Free chapter · Read without an account

Chapter 17

by Salis M Reza · MIJIN AMAL

17
Ta ce "Haka kawai naji gabana na faɗuwa da jawabin wannan likitan Beb". "Ki karanta innalillahi wa innalillahi rajiun, zaki daina jin komai". Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Sai kuwa ta fara karantawa har suka ƙaraso gida. Suna shiga ya shige ɗaki ya fito da takardaun aikin nan. Ya zauna a palo ya fara aikin cike su. Ita kuma ta shiga ɗaki ta adana maganin sannan ta fito ta shiga kichin domin duba abun da zata dafa. Ta kalli kichin ɗin da kyau tana son tuno abun da take marmarin ci yau. Sai kawai ta tuno maganar likita akan abincin da zata koma ci. Hakan yasa ta fito Palo ta same shi. Ta zauna tana kallon yadda gaba ɗaya hankalinsa ya koma kan aikin kamar bai san da ita ba. Ta ce "Wai yau aikin ne har gida kuma?" "Eh". Ya faɗa bai kalleta ba. Ta sake cewa "Wai to a ina zan samu kalan abincin da likitar tace na dinga ci?" Ta faɗa da muryar shagwaɓa domin bata jin dadin yadda yake bata amsa. Ya ce "Sayowa zamu yi mana". Sai ta sake kallon sa tana jin ba dad'i. Ta tura baki tana so su haɗa ido amma ya ƙi yarda. Ta ce "To tunda ba'a sayo ba bari kawai naje yanzu na dafa wanda muke da shi". "Ko kin dafa ba zaki ci ba". Ya sake faɗa bai kalleta ɗin ba. Sai kawai ta tashi a fusace ta shiga kichin ta ɗaura ruwa. Ta zuba wake. Sai da ya kusa dafuwa kafin ta sauke. Ta ɗora wani ruwan na shinkafa. A ranta tana jin sai taga wanda zai hana ta cin abincin Idan ta dafa. Bata fito daga kicin ɗin nan ba sai da ta kammala shinkafa da wake jalof ya sha kayan chiki har ma yafi abincin yawa. Tana fitowa Palo ta ga baƙar leda har da kwali da jarkar manja. Ta kalleshe taga yana ta aikin sa hankalinsa kwance. Ta shiga dubawa. Sai taga komai na kayan abincin da zata dinga ci ne. Ta kwashe ta kai kichin bata ce masa komai ba. Daga haka ta shiga toilet tayi wanka ta fito. Tazo bakin madubi tana tsane gashin kanta, sai ta hango wani sabon ƙurjin a gefen kumatunta. Ta taɓa shi ta ji yana zafi. Ta sake duba sauran taga wasu sun sake fitowa. Tana ta shafa shi tana kallon kanta. Ta saka doguwar riga kawai ta fito. Daidai lokacin ana kiran sallar magriba. Ya tashi ya shiga yayi alaulau ya fita masallaci. Koda ya dawo ya cigaba da aikin sa. Sai bayan sallar Isha ya kammala. Ya kalleta ganin yadda ta kumbura kamar zata fashe. 

Ya ce "Mai ya faru?" 

"Ba komai". 

Ya ce "Tom zan shiga na kwanta ki tabbatar kin sha maganin ki". 

Tayi shiru. Sai ya tashi ya shiga ɗakinta. Ya dauko maganin ya fito. Ya ce "Ina abincin da kika dafa?" Ta yi banza da shi. Ya je ya duba yaga bata data ɗin ba. Ya ce "Ina naki ɗin?" Ta sake kawar da kai. Ransa ya ɗan ɓaci. Amma ya daure ya ce "Magana fa nake miki". Sai ta ce "Tun jiya na lura akwai abun da nai maka, shine ba zaka faɗa min ba sai dai ka dinga share ni, ko magana nai maka a takaice kake bani amsa, mai zai sa ba zaka faɗa min abun da nai maka ba, sai na baka hakuri ba?" Ta ƙarasa tana hawaye. Ya ce "Babu abun da kika min, aiki ne ya sha kaina a ofis, shine yasa nazo da shi har gida nayi". Ta ce "Ai da ba haka kake min ba, duk abun da yake damunka haka kake faɗa min bai wai ka dinga share ni ba". Cikin wata tsawar da bata san ya iya ba ya ce "Haba mana Amal, wai yaushe kika koyi ƙofari ne, baki ji nace miki aiki bane ya min yawa, ko so kike na bar aikin nazo na sakaki a gaba ina kallo". Ta toshe kunnenta tana kallon ƙasa duk ta tsorata. A hankali ta ce "Kayi hakuri idan na bata maka rai". Ya ce "Ɗauki abincin nan kici, daga yanzu kar ki ƙara yin kirki zan kawo wacce zata dinga dafa miki wannan abincin". Ta ce "Kai fa?" "Kar ki damu, har ki samu lafiya zan dinga ci a gidan yaya ko a waje". Ta zauna taci abincin kaɗan ya bata maganin ta sha. Sai ya zauna a palon ya ɗauki waya yana dannawa. Amal dai gaba ɗaya tsoro ma ya bata, hakan yasa tai masa shiru tana ta tunin abun da ya ɓata masa rai. Kusan minti biyar ya tashi ya ce "Zan je na kwanta, kar ki manta da addu'ar kwanciya barci". Ta bishi da kallo ganin ya shiga ɗaya ɗakin da ko gado babu. Ta tashi da sauri. Ta biyo shi ciki ta ce

"Anan zaka kwanta?" Ta faɗa da mamaki.

"Eh" Ya bata amsa a takaice. 

Ta ce "Dan Allah mai nai maka ne?" Ya ce "Amma kin san baki da lafiya ko?" 

"Ko bani da lafiya tare muke kwana, amma mai ya chanja hakan Yau?"  

"Kije ki kwanta, bana son surutu please". Ya faɗa yana rufe ƙofar da karfi. Sai ta bi ƙofar da kallo tana mamaki. Sai ta kasa tafiya tana ta son ta gano daga jiya zuwa yau mai tai masa da zai iya raba ɗaki da ita. Amma ta kasa gano ko abu ɗaya. Sai kawai ta fara hawaye tana tunanin ko dai ya fara gajiya da ita ne kamar yadda ake cewa namiji na gajiya da matarsa. Sai kuma ta girgiza kai tana faɗin ina Yasir ba zai taɓa gajiya da ita ba. Shi ɗin da ita hanta da jini ne, ba zasu taɓa rabuwa ba. Ta daɗe tana kuka da tunani kafin barci yayi gaba da ita. 

Karfe bakwai na safe ta fito bayan tayi sallah ta koma barci. Ta nufi ɗakin da ya kwana ta bubbuga tana mamakin wai yau itace suka kwana a ɗaki daban-daban da Yasir. Jin shiru yasa ta tura ɗakin taga baya ciki. Tana zuwa palo taga takarda an danne ta da remote. Ta ɗauka ta fara karantawa. "Good morning Beb, ina da sauran aiki a ofis ne, akwai wata mata zata zo anjima zata dafa miki abincin breakfast. Dan Allah karki shiga kichin, kuma kina cin abincin ki sha magani. Sai na dawo". Sai kawai ta ce "Allah ya dawo da kai lafiya, ya tsare min kai".

 Gaba ɗaya yau dama ta tashi da zazzaɓin jiki. Ga jirin nan tana jin yana kamata, maƙogaronta ma yana bushewa. Hakan yasa ta kwanta a palon saboda koda matar tazo ta ji. Ai kuwa tun kafin takwas matar tazo. Daga gani ma a gidan abinci ya samota saboda harda rigar ta ta girki. Ta nuna mata kichin ɗin da kayan abincin sannan ta dawo Palo ta zauna tana jin yadda yawun bakinta ke yin ƙaura. Ga juyawa da kanta keyi kamar wacce tayi aiki ta gaji.

Koda yaje ofis ɗin ba wanda yazo. Haka ya cigaba da aikin nan. Allah ya taimake shi Kafin tazo ya kammala komai Ya ɗauka ya kai ofis ɗin nata ya ajiye. Ya dawo ofis ya zauna ya dafe kai yana tunanin abun da yake so yayi. Mai ya dace yayi a tsakanin da da Amal, ta yaya zai fara binciken asalin matsalar, idan baiyi bincike ba kenan a haka za'a ci gaba da rayuwa, maiyi mafita. Ta yaya zai kawo karshen wannan matsalar. Ya daɗe a haka har sai da aka turo ana kiransa a ofis ɗin ceo. Bayan ya shiga sai yaga mutum biyu ne a cikin ofis ɗin. Kafin ma yayi magana yaga mahaifinta ne. Hakan yasa ya gaida shi yana sunkuya. Bayan ya bashi izinin zama ya miƙa masa wata takarda sannan ya ɗora da ƙarin bayani. "Ranar Litinin zamu buɗe samun kamfanin mu a Faransa, shine muke so mutum biyu zasu je domin nunawa sauran ma'aikatan da zamu ɗauka yadda aikin yake. Kuma Suhailait tace tare zaku yafi. Na sati ɗaya ne, ina fatan ba matsala ko?" Yasir ya kalleta, ta daga masa wata harara. Ya ce "Ba matsala Alhaji, Allah ya kaimu". Ya ce "Tom zaka ga sako sai ka sallami iyali kafin ranar ko". Daga haka ya fita bai ce komai ba.

Haka lokacin tafiyar nayi, ya fadawa Amal. A lokacin har kuka tayi domin kuwa bata son tafiyar, duk da dama yanzu ba wata kulawa take samu ba. Ya mata faɗa sosai akan shan magani da kuma cin abun da aka hana ta. Haka suka tashi izuwa Faransa. A cen kuwa ba karamr wahala ya sha ba, domin wata dama ta samu ta ci masa mutumci da aiki koda yaushe, gashi a cikin yan aikin take nuna masa shi ba kowa bane. Shi kuwa bai taɓa tanka mata ba, kawai aikinsa yake yi har suka je suka dawo.

Tun daga lokacin komai ya ja baya. Yasir ya sayo gado ya sa a ɗaya dakin nasa. Tsawon Wata ɗaya kenan basa kwana ɗaki ɗaya. Tayi kukan tayi maganar amma yace mata kawai yana tausayinta ne baya so tana fama da rashin lafiya kuma ya ɗaura mata wani nauyin. Bama ita kwana ba, harta yawan hira da cin abun da ya fito daga ganinta duk ya rage. Tun da ya dawo daga tafiyar nan komai ya sake ja baya, ita kanta ta san ta rasa mijinta da gaske. Gashi kusan duk bayan kwana uku sai ta kwanta rashin lafiya, a cikin wata ɗayan nan ta reme sai dogon wuya kamar marayan raƙumi, ga haske da take yi. Yanzu duk ƙuraje sun bata mata fuska, fuskar nan ba ko kyawun gani. Kullum sai taiwa likita compleng akan wannan ƙurajen idan sunje amma dai abu ɗaya take faɗa mata. Shi kansa hankalinsa ya tashi da wannan ƙurajen, ya ma likitan magana tace su dage da shan magani.

 Bangaren Nana kuwa bata sake jin labarin Mijin nata ba, duk da Mama ta dage Yasir ya kai musu ƙara, koda aka je kai ƙarar aka tambayi sunansa suka ce Alhaji Gali. Ina ne gidan sa, basu sani ba, ina yake kasuwanci nan ma basu sani ba. A takaice dai babu abun da suka sani nasa. Hakan yasa al'ƙali ya kori batun. Haka suka cigaba da rainon ciki. Bangare ɗaya kuma Yasir nata bincike da son gano gaskiyar maganar.

Yauma Kamar kullum ya gama shiryawa ya fito zai tafi ta fito daga ɗakin ta kira sunansa. Bayan ya tsaya ya kalleta ganin yadda ta sake dawowa kamar wata yarinya karama, fuskarta duk ƙurajen sun sauya mata kama. Gashi har yanzu a gidansu ba wanda ya sani, taki fadawa kowa. Ta ce "Yau likita tace mu koma asibiti, kuma zaka fita baka ce komai ba". Ya ce "Idan na dawo zamu je, ai ina sane ban manta ba". "Ta ce "Allah ya tsere hanya ka dawo lafiya". Ya amsa yana barin palon da sauri. Yana fita ta zauna a gurin ta ciro ɗan ƙaramin madubinta tana kwallon kanta a ciki. Ta shafa fuskar tana hawaye. Tana cikin haka mai akin nata tazo. Ta buɗe mata sannan ta koma ɗaki. Ta ɗauki waya ta kira Nana. Sai da matar ta tafi kafin Nana tazo. Da yake ta kwana biyu bata ganta ba, bata san haka ta dawo ba. Ta saki salati tana kallon ta. Ta ce "Anty Amal, wai kece wannan dan Allah? A garin yaya mai ke damunki, ina Mijin naki?" Ta jero mata tambayoyin hankali a tashe. Sai kawai ta fashe da wani sabon kukan tana riƙo hannun yar uwar tata. "Nana ban sani ba, wai wata cuta ce da ake samu idan ciki ya wuce wata biyar kuma ya zube, Nana ina cikin masifa ban san yadda zan yi ba, hatta Yasir ya guje ni akan wannan ciwon, baya kwana dakin da nake, baya cin komai na hannuna, ina cikin masifa. Ban san yadda zan yi ba". Nana ta ƙwace hannunta tana ja baya kaman taga abun tsoro, ta ce "Kenan dai idan aka zauna tare da ke za'a iya ɗauka kenan ko?" Amal ta girgiza mata kai tana son yi mata bayani. Amma ta ja baya tana faɗin "Anty ya kamata ki naimi magani, bari na kira miki Mama tazo asan abun da za'ayi". Daga haka tayi waje harda haɗawa da gudu. Tana zuwa kuwa ta kwashe komai ta fadawa Mama, wai Amal ta dawo kamar abun tsoro, wai ta rame kamar bata cin abinci, ga kuraje sun bata mata fuska tana ta kuka. Ai kuwa Mama ta saka hijjabi tayo gidan. Tace Nana tazo suje tace ba ruwanta tsoro take ji.

Lokacin da Mama ta ganta sai ta tsaya chak tana kallonta kamar ba zata ce komai ba. Amal ta ƙaraso tana kuka tana son rungume uwar tata amma tana tsoron kar itama ta gujeta. Ta ce "Amal kece haka? Ina Yasir ɗin? Baya ganin halin da kike ciki ne? Kunje asibiti ma kuwa?" Ta ƙarasa tana rungume ta. "Munje Mama, kusan duk bayan kwana uku ma muna zuwa, ana min allura da bani magani, amma duk da haka kalli fuska na Mama". To wai me ke damun ki?" Amal ta faɗa mata abun da likitar tace. Sai Mama ta ce "Kira min Yasir ɗin". Kiara ɗaya kuwa ya ɗaga. Ta ce "Nice nake Mama ke magana. Kana ganin halin da Amal ke ciki kuwa Yasir, anya kana da imani kuwa, ko dai giryar kuɗi ce ta kwashe ka, ko kuma asiri kayi da ita dan ka samu kuɗi bata sani ba. To wallahi kazo yanzu ka faɗa min abun da kayi mata. Kuma yanzu zan ɗauke ta na kaiata asibiti, ka shirya biyan komai na faɗa maka". Ta cikin wayar ya ce "Ban yarda ta fita ko ina ba, akwai asibitin da muke zuwa da ita kan ciwon, kuma komai ya kusa zuwa karshe". Mama ta ce "Asibitin banza da hofi, kai wai ka ma san hanlin da take ciki kuwa? Kuma sai ta fita, yanzu ma zan tafi da ita asibiti na faɗa maka". Ya ce "Kiyi hakuri Mama ban amince ba, akwai maganin da aka ɗorata akai". Yana faɗa ya kashe wayar. Mama tabi wayar da kallo. Ta ce "Wai haka ya dawo ne? Ko dai ya sayar da jiniki ne dan yayi kuɗi?" Amma ta girgiza kai Mama ta ce "Tashi kisa hijabi mu tafi". Amal ta ce "No Mama, tunda yace..." "Zanci uwar ki idan baki tashi ba, yar iskan yarinya wacce bata san abun dake mata ciwo ba, yaro ya kunshi ki a gida zai kashe ki kina nan kina biyayyar da bata da amfani, zaki tashi ko sai na falla miki mari yanzu?" Zatayi magana kuwa ta kai mata Wani mari. Haka ta tashi ta saka hijjabi. Jikin Mama har rawa yake yi saboda tashin hankalin da take ci. Suna fitowa sai ga matarsa Yasir da guda ya faka. Ya fito da sauri yana faɗin "Mama nace ban yarda matata taje ko ina ba". Ya faɗa yana shan gabansu. Ta ce "Idan ka cika ɗan halak to ka hana ta fita a gidan nan dan ubaka". Yace "Muddin ita ɗin matata ce, kuma ina auranta to ba zata fita ba". Amal ta kalleshi ganin yadda ya haɗe rai, kuma kamar ba shi ba. Ta ce "Yasir Mama ce fa, Mama ta ce fa" ya ce "Na san ita ɗin ce, shi yasa nake faɗa mata hakan cikin mutunci" gaban Mama ya faɗi, ta kalli Yasir da kyau, tana son tabbatar da cewar shi ne kuwa. Ta ce "Ni kuma idan har Amal ƴata ce sai naga mai hana ni fita da ita daga nan gidan. Idan ma tsafi kayi da ita wallahi sai ka warware shi. Ta ja hannunta da karfi. Yasir ya riƙe ɗaya hannun nata Yace "Muddin ta fita daga cikin gidan nan bada izinina ba to a bakin auranta, karta dawo min gida idan kun je asibitin...📝

Lamari fa ya girmama

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol