Free chapter · Read without an account
EP_________1️⃣
🕊️DESTINED MARRIAGE🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM
EP_________1️⃣
Ƙarar ƙwanƙwasa ƙofar da akayi ne ya dakatar da ita daga rubutun da take. Ta ɗago ta saci kallon TV dake opposite da ita kafin ta maida hankalinta ga aikin da take tana me faɗin, "Yes, come in".
Wata budurwa ce da zasu iya yin sa'anni ta turo ƙofar, ta shigo, cikin girmamawa ta ɗan sunkuyar da kai kafin ta ce, "Ranki ya daɗe, you have a guest".
"Who?....". Ta tambaya da calm voice ɗin ta marar hayaniya. Saidai kafin ta kai ga bata amsa, aka turo ƙofar. Wani matashin saurayi ne da baifi ya girme su da shekaru huɗu ba ya shigo riƙe da hannun wata yarinya da shekarunta ba su wuce biyar ba.
"Faryal, ya kamata ki yi wa wannan Secretary ɗin taki magana, saboda a duk lokacin da na zo nan, sai ta yi kamar ba ta taɓa sani na ba. Kamar ni ace in zan shigo office ɗinki sai an min iso"
Kafin Secretary ɗin da ke tsaye ta samu damar ba shi amsa, Faryal ta ɗaga mata hannu tare da faɗin, "Ya isa Aysah. Za ki iya tafiya".
"Okay ma'am". Ta amsa da sauri kafin ta juya ta fice daga Office ɗin.
Bin ta yayi da kallon gefen ido har ta rufo Kofar kafin ya motsa ya nufo wurin table ɗin nata ya ja ɗaya daga ciki visitors chair din ya zauna.
Tasowa Faryal ɗin tayi daga wurin zamanta ta dawo gaban table ɗin itama ta zauna a ɗayar visitor chair ɗin dake kallon tasa. Ta miƙa hannu ta ɗauki yarinyar dake jikinsa, ta ɗora ta bisa cinyarta, tana murmushi, cike da nutsuwa ta maida kallonta gare sa tana faɗin, "Good afternoon Sir".
A maimakon ya amsa sai cewa yayi, "Wannan Secretary ɗin taki tana bani ciwon kai a duk lokacin da nazo Company nan whl. Gaskiya ta fara isata, ni inaga kawai daina zuwa zanyi".
Faryal ta ɗan yi murmushi kaɗan kafin ta ce, "Matsalata dakai Hamdan mita whl" ............ "Au mita ne ma nake yi? To shikenan Nagode".
"Kaga, duk abun bai kai haka ba, ka yi haƙuri dan Allah. Aysah dai aikinta take yi, amma in sha Allah zan yi mata magana, hakan baza ta sake faruwa ba".
"Ah tou dai, dan zuwa wannan lokacin in da tana da hankali ai ya kamata ta gane da Company da CEO ɗin duk mallaki na ne. Tunda da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne".
Murmushin ta sakeyi tana wasa da hannun yarinyar dake kan cinyarta ta ce, "In sha Allah. Kuma kaga ma da ka amince da abin da muka tattauna akai tun farko, ai da yanzu komai yana ƙarƙashin ka ne, su kansu ma'aikatan namu ƙarƙashin ka zasu koma".
"Manta kawai, yanzu dai kinga tashi ki samo min abinda zan kora". Ya faɗa yana ɗan gyara zamansa.
Girgiza kai tayi kawai ta mike tana faɗin, "Something cold?".
"A'a butar shayi zaki kawo min Kinji". He replied sarcastically.
Dariya tayi tana karasawa gaban fridge ɗin ta ce, "Kaii My dear, daga tambaya".
"Ah to, gani nayi kin fi kowa sanin abin da nake sha da wanda ba na sha".
Tumbler ta ɗauko da robar ruwa me sanyi ta dawo, ta daura tumbler ɗin akan table ɗin tana ƙoƙarin zuba masa, ya karbe robar ruwan yana faɗin, "Barshi kawai na hutassheki, i can do it myself ".
Sakar masa tayi ta koma ta ɗauko robar bobo tana faɗin, "Dear, zan iya bawa Naesha wannan kuwa? Akwai dan sanyi dai gsky".
"Kinga bata kawai, ta riga data saba da sha ako ma yaya ne".
"Oh, my God! Karka ce min yadda ka saba durawa kanka abubuwa masu sanyi, haka itama kake bata? idan kuwa haka ne, zan gaya wa Jiddah ta daina bar maka yarta whl. Tayi kankanta da yawa ai sai sanyi ya kamata". Ta faɗa tana buɗe marfin ta zira mata straw din sannan ta miƙa mata.
"In ma kin faɗa ba yadda zatayi. Dan yadda yaran nan suke manne min ako da yaushe, ina ga ko iyayensu ba sa mannewa haka".
"Ai dama shi yaro haka yake. Muddin zaka sauko da shekarun ka daidai da nasa ka yi wasa da shi, ji zaiyi duk duniya babu ya kai, ba kuma wanda yake sonsa kamar ka".
Duba agogon hannunsa yayi sai kuma ya miqe yana faɗin, "Bari kiga in tafi in ɗauko yaran can daga makaranta. Dama akan hanya muke nace bari na biyo naga princess".
Faryal ta yi murmushi cike da jin daɗi kafin ta ɗan ɓata fuska tana haɗe gira ta ce. "Amma me ya sa kullum ka fi son mu ringa haɗuwa a waje?".
Dan kallonta yayi kafin ya ce, "Bana zuwa gidan ne?".
"But..."
"Ah ah, ba wani but. Tambayar ki nayi bana zuwa gidan naku ne?".
"Kana zuwa, amman..."
Dariya yayi kafin ya ce, "Kama kanki da kanki dai".
Numfashi ta furzar kafin ta ce, "Yanzu dai, yaushe za ka zo?".
"In sha Allah, Maybe on the weekend".
Tashi tayi ta koma kan asali kujerarta tana faɗin, "Haka dai, haka dai, kullum zan zo, zan zo! Amma kafin ka zo ɗin nan sai na ci baƙar wuya".
"Kinga, kinga, za ki fara ko?".
"Shikenan to. Na yi shiru. Allah Ya kaimu".
A dai dai lokacin ne wayarsa ta fara ƙara. Ya zaro ta daga aljihunsa, ya duba sunan mai kiran kafin ya ɗaga. "Hello, Khalid".
Daga ɗayan ɓangaren, Khalid ya ce, "Kana ina ne? Gani a gidanku amma an ce min ka fita".
"Kai, gani tare da matata ne. Me kake so ne?".
"Too, sannu ka ji Me mata. Kace ina gaisuwa".
Juyawa Hamdan yayi ga Faryal tare da faɗin, "Khalid yana gaisheki".
Murmushi tayi kafin ta ce, "Ina amsawa, ni ma ina gaishe shi".
Yar dariya yayi kafin ya maida hankalinsa kan wayar ya ce, "Ta ce ba ta karɓi gaisuwarka ba".
Da sauri ta ce, "Oh, my God! Ba haka na ce ba fa yallabai".
Kashe wayar yayi yana dariya, kafin ya kalleta ya ce, "Ki ƙyale shi, ɗan iskan yaro ne ai. Bari kiga na wuce kar yaran nan su tashi su zauna suna jirana".
Dan karyar da kai tayi kafin a ɗan shagwaɓe ta ce, "Dan Allah, ka samu ka hau online yau. Jiya haka ka ce min in jira ka amma nice har ƙarfe ɗaya baka hau ba, a cikin yanayi na jiran naka ne ma bacci ya ɗauke ni".
Dakatawa yayi da tafiya ya juyo yana faɗin, "Albishirinki".
"Goro". Ta amsa tana kallonsa.
"Muna dawowa daga ball na ɗan shingiɗe in huta kafin na tashi yan iskan yaran can su lele sun kunna hotspot sun tsotse datar tas".
Dariya tayi kafin ta ce, "Ai kai din ne ma in kana bacci sai ayi cinikinka baka sani ba".
"Baza ki gane irin karainiyar da nakeyi bane daga fitowar rana zuwa faduwarta Shiyasa".
"To naji, Amma seriously yau idan ba ka hau online ba, zan yi fushi sosai".
"Karki wani damu. Zan hau in sha ALLAH".
"To, shikenan. Zan gani ai. Allah Ya kai ku gida lafiya. Naesha, ki gaishe min da mamarki kinji".
"Za su ji in sha ALLAH". Ya faɗa yana rufo mata ƙofar office ɗin.
Komawa tayi ta jingina da headrest ɗin kujerar tana ɗan lilawa a hankali. Fuskarta dauke da wani cool smile dake bayyana farin cikin da take ciki. A hankali ta furta, "Ya Allah, Ka nuna min ranar da zamu kasance miji da mata ni da Hamdan, Ka sanya shi ne mijina har a Aljanna". Ajiyar zuciya ta sauke Kafin ta ɗauki wayarta, ta buɗe, ta shiga gallery, ta buɗe wata folder da aka rubuta life partner ta shiga kallon hotunan Faysan ɗin dake ciki iri iri.
Ta kwashe kusan 30 minutes ba tare data sani ba dan har saida aka kirata sannan ta farga. Amsa kiran tayi, da faɗin, "Hello".
Daga ɗayan ɓangaren, akace, "Hello, Aunty Faryal. Good afternoon".
"Afternoon Bahijjah. Yaya aikin?".
"Alhamdulillah, komai yana tafiya daidai Aunty Faryal". Bahijjah ta amsa.
"Masha Allah. Haka ake so ai".
"Umm... Daman...". Bahijjah ta shiga ɗan kame kame kamar me shakkar faɗar abinda ke bakin nata.
Faryal da ta fahimci akwai magana a bakinta ta ce. "Wani abu ya faru ne Bahijjah?".
"Ehhh tho, batun gidan senator ne daman. Sun ce su lalle sai kina tsaye, duk da kuwa su Deejah da sauran ma'aikatanmu suna can, amma matar ta dage lalle sai kinje, tace zata ƙara mana kuɗi ma. Ita dai kawai tana son ki kasance a wajen ne da kanki, dan gudun samun kuskure".
"Oh, to ai wannan ba matsala ba ce. Ki turo min da address ɗin kawai, dan mail ɗin su yayi ƙasa a wuri na ba zan iya duba shi yanzu ba".
"To Aunty Faryal. Godiya muke".
Kashe wayar Faryal tayi tana ɗaukan landline, ta shigar da wasu numbobi sannan ta kara a kunne.
"Hello, Aysah. Ki zo ki kai wa accountant waɗannan document din". Tana faɗin haka ta ajje wayar.
Ba a ɗau wani lokaci ba, Aysah ta shigo office ɗin. Faryal ta miƙa mata takardun data haɗa, tana faɗin. "Ki kai masa waɗannan, sannan ki faɗa masa ya turo min sauran bayanan ta email dina, dan tafiya zanyi yanzu. Akwai wani aikin da ya taso min ne. Hope we are done with today's schedule?".
"Yes ma'am".
"Alryt". Ta faɗa tana tattara kayayyakinta, ta saka su cikin handbag din ta, sannan ta fice nufi ƙofa dan fita daga office ɗin.
Ko data fito daga main building ɗin, zubewa ma'aikatansu suka shiga yi suna gaisheta cikin mutunci da girmamawa. Faryal yarinya ce me ladabi da kuma girmama manyanta. Bata duba cewa Companyn mahaifinta ne in dai kai babba ne, kuma ka kama girmanka to zata mutuntaka ko da kuwa kai ɗin cleaner ne. Wannan halayyata ta yasa ta sake zama top priority fiye da Mahaifinta a Company. Sannan daɗin dadawa hannunta a buɗe yake, sam bata da rowa ko kadan.
Motarta ta ƙarasa ta shiga, ta kunnata, sannan ta yi horn aka buɗe mata gate ɗin, ta cilla hancin motar waje, securities ɗin na daga mata hannu haɗi da addu'ar isa gida lpy.
Ko da ta isa gida, a parking space ta paka motarta, kafin ta buɗe ƙofar motar tana shaqar fresh air kusan minti 2 kafin a hankali ta sako ƙafafunta waje, riqe dan dankwalin atamparta tana me gyara gyalen kanta dake zamewa saboda santsin gashinta. Entrance din da zai sadata da cikin gidan ta nufa kai tsaye.
Da sallama ta shiga dukda ba kowa a falon, ta shiga cilli da kayayyakin hannunta. Dankwalin, gyalen da kuma handbag dinta, kafin ta fada kan kujera tana zare medicated glass din dake idonta ta shiga kwala kiran. "Maama! Maama! Daadee! Na dawo".
Wata mata ce ta shigo falon, kana kallonta zaka fahimci mahaifiyarta ce Saboda tsananin kamannin da suke da juna, duk da ma idan ka kallesu a tare baza ka taɓa cewa ita ta haifi Faryal ɗin ba saidai kayi tunanin yayarta ce, saboda kyawun jikinta. Kallon agogon bangon da ke falon tayi kafin ta ce, "Faryal, har kun dawo kenan? Amma dai yau babu aiki sosai dan naga kun tashi da wuri".
"Kaiii Maama! Yanzun ne wuri? Saboda kina gida ne fa kawai kike ganin kamar yanzu wuri ne, amma 2pm ma ta wuce ai. Ko da yake ma dai babban dalilin dawowar tawa ma saboda kiran dana samu daga Faryal's Touch of Elegance ne. Akwai yar wani senator da za ta yi aure, to mu zamu yi masu yi musu event decor ɗin wushe wushe ɗin da zasuyi. Na tura ma'aikata na, amma mahaifiyar amaryar ta nace sai na je da kaina. Ba ta son kuskure, you know how clients are at times".Ta ƙarashe tana ɗan Murmushin dake bayyanar da gajiyar dake tattare da ita, hakan kuma sai ya sake fitar mata da wani sirritaccen kyau.
Jinjina kai Maama tayi kafin ta ce, "Wannan ai ba wata matsala ba ne. Da Hadiyyah tana nan ne ma da sai nace ku tafi tare".
"Karki damu Maama. Zan je in ɗauki Manira, idan kuma ba ta nan, sai mu tafi tare da Kainat".
"To shikenan. Ki fara kira dai ki tabbatar ko tana nan ɗin".
"To Maama. Amma bari na ɗan watsa ruwa a gurguje kar lokaci ya kure min".
"Alryt amma ki tabbatar kin ci wani abu kafin ki fita, Okay? Sannan ki kira ta ki tabbatar ko tana nan. Idan ba ta nan, kawai karki bata Lokacin ki, ki wuce zuwa inda zaki".
Faryal da ta miƙe, tana tattare kayayyakinta da ta zubar a kan kujerar, ta sarawa mahaifiyarta ta kafin ta ce, "Your wish is my command Maa".
Murmushi Maama tayi kafin ta ɗan jinjina kai ta ce, "ALLAH ya shirya min ke Faryal. Ban san lokacin da za ki girma ba, ke dai".
Ɗakinsu ta wuce da ɗan gudu gudu tana dariya. Wankan ta fara yi kamar yadda ta faɗa, kafin ta shirya cikin comfy long cotton gown. Ta gyara dogon baƙin gashinta, me tsantsi da cika, ta tattara shi ta ɗaure in a low bun. Hula ta ɗauka ta saka sannan ta sanya medicated glasses ɗin ta, ta ɗauki mayafin rigar, jakarta da wayarta, sannan ta fita zuwa falon, ta ajiye su akan kujera ta wuce dinning area.
Tana buɗe warmer ɗin farko, yanayin fuskarta na sauyawa kamar wadda take jiran kaɗan ta fashe da kuka. "Ni wallahi ban san dalilin da ya sa Maama ta maqalewa kayan cikin ruwan haka ba. Mu ba yan ruwa ba, amma kullum abincin mu sai an haɗa da halittun cikin ruwa fisabilillahi". Ta cigaba da mita tana zuba jallof ɗin shinkafar da taji kifi. Bata wani zuba da yawa ba, ta ja kujera ta zauna tana kallon plate ɗin kamar me ƙirga ƙwayoyin shinkafar da ke ciki. Kafin daga ƙarshe kuma ta furta, "Bismillah". Ta diba a spoon ta kai bakinta tana sake bata fuska.
Ba ta wani jima sosai ba ta kammala cin abincin. Ta miƙe, ta kai plate ɗin kitchen, sannan ta fito ta nufi ɗakin kakarta.
Bata ciki, saidai kafin tayi wani tunanin ƙofar bathroom ɗin ta buɗe, juyawa tayi, idanunta suka sauka akan kakarta ta dake fitowa. Da sauri ta ƙarasa wajenta, ta rungume ta tana faɗin, "Ya Allah, ka bawa wannan tsohuwar tamu tsawon rai".
Murmushi tayi, kafin ta ce, "To sakarni! Ko sai kin karya ni, ki yi wa ya yana asara, ki barsu da jinya Ehh?".
Dariya Faryal tayi tana taɓe baki ta ce, "Indeed, dan kuwa ni bani da asara". Ta Ƙarashe tana sakarwa kakarta ta peck a goshi, still da murmushi akan fuskarta ta sake cewa, "Zan fita Daadee, ko akwai wani abun da kike buƙata?".
Haɗe rai Daadee tayi kafin ta ce, "Yaushe ma kika dawo har da kike maganar sake fita kuma? Domin ni dai na san tun da yan uwanki suka tafi makaranta, daga ni sai Sharmila ne kawai a gidan nan".
"Kaiiii, Daadee! Kin dai san cewa yanzu ba lokacin tashi aiki bane yayi. Tunda sai ƙarfe huɗu nake dawowa. Wani aikin ne kawai ya taso min, shi ya sa ma na baro can ɗin ".
A hankali Daadee ta fara tafiya saboda matsalar ƙafafu da take fama da ita. Ta zauna a bakin gado, sannan ta ɗago ta kalli jikartata ta fari, cike da ƙauna, ta ce, "To, na ji. Allah ya tsare, ni goro kawai zaki kawo min".
"Da kuma me?". Faryal ta sake tambaya with a playful tone.
"Yww to sai kuma wannan abun me zaƙi zaƙi da kike kawowa, me kama da cake ɗin nan. Ban san ko zaki wuce ta wurin ba?".
Faryal ta fashe da dariya kafin ta ce, "Tsohuwar nan, kema da kin san daɗi, Yanzu dai a takaice basbousa kike nufi?".
"Yauwa eh ita kinji yar albarka".
"To shikenan In sha Allah, zan kawo miki". Ta faɗa tana matsowa, ta durƙusa a gabanta, tana murmushi. Ta ce, "Ki min addu'a".
Ɗaura hannunta tayi akan Faryal ɗin tare da faɗin, "Allah Ya albarkace ki, ya kare min ke. Ya faranta miki zuciyarki ya kuma nuna min ranar auranki tun ina raye".
"Ameen ameen ya Allah My Daadee. In sha Allah nan ba da daɗewa ba. Ai dole ma ki kashe gwagwaro a cashe dake".
"Ina roƙon Allah kar ya karɓi raina har sai na ga wannan ranar Faryal, Allah ya zaba miki miji na garih".
"Ameen Daadee na".
A dai dai lokacin ne Maama ta shigo ɗakin, kallonsu tayi kafin ta ce, "Dama kina nan? Kin barni inata neman ki, nayi tunanin ma har kin wuce".
Miqewa tsaye Faryal tayi tana faɗin, "Wane ni in yi wannan gangancin, fita ba addu'ar tsohuwata a gareni, me nayi kenan".
Rankwashinta Maama tayi tana faɗin, "Kin fi ni zama tsohuwa ai yarinya".
Faryal ta ruga waje da gudu tana dariya, dan ta san cewa ta kunno mahaifiyarta ta, saboda ta tsani ace mata tsohuwa ko kuma ace ta fara tsufa, dan ita kullum jinta take kamar wata yar 30s.
Girgiza kai tayi tana murmushi ta ce, "Allah Ya tsare. Ki kula da kanki".
Dan daga murya tayi wurin amsawa da, "Ameen Maamana". Daga haka ta fice zuwa compound.
Saida ta shiga motarta ta zauna sannan ta zaro wayarta ta shiga jerin lambobinta. Wata number da akayi saving da Partner in Crime ta dannawa kira.
Ana ɗagawa, cikin zolaya ta ce, "Madam Chef, kina available ne? Cox I know you always have a busy schedule".
Daga ɗayan ɓangaren, aka amsa da, "Sai yanzu kika ga damar kira na, bayan duk missed calls ɗin da na ajiye miki a daren jiya? Okay, saboda kin san abin da kika yi, ko?".
Kunna motarta tayi, ta danna horn sannan ta saka reverse, tana riƙe da wayar a kafaɗarta. Ta ce, "Matsalata da ke rashin haƙuri, shiyasa bakya cin ribar duniya".
"Kin yi Sa'a ne da ma na ɗaga wayarki, banza kawai". Ta faɗa a ƙule.
"Gani a hanyar zuwa wurinki. Kina gida?". Faryal ta faɗa ba tare data bi ta kan maganarta ta ba.
"Eh!". Ta amsa a takaice.
"To gani nan".
"Sai kin zo". Ta faɗa tana kashe wayar.
Sai data fara tsayawa ta sayi duk abubuwan da Daadee ta buƙata. Kafin ta kira Deejah, ta sanar da ita cewa tana kan hanya, sannan ta tambayi abubuwan da sukayi, ta ɗan ƙara musu abubuwan da zasu ƙara kafin ta iso. Sannan ta nufi gidan mai.
Hanyar gabaɗaya ba kyau, kuma kun dai riga kun san yanayin tuqin mu na mata. Kafin ta gama tantance ta inda zata raɓe sai ga wata mota kirar Porsche ta shigo daga bayanta ta wuce. Faryal na ganin hakan, sai kawai ta bi bayanta, amma kafin ta ankara me motar ya taka birki wanda yasa motarta ta doki tasu.
Kashe motar akayi kafin wasu samari biyu su fito daga cikinta, ganin haka yasa itama ta fito da sauri, ta isa wurinsu tana basu haƙuri. "I'm so sorry. Ban lura da lokacin da kuka taka birki bane, dan Allah kuyi haƙuri". Ta faɗa tana duba inda ta buga musu. Allah ya taimake ta motarsu bata samu wani damage sosai ba dan abun akan motarta ya kare.
Wanda ya fito daga mazaunin driver ne ya buɗi baki zaiyi magana amma sai wanda ya fito daga passenger front seat ya tare shi, cikin ɓacin rai ya ce ..........