Free chapter · Read without an account
Madugu
INUWAR ƘADDARA 🖤
Book 1
Page 10 ✍️
Meelah Bazata
A hankali Ammar yake tuƙa motar, amma hankalinsa a mugun tashe yake. Duk da cewa ya saba jin ana tsoron Madugu, bai taɓa tunanin zai shiga irin wannan yanayi ba. Gani yake yadda Madugu yake wa babansa aiki, kamar zai iya yin duk abin da ya ga dama, sai ga shi yau kwana uku ana azabtar da shi.
Ko da suka isa gidan kansila, horn ya danna. Mai gadin ya zo ya buɗe, ya shiga da motar har ciki. Ya kasa kallon Madugu, ga shi ko a motar ya kasa ko yin numfashi yadda ya kamata saboda tsoro.
“Mun iso, ranka ya daɗe.”
Yaron ya faɗa har yana ɗan duƙawa.
Bai ce komai ba, ya buɗe ƙofar motar ya fito, sannan ya nufi cikin gidan ba tare da ya jira Ammar ɗin ba ma, sai dai shi ne ya kasance yana bin sa a baya cikin fargaba.
Alhaji Haladu yana falonsa tare da wani baƙonsa, kawai ya ga Madugu ya shigo, sai da ya miƙe cike da tsoro saboda bai san kuma da me ya sake zuwa ba.
“Madugu? Me ya dawo da kai kuma?”
Cike da tsoro yake maganar. Madugu ya zauna a kujerar da take kallon wacce Alhaji Haladu ya miƙe yana kallonsa, sannan ya juya ya kalli Ammar, wanda ya shigo a rakuɓe, daga shi sai ɗan wandonsa gajere, jikinsa ko ina cizon sauro.
“Ga ɗanka nan na dawo maka da shi, kansila. Ka san ni, ka san aikina, ka san in na ce zan yi, to zan yi. Ka san me zan iya aikatawa.”
Kansila ya waiga ya kalli Ammar. A yadda ya gan shi, sai da zuciyarsa ta buga, amma haka ya ke ta ƙoƙarin dannewa.
“Hakan ba za ta sake faruwa ba, ƙasar ma zai bari gaba ɗaya, amma bai kamata ka yi masa wannan hukuncin ba. Haka, Madugu, duba jikinsa fa ka gani!”
Madugu ya ja wani dogon tsaki, sannan ya juya ya ce wa Ammar, “Zo nan!”
“Don Allah ka yi haƙuri, wallahi na gaya maka kuma na yi alƙawarin ba zan sake ba.”
Gwiwa ya sa a ƙasa yana roƙonsa. Zuciyar kansila kuwa kamar za ta yi bindiga don ganin ɗansa wanda ya fi ƙauna fiye da komai a duniya, amma ga yadda Madugu yake wa jigarsa ta rayuwa.
Baƙon da suke zaune ne ya miƙe cike da mamakin ganin abin da Madugu ya yi. Ya san yadda Alhaji Haladu ya tsani ko kallon banza ka yi wa ɗansa, yanzu kuma ga wani yana masa irin wannan cin zarafi, kuma a gabansa.
“Kai, bawan Allah, wane ne kai? Wani irin rashin tarbiyya ce wannan? Za ka shigo har gidan mutum kana cin zarafin ɗansa kuma a gabansa? Me kake takama da shi ne? Ko kuma shaye-shaye irin naku na ’yan iskan matasa...”
“Tassssss!”
Sautin marin da ya ratsa kunnuwansu kenan. Ammar kuwa, da aka mara, take ya yanka ihu yana riƙe idanunsa da suke barazanar daina gani.
“Mahaukaci, ina ne k—”
“Tassssssss!”
Wani sabon sautin marin da ya fi na farko ya sake karaɗe falon, wanda sai da Alhaji Haladu ya dafe kuncinsa, saboda shi ma ya ji zafin marin. Shi kuwa yaron ya gama gigicewa saboda azaba.
Duk da haka, wannan baƙon bai fahimci abin da Madugu yake nufi ba. Ƙoƙarin sake buɗe baki yake ya yi magana, da sauri Alhaji Haladu ya yi tsalle ya damƙe bakinsa da ƙarfi, cikin ihu ya ce:
“Haba, Alhaji Badaru! Wa ya sa ka yin magana? Tun da ka ji ban ce komai ba, ai kai ma bai kamata ka yi magana ba. In za ka yi magana sau ɗari, to sai ya duke shi sau ɗari. Ba ka ganin halin da yake ciki ne?”
Danne zuciyarsa ya yi, ya ce:
“Zauna, Madugu, za mu tattauna.”
Waigawa ya yi, yana kallon kansila da wani irin kallo, kafin ya ce:
“Ba komai ne ake buƙatar tattaunawa a kansa ba. Ka san ni, ka san aikina. Shi kuma ka gaya masa, ba a sa wa Madugu baki a cikin magana.”
Yana gama faɗin haka ya fita, ya bar su a daskare a wurin.
Yana fita daga falon, kansilan ya narkar da wani uban zagi da tsinuwa yana jefawa Madugu. Da gudu ya ƙarasa kan ɗansa ya ɗaga shi yana duba jikinsa. Har lokacin yaron bai dawo daidai ba, idanunsa duk sun yi ja, fuskarsa kuwa shatin hannun Madugu raɗau.
Ammar kuwa, da bai samu damar kuka gaban Madugu ba, hakan ya sa yanzu da ya fita kawai ya saki kukan azabar da yake dannewa. Yana ta kuka, yana riƙe da mahaifinsa, wanda shi ma zuciyarsa ta cika da baƙin ciki. Bai taɓa tunanin ranar da zai ga ɗansa cikin wannan yanayin ba, balle a gabansa wani ya yi masa haka, kuma ya kasa yin komai. Gaskiya ba zai iya ƙyale Madugu ba, sai dai kuma in ya ce zai haɗa shi da hukuma, ya yi aikin banza, domin ba za su iya ba.
“Daddy, wallahi ba zan sake ba. Ka ce masa ya rabu da ni, don Allah! Kawai, Daddy, ni ba zan zauna a ƙasar nan ba.”
Ammar ya faɗa cikin kuka, yana kallon mahaifinsa.
Alhaji Haladu ya haɗiye yawu mai ɗaci, sannan ya zaunar da ɗansa a kan kujera. Ya dube shi sosai, yana jin wani irin baƙin ciki.
“Ka yi shiru, Ammar, ka kwantar da hankalinka. Babu abin da zai sake yi maka, amma kai kanka ka san na hana ka wannan ɗabi’a, amma ka yi biris. Yanzu kana ganin abin da wancan addababben ya yi maka.”
Ammar ya sunkuyar da kansa, bai iya cewa komai ba. Shi kaɗai ya san wahalar da ya sha a kwanakin da ya yi a wurin Madugu.
Alhaji Haladu ya girgiza kai, yana jin haushi da takaici. Ya san ɗansa yana da taurin kai, amma bai taɓa tsammanin zai kai ga shiga hannun Madugu har haka ba. Kuma bai yi tunanin Madugu zai iya yi wa ɗansa irin wannan wulaƙancin ba.
A hankali ya juya ya kalli Alhaji Badaru, wanda har yanzu yake tsaye cikin mamaki, da kuma tambayar kansa, wane ne Madugu da yake da irin wannan tsaurin ido? Kallon Alhaji Badaru ya yi, ya ce:
“Ka ga abin da nake gaya maka kenan. Wannan yaron da kake gani ba ƙaramin shaiɗanin yaro ba ne, ba ya jin magana, kuma ba ya tsoron kowa. Hatta da hukuma, babu wani mataki da za ta iya ɗauka a kansa.”
Alhaji Badaru ya nemi guri ya zauna, yana mai kallon ƙofar da Madugu ya bi.
“To, Alhaji Haladu, har yaushe za ka bar shi yana yi maka haka? Kai fa ba ƙaramin mutum ba ne a wannan garin. Kana da matsayi, kana da kuɗi, amma ka bar wani mara kunya yana shiga gidanka yana wulaƙanta ka da ɗanka a gabanka!”
Alhaji Haladu ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce:
“Da ka san abin da nake ciki da wannan yaron, da ba ka yi mini wannan tambayar ba. Madugu ba mutum ba ne da za ka yi wasa da shi, hatsabibi ne.”
Ya kalli Ammar, wanda har yanzu yake ta sauke ajiyar zuciya. Fuskarsa zuwa yanzu gaba ɗaya ta kumbura, sai yanzu ya ji zafin da yake a jikin yaron.
“Ka tashi ka je ka yi wanka yanzu, sannan ka zo mu tafi asibiti, domin kana buƙatar ganin likita.”
Ammar bai ce komai ba, ya miƙe ya fita daga falon babansa ya nufi hanyar ɗakinsa. Hamdala yake a zuciyarsa da ya kuɓuta daga hannun azzalumi.
Shi kuwa Alhaji Haladu, suka ci gaba da tattaunawa da abokinsa, zuciyarsa cike da tunanin yadda zai magance matsalar Madugu.
Matar Alhaji Haladu tana zaune a falo, ta ga ɗan nata a wannan yanayi. Ta ji daɗi da ya dawo, amma daga ganin yanayinsa ta san ya wahaltu. Amma ba ta ko kalle shi ba har ya shige ɗakinsa, saboda ba ta jin daɗin ɗabi’ar da yaron ya ɗauko, amma duk abin da ya yi, uban ba ya kwaɓa masa.
Ko da ta ji yaron yana hannun Madugu, hankalinta ya tashi saboda sanin ko wane ne Madugu, amma haka ta daure ta ci gaba da yi wa yaron addu’a, domin ta san dai duk zaluncin Madugu, ba zai kashe shi ba.