Free chapter · Read without an account
76
A cikin gidan, babu abin da kake ji yana tashi sai hayaniyar mutane masu hadadar biki.
Kowa na da abin da yake yi, wasu na kai-komo da kayan abinci, wasu na faman tarbar baƙi, yayin da wasu ke ta faman gudanar da sauran shirye-shirye.
Inna Kareema ta fito daga sashin Kawu Abdullahi, hannunta ɗauke da ƙatuwar kula ta abinci, tana nufar sashin Jagarɗo. Sai ta yi kiciɓis da wata baƙuwa da ke shigowa.
Ta dakata fuskarta ta washe da tsantsar fara'a. Ta ajiye kular a ƙasa tana cewa,"Maraba, maraba da mutanen Abuja! Wato ku sai yau kuke tafe?"
Ta faɗa tana ƙarasawa gare ta, ta tarbe ta hannu bibbiyu tare da karɓar ƙatuwar jakar da ke hannunta. Daga yanayin fuskokinsu, a bayyane yake cewa dukkansu sun yi matuƙar farin cikin sake ganin juna.
Dattijuwar baƙa mai suna Yaya Sahura ta yi murmushi ta ce,"Yo ke Kareema, ai wannan biki da sai an gama za ku gan mu."
Inna Kareema ta ɗan ja da baya tana kallonta.
"Kai haba dai! Lafiya kuwa?"
"Ƙalau. Mu da zatonmu Litinin ta sama aka ce za a kawo lefe, taron biki kuma a fara ranar Laraba. Sai daren jiya da Lamiɗo ya kira waya yake cewa da Baban Yara ai bai ga gimlawarmu ba. Shi ne yau fa babu shiri, muka bugo sammako."
Inna Kareema ta ɗauki kular abincin, suka ci gaba da tafiya tare.
"To ai kin san a yadda auren ya zo. Shi Dottijo ma cewa ya yi mene ne na cewa sai an yi wani taron biki, tun da dai an jima da ɗaura aure. A kai yarinya ɗakinta kawai. To kuma kin san lamarin Daada. Ita taron ma cewa ta yi sai an yi sati guda ana yi, yadda Kakar mijin zata gane su ne ƙanan alhaki. Da ƙyar Dottijo ya shawo kanta fa. Yanzu dai za a yi kwana biyu. Jiya an yi Kamu, yau za mu yi al'adarmu ta Fulani da kika sa ni, sai gobe kuma a kaita gidanta."
Yaya Sahura ta yi dariya, suka wuce suna ci gaba da tattaunawa.
"Hmmm, ai da yake Kakar mijin ce ta so ta ɓata lamarin, kada ki ga irin tataɓarzar da aka sha kafin Daada ta yarda ta janye batun saki. Amma da tsaye ta yi, ta ce ko zai mutu sai ya sakar mata jika. Da ƙyar su Dottijo dai suka shawo kanta ta haƙura."
A parlon Hajjah suka yada zango, inda babu kowa a lokacin. Da shigarsu idanun Yaya Sahura suka sauka kan jerin akwatunan da aka jera waje guda. Ta zaro ido waje, ta kasa ɓoye mamakinta.
"Wannan uban akwatunan fa kamar za a buɗe sabon kanti! Kar dai ki ce min su ne lefen?"
Inna Kareema ta wuce ta ajiye kular hannunta, tana cewa,"Ai ko dai abin da kowa ke faɗa kenan. Fullo abin nata sai son barka! Ƴa ta yi goshi fa, domin kaf jikokin gidan nan albarka. Na ce da yanzu Daada ta ja mata, ta yi asarar wannan abin arziƙin."
"Ma sha Allahu! Ki ga akwatuna kamar ba a rashin kuɗi a ƙasar nan. Kalli fa yadda aka ɗaure su da ribom, ka ce lefen da ake kaiwa gidan sarki ko gidan shugaban ƙasa."
Yaya Sahura ta faɗa tana taɓa akwatunan da aka jera a wuri guda, ɗaiɗai har guda talatin.
Inna Kareema ta wuce ta rufe ƙofar parlon, sannan ta dawo tana cewa,"Buɗe su duk ki gani. Gwalagwalai ne a ciki sun fi goma. Lefen nan dai in faɗa miki, tun ranar farko ba a ƙara buɗe su ba. Kin san ba zuciyar kowa ce mai kyau ba. Masu ɗan hali kuma ba a gane musu. Zan rantse miki kaf kayan da ke ciki babu na ƙasar nan. Daada ta ce ko ɗankwali ba za a taɓa ba. Sai ta je gidan mijinta ta dinga ɗauka tana ɗinkawa."
Nan suka shiga buɗe akwatunan, suna ɗauko kaya suna dubawa, suna ta nuna wa juna abubuwan da suka gani, irin kayan ma da ba su taɓa gani ba, duk kuwa da irin yadda zuri'ar gidan ke auren manyan masu kuɗi. Yaya Sahura sai saka albarka take yi, tana yabawa da irin kayan.
A ɗayan ɓangaren, a ɗakin Daada, waya ce maƙale a kunnenta. Tana magana cikin fushi, muryarta cike da rashin amincewa.
"Ka ga Arɗo, ni bana son wannan magana. Su kwashe kayansu kawai! Duk wani kaya da suka zuba a kwashe su a kai musu gidansu. Haka kawai yarinya ta tare, daga baya a riƙa goranta mata, ana cewa ai kayan ɗakinta ma iyayen miji ne suka yi mata. A'a sam! Ku kwashe musu kayansu ku jera na ku."
Daga cikin wayar, Arɗo ya ce, "To Daada wallahi duk mun rasa yadda za mu yi da su fa. Ita mahaifiyar yaron ta ce gudummawarta ce, Fullo ƴa ce a wurinta..."
Ta yi saurin katse shi, ta runtse idanunta tana girgiza kai.
"Arɗo akwai ka da shegen gardama! Ka faɗa musu gudummawar da za su bayar ba ma so. Jikata bata buƙata."
Arɗo ya amsa cikin ladabi, "To shikenan Daada. Yadda kika ce."
Ta sake tambayarsa,"Yanzu an kammala kawo kayan gaba ɗaya?"
"A'a. Da yake bedroom ɗin guda huɗu ne, mu kuma order ɗin biyu aka yi, to amma yanzu Saifullahi ya kira wani abokinsa da ke can ƙasar Turkey kan ya taho da su. Zuwa gobe idan zai dawo, zai kawo su."
Daada ta gyaɗa kai, kamar yana gabanta.
"To shikenan. Hakan ya yi. Ina fatan kun faɗa masa kaya masu kyau da tsada ake buƙata ko? Ka ga mun san akwai na wajen anan, amma ni na fi so a karɓo su kai tsaye daga can. Zan fi yarda da ingancinsu."
"An sanar da shi Daada."
"Ku yi maganar kuɗi da shi, sai ka kira Maudo ka faɗa masa. Akwai wasu kayan ƙyale-ƙyale ma da Amatullahi ta nuna min jiya, kuma ba mu taho da su daga can Saudiyya ba. Zan sa ta turo maka hotunansu a waya, sai ya duba ya ga ko akwai irin su a can ƙasar, idan akwai a taho mata da su."
"To Daada. Sai ta turo yanzu."
"Yo na ji. Giɗaɗo ma sun taho yanzu da sauran kaya. Don Allah, ku yi wa ƴar nan jere na musamman. Ina nufin irin jeren da zai hana wannan figaggiyar tsohuwar samun kwanciyar hankali. Ni ban so ma ya haɗe musu gida ba wallahi. Na so a raba su. Sam bana son abin da zai ɗaga wa jikata hankali. Ina tsoron a haɗe su gida ɗaya, su riƙa cutar da ita. Tun da Allah bai yi ta da baki ba, shashasha ce, banda kuka babu uwar abin da ta iya."
Arɗo ya yi murmushi yana cewa, "Daada ai ko hakan ma kamar ya raba musu gidan ne. Kowacce da part ɗinta, kuma akwai tazara sosai tsakanin part ɗinsu."
Ta taɓe baki, ba ta ce masa komai ba. Sai ta kashe wayar ta ajiye a gefenta, sannan ta juya ta dubi Safara'u.
"Ke jiya da kuka je gidan su mijin, kun gani da gaske ba shi da lafiya, ko kuwa iskanci ne da rainin hankali kawai za a yi mana saboda ba ya son zuwa bikin?"
Safara'u ta amsa, "Ƙwarai kuwa Daada. Don zuwan mu asibitin ne aka sallame shi ma. Ba shi da lafiya sosai. An ce yana fama da ciwon ƙoda ne."
Daada ta taɓe baki.
"Allah ya kawo sauƙi. Rashin lafiyarsa dai ba ita za ta hana mu shagulgulan biki ba."
Ta waiga ta kalli Amatullahi da ke charting a wayarta.
"Abin jiya da kika nuna min, ki tura wa Arɗo yanzu."
Sannan ta juya ga hadimarta da ke matsa mata ƙafa.
"Ki leƙa ɓangaren Gaji ki kirawo min Fullo. Idan ba a yi wasa ba, tana can tana wannan ɗan banzan halin nata. Don yau ko ganinta ban yi ba tun safe. Ina kyautata zaton ma ko abinci ba ta ci ba."
Tana rufe baki, Maijidda ta shigo ɗakin. Ta wuce tana ajiye kayan da ke hannunta. Daada ta dubeta.
"Yauwa, ke ina wannan ƴar take?"
Maijidda ta turo baki, ta ɓata rai.
"Tana can."
Daada ta ɗago kai, amma kafin ta yi magana Maijidda ta yi hanyar wucewa. Nan take ta rarumi sandarta ta buga mata.
"Can ina? Dan ubanki ko sheɗan ya san can ɗin ne da zan tambaye ki, ki ce min wani can. Sai yanzu ma na gane mugun halin da Fullo ta kwaso wajenki ta koya. Ai Hausawa ba su yi ƙarya ba da suka ce abokin ɓarawo ɓarawo ne, haka ma zama da maɗaukin kanwa. Sam sam ba ki yi halin ƙwarai irin na kakarki ba. Dole na raba ƙawancenku, don ba za a kaita gidan miji ba ki je ki lalata mata aure."
Maijidda ta dafe wurin da aka duketa, tana shafawa saboda zafin da ta ji.
"Tana sashin Kawu Musbahu, a ɗakin Adda Amina."
Daada ta yi hanyar fita, amma sai ta sake juyowa ta kira ta.
"Ke zo nan."
Maijidda ta dawo tana taku a hankali, ta tsaya a gabanta tana rakuɓewa wuri ɗaya. Daada ta zuba mata ido na ɗan lokaci kafin ta tambaye ta,"Me aka yi miki da ma?"
Maijidda ta fara hawaye.
"Tun jiya take ta kuka. Na tambayeta abin da aka yi mata, amma ta ƙi faɗa min. Ina ta rarrashinta ma ta ƙi yin shiru. Zazzaɓi ya rufeta, na ba ta magani ma ta ƙi ta sha."
"Wace ce dama?"
"Hussainata mana."
Daada ta miƙe, ta jingina da sandarta sannan ta fice daga ɗakin rai ɓace. Ta shiga parlon Amina, mutane na ta gaida ita. Ba ta amsa wa kowa ba; kai tsaye ta wuce cikin ɗakin.
Tanaa shiga, ta sami Fullo kwance a kan gado, ta yi ruff da ciki jikinta a dunƙule. Daada ta ƙarasa gare ta, ta ɗaga sandarta ta buga mata a gadon baya.
Fullo ta miƙe a zabure, tana dafe wurin da aka duketa. Hawaye suka sake cika idanunta, suka gangaro a kan fuskarta, duk da cewa kukan da ta sha yi a kwanakin nan ya ɗan tsagaita. Amma zafin dukan ya ratsa ta sosai, har sai da ƙashin bayanta ya amsa.
Daada ta tsaya tana kallon idanunta da suka yi jawur, sun kumbura saboda yawan kuka. Fuskarta ma ta yi ja, ko tausayawa kanta ba ta yi.
Cikin matuƙar ɓacin rai ta ce,"Ke wai dan uwar ubanki, tare da kuka aka haife ku ne, ko kuma an haife ki ne don ki yi ta kuka a duniya?"
Ta nemi wuri ta zauna, tana ci gaba da faɗa.
"Ƴar banzar yarinya mara tawakkali! Idan ba za ki iya jurar rashin uban naki ba, ki sha fiya-fiya ki bi shi mana. Idan kuma auren ne ba kya so, ki buɗe baki ki faɗa."
Ta ɗan karkata jikinta zuwa gare ta, muryarta na ƙara kauri.
"Nan na tayar da jijiyoyin wuya a kan sai an sake ki saboda ina so na ƙwatar miki ƴancinki. Iyayen yaron nan suka zo suna ba ni haƙuri, na ƙi na haƙura. Har sai da aka kai ƙarata gaban mahaifina tukunna."
Ta girgiza kai cike da takaici.
"Ko kaɗan bana jurar ganin an wulaƙanta min jinina. Da kika san ba za ki iya zama da shi ba tun ranar da suka kawo lefe, ba sai ki faɗa ba, a ce su juya da abinsu."
Fullo ta ɗago idanunta a hankali, waɗanda take jin sun yi mata nauyi, ta kalli Daada.
"Banda lafiya ne fa."
Daada ta zabga mata uwar harara.
"Da ba ki da lafiya, kuma sai aka ce kuka ne zai yi miki magani? Mtswww."
Ta miƙe ta fice daga ɗakin, tana ci gaba da mita. A cikin parlon ta sami Ammi a tsakiyar mutane, tana raba musu abinci. Nan take ta kira ta, Ammi ta ajiye abin da ke hannunta, ta amsa kiran da gaggawa.
"Ɗanki ya wuce ko yana nan?"
Ammi ta ɗan kalleta.
"Wanne a ciki?"
Daada ta harare ta kafin ta amsa.
"Mutanen ƙwarai ake nema ba ƴan wiwi ba. Likitan nake tambayarki, ba wannan mara kunyar yaron ba."
Ammi ta ce, "Yana nan, amma ina jin kamar shi ya wuce kai Maudo airport ɗazu."
"To ina waccan yarinyar ƙanwarsa, mai aikin asibitin?"
"Sun je gidan Fatima, anjima kaɗan za su dawo."
Daada ta ja tsaki.
"Maza kirawota ta dawo, ta zo ta duba jikin yarinyar nan. Ta yi mata allura yadda zazzaɓin zai fi saurin sauka. Kin ga anjima akwai taro. Ba a tara jama'a babu amarya ba."
Ammi ta ɗan firgita.
"Bata da lafiya ne?"
Daada ta kaɗa kai cikin takaici.
"Yo gata can dai tana neman kashe kanta. Ciwo yana cinta babu wanda ta faɗawa saboda shegen nurƙufanci da miskilanci da baƙin hali irin na Hayyo."
Ammi ta ɗauki wayarta ta kira Yusrah. Tana ɗagawa ta gaya mata ta dawo yanzu.
Daada ta sa aka kira mata Ummi. Itama sai ga ta cikin hanzari ba tare da ɓata lokaci ba.
"Ki shiga ciki ki ji damuwar ƴarki, tun da ke dai soluwar uwa ce."
Ta faɗa tana bin Ummi da harara. A gefe guda tana jin haushinta. Fullo dai tun bayan ficewar Daada da sauran mutanen, tana zaune a kan gadon, hannunta riƙe da farar takardar da Turaki ya ba ta ranar da suka je dubansa a asibiti lokacin da ba shi da lafiya.
Ta juya takardar ta kuma juya ta. Duk lokacin da zata kalli takardar, sai ta ji wani sabon nauyi ya ƙara danne zuciyarta. Kuma duk yadda take ƙoƙarin riƙe hawayenta, amma sai hakan ya faskara, har idanunta suna dusashewa wajen ganin rubutun.
Ta jinginar da kanta a jikin bango, ta runtse idanunta sosai, tana ƙoƙarin danne kukan da ke neman cin ƙarfinta. Hawayen suka gangaro mata a kumatu, sannan kukan da take ta ƙoƙarin ɓoyewa ya kuɓuce mata da ƙarfi.
A daidai lokacin ne Ummi ta shigo ɗakin. Ta ƙarasa bakin gadon tana tambayarta cikin damuwa,"Lafiya Auta?"
Fullo ba ta ma san ta shigo ba sai a lokacin da taji maganarta. Da sauri ta cusa takardar a cikin rigarta, tana share fuskarta da bayan hannu.
Ummi ta zauna a gefenta, ta kwantota a kafaɗarta, tana lallashinta tare da ba ta haƙuri.
A tunaninta, kukan Fullo ba wani abu ba ne illa irin kukan da kowacce amarya kan yi na rabuwa da gida.
Fullo ta sha wahala kafin ta samu damar rarrashin zuciyarta. Ba ta son Ummi ta gano abin da ke faruwa. Domin ba ta san irin halin da zata shiga ba idan ta ga takardar sakin da take ɓoye a jikinta. Ba lallai ta iya ɗaukar wannan ƙaddarar ba.
Za ta ga kamar ita ma ba ta yi dace da samun miji ba, kamar yadda ita kanta ba ta yi sa'ar samun miji ba a lokacin da ta auri mahaifinta. Wannan tunanin ne ya ƙara tabbatar mata da cewa dole ta ɓoye takardar.
Ba ta da niyyar gaya wa kowa abin da ya faru a yanzu. Tun da dai za ta zauna a gidan miji har lokacin idda ya ƙare, za ta jira har ta kammala iddarta a can kafin ta sanar wa da kowa gaskiyar abin da ya faru. Amma ba yanzu ba, ba a lokacin da ba ta san irin halin da Ummi zata shiga ba.
Babu daɗewa, Yusrah ta shigo ta yi wa Fullo allura. Aka ɗebo mata magunguna da yawa daga first aid ɗin da aka ɗauko a ɗakin Innah, aka ba ta.
Ummi ce da kanta ta zaunar da ita, ta bata abinci. Fullo ta ci a hankali, duk da cewa ba ta jin sha'awar cin komai. Amma a hakan ta daure sai da ta ci da dama sannan Ummi ta ƙyale ta.
Ummi ta shafa kanta cikin tausayi.
"Ki daina kukan haka nan, kin ji Auta. Bari na je ana ta baƙi daga ɓangarenmu. Idan kika ji daɗin jikinki, sai ki zo ku gaisa da su Yaya Murja."
Fullo ta ɗago kai ta kalli Ummi, fuskarta ce ta bayyana tambayar ba muryarta ba.
"Wace ita?"
Ummi ta ce,"Da babarta da kaka, ubansu ɗaya, suna can sun zo ma fa da yawansu. Tambayarki kawai suke yi. Na yi zaton kuna can gidan Asma'u ne, shi ya sa."
Fullo ta gyaɗa kai kawai ba tare da ta ce komai ba. Ummi ta miƙe ta fita, daidai lokacin da su Maijidda suka shigo ɗakin suna ta masifa kan ɗinkin kayan da tela ya yi musu ba daidai ba.
"Na rantse da Allah, in da ba yau za mu sa kayan nan ba, sai ya biya ni zan baro shagonsa. Ɗan iska mai kama da ɗan daudu."
AmaturRahman ta faɗa cike da fushi. Maijidda ta yi watsi da nata kayan a kan gado, sannan ta ce,"Ai ni idan kika ga na saka waɗannan kayan, to an sauya ni ne. Gwamma idan na koma gida na dinga saka su idan zan yi aiki, amma ba a bikin Hussainata ba. Ban da rainin hankali, ɗinki sai ka ce an ce masa tsofaffi ne za su saka."
Amatullah ma ta shigo ta jefar da ledar da ke hannunta. Raudha ma haka ta yi. Duk wanda ya kalle su dai zai gane cewa babu wadda ranta yake daɗi.
Raudha ta tsaya a jikin wardrobe tana fuskantar Fullo, ta harɗe hannayenta a ƙirji, cike da damuwa akan ƴar uwartata ta ce, "Kin ga yadda fuskarki ta kumbura kuwa?"
Fullo ta runtse idonta kawai, ta kwanta ta juya musu baya kamar ba ta ji ta ba.
Amatullah ta ce,"Ɗazu Hammah Abdulhamid cewa ya yi idan ya dawo ya tarar ba ta daina ba, sai ya zaneta. Ya ce babu ruwansa da matar aure ce, ni na rasa me aka mata. Gata da zurfin ciki ta ƙi ta buɗe cikinta. Yanzu idan ba ki faɗa mana damuwarki ba wa za ki faɗawa. Bana jin ko Ummi kin sanarwa."
Raudha ta sauke numfashi, ta girgiza kai kaɗan.
"I never see such a kind of person mai shegen kuka ma irinta. Da muna Saudiya na yi zaton ko don Daada ta ce sai an saketa ne. Amma yanzu da muka dawo, na kasa fahimtar auren ne ba ta so, ko kuwa kukan barin gida ne."
"Kin taɓa ganin amaryar da take kuka irin haka saboda za ta bar gida? Ita dai ku barta. Ƴar auta ce, shagwaɓa ta yi mata yawa."
AmaturRahman ta faɗa tana wucewa zuwa toilet. Raudha ta ƙarasa ta zauna kusa da Fullo, ta kamo hannunta ta riƙe. Daga nan ta ɗauki wayarta ta kira mai kwalliyar da za ta zo ta yi wa amaryar makeup kafin lokacin Fulani Day. Bayan sun gama wayar, suka ci gaba da tattauna abubuwan da za su yi a wajen taron.
Da ƙarfe uku na rana aka fara shirya amarya. Wata cousin ɗinsu da ta zo daga Benue ta ci gaba da complain kan rashin zuwan ango, tana ta ƙorafin su ba haka suka so ba. Ta yi ta masifa har sai da aka yi mata bayanin cewa ba shi da lafiya, sannan ta ɗan lafa.
Fullo dai ko kaɗan babu walwala a fuskarta. Ƙwayar idanunta suna manne a cikin mudubi, ka rantse da Allah kanta take kallo. Sai dai ko kusa babu abin da take gani a cikin madubin, sai hoton ranar da suka je asibiti.
Tana hasko lokacin da suka shiga ɗakin da Turaki yake kwance, an sa masa oxygen, ga wasu na'urori da aka haɗa a jikinsa. Kallo ɗaya kawai za ka yi masa, idanunka su cika da ƙwalla, tsoron Allah ya kama ka.
A lokacin da ta gan shi, ta yi mugun tsorata, tsoron da har ta ji kamar ƙafafunta ba za su iya ɗaukarta su kaita gabansa ba.
Jikinsa ya kumbura kamar wanda aka hura. A irin yadda yake ma za ka iya rantsewa gawar mutum kake kallo, ba mai rai ba.
Har zuwa yanzu da take kan kujerar nan za a mata kwalliya. Ta kasa samun kalmomin da za su bayyana abin da ta ji a lokacin da ta gan shi, balle kuma abin da take ji yanzun.
Ta runtse idonta, tana ƙoƙarin sake hasko duk abin da ya faru a lokacin, a waccan ranar.
Tana tuna yadda ta gyara masa hannunsa a kan gadon bisa buƙatarsa. Tana tuna yadda bayan ta riƙe hannunsa, ta kasa sakewa. Ta riƙe shi, wani irin riƙo da ba ta taɓa yiwa hannun wani mahaluƙi ba.
Har yanzu tana jin sautin muryarta a kunnuwanta, muryar da ta dinga fita da amo saboda tsananin tausayi, tana maimaita masa kalmar "sannu" kamar dai a lokacin, yawun bakinta ne kaɗai zasu yi tasirin rage masa raɗaɗin ciwon da yake ji.
Sai kuma a lokacin ta ji a jikinta kamar yana buƙatar wani abu daga gare ta. Tana tuna yadda ya riƙo ɗayan hannunta, ya zura mata farar takarda a ciki, idanuwansa na rumtsewa, don in har da ta gani da kyau, zata iya ganin yadda zuciyarsa ta harbo ƙirjinsa a lokacin da yake bata.
A yanzun da take zaune, tana iya jin yadda hannunta ke karkarwa, irin karkarwar da hannunta ya dinƙa yi lokacin da ya saka mata farar takardar a hannu. Farar takarda mai ɗauke da baƙin rubutu, rubutu mai ɗacin karantawa da haifar da ciwo a zuciya.
Ta san cewa ba ta son Turaki. Ko da bugawar daƙiƙa ɗaya ta agogo, ba ta taɓa jin wani abu a zuciyarta da za ta iya kira soyayya a gare shi ba. Tausayinsa kawai take ji, wanda ita kanta ta san Allah ne ya ɗora mata tausayinsa.
Sai dai gaba ɗaya ta rasa dalilin da yasa take jin ciwon sakin da ya yi mata. Sakin fa take nema, to why kuma yake nema ya zamar mata damuwa, why take jin kamar zuciyarta ba zata iya jurewar ɗauka ba?
Ta damu! Ta damu sosai da har take jin kamar numfashinta na gab da katsewa.
A tunaninta, sakin da Turaki zai yi mata tamkar cire ruɓaɓɓiyar ƙaya ne daga tafin ƙafarta. To amma me yasa akasin hakan?
Lokacin ɗaya ta ji kamar an fizge wani abu daga cikinta. Wani abu da ba ta san cewa tana ɗauke da shi ba sai a lokacin da aka ɗauke shi.
Ta sake hasko yadda ta ɗauki tsawon daƙiƙu uku tana kallon takardar kafin ta iya ɗaga idanunta, ta sauke su kan fuskarsa. Yana kallonta ne a lokacin, kuma ta ga akwai wani irin rauni a cikin idanunsa, raunin da har yanzu ta kasa mantawa da shi, raunin da take da tabbacin na ba shi da wani zaɓi ne. Ta san lokacin da idanunta suka manne a cikin nasa, amma ba za ta iya sanin ta yadda wasu azababben hawaye suka sauko mata ba.
Ta san cewa ta daɗe tana kallonsa, har sai da shi ya fara kau da nasa idanun daga nata. Ya juya fuskarsa gefe. Kuma wannan kauda fuskar ita tasa ta ji kamar an tsikare ta akan kujerar da take zaune. Cikin gaggawa ta miƙe, ta saki hannunsa da take riƙe da shi, ta fice daga ɗakin tana danne kukanta.
Kukan da har yau babu wanda ya iya gano dalilinsa, har da ita kanta. Kukan da duk ƙoƙarin da take yi na ganin ya tsaya, ya ƙi tsagaitawa. A zahiri, tana zaune gaban mai kwalliya, amma a baɗini tana can a ɗakin asibitin, tana kallon mutumin da ta yi imanin cewa ba ta son sa, amma sakin da ya yi mata, yasa tana jin kamar ta rasa wani ɓangare na rayuwarta ne.
Hawaye suka fara gangarowa a kan foundation ɗin da mai kwalliyar take blending mata.
Matar ta ja tsaki, ta matsa baya kaɗan tana kallon Fullo cikin ɓacin rai.
"Haba ke kuwa don Allah! Haka fa jiya ma kika yi mana, kika sa akai ta wasting time. Idan ba za ki iya daina kukan ba ki ce a fasa yi miki mana, ki daina wahalar da ni. Ni wallahi ban taɓa ganin amarya mai masifaffan kuka irin ki ba."
Ta faɗi hakan cikin murya, na wadda haƙurinta ya kusa ƙarewa.
Nan kowa ya fara hayayyaƙowa Fullo, wanda a ganinsu kukan da take bai dace da irin wannan ranar ba. Ran kowa ya ɓaci, Maijidda da Amatullah suka fita daga ɗakin suna gunaguni, Raudha kuma na tare da ita tana nuna mata rashin jin daɗin abinda take a fili.
Raudha ta miƙe ta ƙarasa ta kama Fullo, ta raka ta zuwa toilet, ta taimaka mata ta wanke fuskarta. Mai kwalliyar dai ta ƙi tashi daga inda take zaune. Duk da kuɗin da za a biya ta masu yawa ne, ba ta jin za ta ci gaba da wannan aikin wahalar da yake zama kamar ba shi da ƙarshe.
Sai da Ammi ta shigo ta yi mata magana, sannan ta miƙe, tana sake jaddadawa Fullo cewa kada ta ƙara ɓata mata aiki. In ba haka ba wallahi ko duk kuɗin duniya za a bata ba zata yi mata ba, ai jikinta ke aikin ba inji ba.
Fullo kallonta da saurarenta kawai take yi. Masifa take so ta yi, amma halin da Turaki ya jefata a ciki ya cire mata duk wani kuzari da ta san ubangiji ya halicceta da shi. Ba don haka ba, da makeup artist ɗin nan bata sake gigin ɗaga mata murya ba.