Free chapter · Read without an account
TSORON LEENAH😂
INUWAR ƘADDARA 🖤
Book 1
Page 11 ✍️
Meelah Bazata
Bayan tafiyar Ammar zuwa ɗakinsa, Alhaji Haladu ya ci gaba da tattaunawa tare da abokinsa, Alhaji Badaru, wanda har yanzu abin da ya gani yake ta maimaitawa a cikin ransa. Bai taɓa tunanin akwai wani ƙaramin yaro da zai iya shigowa gidan Alhaji Haladu ya wulaƙanta shi a gabansa ba, balle har ya mari ɗansa sau biyu ba tare da ya nuna alamun tsoron komai ba.
“Wallahi, Alhaji Haladu, abin da na gani yau ya ba ni mamaki matuƙa. A yadda ka san ka dai, na san ka da girman kai, kuma na san yadda kake son ɗanka, amma yau na ga abin da ban taɓa tsammanin zan gani ba.”
Alhaji Haladu ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya jingina da jikin kujera.
“Ka san mene ne abin da ya fi ba ni haushi? Ba wai kawai yadda ya shigo gidana ya yi wa ɗana abin da ya ga dama ba ne. Abin da ya fi ba ni haushi shi ne, na kasa yin komai a kansa. Ni da nake ganin zan iya yin komai da kuɗina da matsayina, yau na zauna ina kallon wani yaro yana wulaƙanta ɗana a gabana.”
Alhaji Badaru ya girgiza kai.
“To, me ya sa ba za ka nemi taimakon waɗanda suka fi shi iskanci ba? Ka ce babu wani mataki da hukuma za ta iya ɗauka a kansa, saboda suna tsoron sa. Wai waye shi ne ma da har hukuma take tsoron sa?”
Alhaji Haladu ya yi wani murmushi irin na takaici.
“Da ka san abin da ya faru tsakanina da shi tun farko, da ba ka yi wannan maganar ba. Na yi ƙoƙarin ganin na shawo kan matsalar, amma sai abin ya ƙara ta'azzara. Wannan yaron da kake gani ba ƙaramin taƙadirin yaro ba ne. Ka san lokacin da na fito takarar kansila, kafin kowa ya san yadda nake da gabar da Alhaji Kabiru, kuma duk yadda na waiga, alamar rashin nasara nake hangowa. Daga lokacin da na buƙaci Madugu ya taimaka min a harkar siyasa ta, da kansa Alhaji Kabiru ya janye takararsa. Yanzu da kake gani na matsayin kansila, Madugu shi ne sanadin hakan, kuma ba don kuɗin da zan biya shi ba. A'a, kawai idan ka ba shi aiki, sai ya kammala ne.”
Sauke numfashi Alhaji Badaru ya yi cike da mamaki.
“Amma fa, Alhaji Haladu, duk da abin da ya yi maka, ba za ka ci gaba da zama haka ba. Yau ɗanka ne, gobe kuma kai zai iya yi wa irin wannan abin. Dole ne ka nemo hanyar da za ka magance wannan matsala.”
Alhaji Haladu ya yi shiru, yana kallon ƙasa. A zahiri, ya san abokinsa yana faɗin haka ne saboda bai san waye Madugu ba, amma matsalar ita ce, bai san hanyar da zai bi ba domin gaba da shi hatsari ne, yaron.
A ɗaya ɓangaren kuwa, Ammar yana shiga banɗaki ya nufa domin wanka. Yana fitowa, ya nemi guri ya zauna a bakin gadonsa. Duk da yadda ya wanke dattin jikinsa na tsawon kwana uku, amma hakan bai rage masa zafin da yake ji a jikinsa ba. Fuskarsa kuma har zuwa lokacin a kumbure take, ga jajayen shatin hannun Madugu da har yanzu suke bayyane a kumatunsa.
Ya ɗauki wayarsa da ke gefen gado, ya kunna ta. Saƙonni ne ke ta rigingimo na shigowa.
Abokansa ne suke ta nemansa, musamman waɗanda suka saba fita yawon banza tare da shi.
Ya buɗe saƙon ɗaya daga cikinsu.
Bro, ina ka ɓuya ne? Mun yi ta kiranka, wayar ba ta zuwa. Tun jiya na so zuwa gidan ku, ko dai ka samu wani guri ne ka lafe?
Ammar ya yi wani dogon tsaki na takaici. Ya rasa abin da zai ce musu, kowa haushinsa yake ji. Ta yaya zai gaya musu cewa ya kwashe kwanaki uku a hannun Madugu, yana shan azaba?
Ya ajiye wayar, sannan ya dafe kansa.
“Wallahi, sai na rama!”
Ya furta maganar cikin fushi, yana kallon kansa a madubin da ke gabansa.
Sai dai kafin ya gama maganar, ya tuna da marin da Madugu ya yi masa, tsananin azabar marin ya tuna. Take jikinsa ya ɗauki rawa, ya girgiza kai da ƙarfi yana faɗin:
“Astagfirullah! A'a, ba zan sake kusantar wannan mahaukacin ba. Ni ƙasar nan zan bari.”
Yunwar da yake ji ce ta sa shi fitowa daga ɗakin. Ya sami mahaifiyarsa a falo, tana zaune tana kallon wani shiri a talabijin.
Ta ɗago ta kalle shi, sannan ta mayar da dubanta ga talabijin ɗin.
“Ammar, zo nan.”
Ya tsaya, yana kallonta, kafin ya ce:
“Na'am, Mami.”
“Ka zo ka zauna, na ce.”
Zuwaya yi ya zauna a kujerar da ke kusa da ita, amma ya kau da kansa gefe guda. Mahaifiyarsa ta dube shi sosai, tana kallonsa, ganin yadda kamanninsa suka sauya, fuskar ta yi jajir, har wani ƙyalli take.
“Ka ga abin da ya faru da kai ko? Me kake so ka zama ne, Ammar? Me ya sa ka ƙi jin maganar da nake gaya maka, har ka jefa kanka cikin wannan matsala? Ka ga yadda ka koma kuwa?”
Ammar ya haɗiye yawu, ya ce:
“Mami, na san na yi kuskure, amma wallahi ban yi tunanin zai kai ga haka ba, kuma ba zan ƙara ba.”
“Ba ka yi tunanin me zai faru ba? Na hana ka wannan ɗabi'ar, amma ka ƙi ji, kake biyewa yaran banza. Yanzu ga sakamakon abin da ka aikata.”
Ya sunkuyar da kansa, bai ce komai ba. Mahaifiyarsa ta sauke ajiyar zuciya.
“Ba na jin daɗin ganin abin da ya faru da kai ba, Ammar. Kai ɗana ne, kuma duk abin da ya same ka yana damuna. Amma ba zan goyi bayan abin da ka yi wanda ba daidai ba saboda kawai kai ɗana ne. Zan ba ka shawara kamar yadda na saba a yanzu, a matsayin mahaifiyarka. Hanyar da ka ɗauka ba mai ɓillewa ba ce. Duka-duka shekarunka nawa? Karatu ya kamata ka tsaya ka yi, ba shirme ba.”
Ammar ya ɗago ya kalle ta a raunace, sannan ya ce:
“Mami, wallahi na yi nadama. Ba zan sake ba. Amma ina roƙon ku, ku bar ni in tafi daga wannan garin. Ba zan iya ci gaba da zama a nan ba, ina tsoron sake haɗuwa da shi.”
Murmushi ta yi, a zuciyarta tana godiya ga Allah da ya kawo Madugu cikin rayuwar ɗan nata, domin duk lokacin da take masa faɗa, bai taɓa nuna nadama ta tsoro kamar yau ba. Har zuciyarta take hango abin da yake faɗa gaskiya ne. Shiru ta yi na ɗan lokaci.
“Ka tashi ka je ka ci abinci, sannan ka samu magani ka sha, kiɗan waɗannan raunukan na jikin ka.”
“Ai ba magani ba, ya ci abincin kawai mu tafi, in kai shi asibiti.”
Alhaji Haladu ya ke faɗin haka daidai lokacin da yake shigowa falon. Ba ta sake cewa komai ba. Ita dai, haka Ammar ya zauna ya ci abincin sosai, kafin suka tafi zuwa asibitin.
Daga gidan kansila gida ya nufa, ko da ya shiga falon Ammah, yunwa ce ta dawo da shi gidan da ba zai dawo yanzu ba.
Ammah na zaune a falo, ita kuwa Rooman tana sanye da uniform ɗin makaranta, ga littafinta a gabanta, da alama wani aikin aka ba su a makarantar take ƙoƙarin kammalawa kafin ta tafi.
Yana sallama suka haɗa ido da Ammah, saurin sunkuyar da kansa ya yi, ƙasa yana turo baki.
Rooman ta ce, “Kasan, Yaya ka dawo, in zubo maka abinci ko ba ka jin yunwa?”
“Ban sani ba, ai kin san Sahabi ne ni, dole ki tambayi ko ina jin yunwa.”
Ya faɗa yana muzurai, duk yanayin hakan ne kuma saboda kada Ammah ta yi masa magana a kan abin da ya yi.
Kusa da ƙafarta ya nemi ya zauna, sannan ya yi ƙasa da kai.
“Hutawarki lafiya, Ammah. Sayyid ɗinki na jin yunwa, yau ban ci komai ba fa.”
Har lokacin ba ta ɗauke ido a kansa ba. Rooman kuwa, tun bayan maganarsa ta tashi ta je ta zubo abincin ta kawo masa.
“Abin da ka yi ka kyauta kenan, Sayyid? Iya kakarka ce fa, sauran kuma ’yan uwan mahaifinka ne. Ya kamata ka dinga girmama su, bai kamata ba abin da ka yi. Don haka, ba na son hakan ya sake faruwa.”
“Ammah, babu girmamawa tsakanina da wanda ba ya mutunta ki, ko waye shi. Ni, ba ni da dangin mahaifi, ke da kai gare ni, sai kuma Rooman. Amma ni, waccan munafukar tsohuwar ba kaka ta ba ce...”
“Sayyid!”
Ammah ta katse shi da tsawa, abin da ya fi tsana a rayuwarsa, wato a yi masa tsawa ko kuma a yi masa tsaki, amma da yake Ammah ce, sai ya ƙara tsugunar da kai.
“A huce haka, Ammah.”
Ya faɗa yana tura abincin da yake gabansa gefe. Sanin halinsa, yanzu zai iya ƙin cin abincin, ya sa ta sassauta.
“Ka saka hannu a abincin nan, ka yi sauri ka cinye shi, na gaya maka. Sannan ka gama, ka tashi ka je ka ba su haƙuri!”
Da wani irin sauri ya ɗago ya kalle ta, ransa a matuƙar ɓace. Nuna kansa yake da hannunsa yana faɗin:
“Ni! In je na ba su haƙuri, Ammah? Lallai, kusa kin ja musu masifa! Na rantse da Rahmanu, muddin na ba su haƙuri, ni Sayyid da kaina, to, abin da zan yi musu ya fi wanda na yi da farko! Ba dai kin ce na je na ba su haƙuri ba? Zan je!”
Ya faɗa yana miƙe tsaye zai fita.
Ta san halinsa, yana da zuciya sosai, kuma duk duniya babu abin da ya tsana irin a tursasa shi yin abu. Ta sani yanzu fitinar ba za ta mutu ba, haka ya sa ta kira shi da ƙarfi.
“Sayyid! Dawo ka zauna ka ci abinci.”
Bai sake taki ba, ya dawo ya zauna yana ta huci kamar kumurci. Ta yaya ma Ammah za ta ce ya je ya ba su haƙuri, mutanen da suke wulaƙanta rayuwarsu? Shi har abada ba su da wani amfani a gare shi, balle kuma har ya kira su da ’yan uwan mahaifinsa.
Kallon da Ammah take masa ne, tare da ɗaukar ruwa ta ba shi, ya sa ya amsa ya sha kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fara cin abincin. Sau biyu ya ci, suka tsinkayi wata murya a hankali, mai cike da yarinta da kuma sanyi tana faɗin:
“Assalamu alaikum, Ammah, Rooman. In shigo? Ba ya nan?”
Tsayawa ya yi da cin abincin saboda mamakin jin wata murya kamar ta ɗan tsuntsu, kuma ga shi babu kowa.
“Ammah, maganin ki ne Mama ta ce na kawo miki. In shigo? Ba ya nan?”
Ta sake maimaita maganar, kuma har lokacin ba ta shigo ɗakin ba. Muryarta kawai suke ji.
Ammah ta gane waye, haka Rooman wacce take danne dariyarta, domin ita har ga Allah, drama ɗin ’ya’yanta da Leenah yana ba ta dariya.
“Shigo mana, Leenah. Me kika tsaya daga waje kina magana?”
Ammah ta faɗa da mamakin halin Leenah ɗin da rashin wayawarta. Ta san dole Mamanta ta yi mata, in ba haka ba, da ba za ta taɓa shigowa ba.
Ita kuwa, tun da ta ji Ammah ta amsa mata da ta shigo, sai ta ɗauka ba ya nan. Rawar da jikinta yake yi ya ɗan ragu, sannan ta ɗaga labule ta shigo.
Sai da ta kawo tsakiyar falon, idanunta ya sauka a kansa, yana zaune kusa da Ammah yana cin abinci. Sakin maganin ta yi a ƙasa da ƙarfi, ya fashe. Rawar da jikinta yake yi sai ga shi ya dawo sabo.
“Na gaya wa Mama ba zan shigo ba, amma ta ce dole sai na zo. Ni dai ina kwana ne, yake shirin ƙarewa...”
Ta faɗa tana kuka sosai da sosai. Wani irin baƙin ciki ne ya tokare zuciyarsa. Ture abincin ya yi gefe, ya miƙe ya nufi inda take. Yau zai yi maganinta kuwa, dama dazu ba wai ya ƙyale ta ba ne, yanzu ga shi ta sake taka ƙafarta gidansu.
Ita kuwa, ganin tasowarsa ya sa kawai ta kwanta kafin ya ƙaraso. Sosai ta runtse ido, da rawar baki take faɗin:
“Ko za ka yanka ni, Yaya Madugu, na riga na kwanta. Amma don Allah kada ka yanka ni da wannan wuƙar taka, kuma wallahi ban san kana gidan ba, da ba zan shigo ba. Yanzu ma ƙarshen kwana ne ya kawo ni...”
“Ke mahaukaciya! Miƙe nan ki kalleni!”
Ya daka mata tsawa, haushin da yake ji zai sauke shi a kanta kuwa, ina, ba ta yi wasa ba.
“Sayyid!”
Ammah ta kira shi.