Free chapter · Read without an account

Page 8

by Fatima Sunusi Rabi'u · FARAR TUMFAFIYA

‎...FARAR TUMFAFIYA.
‎
‎
‎
‎©UMMU AFFAN
‎
‎
‎
‎Page *7*
‎
‎
‎
‎Barirah.
‎Ba ta ƙara sanin komi ba tun daga lokacin da ta sume a jikin Yaya Aliyu, sai farkowa tayi ta ganta kwance a parlourn Iyah ba kowa ciki sai ita. Da sauri ta miƙe ta fara waige-waige, ba ta ga kowa ba hakan ya saka ta sakin wata ajiyar zuciya ta koma ta zauna, a hankali takai hannu goshinta sai taji kamar wani abu aka saka mata a wurin, don wani iri take ji na rashin daɗi a goshin nata, ta miƙe a hankali ta shiga ɗakin Iyah, gaban Mirror ta tsaya sai ta ga fuskarta har lokacin da jurwayen hawayen da ya bushe, ga bushashshen jini ba duk a gefen goshin nata, ashe magani Iyah ta saka mata a goshin ƙilan Ararraɓi ne shi ya sa take jin wani iri a gurin, jiki a sanyaye ta dawo parlourn ta zauna saman kujera, da ace zata samu ruwa mai zafi sosai tabbas da wanka za tayi ta gasa jikinta, amma babu dama don tsoron fita take ba tasan yadda karonsu zai kaya da Andi ba, mugun tsoronta take ji musamman yadda ɗazun ta dage sai an binne ta tare da Saudatu.
‎
‎Tana zaune a gurin cikin taraddadi Iyah ta shugo ɗakin, da sauri ta zabura cike da tsoro, ganin Iyah ce sai ta zauna tana sauke numfashi, gabaɗaya jikinta ciwo yake mata amma ba ta da yadda zata yi. Iyah ta ƙaraso ta zauna kusa da ita.
‎
‎"Barirah kin tashi kenan?"
‎
‎"Uhmmm!"
‎
‎Ta faɗa a hankali kanta kuma a ƙasa, Iyah ta girgiza kai cike da tausayi.
‎
‎"Akwai ruwan zafi a kitchen, kije ki juye ki shiga banɗaki kiyi wanka kizo kici abinci ki sha magani."
‎
‎Sosai taji daɗin maganar Iyah, tabi bayanta da kallo bayan ta tashi ta shige ciki, kusan minti biyu bata ko motsa daga inda take ba, kafin cikin sanyin jiki ta miƙe ta leƙa wajen, ba ta ga mutane sosai ba sai mutum biyu ɗaya ta fito daga falon Andi za ta fita ɗaya kuma zaune a ƙofar falon da yaronta tana shayar da shi, ga takalma nan ƙofar da alama akwai mutane a ciki.
‎
‎Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ta fito salalam tana tafiya har zuwa ƙofar kitchen ɗin, bokitin wankan ta hango yashe inda tayi shanya jiya, ta ƙarasa ta ɗauko sannan ta dawo, ta shiga ta ga ruwa saman gas ta ɗin har ya fara tafasa, kashe gas ɗin tayi ta juye ruwan a bokiti sannan ta fito ta ƙarasa wajen bohul ta kunna ta surka ruwan daidai yadda take so, bayin da ke tsakar gidan ta shiga, ta daɗe tana gasa jikinta, ta wanke fuskarta sosai inda taga jini ya bushe ɗazun, sannan ta ƙarashe wankanta ta fito, ɗakin Iyah ta koma ta iske ta ajiye mata man shafawa da kayan sakawa, da sauri ta saka kayan don iskar da tasha bayan ta fito taji jikinta ya ɗauki sanyi da alama zazzaɓin ne zai dawo mata.
‎
‎Ta shafa man Iyah ta kawo mata ruwan tea mai zafi yasha haɗi ga madara sosai, taji daɗin hakan domin tasan ba zata iyacin abinci ba bakinta ba daɗi, ta amsa ta fara sha a hankali har ta shanye shi, taji daɗinsa sosai, sannan Iyah ta ɓallo mata panadol ta ce ta sha da ruwa ta kuma ba ta maganin gargajiya wanda ta jiƙa mata, kuma ta sake manna mata wani a goshinta, godiya tayi mata ta ɗauki hijabi ta fara sallah don bayan ta fito sai da ta ɗauro alwala kafin ta shugo.
‎Daga ƙarshe a zaune ta ƙarashe sallar don a tsayen sai ta fara jin jiri, tana idarwa kuwa ta nannaɗe a gurin don wani sanyi taji tanaji, daman tana fara sallah Iyah ta fice daga ɗakin, nan ta dunga rawar sanyi kafin barci ya ƙara ɗaukarta a gurin.
‎
‎Sai dai dukan da taji ta ko ina a jikinta ne ya sakata tashi a furgice tana zuba ihu.
‎Andi ce ke dukan nata yayin da mutane ke riƙeta,
‎"Ku bar ni na daki banza, ita tazo nan tana barci ga Usman can tun jiya ya kasa runtsawa ku ce ta sakar mini shi kawai tun da ta kashe Saudatu!"
‎
‎"Ya subuhanah!"
‎
‎Cewar wata mata maƙociyar gidan da ake kiranta da Kuluwa, sannan ta ɗaura da faɗin.
‎"Haba Rakiya, abin da ki ke faɗa ba shi da kyau, naji ance fa yarinyar nan ita ma 'yarki ce. Allah kuma ke ɗaurawa bawa ba mutum ba."
‎
‎"A'a mutum ma yana ɗaurawa ɗan'uwansa mutum idan ya saka son zuciya, kuma da ki ke faɗin 'yata ce Kuluwa, lalalala da ace 'yata ce ba zata aikatawa 'yan'uwanta haka ba, yau fa a gidan nan ko ni ko Barirah!"
‎
‎Ta ƙara nufar kan ta da sauri suka kuma riƙeta, daidai nan Kawu Balarabe ya shugo gidan shi da wani mutumi da a ƙalla zai yi shekarun Kawun, sai dai yafi Kawu tsufa da furfura sakamakon kana ganinsa ka ga baƙauye kuma bara galihu na rayuwa kamar ma ba kan shi ɗaya ba.
‎
‎Ganin yadda mutane suka yi cirko-cirko ya ce,
‎"Idan dai muhawara ake akan Barirah don Allah ku bari, daga can ƙauye nake Kalambaina kuma na saka aka yi mini cigiyar wanda yake son ya auri Barirah ban ɓuye komi na daga halayenta ba don na faɗawa 'yan'uwa tare muka yi wannan shawarar na aurar da ita nima in huta."
‎
‎Ya nuna mutumin da hannunsa wanda suka shugo tare.
‎"To anyi dace da kyar dai wannan bawan Allah ya amince don ba a ɓoye masa komi ba 'yar Tsaiba ce da Runduna, don nasan a dai nan babu wanda zai ce yana son ta shi ya sa naje can ƙauye mun zo da shi ne ya ganta, don naso ma a ɗaura auren yana zuwa ya tafi da ita amma dai 'yan uwana sun ce mu fara zuwa ya ganta kar azo kuma ba tayi masa ba!"
‎Kawu ya ƙarashe maganar yana nunawa mutumin Barirah.
‎
‎Gabaɗaya mutanen da ke gurin suka kalli mutumin sannan suka kalli Barirah wacce duk tana jin komi tun farkon zuwan su Kawun har maganganun da ya yi, ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tuno yadda 'yan garin Kalambaina suke gudunta haka Kaka Kulu ta dunga ɓoyenta cikin gida, duk yadda matan su Kawu Bature suka su su mayar da ita 'yar aikensu haka suka haƙura a dolen dole don Kaka ta ce ba zasu aike ta ba ta fita yara na tsokanarta ko cin zarafinta ba, don idan tsautsayi ya saka ta fita to zata dawo ne tana kuka ko anyi mata duka ko an faɗa mata maganganu fara sa daɗin saurare.
‎
‎Ta ɗago kan ta da ya ƙara mata nauyi a hankali ta dubi mutumin da aka ce za ta aura, gabanta ya buga da ƙarfi lokacin da ya washe jajayen haƙoransa da suka dafe sosai da goro yana dubanta.
‎
‎"Kawu walle yarinyat ta yi, wagga ai ko shiyammu babu kamat ta."
‎
‎Ya faɗa cikin hausarsu tare da ɓantarar goro da ya lalumo a gaban aljihun rigarsa, milk colour ce amma tsabar dauɗa da dafewa ta koma ita ba ash ba ita ba burawun ba. 
‎
‎Andi ce ta rangaɗa buɗa ko ta manta da yau 'yarta ta mutu kuma ɗanta na cikin rayuwa ko mutuwa oho! Don hatta mutanen da ke gurin kallonta suke cike da mamakin wacce irin tsana ce tsakaninta da Barirah har haka? Shin ko akwai wani sirri ne da ba a so kowa ya sani? Haka dai kowa ya bar tambayarsa a cikin zuciyarsa don ba su da mai ba su amsarta a yanzu kam.
‎
‎Kawu Balarabe ma ya yi murmushin gefen leɓe, kana gani kasan yaƙen dole ne ya ce.
‎"To madallah tun da tayi maka malam Ubale, yanzu ka koma can ƙauye, zuwa gobe zamu taho tare da ita sai a ɗaura auren a can kamar yadda muka tsara."
‎
‎Yana ɓantarar goronsa da murmushi a fuskarsa ya ce.
‎"To,to,to amma Kawu kasan ai kai ka biya mini kuɗin motar ko a gida na faɗa maka ba ni da kuɗi, auren ma don ka ce mini sadaka ne ku zaku biya mini sadakin ya sa na sami kwarin gwiwar amincewa, to yanzu sisin da zan koma gida ba ni da aradu."
‎
‎Kawu Balarabe ya saka hannu aljihu ya zaro dubu biyar ya miƙa masa, ai kamar zai masa sujjada tsabar godiya, sannan ya dubi Barirah yana murmushi.
‎
‎"To Amaryata sai kun iso goben."
‎
‎Yana magana dussar goro na feshi daga bakinsa, haka ya fice a gidan Kawu ma shigewa ya yi ciki Andi tabi bayansa cikin farin ciki, ta bar matan da ke gurin tsaye cirko-cirko kafin  kowa ya fara fita jiki a sanyaye, a hanyar shugowa Kuluwa suka ci karo da Iya za ta shugo ciki, domin ta ɗan fita ne lokacin da duk abin ya faru.
‎
‎"Yanzu na ga wani kamar mahaukaci ko ɗan shaye-shaye ya fito daga gidan nan! Wallahi na dunga sauri ina tunanin ko lafiya."
‎
‎Iyah ta faɗa tana duban Kuluwa don suna shiri sosai da ita.
‎
‎"Hmmm! Ni na rasa ma me zan ce, wai nan fa shi mijinku ya zaɓowa Barirah za ta aura."
‎
‎"Kamar ya ban gane ba?"
‎
‎Ta furta tana zazzaro idanuwa, nan Kuluwa tayi mata bayanin komi ta ɗaaura da cewa.
‎"Da zaku taimaki yarinyar nan da ba ku aura mata mutumin nan ba, kuma fa wai sadaka aka ba shi mijinku zai biya masa sadaki, me ku ke so ku mayar da rayuwar yarinyar nan?"
‎
‎Ai da sauri Iyah ta shige cikin gidan har tana tuntuɓe tsabar shiga ruɗun da tayi, tana leƙa parlournta ta hangi Barirah ita kaɗai zaune a ƙasa ko ba a faɗa mata ba tasan kuka take, da sauri tazo ta rarumi hannunta suka doshi hanyar ɗakin Andi, maganar da suka ji Kawu Balarabe na faɗa ne yaa sa suka tsaya cur a gurin kamar waɗanda aka dasa suna kallon-kallo.
‎
‎
‎Sadiya.
‎Ta ƙarasa gida cikin farin ciki, da mafarkin ta kusa mallakar abin ƙaunarta, sannan ta saka a zuciyarta ko ana ha maza ha mata sai ta cikawa Sadauki burinsa muddin zai so ta, ya ƙaunace ta babban burinta kuma ya aure ta, ita fa ko da Sadauki baya da aiki tana jin zata iya zama da shi a haka, tana saƙar zuci har ta shiga ɗakin Hauwa, wacce tana ganin ta shugo ta washe haƙora tana miƙa hannu ta amshi ledar hannun Sadiya.
‎
‎" 'Yar albarka irin alheri, nifa na haifi gadara Allah ya ƙaro mana irinsu Alhaji Bashar sau dubu."
‎
‎Ta ƙarashe maganar da ciro lemun roba ɗaya ta ɓalle murfin ta fara kwankwaɗa ko a jikinta.
‎
‎"Ai Sadiya ban taɓa cikin da ya kwashi daɗin mukuraɗiyya irin wannan cikin ba, Alhajin nan yana ba mu kayan daɗi, ni fa cikin nan ma da yardar Allah shi ne auta haihuwa goma ina laifi ka yara 'ya'ya a gida irin na Bagiyo idan ba ma dole ba me ya aike ka, ko da yake akwai ƙaddara ma, ni dai fatana Allah ya saa mace zan haifa ku zama ku huɗu mata haihuwar 'ya mace ai wata kadara ce ajiyayya."
‎
‎
‎Sadiya dai murmushi take kafin ta ce.
‎"Ai Hauwa sai kin ji yadda yake ƙara koɗa ni har cewa ya yi fa idan na amince har gida zai saya muku amma....!"
‎
‎"Amma me Sadiya? Don Allah kar ki ƙarasa mini barni haka ma, ki amince masa, don Allah ki amince ke zaman gidan hayan nan bai damunki? Ji be mu a wulaƙance ba ka da sirri kodayaushe faɗa da cacar baki da matan gida, ga hayaniyar yara da tarkacen 'yan bani na iya da gulma da tsugudidi, har ya ce zai saya mana gida ki saka wasa? Don Allah ki amince kuma ba na son naji wata magana kuma."
‎
‎Sadiya ta sauke numfashi, don ta so ta ce mata amma ta ga kamar ba fa da aure yake son ta ba, amma ta katse ta, sai ta bar ta ta ɗauki kwali biyu a cikin lemukan da wata roba da ta gani kamar dambun nama ne a ciki, ta ɓoye kwali ɗaya da dambun naman a jakar kayanta sai ta tafi wajen suya da ɗayan don tasan idan ba ɗauka tayi ba idan ta dawo ya zama haramiyarta don ba gani za tayi ba, tsaf Hauwa za ta rabewa yara da maƙota don ace sunci daɗi.
‎
‎"Hauwa almajirai sun tafi da kayan ko?"
‎
‎"Eh tun ɗazu."
‎
‎"To sai na dawo."
‎
‎Haka ta fita daga gidan cikin farin ciki, da ta tuna yadda Sadauki ya dinga kiran sunan a ɗazun sai ta saki wani lallausan murmushi, yau cike da nishaɗi ta fara tuyar don yadda takewa kowa fara'a zaka gane tana cikin farin ciki.
‎
‎
‎Maryam ce ta fito daga gida, sayen dankali don wata ƙawarta 'yar islamiyyarsu ce tazo, ga shi abincinsu ɗumamen na dare ne da shi suka karya sai kokon da Inna ta dama musu saboda Sadauki ne ma amma ya fita bai sha ba shi ne har suka samu cikin kofi ɗaiɗai kowa, tasan ba girkin rana suke yi kullum ba, wataran sai daren hakan ya sa ganin tana da wata ɗari ta ce bari ta saya mata dankalin don idan ita ce taje gidansu hidima sosai take yi da ita, da kunya tazo kuma gurinta a ce tsurar ruwa zata bata duk da tasan halin da suke ciki.
‎Tana ƙarasawa Sadiya ta washe baki.
‎
‎"Mairo manyan gari yau ke ce ki ka fito ba Ummul ba?"
‎
‎"Ni ce Sadiya, wai dankali zan sayawa Bahijja ce tazo gurina."
‎
‎"Eh naga shigarta ai har muka gaisa, da yake ni yanzu ba zuwa islamiyyar nake ba har tana mini tsiya.!"
‎
‎Maryam tana dariya ta amsa da.
‎"Ai ku manya ne tuni kula sauke Sadiya."
‎
‎Murmushi kawai tayi ba ta ce komi ba ta irga mata dankali na ɗari biyu ta ce,
‎"Ga shi nan ki ba ta, na Inna idan an soya zan aiko mata da shi ko Ummul idan ta fito ta amsa."
‎
‎"To ai ga ɗarita nazo da ita fa Sadiya!"
‎
‎"Ki riƙe ɗarinki, in ce Bahijjar ba 'yar ajinmu ba ce, kar ki damu yiwa kai ne."
‎
‎Maryam ta amsa tana godiya ta wuce cike da tunanin Sadiya kirkinta har yana so ya yi yawa, ga shi Sadauki kam wanda take musu din shi ba ta tunanin zai iya sonta don lamarinsa kam ba a iya gane gabansa ballantana kuma bayansa.
‎
‎Sadiya kuwa tabi bayan Maryam da kallo a ranta tana aiyana 'Ai yanzu ke ƙanwar mijina ce nan gaba kaɗan Maryam.'
‎
‎Haka taci gaba da suyar ta da layi ya ragu ta suyawa Inna na ɗari biyar har da kwai, da yake tana soyawa har da kwai ga masu son da shi ɗin, ta aika wani yaro ya kai mata, sai ga Maryam sun fito zata raka Bahijja ta ce.
‎
‎"Sadiya Inna ta ce ayi miki godiya, wai baki gajiya ne? Gaskiya Sadiya ki daina kar ki karya muku jari a banza kowa fa yasan yadda rayuwar nan ta koma yanzu lallaɓa rayuwa ake."
‎
‎"Maryam kenan! Wallahi fin haka idan na ba Inna ba ni da damuwa sannan duk abin da na ɗauka ina saka kuɗin ba wai ina kaiwa babu su ba ne, kar kuji komi mun zama ɗaya yanzu."
‎
‎Maryam ta gyaɗa kai tana ƙarasa inda Bahijja ta tsaya, bakin titi take son rakata sai ta ƙarasa gida don suna da ɗan nisa amma kaɗan da ƙafa ma zaka iya zuwa abin ka sai dai kuma idan sauri kake haka islamiyyarsu duk a wajen layin su Bahijjar take. Suna zuwa titi Bahijja ta ce,
‎
‎"Amma Maryam nifa ina mamakin Sadiyar nan, anya da zuciya ɗaya take ba ku?"
‎
‎"Hmmm wai nan Yaya Sadauki take so, shi kuwa bai san ma tana yi ba, Jiya har maganar muka so yi mi shi da Inna ya gwasale mu kin san dai hali."
‎
‎Bahijja ta ɗan ɓata rai don ko ita Yaya Sadaukin yana burgeta sosai, sai ta ce.
‎
‎"Amma dai taji kunya abu ko aji babu, ni kin ga bari na wuce sai mun haɗu a islamiyya anjima sauran kiyi irin na jiya kiƙi zuwa daman malam mai agogo yana jiranki zaki sha bulala, kin san dai yadda muka fara karatun saukar nan ba a so muna fashi idan kuma ana wani abin baki gane ba ya ce ba zai dawo baya don ke ba don ma kina da hazaƙa."
‎
‎"In sha Allahu zan zo, kin san shekaran jiya kuɗin wata ne ba mu biya ba hedimaster ya ce mu kawo, to Inna ɗan jarin ta kwashe jiya ta ba Ummul ta kai nata, yaya Sadauki ke biya mana daman da alamu wannan watan bai samu kuɗi ba ne, amma idan ya dawo zan tuna masa zaki ganni in sha Allahu."
‎
‎"To Allah ya rufa asiri mu wuni lafiya."
‎
‎Ta wuce ita ma Maryam ta juyo zuwa gida, cike da tunanin me ya sa ta ga ran Bahijja ya ɓaci don ta ce Sadiya tana son yaya Sadauki, don ɓacin ran nata sai da fuskarta ta nuna, da wannan tunanin ta ƙarasa gida..
‎
‎
‎Sadauki.
‎Yana tafe a hanya yana tunanin tattaunar da suka yi da Sadiya, tabbas wata dama ce ya samu babba, da ba zai so ya yi wasa da ita ba, to amma son fa, ya cika iska a baki ya fesar, yarinyar da suka haɗu da ita ɗazun ce ta faɗo masa.
‎
‎'Ka taimake ni, ka taimake ni!'
‎
‎Maganar da tayi ta dawo masa raɗam tamkar yanzu take biya masa ita, amma me yasa fuskarta za ta faɗo masa bayan tunani yake akan Sadiya da makomar hisabinsu a gaba idan har burinsa ya cika?
‎Wani ɓarin na zuciyarsa ya ba shi amsa da,
‎'Saboda kaji tausayinta ne, kuma kana tausaya mata ainun.'
‎Lallai zai so ya ƙara ganin yarinyar nan ko sau ɗaya ne domin ya tambaye ta waye wannan a gare ta? Kuma me ya sa take neman taimakonsa?
‎
‎Da haka ya ƙarasa gida, ya ga duk ga kayan suyar Sadiya nan an ajiye su amma ba ta gurin, ya tura babur ɗinsa har cikin gida sannan ya dawo ɗakinsa yana cigaba da tunanin me ya kamata ya yi? Ya ciro kuɗin ya tasa su a gaba yana kallo, gaskiya ba zai bar damar nan ta wuce shi ba, amma kuma baya son Sadiya da aure har ga Allah, ita ba ajinsa ba ce, yadda yake son ilmi taya  zai iya kwasarta a haka wacce babu arabi ba boko, sai dai kuma fa dole kuɗin nan su fito daga hannunta don ba shi da wata hanya da ta wuce ta wajen nata, jin cikinsa ya fara masa ƙugi don tun safen da ya fita ko ruwa bai iya korawa a cikinsa ba, ya ɗauko Exotic ɗin da ta ba shi ya buɗe ya fara sha, lokaci guda ya lumshe idanuwanshi wata natsuwa na ƙara shigar shi, sai da ya shanye shi duka sannan ya ajiye kwalin yana jin wani barci na zo masa, gyara kwanciyarsa ya yi ya kwanta ai kuwa bacci ya ɗauke sa.....


***


Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.



Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.

Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol