Free chapter · Read without an account

Page 13

by Fatima Sunusi Rabi'u · FARAR TUMFAFIYA

...FARAR TUMFAFIYA.



©UMMU AFFAN



Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.



Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.



Page *13*


Murjanatu.
Lokacin da agogon da ke ɗaure a farar fatar  hannunta ya nuna ƙarfe biyar na yamma, daidai lokacin ta tattara kayanta da ke saman teburin ofishin nata cikin sanyin jiki da tunanuka kala-kala a zuciyarta, duk da cewa ma'aikata da dama suna ta fita suna yi wa juna sallama har ita wasu da yawa ganin yau suna ta rigata fita sun shugo sun mata sallamaa, amma ita da ta fito ba ta bi takan kowa ba don abin da ke damunta ma kawai ya isheta, gata nan dai jin ta take tamkar mara lakka a jiki, kanta a ƙasa jakarta rataye a kafaɗarta ta fito daga ofishinta. Tun daga fitowarta daga katafaren ginin kamfanin har zuwa motarta zuciyarta ba ta dainawa bugawa da sauri-da-sauri ba, direbanta ya yi saurin buɗe mata ƙofar baya yana furta.

"Barka da yamma Hajiya."

Ta ɗaga kai kaɗan ta dube shi, sai kuma tayi ƙasa da kai da sauri.

"Barka."

Ta amsa a takaice kuma muryarta a sanyaye, direban bai ce komi ba saboda duk abin da ya faru a safiyar yau yana da masaniya, don gurin mai gadi yaji komi da yake duk idan ya kawota da safe suna gaisawa haka da yamma idan yazo ɗaukarta yana daɗewa gurinsa suna hira domin yana zuwa tun huɗu ne anan ma yake sallar la'asar don tafiyar tata daga huɗunne zuwa abinda ya samu.

Da motar ta fara tafiya Murjanatu ta jingina kanta da kujera, idanunta suka sauka kan titin da ke ratsawa cikin unguwar tasu ta Kakuri, ba ta da nisa da kamfanin amma yau ɗaya tafiyar ta yi mata nisan gaske, nisan da ta ga sunƙi ƙarasawa gida haka ta ƙurawa hanya ido, amma a gare ta kamar babu komai kamar babu abin da take gani tana kallon titin ne kawai, zuciyarta kuwa tana wani guri dabam, gurin Nazifi! Sunan ya sake ratsawa cikin zuciyarta tare da amsa kuwwa a masarrafar sautinta, ta lumshe idanunta da ƙarfi.

'Kada ki sake tuna shi, abin da ya wuce ya riga ya wuce, kawai ki fuskanci gabanki da abin da kazo ya kai.'

Wani ɓarin na zuciyarta ya yi saurin aika mata gwagwgwaɓan jan kunnen, sai dai zuciya ba ta da ƙashi tana cike da rauni, ganin sa ya fama mata tsohon mikin da ta daɗe da binne shi, maimakon ta daina tunaninsa sai hotunansa suka fara bayyana ɗaya bayan ɗaya a ƙwaƙwalwarta, ta tuna yadda yake yawan tsokanar ta idan yana cikin raha, ta tuna yadda yake cewa ba ya son ganin ta cikin damuwa, ta tuna irin yadda yake saurarenta idan tana ba shi labarin abin da ya faru a makaranta lokacin da ta fara zuwa jami'a, ta buɗe idanunta cikin sauri, ta fara girgiza kai.

Sai dai duk yadda ta yi ƙoƙarin kore waɗannan tunane-tunane, suna ƙara dawo mata ne da ƙarfi, abin da ya fi damunta shi ne yadda ta ga Nazifi yau, ba ta ga wani canji a halinsa ba, har yanzu yana da irin wannan natsuwar tasa mai tafiya da imanin mai kallonsa, har yanzu idanuwan nan nasa suna nan masu aika maka sako mai wuyar fassara, kamala, kwarjini da haibarsa sai ma nunkuwa da sukayi.

Idan Nazifi ya fara zargin wani abu, ba ya dainawa sai ya gano gaskiyarsa, ta sansa da wannan nacin shi ya sa ma ya zaɓi ɓangaren bincike, ta sauke numfashi mai nauyi.

"Ya Allah, me ya sa sai wannan lokacin?"

Ta tambayi kanta a fili, don direba ma sai da ya tambayeta me take cewa, ya ɗauka da shi take magana, ta kuwa share shi ba tare da ta tanka masa ba, motar ta kutsa cikin layin nasu, mai yalwatacciyar kwalta da ta ƙarawa unguwar tasu kyau da tsali, yana parking ta fice. Ita ma gidansu babban gida ne mai faɗin haraba, an raba shi zuwa sassa daban-daban kamar ma yaso yafi gidansu Nazifin girma da tsaruwa, ɓangare guda na iyayenta Alhaji Ibrahim da matarsa Hajiya Batula wato Mami kamar yadda yaran ke kiranta, su huɗu ne yaran gidan Murjanatu ce babba mai shekaru talatin da biyu yanzu a duniya sai Hasiya sannan Mufida sai Muhibbah auta da suke kira da Hibbah, Hasiya tana da aure da yaranta uku sai Mufida ita ma tayi aure yaronta ɗaya sai cikin na biyu yanzu, Hibbah kam tana gida karatu take a jami'ar jihar Kaduna KASU yanzu haka.

Ɗaya ɓarin kuwa ɓangaren tsohuwar gidan ne wato Hajja, wacce shekaru sun fara ja, domin mahaifiya ce ga Alhaji Ibrahim kaka a wajen su Murjanatu, amma har yanzu muryarta da ƙarfinta kuma jikinta da lafiyarsa saboda irin kulawar da take samu ga ɗanta da ma surukarta zuwa jikokinta, duk da fitinanniyar tsohuwa ce ta ƙarshe don ba mai iya mata sai Allah, idan ta saka ka gaba, to mai rabaku sai Lillahi, don naci da ƙorafi aikinta ne.

A hankali take tafiya ba wani kuzari tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, da  murmushin dole kuwa take amsa gaisuwar da gadiman gidan ke bin ta da ita.

Maimakon ta nufi ɓangaren iyayenta kamar yadda ta saba yi idan ta dawo daga aiki, ko ɓangarenta idan a gajiye ta dawo sai ƙafafunta suka juya zuwa ɓangaren Hajja, ta san idan ba ta shiga ta ga Hajja ba ƙorafi kuwa har gurin Daddy, sai ta saka ya kirata ta bata haƙuri kuma hakan ba zai saka ta daina mitar ba har sai ta samu wani abin da zai ɗauke mata hankali kuma ta koma kan shi.

Da ta shiga falon ta tarar da Hajja zaune kan doguwar kujera tana kallon tashar BBC Hausa suna labaran yamma, tana ganin Murjanatu ta tsuke baki tare da gyara zaman tabarau ɗin idanunta masu ƙara mata ƙarfin gani tana dubanta sosai.

"To ga uwar iya nan ta dawo sannu."

Murjanatu ta durƙusa kusa da ita, cikin dauriya da ƙoƙarin ɓoye abin da ke fuskarta ta furta.

"Sannu da gida Hajja, ina yini."

"Lafiya lau, sumul ƙalau."

Hajja ta amsa, amma daga ganin yanayin Hajjan da yadda take motsa baki ta san akwai abin da zai biyo baya. Ai kuwa gani tayi ta kafe ta da ido.

"Kullum aiki dai aiki dai baki da lokacin kanki takwarata, ni kam ban san irin wannan rayuwar ba, yarinya ta kai shekaru talatin da biyu, amma kullum abin da ta sani shi ne aiki?"

Murjanatu ta ɗan saki murmushin yaƙe.

"Hajja!"

"A'a, bari in gama."
Hajja tayi saurin tarar numfashinta tun kafin ta kai aya.

"Ƙannanki biyu duk sun yi aure, kowacce tana can gidanta da mijinta da 'ya'yanta, ke kuma kina ta bin titi tun safe har dare da sunan aiki! Wacce irin rayuwa ce muke ciki ni Murja? Ga shi Ibrahim ya zuba miki ido sai ka ce ke ce ki ka haife shi?"

Murjanatu ta sauke idonta ƙasa, yau ba ta cikin yanayin da zata biyewa Hajja, sai ta gyara zamanta tana furta.

"Amma Hajja ai..."

"Me ai?"

Hajja ta kuma tarar numfashinta kafin ta ɗaura da.

"Kin fi son ofishinki fiye da gidan aurenki dai, ko ba haka zaki faɗa mini ba?"

Ta ɗan yi shiru tana motsa baki irin yadda tsofaffi fitinannu ke yi.

"Ko mijin zai faɗo daga sama ne tunda kin kori yuaron kirki Nazifi ada klullum sai tazo ya gaishe ni yanzu sai ya yi wata bai zo ba? Oh ni Murja yau naga abin da ya ishe ni bai ishi Allah ba."

Da a baya ne kafin yau
Murjanatu ba za ta yi shiru ba, da ɗazun ne da safe kafin ta fita aiki tabbas ba zata ƙi biyewa Hajja ba, da kafin zuwansa ne kafin ya ɓula mata duk wata jijiya da lakar jiki kafin ya tafi ya barta da tsohon miki kafin yau, yau ɗin dai da take niyyar rusa mata tanajinta na jiya yau ɗin dai da zuwansa ya dawo mata da jiyarsu, da duk kafin nan ne tsiwarta faɗan da suke da Hajja har a gaban Daddy wanda ke rabawa. Da ace kafin yau ɗin dai da tuni ta fara mayar da martani cikin wasa da tsiwa ga Hajja. Amma yau ɗin yau, yau, yau ɗin ta daban ce a cikin sauran ranakun da suka biyo bayan waccen rabuwar.

Miƙewa tayi ta fice daga ɓangaren Hajja ta koma ɓangarensu, falon ma babu kowa sai mai aiki da take sake goge-goge, Mami da Hibbah tasan suna ciki, ba tare da ta leƙa Mamin ba ta shige ɗakinta, ta rufe ƙofa a hankali ta cire mayafinta ta ajiye, jakarta ma ta faɗi kan kujera ba tare da ta kula ba, ta ƙarasa bakin gado ta zauna tare da dafe kanta da hannayenta duka biyu.

Sai ta kwanta rigingine a kan gadon tana kallon saman ɗakin da aka ƙayatashi, ga wasu fitulu masu kyau masu bada kala-kala da suka haskaka ɗakin, shiru ya mamaye ko'ina, sai ƙarar na'urar sanyaya ɗaki kaɗai ake ji, amma cikin zuciyarta kuwa hayaniya ce mai zafi ke mamayeta. Ta sake ganin fuskar Nazifi yadda ya zauna a ɗakin taron, yadda ya yi magana cikin natsuwa yadda bai nuna wata alamar cewa ya san ta ba, hakan ne ya fi komai ɗaga mata hankali domin ta san Nazifi, idan ya nuna kamar bai damu da wani abu ba, to a lokacin ne yake tattara dukkan bayanan da zai haɗa su wuri guda. Murjanatu ta lumshe idanunta ba tare da ta shirya wa hakan ba, wasu lokuta masu daɗi suka fara dawo mata, lokutan da rayuwa take da sauƙi, lokutan da dariyarta ba ta da nauyi, lokutan da mafarkinta da na Nazifi suke tafiya tare kamar abu ɗaya, ta tuna yadda suke zama suyi ta gardama kan ƙananan abubuwa, daga ƙarshe kuma su yi dariya cikin shauƙi da nuna kulawa.

A lokacin ta gasgata maganarsu ta yi kuma imanin babu abin da zai taɓa raba su, sai dai rayuwa tabbas rayuwa tana da nata shafin da ba mutum ke rubutata da kan shi ba, domin da shine wataƙila bazai bari ya rubuta wata ƙaddarar ba. Murjanatu ta buɗe idanunta a hankali, wasu hawaye na sulalowa daga gefen idonta.

'Abin da ya wuce ya riga ya wuce Murjanatu.'
Taji zuciyarta na tunatar da ita wwani ɓigire da ta mance sai dai duk yadda take ƙoƙarin faɗawa zuciyarta haka, wani sashe na zuciyar ya ƙi yarda domin yau, bayan shekaru masu yawa da ƙaddara ta raba hanyoyinsu, sun sake haɗuwa kuma wannan karon ba soyayya ce ta haɗa su ba bincike ne, duk da tana zuwa gidansa ganin Ayrah amma tana kiyaye lokacin haɗuwarsu shi ya sa ma ba ta taɓa zuwa suka haɗu ba.


Murjanatu ta juya a kan gadon, kafin ta tashi zaune ta ɗora bayanta kan matashin kai duk lokacin da ta rufe idanunta, sai fuskar Nazifi ta sake bayyana a gabanta, a ƙarshe ta juyar da kanta zuwa gefe sai wata tsohuwar magana ta dawo mata a rai, maganar aurenta da Nazifi.

Wannan batun ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka mamaye rayuwarsu a lokacin, iyayensu ba su ga wani dalilin da zai iya zuwa har ma ya hana su zama ma'aurata ba. Alhaji Ibrahim da Alhaji Al-Hassan sun yi aiki tare, sun taimakawa juna fiye da tunanin mai tunani, sun raba farin ciki da damuwa a tsakaninsu, zumuncinsu daman tuni ya kasance  tamkar na 'yan uwa ne, ba iya wasu ba 'ya'yansu har danginsu sun san da wannan ɓigeren na rayuwarsu da wuya sha'anin wannan ya tashi baka ga 'yan uwan wannan a ciki ba.

Da suka fahimci cewa Murjanatu da Nazifi sun fara son juna, sai suka fi suma farin ciki, a ganinsu auren zai ƙara ɗaure danƙon zumuncin da ya daɗe yana tsakaninsu, shi Alhaji Ibrahim mutum ne mai son farin cikin iyalansa, musamman yaransa yana matuƙar ƙaunarsu tare da girmama ra'ayinsu, ko lokacin da Murjanatu ta faɗa masa Nazifi ya ce idan sunyi aure ba zata yi aiki ba don haka ta shirya rabuwarsu bai musa mata ba, don a ganinsa an wuce wannan lokacin na cewa mace ba zatayi aiki ba, ko wacce mace tana da 'yanci da zaɓar duk abin da taga yafi mata.


Gashi a lokacin Murjanatu ta riga ta fara gina kanta, ta samu gurbin aiki mai kyau a fannin da ta yi karatu wato Civil Engineering haka  bayan kammala digiri ta ɗaya da ta biyu tayi masters ɗinta a ɓangaren Quantity Surveying shi ya sa ma ta sami aiki mai kyau kuma tana da burin kaiwa wani matsayi mai girma sosai, ta san abin da take so, ta san inda take son zuwa, kuma ba ta son wani ya zo ya dakatar da mafarkinta ko kaɗan.

Nazifi kuwa yana da nasa ra'ayin shima ta sani kwarai, don babu wani motsi da zai yi da bazata gane mai yake nufi ba a lokacin, kusan tare suka kammala karatun don da shekara ɗaya ya fita, kamar yadda ko a shekaru na haihuwa uku kachal ya ba ta.

Wata rana suna zaune a wani wurin cin abinci, Murjanatu na yawan gaiyatarsa gurin don ta ce tana samun natsu a gurin har su tattauna a natse, bai yi ƙasa a gwiwa ba ya faɗa mata abin da yake cikin zuciyarsa.

"Murjanat idan muka yi aure, ina son ki daina aikin nan."

Ta kalle shi cikin mamaki.

"Me ya sa?"

Ta faɗa ba ta daina shan Ice cream ɗin da take sha ba, Nazifi ya ɗan yi shiru kaɗan kafin ya ce,
"Saboda ina son ki mayar da hankali a gidanki, ki kula da tarbiyyar yaran da zamu haifa, ni kuma nayi alƙawarin faranta muku. Ina son idan na dawo gida in same ki, ba wai kullum kina wurin aiki ba, yaranmu ba zasu samu kulawa daga gare ki ba, haka ma ni, eh ƙwarai ni kinsan ni mutum ne da ke matuƙar son kula tattali da kuma girmamawa idan kina aiki zan rasa duka waɗannan Murjanat musamman aiki irin naki."

Murjanatu ta yi murmushin gefen baki wato na tsantsar yaƙe, wannan karon kallon da take masa na abubuwa da yawa ne, wai kamar ita yake nufi ta zamo matar gida? Matar kulle? Ta kula da yara fa yake magana! Oh har wasu tarin yara yake tunanin za ta haifa masa? Ko don ya ganshi su biyu kachal iyayensa suka haifa, daga shi sai ƙaninsa Nazir shine yake so ita ta cika masa gida, me Nazif yake nufi da ita? Koma ta ce me ya mayar da ita? Duk da tasan su huɗu iyayenta suka haifa to ita kam yarinya ɗaya ko yaro ɗaya take buƙata, don tana ganin yadda masu yara da yawan suke fama duk da tasan gidansu duka sun sami kulawa ta uwa da uba ga kakarsu, haka karatun nan sunyi shi daidai gwargwado boko da islamiyya to me kuwa zasu nema ga iyayensu bayan wannan? Amma ita kam ba zata iya wahalar da nasu iyayen suka yi ba akan kula da yara da yawa.

"To Nazif, ni kuma ina son in yi aiki."

Ta faɗa a takaice tare da kauda fuskarta gefe.

"Za ki iya yin wani aikin da ya dace da matar gida, amma ba irin wannan ba."

"A'a."

Ta amsa kai tsaye, zuwa lokacin ya fara kai haƙurinta bango, kafin ta ɗaura da cewa.

"Ba zan daina aikin da nake so ba Nazif."

Nazifi ya kalle ta sosai tare da ajiye cokalin hannusa ya haɗe hannuwan guri guda akan teburin da ke gabansu.

"Me ya sa kike ɗaukar maganata da wasa Murjanat? Kin san dai ajiye aikin da zaki yi ba zai rage ki da komi ba, idan ma albashin kike so zan dinga baki duk wata amma ki zauna a cikin gidana."

"Saboda wannan shi ne abin da kake so kuma ra'ayinka?"

"Ba haka ba ne, amma..."

"To yaya ne?"
Tayi saurin katse shi cikin zafin rai. Nazifi ya sauke numfashi.

"Saboda ni ne zan zama mijinki, ina son ki kasance kusa da ni a duk lokacin da nake gida."

Murjanatu ta girgiza kai tana kallonsa ido cikin ido.
"Ni kuma ina son mijina ya fahimci cewa, aiki ba yana nufin bazan zauna kusa da shi ba ne, amma aikina yana da muhimmancin da babu wani abu da zai saka a karon kaina na barshi, to mene ne amfanin karatun da nayi?"

Maganarta ta ƙarshen tayiwa Nazif zafin da ba ta taɓa zato ba kuma a ranar ne Nazifi ya faɗi kalmar da har yau idan ta tuna ta sai taji zafin abin, yanzu ma sai da wasu zafafan hawaye suka sakko mata, ranar da suka yanke alaƙa da junansu ranar da ya ce ta zaɓa ko shi ko aikinta.

"Idan aure zai sa na rasa aikina, to gara mu rabu Nazifi gara mu yanke igiyar tun yanzu kafin muyi aure ya zamana mun kasa samawa junanmu kwanciyar hankali da farin ciki, mu rabu kawai, mu rabu kawai! Na ce maka mu rabu kawai!!."

Har yanzu sai da ta jiyo kuwwar da tayi masa da sauri ta toshe kunnuwanta ta saki wani sabon kukan da alokacin ma cikin kuka ta tashi ta tafi ta bar shi a gurin zaune yana bin ta da namujiya.

Ba wanda ya yi tsammanin kalmar za ta zama ta ƙarshe a tarayyarsu, amma ta zama haka, auren da iyayensu suke ganin zai ƙara haɗa zumuncinsu, ya zama dalilin da ya girgiza zumincin nasu inda ya fara tangal-tangal.

Alhaji Ibrahim bai yi wata-wata ba ya amince da ra'ayin 'yar sa, har yana cewa baya goyon bayan a ce mace ba za ta yi aiki idan ta yi aure ba wannan tauye haƙƙin 'yancin mata ne.

Wannan magana ta ƙara ɗaga hankalin Alhaji Al-Hassan sunyi zama da yaran amma kowa ya dage a matsayarsa suka nuna musu suma yaran zamani ne da ba za a yanke hukunci akansu kai tsaye ba, musamman ma Murjanat da nan take ta ce kawai a bar maganar auren nasu idan Nazif ya samu mata ya aura ita ma idan ta samu mijin da ya dace da ra'ayinta zata aure shi. Sai ga shi zumuncinsu mai ƙarfi ya koma wani abu daban, ziyarar da suka saba yiwa juna ta ragu sosai, tattaunawar da ta kasance kullum ta zama abin da ake yi lokaci-lokaci idan an samu haɗuwa.

Haka Nazifi da Murjanatu kowannensu ya ɗauki hanyarsa Murjanatu ta ci gaba da aikinta, Nazifi kuwa ya ci gaba da rayuwarsa har ya yi aure, auren da Murjanatu take tunanin na huce haushi ne domin ya guma mata baƙin cikin cewa wata biyar da rabuwarsu sai ga shi da matarsa, matar ma yarinya ƙarama don lokacin da ya auri Shukuriyyah ba tafi goma sha takwas ba, haka maƙotansu ne don kusan kullum daman tana gidansu Nazif ɗin, Murjanatu ba ta taɓa zuwa gidan ba taga Shukuriyyah ta shugo ba, shekarasu biyu kuma ta samu sanarwar da sai da tayi hawaye da tunanin da yanzu ita ce ta haifi yarinyar, lokacin da suka je barka da Mami da ƙannenta ta ƙanƙame yarinyar a ƙirjinta wata ƙauna da batasan tana da ita ga ƙananun yara ba ce ta saukar mata nan take, amma ta danganta hakan daga cikin ƙaunar da take yiwa Nazif ce ta samu wani kaso a ciki, har yau kuma idan taso ganin Baby Ayrah tana zuwa ta ganta, yanzu sai dai taje makarantarsu saboda Shukuriyya har fuska ta sauya mata akan zuwan da take mata da sunan tazo ganin Ayrah ne, har wata rana ta gasa mata maganar da taji takaici da alƙawarin ba ta ƙara zuwa, amma bayan kwana biyu taji ba zata iya ba, tana son yarinyar haka sayayya babu wacce bata mata Shukuriyya kuma ba ta taɓa saka mata kayan da Murjanat ta bata ba, yanzu da taga tana zuwa school sai take zuwa can ta ganta, ita ma yarinyar tana son Murjanatu sosai.

Ta sake lumshe idanuwanta wasu hawaye na bin kuncinta ta sani wasu raunuka ba sa warkewa gaba ɗaya, shekaru sun shuɗe, sai ga shi yanzu Nazifi ya dawo, ba don ya nemi aurenta ba, ba don ya dawo da soyayyarsu ba, ya dawo ne a matsayin jami'in EFCC, kuma an turo shi ne domin ya binciki aikin da take kula da shi Murjanatu ta buɗe idanunta da sauri ta zauna a gefen gado bayan ta sauko da ƙafafuwanta zuwa ƙasa, zuciyarta ta cika da wani sabon tunanin tabbas idan Nazifi a shirye ya wuni, to ita a shirye ta kwana, me ya sakata rauni? Me ya sa tsoro ya shigeta?

'Saboda Nazifi ne!'

Zuciyarta ta amsa mata, ta san abin da take nufi, ba za ta zauna ta zuba ido tana tsoron Nazifi ba, idan bincike ne za ta fuskance shi idan tambaya ce za ta amsa idan ma yana neman hujja ne za ta ba shi damar neman ta, amma ba za ta bari tsoro ya karya mata zuciya ba, ba zata bari abin da ya faru shekaru shida baya ya karya mata zuciya ba, ita mace ce mai kamar maza zata shiryawa haka, ta miƙe daga gadon cike da kwarin gwiwa, ta shiga ɗakin wanka ta yi alwala, sannan ta shimfiɗa sallaya ta gabatar da sallar magrib da aka idar yanzu, bayan ta idar da sallah, ta zauna na ɗan lokaci tana yin addu'a, a hankali zuciyarta ta fara samun sauƙi, ta tashi ta gyara hijabinta jikinta sannan ta fito daga ɗakinta, ta nufi ɓangaren iyayenta zuciyarta fes-fes...
Sakamakon wasu da suka mini magana cewa na ɗanyi promo kafin kammala free pages to na amshi kukenku, yau dai mun yi 13 sauran kwana biyu mu kammala free pages to daga yau zuwa kwana biyu ku tura 500 idan ya wuce kwana biyun to 1k ne kuɗin book ɗina na gode.


*Littafin Farar tumfafiya na kuɗi ne, free pages zai ƙare ne a 15 pages don haka masu buƙatar saya za su tura 700 ne a yanzu, idan mun kammala free pages kuɗin littafin 1k za a tura kai tsaye ta 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC sai shaidar biya ta *** kar ku bari wannan damar ta wuce ku, farar tumfafiya har yanzu sharar fage muke.*


Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol