Free chapter · Read without an account

BABI NA TALATIN

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

KWANA BIYU yanzu Zaid baya min magana. Ko gaisuwar da take haɗa mu chan lokacin baya idan ba ma shiri sosai yanzu ya dena. Idanun shi suna yin ƙasa yanzu sosai kamar yana so ya rufe amma kuma ya buɗe sama-sama. Yana fita ina tunanin aiki yake fita amma baya jimawa yake dawowa saboda lafiyar shi. 

Dawowa ta kenan daga wurin aiki na gan shi zaune a dining area a kujera ya ɗaura kanshi akan table. Kallon shi na tsaya yi na tsawon minti ɗaya be tashi ba nayi tunanin ko yayi bacci ne. Ban tafi wurin shi ba na wuce ɗakina. Wanka nayi nasa doguwar riga na light material tsayin ta be kai ankle ɗina ba. Dawowa parlour nayi na kuma ƙara samun Zaid zaune a dining kanshi na kan table amma kuma naga cup akan table din kusa da kanshi. Zama nayi daidai a yadda zan dinga kallon shi. 

Ina nan zaune ya ɗago kanshi idanun shi se akaina and they look like he's in great battle sunyi ƙasa ya cigaba da kallona. Kaina na ɗaura a headrest na kujera saboda yadda nake jin kallon da yake min da kuma irin tunanin da nake so nayi. 

Wani sabon tunani ya taho min. Da sauri na tashi na shiga kitchen na fara shirye-shiryen dafawa Zaid macaroni. Ina cikin dafawa ta kusa dahuwa na ɗaura dahuwar kifi. Bayan na gama na fito dasu na kawo mishi a dining table yana zaune yasa jikin shi a kujera yana kallona da sleepy-like idanun shi. 
  “Ga abinci ka ci Zaid” na faɗi mishi cikin sanyin murya.
Fara girgiza min kai yayi yana kallona “I'm really not hungry”
   “Na dafa saboda kai kaɗai fa”
   “Thank you” yace a sanyaye be ƙara cewa wani abu ba ya sauke idanun shi akaina ya kuma folding hannuwan shi a kirjin shi.

Komawa nayi na zauna ina tunanin yanzu ze fara cin abincin. Abincin da be ci da kyau ba kenan se bayan abincin ya gama hucewa tukuna naga Zaid ya ɗauki spoon yaci spoon ɗaya daga macaroni, shima kifin ya ɗan tsakura kaɗan daga ciki spoon ɗaya ya ajiye. Kwanukan ya ɗauka ya kai kitchen. Be wani jima da shiga ba ya fito duk akan idanuna. Ban ji haushi ba ko kaɗan se de mamaki da nayi. Nasan duk wanda aka faɗawa irin abinda na faɗiwa Zaid haka ze yi, wani ma ze iya rabuwa dani akan rashin yarda amma shi de gashi har yanzu be ƙara ɗauko maganar saki ba. 

Gobe da safe da yake ranar hutun sati ya fara na shiga ɗakin Zaid da baya nan. Ɗakin nashi gyare yake ba zaka ce an yamutsa shi ba ba'a gyara ba kuma so nake na gyara mishi kuma ina so yasan na shigo na gyara mishi ɗaki. Bedsheet nashi na cire nasa wani me nauyi fari na chanja pillowcase guda biyu. Na ƙara gyara turarrukan dake jikin madubi. Wardrobe ɗin shi na buɗe domin na gyara mishi kayan shi amma dai-dai suke se ban taɓa ba. Banɗaki na shiga, anan ma tsabtace yake se na fito. Ni Ko turaren wuta ma bani da bale nasa idan ya shigo ya ji ƙamshi. 
Fitowa daga ɗakin nayi na wuce kitchen na fara dafa mishi abinci. Ganin jiya be ci abinda na dafa ba yasa ban yi tunanin yin abinci wanda yayi kama da lunch ba. Irish na fere na soya na soya kwai. A plate na zuba nasa mishi ketchup da fork a gefe. Strawberry Lipton da nagani jiya a wurin shi na dafa mishi. Daidai lokacin da na fito na iso parlour shi kuma yana ƙoƙarin kai wa hanyar ɗakin shi. 
  “Na kawo maka abincin ɗakin ka, Zaid?” na tambaye shi cikin murya me sanyi.
Tsayawa yayi ya juyo yana kallona yace “I ate outside”
Fuska ta ta saki “Abincin bayi da zafi kuma kaga bayi da nauyi chips ne harda strawberry Lipton na dafa maka. Ina tunanin zaka so kaci ko kaɗan ne” na jero mishi bayani 
   “Bana jin yunwa Hadiza. Se de ko kici ko ki rufe har anjima”
    “Kana shan maganin ka? Naga maganin ka a ɗakin ka kamar ba'a shan shi”
   “Naji sauƙi kar ki damu” daga haka be tsaya ƙara cewa wani abu ba ya wuce. Bayan shi na bi saboda baya shan maganin shi ya yake so nayi da rayuwa ta? Ko ciwon shi ya dawo ace ni ce?
Murɗa kofa nayi ban tambaya izini ba na shiga. Har ya kwanta akan gadon shi akan zuciyar shi. 
  “Zaid baka kwanci haka fa. Dan Allah ka tashi ka dena kar ciwon nan naka ya dawo” maganar da nayi ko motsawa Zaid be yi ba. Abincin na aje a bedside table na lamp na dawo wurin shi nasa hannuna na tada shi. Jacket da yake sanye da ita na cire mishi. Zama nayi gefen shi “Ko spoon biyu kayi ya isa se ka sha magani dan Allah. Ba saboda ni ba, saboda lafiyar ka”
Zaid rufe idanu yayi yana saurare na. Abincin na ɗauko da kaina na bashi spoon biyu yace ya koshi. Ajiyewa nayi na ɗauko maganin shi da ruwa na bashi ya sha. Bayan duk haka nasa hannuna a wurin muscles ɗin shi ina son mishi massage a wurin saboda yanda naga sun yi dama cikin maganin shi yasha muscle relaxant. Ahankali na fara mishi kar na taɓa mishi chest ɗin shi da kuma inda aka mishi aiki. Ina yiwa Zaid massage amma kallona yake har cikin idanu. And I hate this look it makes me feel extremely guilty. 
Ina mishi massage ɗin ya riƙe min hannu yace it's okay. I'm good. Thank you. Nasan massage da nake mishi be isa ya ishe sa ba amma tunda yace ya isa se kawai nayi murmushi na ɗauka kwanuka na fita dasu. 

Ina shiga ɗakina na fashe da kukan da ban san ina ta riƙewa ba. Ina jin tsoron Zaid da abinda yake tunani a cikin ranshi. Ina jin tsoron rabuwa dashi. 

Washegari ma na shiga ɗakin shi nayi duk abinda ya dace. Haka ranar Litinin, ban gaji ba kuma ba zan gaji da kula dashi ba na koma ɗakin shi and made his bed duk da ya gyara but i made it again na ɗan ƙara gyarawa da pillows a kan gado. Na shiga banɗakin shi na wanke. Dawowa nayi cikin ɗakin, takalmin dake ƙasa na maida a shoe rack. Na ƙara gyara kayan dake jikin madubi tukuna na wuce kitchen na dafa abinci. Bayan na gama na kai dining table. Komawa ɗakina nayi na shirya cikin lace riga da skirt bayi da style se stones da aka sa a gaban riga. Ban taɓa sa high heels a cikin gidan Zaid ba se yau. Na dawo a gaban madubi na ɗaura ɗankwali na tare da fitar da sumar kaina a baya saboda ina da dogon suma tana da tsayi. Harda janbaki na shafa a lips ɗina ba me yawa ba amma idan aka kalle ni ansan akwai janbaki a bakina. Na shafa kwalli a idanuna duk da bana son shafa kwalli ko chan a baya. Fararen eyeballs ɗina suka ƙara fitowa na tsaya ina kallon fuska ta da hasken da na ƙara slightly har hannuwana sun ƙara haske wurin fingernails nawa. I like this my look it's captivating and I hope Zaid sees it. 

A window na na leƙa ko zan ga motar shi naga tun ɗazu ya fita be dawo ba. Ban ga motar shi ba kenan be dawo ba. Waya ta na ɗauka ina so na kira shi amma bana so yaga kamar ina damun shi. Wayar na aje a jikin madubi na zauna a gefen gado. Ina ji ƙarfe shida tayi na tashi na ƙara dubawa nan ma har yanzu be dawo ba. Tsayawa nayi a wurin window ina ta jiran Zaid har aka fara kiran Sallah. Banɗaki na shiga nayi alwala na dawo nayi Sallah. Na ɗan jima kaɗan anan wurin naji kamar an shigo da mota. Da sauri na tashi na duba window motar shi ta shigo. Ina nan tsaye ya jima be fito daga motar ba se chan ya fito a gajiye daga idanun shi da dukkanin shi. Ni idan ma aikin ba ze yiwu ba ya ƙara bari har ya ƙara samun sauƙi kafin ya koma. 
Fitowa yayi a cikin motar duk ina kallon shi ya fara tafiya domin shigowa ciki. Barin window nayi na fito daga ɗakin inaso na haɗu dashi. 
Fitowa ta be shigo ba tukun na tsaya ina jiran shi se gashi ya shigo riƙe da waya a kunnen shi yana waya. Zaid ko kallona be yi ba yana so ya wuce ɗakin shi na riƙe mishi ɗayan hannun shi. A lokacin ne ya ɗago gajiyayyun idanun shi yasa akaina. First, kallon mamaki ne akan fuskar shi yadda ya ganni all decked up harda lipstick a bakina. Na biyu kuma meyasa na riƙe mishi hannu. 
   “Na dafa abinci tun ɗazu nake jiran ka” na faɗi mishi ina kallon shi da idanuna da suke ɗauke da tausayi “Kuma naga duk ka gaji idan ba zaka iya aikin ba ka bari har ka ƙara jin sauƙi”
Hannun shi ya fara cirewa a nawa. A wayar da yake kuma yace “I'll call you later”
  “I was making a call or are you blind?” yace calmly idanun shi na son rufewa ina ma tunanin wani abu
   “I'm sorry” nace “Meyasa kake yi kamar wanda ke jin bacci? Baka samun bacci ne?”
“I'm okay Hadiza”
 “Na dafa abinci. Kayi wanka se ka fito mu ci abinci”
  “Bana jin yunwa, Hadiza”
     “Duk ka gaji fa”
  “Gajiya na da bambanci da yunwa” ya faɗi min yana ƙoƙarin wucewa. Ƙara riƙa hannunsa nayi da kyau ina kallon shi da medium sized idanuna nace “I cooked for you, Zaid. Da ba saboda kai ba ba zan dafa ba amma na dafa saboda kai, kayi haƙuri ka ci dan Allah”
Shiru yayi yana kallona ni kuma na ƙi ɗauke idanuna akan shi. Mun jima a haka ko blinking bana yi yace “Nace bana jin yunwa Hadiza. Da ina ji da zan ci”
  “Ko spoon ɗaya ba zaka yi ba?” na daƙe ina kallon shi 
Hannun shi ya fara ɗaukewa daga riƙon da na mishi yace “Zan yi wanka”
  “Can i help you? You look extremely tired”
  “I'm okay” Yana faɗin haka ya wuce. Tsaye nayi ina kallo har ya shige ɗakin shi. 

A dinning na koma na zauna ina jiran shi har ƙarfe bakwai be fito ba. Hannuwana na ɗaura a chin nawa ina ta jiran fitowar shi se gashi ya iso sanye da light brown three quarter da baƙin singlet. 
  “Welcome Zaid” na faɗa mishi warmly fuska ta a sake ina jin farin cikin fitowar da yayi saboda ina tunanin ba ze fito ba. 
Nodding min kai yayi ya zauna daura dani ban ce komai ba na de ɗauka ze zauna a kusa dani. Tashi tsaye nayi ina so na fara serving namu naji takalmin da na sa sun ɗan yi ƙara. Zaid saukar da idanun shi yayi yana kallon ƙasan mu directly at me. Ganin high heels na saka yasa ya ciro idanun shi daga chan ya ɗaura akan fuska ta. Kunya naji saboda nasan mamaki yake abinda be taɓa gani nayi ba. Hannuwan shi biyu ya haɗe wuri ɗaya ya ɗaura wurin bakin shi da hancin shi idanun shi na ƙasa. Serving nashi na fara yi na kai mishi duk abin buƙata a kusa dashi. Bayan nayi serving kaina na zauna. Har na fara cin abinci Zaid be fara ba daga gani ma wayasani ko be san nasa mishi abinci ba saboda yadda na lura tunani yake yi kuma yayi nisa a ciki. 
  “Zaid, nasa abincin fa” na sanar dashi ya ɗago kai ya kalle ni kenan yasan nasa abincin. 
     “Thank you” yace ya ɗauka spoon ya fara ci. Ina gani be ci dayawa ba ya sha ruwa. Har ya tashi ze tafi ina so muyi magana me tsawo nace “I'm just thinking of whom you might be making call with earlier on”
Kallona yayi me ɗauke da alamar meyasa kike tambaya. 
  “I just want to know. Thought you were done with work the moment you close your office”
   “It was work related”
Ina so na cigaba da magana dashi amma be bani dama ba wucewa ma yayi. Bin bayan shi nayi da kallo na ajiye spoon ɗina yanzun ma hawaye suka fara zubowa a idanuna. Dama faɗar gaskiya ze yi costing nawa irin kulawa da attention da ƙaunar da nake samu daga wurin Zaid?

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol