Free chapter · Read without an account

BOOK ONE CHAPTER 17

by Hindatu Auwal · ƘYAURE KARIYAR GIDA

           *ALIYA*


Tsaye take a kicin tana dafa ruwan tea. Data runtse idanunta ba abinda take gani se yanayin da suka kasance ita da Ustaz adaren jiya.



Tsahon daren bata san abinda ya faru ba tun bayan baccin da tayi. Kiran sallahn asuba ne ya tayar da ita kamar yanda ya tada Ustaz. 


Cike da kulawa ya raba jikinsa da nata ya shiga bathroom ya dauro alwallah ya sanya jallabiya, ya fesa turare.


A nutse ya tako inda take. Ya ran ƙwafo kansa ya sumbaci saman laɓɓanta dake matukar burgeshi fiyeda komai.



Muryan shi a tausashe ya kira sunan ta. Dama duk abinda ya keyi tana jinsa, idanuwa ne batason haɗawa dashi shiyasa bata bude idanun nata ba. Sai ta amsa kawai. Sumbatan daya ƙara yin mata yasan yata runtse idanunta da ƙarfi. Karan rufe ƙofan shi yasan yata sauke numfashi al'ajabi da taraddadin sauyin Ustaz na danne ta.



Seda abinda ta keji yasami zama akanta. Ta miƙe ta shige bedroom din ta tai alwallah tai sallah ta...... saukan hannun Ustaz da taji ya zagaye ƙugunta ya sanya tinanin ta katsewa ta zabura a tsorace. ya ƙara matso ta jikinsa, kanshi na sauka akan kafaɗan ta.


"What are you thinking matar Ustaz?!."


"Nothing." Ta fadi dasauri jikinta na tsuma.


"Wani irin nothing I expect zaki ce tinanin ka na keyi Habibi."


Cikin ƙoƙarin kama kanta da son barin tashan da yake son kai ta tace"ina kwana..."


Yai shiru bai amsa ba. Ta daure ta ƙarada"ya jikin naka?."


"Kin ɗauke komai ai. dama....duk ke kika jawo."


Yayi maganan ararrabe, cikin sanyi da wani irin yanayi alalace da yasanya tsigan jikin Aliya tashi gabadaya. Kanshi ya juya ya kalleta. Ya sakin mata iskan bakinshi acikin kunninta.


Janye jikinshi yayi daga nata. Ya kai hannu ya kashe gas din da ruwan data dora keta tausa.


Aliya tai tsaye kawai tana kallon sa. Ya sake ruwan a flask ya dora musu ruwan wanka ya kamo hannunta suka fito.



Kujerar ya jawo mata ta zauna. Ya bude food flask ya zuba abinci a flate, ruwan zafin data sanya citta, kaninfari da sauran kayan yaji wanda aka sako mata akayan gara ita sai daya ma ta taɓa amfani dashi asanda tayi tuwo sai yanzu data dafa mai ruwan tea dashi.



Atare suka ci abincin a mazubi daya. kanta dai akasa yake har suka ci, suka gama dan daya ɗago kanta zata ganshi yana kallon ta babu ko ƙiftawa.



Gashi tana son tai mai magana akan magani ta kasa. Yanda Ustaz yasauya alokaci guda abin na mata nauyi sosai.



Ganin yana ƙoƙarin fita ahaka yasanyata daurewa tai mai magana"Ustaz har yanzu akwai zazzaɓi ajikin ka. gashi idanuwan ka sunyi jaa alamar mura zai iya kama ka idan bakai taking action akai ba."


Idanunsa da yau suke kanta yaƙara kura mata yana cewa"Nima ina jinshi ajikina so idan na fita zan biya pharmacy na siyo magani tunda kin bani first aid jiya...." Yai ƴar dariya yana cigaba "ɗumin jikinki yanada daɗi sosai. nai fee..."


"Ustaz mana...!" Ta katse shi a shagwaɓe tana turo baki.


Ustaz yai dariya yana ɗago haɓanta da yatsun shi biyu. A taɓare ta kallesa. Ya rankwafo kamar zeyi magana sai kawai yai mata light kiss.



Aliya ta waro idanun arazane. He raised his eyebrows teasingly, a mischievous smile playing on his lips.



Jiki a matukar mace ta girgiza kai tana kallon sa ya ɗaga mata hannu alamar bye-bye yabuɗe kofa ya fice.




*ZAINAB*


Yai horn mai gadi yabuɗe. Suka shiga yai packing, suka nufi ɓangaren sa.


Two bedroom plat ne me kyau. Alhaji Haruna ya murza key a bedroom din.


Batare da wani ɓata lokaci ba Alhaji Haruna ya soma ƙoƙarin tuɓe kayansa.



Zainab ta durƙusa akan guiwoyinta hawaye na saukar mata da muryanta wacce ta rikice da kuka da damuwa ta soma roƙonsa.



"Don Allah kada ka keta min mutuncina....kada ka gurɓatamin rayuwa ta.... Ubangiji yayi hani da wannan saɓon a...."


"Is enough! Ni pha ba dole zan mikiba... it's on your own kiyi ko kibarshi. Khadijah na can akwance tsakanin rai da mutuwa. Ƴaƴanki na zaune da saran zaki tallafi rayuwar su. Farin cikin ki ko nasu seki zaɓa."



Ganin nashi imanin ya gushe ya sanyata miƙewa akan ƙafafuwanta.


Ta juya ta bude dakin tana jiyo muryan Alhaji Haruna yana kiranta sedai ko juyowa ba tayi ba balle ta amsa.



Tafiya ta keyi tana jefa ƙafafunta aduk inda ta samu. Lokaci zuwa lokaci ta kansa hannu ta share hawayen ta. Ko ranar dake dukanta bata ji. Bata san inda ƙafafuwanta ke janta ba seda taganta a tsakiyar kasuwan zaria.



Taja iska me kauri tana cigaba da tafiya duk da zuciyar ta dake bugawa kamar ze tsaga ƙirjinta ya fito. Kallon da mutane ke mata samm bai dame ta ba, don bama shi bane agaban ta.



Kai tsaye ta shiga babban shagon daya ƙawatu da kaya har ya gaji. Manyan mata na ta kara kaina acikin shagon wajen siyayyan kayan sitiru na kece raini a shagon.


Saman bene ta hau inda office din Ahmed yake. Sectary din shi dake zaune na ganin ta ya mike yai mata sanda zuwa sannan ya shiga office ɗin domin yin mata iso.



Befi mintina biyar ba ya fito da sakon daya sanya zuciyar Zainab tarwatse wa afilin ƙirjinta.



"Madam kiya hakuri oga yace ba zai sami daman ganin ki ba."



Murya na rawa tace"kace mai uzuri ke tafe dani....don Allah ya tai maka ya barni na ganshi."



Ba musu dan sakon ya juya da tausayin ta da take hangowa acikin idanunshi.



Tai tsaye tana jira. Sedai awannan karon ba ɗan sakon bane kadai. Shida Ahmed ne suka fito atare.



Ƙafafuwanta dake rawa taja dasauri ta nufeshi batareda tabari ya ƙariso wurin taba. 



Baki ta buɗe zatai magana Ahmed ya katse ta. "Acikin dangin mayu bansan daga wani tsatso kika fito ba. Nace ki fita daga rayuwa ta kin ƙi. Na...."



"Khadijah ne tai accident don...."



"Bana bukatar jin abinda ya faru....ki wuce ki tafi."



Tun kafin ya ƙarika maganan da yake yi ta zube akan guiwoyinta a gabansa, cikin kukan daya ƙwace mata ta buɗe bakinta kalaman Ahmed agareta suka sanyata dakatawa alalen dole.



"Idan har kika ƙara magana abakin igiyoyin dake riƙe dake agidana."



Jajayen idanunta ta ɗago ta kallesa komai na duniya na tsaya mata cak. Ta kalli Ahmed cikin idanu ta girgiza kanta kawai ta soma tafiya da nauyi mai girma atare da ita.



Seda ta fito bakin titin wurin sannan ta iya tsaida abin hawa ta hau tana gaya mai inda ze kaita.


Tafiya kawai suke yi tana kallon hanya da idanunta da suka kafe tun sanda Ahmed ya fesar da kalaman sa na ƙarshe agareta.



Suna isowa ta sauka. Ta nimi lamuninshi ta shiga cikin gidan ta ɗauko mai kuɗinsa sannan ta tambaye shi ko zai iya ɗaukan mata kaya zuwa kasuwa yace "Eh" sai tai mai izini yashigo cikin falonta ya ɗauko deep freezer dinta don ma harseda ta tallafa mai, ta dauko receipt din su suka kama hanya zuwa shagon Asad Electrical Shop dama acan Ahmed ke siyan mata duk wasu kayan electrics, awasu lokutan kuma suje tare.



Gaisawa sukayi a mutunce. Asad Ya duba fridge ganin bai sha wahala ba yasan yashi yin mai tayin daraja saɓanin sauran mutane ƴan kasuwa dake ma kayan mutane tayin wulakanci idan suka gansu a matse cikin yanayin buƙata.


Bata bar wurin Asad ba saida dubu ɗari biyunta cass a hannun ta.


*

Da gudu ta shiga asibitin. Bata je wurin su Khalid ba seda ta fara zuwa ta biya kudaden gabadaya dubu ɗari da tamanin da biyar. Suka bata receipt taje office ɗin doctorn dako sunanshi bata sani ba ta kai mai.



Nan da nan suka soma shirin yin aiki. Akazo aka ɗauketa aka shigar da ita theater room.



Bayan jira na adadin lokutan da bazasu iya ƙayyadewa ba, Doctorn daya soma dubata da sauran likitocin suka fito daga ɗakin.



Zainab ta mike tsaye tana kallon fuskokinsu. Ba suce da ita komai ba, ta fahimci wani abu daban da basu san da shiba yasamu Khadijah.



Doctor yagyara tsayuwa. Acikin aikinsa ba abinda ke bashi wahala kamar wannan, rasa kalaman sa yake, komai ya ƙwace masa, bayada yanda zeyi adole ya tattaro wasu kalmomi ya furta su ga Zainab dake tsaye zuciyar ta na rawa.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol