwa a cikin shirin, sai su fashe da dariya, Nana ta juyo ta kalli Inteesar, murmushi yana shimfiɗe a fuskarta, “Intee, wallahi kin fara sabawa da Abuja,” Inteesar ta yi dariya kaɗan, tana ɗaukar apple ɗaya daga cikin plate ɗin, “Sabawa dole ne, Yaya Nana, ai ba zan zauna kullum ina kuka ba,” “Haka ne,” Nana ta gyada kai, sannan ta ɗan karkatar da kanta, “Amma wallahi, da Daddy ya bar ki a Katsina, da yanzu kin cinye kanki da tunani,” Inteesar ta ɗan yi shiru, murmushin da ke fuskarta ya ragu kaɗan, tunanin Katsina da abubuwan da suka faru a baya ya ratsa zuciyarta, amma ta yi ƙoƙarin danne shi, “Gaskiya ne,” ta amsa a hankali, sai Nana ta ɗan matsa kusa da ita, ta sauke muryarta kamar wadda take shirin tona wani babban sirri, “Amma akwai wani abu da nake son tambayarki,” Inteesar ta ɗaga gira, tana kallonta cikin mamaki, “Wane abu kuma?” Nana ta yi wani murmushi mai cike da wayo, ta ɗan yi mata kallon gefe, “Hmm… akwai wani a school ko?” Inteesar ta zaro ido, apple ɗin da take riƙe da shi ya tsaya a tsakiyar hanyarsa ta zuwa bakinta, “Yaya Nana!” Nana ta fashe da dariya, tana kallonta da wani irin nishaɗi, “Toh me? Kyakkyawar yarinya kamar ki, a Nile University babu ko da admirer ɗaya?” Inteesar ta sunkuyar da kanta, tana murmushin kunya, “Akwai dai…” Nan take idanun Nana suka haska, ta gyara zamanta kamar wadda ta samu labarin da take nema, “Aha! Ashe dai akwai wani abu!” Inteesar ta girgiza kai da sauri, “Ba haka ba ne fa!” “Toh, ya sunansa?” Inteesar ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ɗago kai tana kallon Nana da fuskar wadda ba ta san ta ina za ta fara bayanin ba, “Gaskiya ma ban san sunansa ba,” Nana ta buɗe baki cikin mamaki kafin ta sake fashewa da dariya, “Subhanallah! Ba ki san sunansa ba, kuma kin ce akwai?” Inteesar ta yi murmushi a hankali, tana wasa da yatsunta, “Kawai dai… yana yawan turo min saƙonni ne,” Nana ta daina dariyar a hankali, ta zuba mata ido, “Wait a minute! Kina nufin akwai wani saurayi da yake turo miki saƙonni, amma ba ki san ko waye shi ba?” Inteesar ta gyaɗa kai a hankali, Nana ta buɗe baki cikin mamaki, “Wato secret admirer kenan?” Inteesar ta yi saurin matsowa kusa da ita, ta ɗora yatsanta a leɓɓa, “Shhh! Don Allah, kar Yaya Umar ya ji,” nan take Nana ta dafe baki tana dariya, sai ta girgiza kai, “Allah ya kyauta! Intee, kin san mijin nan nawa, doka kawai ya sani, wallahi, wani lokacin ma sai na ji kamar ni ma yana son ya hana ni sakewa, komai sai an yi a tsari!” Inteesar ta fashe da dariya, “Wallahi, Yaya Nana, ni ma haka nake ji,” Nana ta ɗaga gira, tana kwaikwayon yadda Umar yake kallon mutum idan yana son ya fahimci wani abu, “Ke ma kin gani ko? Da zarar ya ɗaga gira, mutum sai ya manta abin da zai faɗa! Yaya Umar ai fuskar shi kaɗai ta isa ta sa mutum ya yi confession ba tare da an yi masa tambaya ba!” Inteesar ta rufe bakinta da tafin hannu tana dariya, “Wallahi kuwa! Sometimes, I feel like he can read people’s minds,” dukansu suka sake fashewa da dariya, a dai-dai lokacin ne aka buɗe ƙofar falon, dariyar tasu ta tsaya cak, Inteesar ta ɗago da sauri, murmushin da ke fuskarta ya ɓace a take, Yaya Umar ne, gabanta ya faɗi, sanye yake cikin farar shadda mai sauƙi, hannunsa riƙe da key ɗin mota, da alama ya dawo gida ne ba tare da sun sani ba, idanunsa suka sauka a kansu, ya tsaya cak a bakin ƙofar, yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, fuskarsa babu alamun wasa kamar kullum, ya zuba musu ido cikin wani irin kallo mai cike da tuhuma da bincike, kallon da yake sa mutum ya ji kamar an gano duk wani sirrin da yake ƙoƙarin ɓoyewa, Inteesar ta ji zuciyarta ta fara bugawa da sauri, nan take ta gyara zamanta, ta sauke apple ɗin da ke hannunta a kan plate, sannan ta haɗiye miyau a hankali, Nana kuwa ta dake, ta yi murmushi kamar babu abin da ya faru, “Sannu da zuwa,” Umar bai amsa nan take ba, ya kalli matarsa na wasu daƙiƙu, sannan idanunsa suka dawo kan Inteesar, ta yi saurin sunkuyar da kanta, ya taka a hankali ya shigo cikin falon, ya ajiye key ɗinsa a kan centre table, “Sai dariya ake yi ban sani ba,” ya faɗa cikin sanyin muryarsa mai laushi, Nana ta yi murmushi, “Toh, ai dariya ma sadaka ce,” Umar ya ɗan ɗaga gira, amma bai ce komai ba, ya nufi fridge, ya ɗauki bottle ɗin ruwa, ya buɗe ya sha kaɗan, sannan ya dawo ya zauna a kujerar da ke kallon nasu, ya jingina bayansa da kujerar, ya ɗora hannayensa a kan armrest, idanunsa kuma suna yawo tsakanin matarsa da Inteesar, “Wai me ya ba ku dariya haka?” ya tambaya a hankali, Inteesar ta ji gabanta ya sake faɗuwa, kafin ta samu damar cewa wani abu, Nana ta yi saurin amsawa, “Ni fa ina tsokanar Intee ne kawai, tun ɗazu muna hira,” Umar ya ɗan gyaɗa kai, “Hmm,” kalmar guda ɗaya ce kawai, amma yadda ya faɗe ta ya sa Inteesar ta ji kamar akwai tambayoyi a cikin ransa fiye da waɗanda ya yi magana a kai, shiru ya sake ratsa falon, Inteesar ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, duk da tana ƙoƙarin nuna kamar komai lafiya, ta kasa kawar da tunanin cewa Umar yana nazarin kowane motsinta, can sai ya kira ta, “Inteesar,” ta ɗago kai da sauri, “Na’am, Yaya,” “How is school?” “Alhamdulillah,” “Lectures fa?” “Alhamdulillah,” Umar ya ɗan karkatar da kansa, “Everything?” Inteesar ta haɗiye miyau, “Alhamdulillah, Yaya,” ya ɗaga gira ɗaya, “Kullum Alhamdulillah, ina tambayar ko kina coping ne, kina fahimtar lectures ɗinki kuwa? Ko akwai wani abu da yake damunki?” “Eh… ina coping,” Umar ya yi shiru na ɗan lokaci, yana nazari a kanta, sai ya ɗan karkata jikinsa gaba, ya ɗora hannayensa a kan gwiwoyinsa, “Amma na lura kwanan nan kina yawan tunani,” nan take zuciyar Inteesar ta buga da ƙarfi, Nana ma ta ɗan ɗago kai, tana kallon ƙanwarta a gefe, Inteesar ta yi murmushin yaƙe, ta ƙoƙarta ta daidaita fuskarta, “Babu komai, Yaya,” Umar ya zuba mata ido na wasu daƙiƙu, kamar yana jiran ta ƙara wani bayani, “Hmm, babu komai kenan,” yadda ya faɗi kalmar ya nuna a fili cewa bai amince da amsar ba gaba ɗaya, Nana ta lura da yadda yanayin falon ya sauya, don haka ta yi saurin sauya zance, “Babe, ka ci abinci kuwa?” “A’a,” “To, bari na je kitchen,” ta miƙe daga kujerar, amma kafin ta kai ga ƙofar kitchen din, Umar ya dakatar da ita, “No, ki bar shi, zan ci anjima,” ta tsaya, ta juyo tana kallonsa, “Okay,” sai ta dawo ta zauna, daidai lokacin ne wayar Inteesar da ke gefenta ta yi vibration, ƙaramin sauti ne kawai, amma saboda shirun da ke falon, dukansu ukun suka ji shi, gabanta ya faɗi dumm! Idanun Umar suka sauka kai tsaye kan wayar, sannan suka dawo kan fuskarta, Inteesar ta ji tafin hannunta ya yi sanyi tsabar tsoro, ta yi saurin ɗaukar wayar ta juya screen ɗin ƙasa, ba tare da ta buɗe saƙon ba, Umar ya lura da abin da ta yi, ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya sake buɗewa a hankali, Nana ta kalli Inteesar, ta kalli wayar, sannan ta yi ƙoƙarin ɓoye murmushin da ya zo mata, “Intee, ba za ki duba ba?” “A’a… ba komai ba ne,” Umar ya ɗan matsa jikinsa a kan kujerar, idanunsa har yanzu suna kan Inteesar, “Are you sure?” Ya tambaya cikin sanyin muryarsa, amma a wurin Inteesar, wannan sanyin muryar ya fi tsawa firgitarwa, ta haɗiye miyau da ƙyar, “Eh, Yaya,” ya gyaɗa kai a hankali, “Okay,” amma idanunsa ba su bar fuskarta ba, Inteesar ta yi ƙoƙarin yin kamar ba ta damu ba, sai dai zuciyarta na bugawa da sauri, a ranta tana roƙon Allah kawai wayar kada ta sake yin sauti, amma kamar wanda ke son ya ƙara tayar mata da hankali, wayar ta sake yin vibration karo na biyu, sai kuma karo na uku, duk a jere! Kamar wanda ke matsanancin son a amsa masa saƙon nan take, Inteesar ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana jin kamar ƙasa ta buɗe ta haɗiye ta, Umar ya kalli wayar, ya kalli Inteesar, sannan ya kalli Nana, Nana kuwa ta yi saurin kau da kanta, tana ƙoƙarin kada ta nuna irin mamakin da take ciki, ba tare da Umar ya ce uffan ba, ya miƙa hannunsa ya ɗauki key ɗin motarsa da ke kan tebur, “Zan shiga ɗaki,” ya faɗa a taƙaice, ya miƙe tsaye, ya gyara gefen shaddarsa, sannan ya ɗauki wasu matakai kafin ya tsaya ya waiwayo a hankali, “Inteesar,” gabanta ya kusa tsayawa, “Na’am, Yaya?” Ya zuba mata idanunsa masu zurfi da firgitarwa, “Whatever it is… kar ki bari ya ɗauke miki hankali daga abin da ya kawo ki Abuja,” ya ɗan dakata, kamar yana son ƙara wani abu, amma daga ƙarshe ya girgiza kai kawai, “Pay attention to your studies,” daga haka ya juya ya bar falon, Inteesar ta bi shi da kallo har ya ɓace daga ganinta, sai da ta tabbatar ya tafi sannan ta saki wani nannauyan numfashi da ba ta ma san tana riƙe da shi ba, Nana ta dawo ta zauna kusa da ita, ta dafa kafaɗarta tana murmushi, “Relax, Intee, ki daina daga hankalinki haka, ki rage wannan tsoron nan dan uwanki ne fa amma kalli yanda kike rikicewa idan yana waje,” Inteesar ta juya ta kalleta, amma ta kasa ko da murmushi, “Yaya Nana, you don’t understand, na ji kamar ya fara zargina,” Nana ta ɗan ɗaga kafaɗa, “Zarginki da me? Ke fa ba ki yi komai ba,” Inteesar ta buɗe baki za ta amsa, amma wayarta da ke hannunta ta sake kawo haske, ta yi saurin kallon screen ɗin, saƙonni guda biyu ne suka shigo daga lambar sirrin, ta buɗe na farkon, Unknown Number: “I missed you, beautiful…” Inteesar ta ɗan daure fuska, ta ji wani irin yanayi ya gauraya a zuciyarta, a gefe guda, saƙon ya nuna kamar mutumin ya daɗe yana saninta, a ɗaya gefen kuma, yadda yake magana da ita cikin kusanci ya ƙara mata tsoro, kafin ta gama nazarin saƙon farko, sai ta buɗe na biyun, Unknown Number: “And I think your dear Yaya Umar almost caught us…” Jikin Inteesar ya ɗauki rawar sanyi, ta sake karanta saƙon, sau ɗaya, sau biyu, kuma a karo na uku, zuciyarta ta fara bugawa da sauri, caught us? Us? Ta ɗaga kai a hankali ta kalli Nana, wadda har yanzu take kallonta cikin mamaki, “Intee? What is it?” Inteesar ba ta amsa ba, a hankali ta juya kai ta kalli hanyar da Umar ya bi zuwa ɗakinsa, kamar tana tsammanin zai sake dawowa ya tambaye ta game da saƙonnin, numfashinta ya tsaya cif, wannan mutumin ba wai kawai yana sanin inda take ba ne, yana sanin abin da take yi, lokacin da take yi, har ma da abubuwan da suke faruwa a kusa da ita, amma Ta yaya zai san ainihin abin da ya faru a cikin falon nan a daidai lokacin? Kuma me ya sa yake magana kamar ita da shi suna da wani sirri da ya haɗa su? Inteesar ta sake kallon wayar da ke hannunta, yatsunta suna rawa a hankali, tambaya guda ɗaya ce ta mamaye tunaninta, tana maimaituwa a ranta kamar amo da ba ta da hanyar tserewa daga gare shi..
WHO ARE YOU… AND WHY ARE YOU WATCHING ME?
*** ✍️