Free chapter · Read without an account

Page 10

by Fatima Sunusi Rabi'u · FARAR TUMFAFIYA

‎...FARAR TUMFAFIYA.
‎
‎
‎
‎©UMMU AFFAN
‎
‎
‎
‎Page *10*
‎
‎
‎
‎Ko da suka shiga ɗakin Hauwa ba ta daina faɗa ba, saboda mace ce mai murya sosai, shi ya sa tun daga wajen Ramatu na jiyo irin na maguzawan da take feso mata, ita ma bakinta bai mutu ba, yaran gidan kuwa idan ban da ihu da cece kure suna rawa babu abin da suke. Malama Baraka ta kalli yaran gidan a fili tana faɗin.
‎"Rabbana hablana min azuwajuna wa zurriyatuna Qurrata aynun, waja'alna lil muttaƙina imaama."
‎Tabbas matan gidan nan da yaransu marasa tarbiya za su iya hallaka nata yaran, shi ya sa ma ta dagewa Babansu akan ya nemar musu wanin gidan hayan, saboda idan suka ci gaba da zama anan komi zai iya faruwa na tarbiyyar 'ya'yansu. Abin haushin ba matan ba ba kuma yaran ba kowa kwallon kansa ne, taja hannun yaronta da ke tsaye yana kallo ta tura shi ɗaki, don sauran ukun suna hadda kuma sai sunyi sallar magriba a can suke dawowa gida shi ne ƙarami shekarunsa bai kai na shiga ba shi ya sa ba take barinsa a gidan, amma ko da yaushe idan ba ta makarantar da take koyarwa don da shi take zuwa to fa suna ɗaki kunshe babu ruwanta da hayaninyar mutanen gidan hakan ya sa ma suka tsane ta don tsakaninta da su raba faɗa ne sai nasiha da wa'azin da take musu shima sai ta ga suna faɗan nasu da suka saba ne.
‎
‎Sadiya ce kawai jininsu yazo ɗaya, duk da mahaifiyarta Hauwa ba sa wani shiri amma Sadiya kam tana ganin girmanta shi ya sa ma har ta fara sakar mata jiki suka saba sosai, haka yaranta tana jansu a jiki, ko islamiyya zasu idan suka bi ta inda take suya to fa indai ta gansu sai ta kirasu ta ƙulla musu ta ce suje makaranta da shi, haka in dai ita tayi girki to sai ta ba malama ta ce ta ajiyewa yaran ko da basu nan don ba su cika zaman gida ba indai akwai makaranta. Har ta hura wutar gawayinta a ƙofar ɗakinta, su Hauwa ba su daina aikawa juna da ashariya ba, da ta ɗaura tukunyarta ta kalli Ramatu ta ce,
‎
‎"Don Allah ke kuwa kiyi haƙuri haka, idan ɗaya ya yi shuru ɗaya ma dole ya yi."
‎
‎Ramatu ta galla mata harara, kamar daman jiranta take ta ce,
‎
‎"Idan ba ayi shurun ba kuma fa? Manufaka wai ita malum-malum masu ci da addini amma ana munafurci.
‎Mene ne ba mu sani ba, wai har kura za ta cewa kare maye?"
‎
‎
‎Malama Baraka murmushi kawai tayi tana girgiza kanta ba tare da ta ƙara cewa uffan ba, don ta sani Ramatu jiranta kawai take ta sauke mata gwala-gwalan rashin mutumcinta, don haka ta gyara wutar gwawayinta tayi shigewarta cikin ɗaki.
‎
‎Sadiya kuwa jin Ramatu tayi shuru lokacin da take mayarwa da Malama baƙar magana ta samu da kyar Hauwa ma tayi shuru.
‎"Wai ko nauyin cikin nan ba zai saka ki rage wasu abin ba Hauwa? Ana tausaya miki ke kuma baki tausayin kanki??"
‎
‎"Wallaihi ina sauyin kaina Sadiya, matar can Ramatu icce ce sai da wuta idan kayi mata salalo sai ta rainaka ta takaka a ƙasanta, ni kuwa Hauwa nafi ƙarfinta wallahi."
‎
‎"To naji kin fi ƙarfinta don Allah kiyi shuru ki sha ruwa."
‎Shurun tayi, Sadiya ta kawo mata ruwan tasha sosai kuwa tana sauke numfashi, nan ta bata kuɗin suyar tana faɗin.
‎"Ga kuɗinki nan, bari naje ɗakin malama na amso wayata."
‎
‎"To Sadiya, amma yau Alhaji Bashar bai zo ba ne? Naga ɗazun ma bai baki kuɗi ba?"
‎"Kai Hauwa, yanzu kayan daɗin da ya kawo mini kika ci ba kayan kuɗi ba ne? Kuma ya yi tafi sai bayan sati ɗaya zai dawo."
‎
‎"To Allah ya dawo da shi lafiya, don Allah kiyi masa magana akan gidan da ya ce zai saya mana mu bar gidan nan ko baƙin ciki da hassadar da Ramatu take mana zai saka ta mutu har lahira saboda baƙin ciki."
‎
‎"To idan ya dawo zamuyi maganar."
‎
‎"Yauwa Sadidina 'yar gudaliyata Allah ya miki albarka ya ƙara azurta mini ke."
‎
‎"Amin."
‎
‎Ta amsa tana ficewa daga ɗakin.
‎
‎
‎Nazifi.
‎Da yammacin ranar ne dai ta litinin ɗin motocin EFCC suka sake shigowa harabar ofishin shiyyar Kaduna cikin tsari, tun kafin motar Nazifi ta tsaya, wasu jami'an binciken suka riga suka sauko suna ɗauke da manyan kwalayen da aka cika da fayiloli, kwamfutoci da na'urorin ajiya da aka kwace daga kamfanin. Aikin da suka fara matakinsa a farko anyi nasarar samar da abubuwan da za su buƙaci dogon nazari.
‎
‎Nazifi Hunƙuyi ya fito daga motarsa ba tare da ya tsaya maganantuwa da kowa ba, daman sun san wannan na ɗaya daga cikin ɗabi'unsa, bai yadda ya tattauna da kowa ba, don bai yarda da kowan ba sai kan shi kaɗai, kai tsaye ya fara takunsa cikin mazantaka zuwa ofishinsa.
‎Ofishin ba shi da yalwar kayan alatu sosai, tebur mai faɗi ne kawai, sai kujeru biyu, ɗakin ajiye takardu, da wani babban allon bangon da ake manna hotuna da bayanan bincike domin haɗa alaƙar abubuwan da ake zargi, ya cire hular aikinsa ya ajiye a gefe sannan ya zauna, ya fesar da wani huci tare da tura 'yan yatsun hannusa gabaɗaya cikin sumar kansa yana ƙara yamutsata.
‎
‎Sakon ɗaya, biyu, kafin   ya lumshe idanunsa na wasu daƙiƙu, wannan wata dabara ce da ya saba yi idan yana yanayi irin wannan, ba ya son ya fara kallon abu kai tsaye, sai ya yi aiki da tunani a ƙwaƙwalwarsa sosai.
‎
‎"Mene ne nake da tabbacin sani?"
‎Kai tsaye ya yiwa kansa tambayar kafin ya buɗe lumshasshun idanuwansa da suke kamar mai jin barci haka yanayinsu yake ko yaushe, ya ɗauki bairo ya yi rubutu a saman littafin dake gabansa. Takardu sun nuna an biya kayan aikin da ba a gani a wurin ginin ba, an yi yunƙurin goge bayanan kwamfuta da zuwansu, ya ɗan tsaya yana kallon abin da ya rubuta, kafin ya gyaɗa kai. Shin Murjanatu ce ta shirya komai? Ko kuwa ana amfani da sunanta ne? Wa ya ci ribar kuɗin? Ina kuɗin suka shiga? Ya jingina da kujerarsa tare da ƙara lumshe ido a karo na biyu.
‎
‎Abu ɗaya na damun zuciyarsa sosai, wato Murjanatu, tun lokacin da idanunsu suka haɗu a kamfanin, bai bari tsohuwar sanayyarsu ta rinjayi tunaninsa ba, amma a matsayinsa na ƙwararren mai bincike, ya san abu ɗaya, mutumin da ya fi bayyana a fili ba lallai shi ne mai laifin ba, sau da yawa, babban mai laifi yana ɓoyewa ne a bayan wanda ake gani a zarga, ya miƙa hannu ya ɗauki rahoton ziyarar wurin aikin makarantar, ya fara karantawa a hankali.
‎
‎"An biya siminti buhu dubu huɗu....."
‎
‎Ya ɗaga gira da ɗan taɓe baki kaɗan tare da shafa kwantaccen sajen fuskarsa da tsabar gyara har wani sheƙi yake.
‎Ya juya zuwa hotunan da aka ɗauka a wurin aikin, an ga ginshiƙai kaɗan, an ga tubali, amma babu alamar yawan simintin da aka ce an yi amfani da shi, ya sake ɗaukar wani fayil ɗin.
‎
‎"An biya kuɗin ƙarafunan rufi."
‎Ya duba hoton wurin, ba a kai matakin rufi ma ba ma, ya ɗan  murmusa kaɗan, ba wai murmushi ba ne na farin ciki murmushi ne na gefen baki, sai dai wannan ɗin yana ɗaya daga cikin ɗabi'arsa musamman a irin wannan yanayin idan yaji yazo wani matakin da kansa ya gwaru.
‎
‎Cikin sassarfa kuma cike da mazantakarsa ya nufi allon binciken da ke kafe a bangon ya manna hoton makarantar, ya manna hoton kamfanin sannan ya manna sunan Murjanatu.
‎
‎
‎Yana tsaye a wurin ƙofar ofishin tayi ƙara, alamar ana son shugowa ciki.
‎
‎"Shigo."
‎
‎Ya furta da ɗan sauti har lokacin idanuwansa na kan allon bangon, jami'insa Bashir ya shigo da wata ƙaramar jaka a hannunsa.
‎
‎"Yallabai, masu binciken kwamfuta sun ce akwai wani faifan ajiya da aka yi ƙoƙarin lalata shi, amma suna ganin za su iya dawo da bayanansa."
‎
‎Nazifi ya ɗaga kai ya dube shi.
‎"Kar a taɓa buɗe shi ba tare da rubuta komai a kundin shaidu ba."
‎
‎"An gama."
‎
‎"Kuma a tabbatar babu wanda zai yi aiki a kansa shi kaɗai, ina son jami'ai biyu su kasance tare, koma fiye da hakan."
‎
‎"To, yallabai."
‎
‎Da Bashir ya fita Nazifi ya sake komawa ya zauna, tare da zaro wayarsa, akwai saƙonni da dama da bai karanta ba, mafi yawansu daga ofishin aiki ne.
‎
‎Idanuwansa suka sauka a hoton da ke saman screen ɗin wayarsa, ya fara shafa hoton da yatsun hannunsa a hankali, yarinya ce da ba ta wuce shekaru biyar ba, sanye take cikin kayan makaranta, tana murmushi har gefen kumatunta sai da ya lotsa ga jakar baya a bayan nata tayi kyau sosai ba ta da maraba da Nazifi ko a fuska.
‎
‎Nazifi ya kalli hoton na ɗan lokaci, murmushi ya bayyana a fuskarsa, karon farko tun safe, bayan wanda ya yi na yaƙe ɗazun, ya danna wayar ya kira lambar Mummynta Shukuriyyah ƙaramar muryarta mai zaƙi ta ratsa masarrafar sautinsa.
‎
‎'Ayrah!'
‎
‎Yaji sautin sunan yarinyar cikin zuciyarsa.
‎
‎"Assalamu alaikum, Daddy!"
‎
‎"Wa alaikumus salam, gimbiya."
‎
‎"Daddy yaushe za ka dawo?"
‎
‎Nazifi ya kalli agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa, kafin ya ƙara kishingiɗa a kujerar da yake zaune.
‎
‎"Nan ba da jimawa ba gimbiya."
‎
‎"Ka zo da wuri don Allah na yi kewarka Daddy."
‎
‎Kalaman Ayrah suka sauka kai tsaye har cikin zuciyarsa.
‎"In shaa Allah."
‎
‎Ya kashe wayar a hankali, ya tattara fayilolin da zai tafi da su gida, bincike irin wannan bai san lokacin aiki ba takamaimai ba, don haka a ko ina sai ya yi nazari, kuma dole ne ya ƙara damƙe dantse domin komi zai iya faruwa..
‎
‎Yamma sakaliya don biyar har ta gota, da yake lokaci ne na damuna garin ya lulluɓe kamar dare ya fara, daidai lokacin da motarsa ta tsaya a gaban katafaren gate ɗin gidansu da ke Unguwar rimi, hurn ya buga mai gadi yazo ya buɗe masa, babban gida ne mai faɗin gaske ga wadatacciyar haraba.
‎
‎Sashen Alhaji Al-Hassan da Ammi yana gaba, a baya kuma akwai wani sashe mai zaman kansa da Nazifi da iyalinsa suke zaune. Bai nufi sashinsa ba sai da ya fara shiga ya gaishe da Ammi ya tarar Alhajinsu bai shugo ba bayan ya fito kai ya wuce nashi sashin cikin sassarfa. 
‎
‎Yana buɗe ƙofar Ayrah ta rugo da gudunta.
‎
‎"Daddy!"
‎
‎Ta faɗa tana rungume ƙafafunsa. Nazifi ya sunkuya ya ɗauke ta ya cillata sama.
‎"Gimbiyata Ayrah 'yan matana." 
‎
‎Ta kwalkwale da dariyar farin ciki irin wacce yara ke yi idan sun ga mahaifinsu ya dawo gida, ya sumbaci goshinta.
‎
‎"Kin ci abinci?"
‎
‎"Eh, amma Mummy ta ce kai ma ba ka ci ba."
‎
‎A lokacin ne Shukuriyya ta fito daga kitchen, sanye take cikin doguwar riga mai sauƙin ado, fuskar nan tata mai cike da natsuwa da annuri a sake kamar kodayaushe, ya sauke Ayrah yana faɗin.
‎
‎"Nima tunda na dawo Mummy za ta ba ni nawa ko?"
‎Ta gyaɗa kai tana nufar kujera, bayan ya ciro mata sweet a aljihunsa ya miƙa mata.
‎
‎"Barka da shugowa Yallaɓai."
‎
‎Ta furta tana kallonsa sosai kuma cikin ladabi.
‎
‎"Barka Yallaɓiya."
‎Ya amsa cikin zolaya yana tafiya domin ƙarasawa bedroom ɗinsa 
‎
‎"Ya aikin?"
‎
‎Muryar Shukuriyyah ta ƙara shigarsa.
‎
‎"Lafiya."
‎
‎Ya amsa mata a takaice daidai lokacin da ya buɗe ƙofar bedroom ɗinsa ya tura kai ciki.
‎
‎
‎Murjanatu.
‎Ta daɗe zaune a ɗakin taron bayan Nazifi da jami'ansa sun fice,  duk hayaniyar da ta cika kamfanin ba ta bari ta shiga kunnuwanta ba don tasan ba abu mai daɗi ba ne. Ta zubawa teburin da ke gabanta ido, zuciyarta kuwa ta shiga wani irin bugawa da ba ta taɓa ji ba tsawon shekarunta, wata daga cikin ma'aikatanta ce ta shigo cikin gaggawa jikinta na ɓari.
‎
‎"Madam su na ta bincike a sashen lissafi, sun ce a kawo dukkan takardun aikin makarantar."
‎
‎Murjanatu ta ɗago kai a hankali, idanuwanta tuni suka sauya launi, ga wani ciwon kai da ya saukar mata lokaci guda.
‎
‎"Ku ba su duk abin da suka buƙata."
‎
‎Tayi furucin tana juyar da fuskarta gefe.
‎
‎"To.. amma..."
‎
‎"Na ce ku ba su."
‎
‎Murjanatu ta katse ta cikin hanzari da ƙosawa, ma'aikaciyar ta yi shiru na sakonni, kafin ta juya ta fita jiki a sanyaye cike da tausayin uwarɗakin nata, domin kowa a kamfanin yasan Murjanatu na da tausayin na ƙasa da ita ga kuma sakin fuska duk da ba kuma ta ɗaukar raini.
‎
‎Murjanatu ta jingina bayanta da kujera, ta rufe idanunta na ɗan lokaci kaɗan, wata irin kasala ta ratsa dukkan jikinta, ba tsoron binciken ne kaɗai ya mamaye ta ba, abin da ya fi tsaya mata a rai shi ne fuskar mutumin da ke jagorantar binciken.
‎
‎"Nazif!"
‎Ta furta sunansa a cikin zuciyarta kamar yadda lokacin baya suke kiransa.
‎
‎"Me ya sa sai kai Nazif?"
‎
‎Ta buɗe idanunta ta kalli saman ɗakin.
‎"Duk Najeriya me ya sa sai kai aka turo?"
‎Ba ta taɓa tunanin wata rana za su sake haɗuwa a irin wannan yanayin ba, a tunaninta rayuwa ta riga ta ɗauki kowannensu ta mai da wata hanya dabam, amma yau ƙaddara ta sake haɗa su, sai dai ba a matsayin masoya ba, ba a matsayin abokai ba, a matsayin jami'in bincike da wacce ake bincika.
‎
‎Murjanatu ta miƙe tsaye ta taka zuwa bakin tagar ofishin, ta buɗe labulen kaɗan, a ƙasa jami'an EFCC suna ci gaba da gudanar da aikinsu, wasu na ɗaukar kwalayen takardu, wasu kuma na ɗaukar hotunan wasu sashe na ginin, ta hango Nazifi tsaye kusa da wata mota yana magana da wani jami'insa, ko daga nesa yanayin tsayuwarsa bai canza ba, irin yadda yake tsayawa tun shekaru da dama kenan, cikin nutsuwa da kamalarsa.
‎
‎Sai dai idanunsa kullum suna kallon abin da wasu ba sa gani. 
‎Murjanatu ta janye daga tagar, tunaninta ya fara komawa shekarun baya, a lokacin gidansu da gidansu Nazif tamkar gida ɗaya ne kafin ƙaddara tayi musu juyin juyaa hali da juyin waina a kaskon suya.
‎
‎Ba jini ne ya haɗa iyayensu ba aminci ne, shekaru masu yawa suna aiki a kamfani guda, sun fara daga ƙananan mukamai tare suka sha wahala tare, suka yi nasara tare.
‎Har mutane suka daina kiransu da sunayensu sai dai su ce musu jini ɗaya, haka da yawa ana musu kallon nan gani nan bari farar tumfafiya, sai dai ƙaddara ba tabar komi ba.
‎
‎A baya zumuncinsu ya wuce na aiki, ya koma na iyali, babu ƙarshen makon da ba za a tarar da ɗaya daga cikin iyalan a gidan ɗayan ba, idan Alhaji Ibrahim ya yi tafiya, Alhaji Al-Hassan ne yake kula da wasu al'amuransa, haka idan kuma Alhaji Al-Hassan yana da wata matsala, Alhaji Ibrahim shi ne farkon wanda zai tsaya masa.
‎
‎A haka ne Nazif da Murjanat suka taso, a tare suna zuwa makaranta da suka girma abota ta fara sauyawa, ba tare da sun furta wa junansu komai ba.
‎
‎Murjanatu ta tuna wani yammaci da suke zaune ƙarƙashin bishiyar mangwaro a lambun gidansu Nazif.
‎
‎Nazifi yana riƙe da wani littafi yana dubawa, domin mutum ne shi mai son karance-karance na turanci da kuma na Hausa, ya ɗago idanuwansa ya zuba akanta don sosai ya shiga tsananin jin zafi akan abin da ya faru da jarumin labarin da yake karantawa.
‎
‎"Wata rana zan yi aikin da zan riƙa kare haƙƙin mutane,  ba na son ganin masu zalunci suna cin nasara Murjanat."
‎
‎Ta yi dariya sosai fararan haƙoranta na ƙwalli shima har ya shagalta da kallonta, har yau da take tunawa ba ta manta irin kallon da yake yi mata a lokacin ba, kallo ne mai cike da shauƙi da wani irin saƙon da yake fitowa daga idanuwansa zuwa nata idon, ba na kwaɗayi ba, ba na riya ba sannan ba na yaudara ba.
‎Nazifi bai taɓa ƙaunarta don ya cutar da ita ba, ya ƙaunace ta ne saboda ita,
‎saboda yadda take magana, saboda yadda take dariya, saboda irin mafarkan da suke ginawa tare da junansu.
‎
‎Da ƙarfi Murjanatu ta runtse idanunta, wani irin zafi ya ratsata.
‎
‎"Da ace..."
‎
‎Ta fara faɗa, sai kalaman bakinta suka tsaya cak ta fara girgiza kai.
‎
‎"A'a, a'a."
‎
‎Ba lokacin tuna abubuwan da suka shuɗe ba ne, yanzun akwai wata matsala mafi girma, ta koma bakin teburin ta zauna tare da buɗe wata drawer a hankali.
‎
‎A ciki akwai wata ƙaramar na'urar ajiya ta ɗauke ta, ta daɗe tana kallonta, a cikin wannan ƙaramar na'urar akwai wasu bayanan da ba ta taɓa son su faɗa hannun Nazifi, ba don tana son ta kare kanta kawai ba, a'a akwai wasu mutane da idan sun ji binciken ya kai wannan matakin, ba za su tsaya suna kallo haka kawai baa.
‎
‎Murjanatu ta riƙe na'urar da ƙarfi, ta san Nazifi ta san yadda yake aiki, ba ya haƙura da duk abin da yasa gaba, ba ya gajiya idan ya saka kansa a kowacce hanya to fa sai ya ga ƙarshenta.
‎
‎"Ya Allah!"
‎
‎Ta furta cikin sanyin murya.
‎
‎"Kada Nazifi ya gano abin da yake nema."
‎Sai ta girgiza kanta idanuwanta suka ƙara kaɗawa da sauri ta shiga girgiza kanta kamar tana gabansa.
‎
‎"A'a! Kada ya kusanci gaskiyar da za ta iya jefa rayuwarsa cikin haɗari."
‎Wannan tunanin ne ya fi komai girgiza zuciyarta, domin a karon farko tun da binciken ya fara, Murjanatu ta fahimci cewa ba ta tsoron abin da zai same ta, abin da ya fi damunta shi ne abin da zai iya samun Nazifi idan ya ci gaba da tona abin da wasu suka yi duk mai yiwuwa domin ya ci gaba da kasancewa a ɓoye, take ta saka ƙaramar na'urar nan jikin jakarta tana sauke numfarfashi tamkar wacce tayi tseran gudu....


*Littafin Farar tumfafiya na kuɗi ne, free pages zai ƙare ne a 15 pages don haka masu buƙatar saya za su tura 700 ne a yanzu, idan mun kammala free pages kuɗin littafin 1k za a tura kai tsaye ta 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC sai shaidar biya ta *** kar ku bari wannan damar ta wuce ku, farar tumfafiya har yanzu sharar fage muke.*

Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.



Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.

Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol