Free chapter · Read without an account

Chapter 6

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*













*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)







006

Bayan sun sauka Hannatu ta sallami masu mashina ita Murja daman ƴar rakiya ce, haka suka taka har gidan bokan, akwai layi amma ba mai tsayi ba sai suka bi layi har ya iso kansu sannan suka shiga ɗakin, ai da wani irin sauri Hannatu da Murja suka ja da baya, zuciyar kowa ta tsinke.

Ganin bokon da kayan mata fuskarsa har da hoda  da jan baki, ga gashin doki ya saka a kansa,abinda yafi ɗaure musu kai shi ne shatin brazier da suka gani,ga nonuwa sun bayyana a cikin ɗinkin rigar na breast cut, sosai mamaki ya cika su har suka kasa ƙarasowa cikin ɗakin.(Allah yasa ba lemu ya saka a cikin brazier ba🤭🤭🤭) 

Cikin murya ƴan daudu ya ce dasu 

"A'ahhh yau naga tsigi-tsila kun wani tsaya cirko-cirko daku kuna kallemin jiki sai ka ce kwartaye kun ga ƴar duma-duma mai cikar halitta son kowa ƙin wanda ya rasa mtwsss!" 

Yana maganar yana rangwaɗa kamar wata mace macan ma riƙakƙiyar karuwa, har da lanƙwasa hannu da kashe ido yake. Su Hannatu jiki ba ƙarfi haka suka shigo cikin ɗakin tare da samun wuri suka zauna don bakinsa ya daɗe da rufewa,basu da abin faɗa sai dai kallo don wannan al'amari ya girme ma tunaninsu.Bayan sun zauna ya ce 

"Sannunku dangin ƴan gulma, ai na ji komai ɗazu" 

Saurin kallon junansu suka yi suna mamaki

"Au mamaki kuke yi hhhh ai aljana Yalisa ta sanarmin komai don tana kusa daku a lokacin da kuke hirar " 

Nan fa hankalinsu ya tashi, kenan akwai aljana kusa dasu ɗazu suketa ɓarin zance wayyo sun shiga uku, da sauri kamar mai shirin kuka Hannatu ta ce

"A yi mana afuwa Boka mai Zamani,suɓutar baki ne,mun tuba" 

Cilla mata harara ya yi har da murguɗa mata baki,cikin muryarsa ta ƴan daudu ya ce

"Meke Tafe daku" 

Zama Hannatu ta gyara sannan ta sanar masa abinda ke tafe dasu, madadin ta ga ya ce wani abu sai kawai  ya tuntsire da dariya, yana ƙara gyara zaman gashin dokinsa saboda rufe mishi fuska yake. Ya daɗe yana dariya sai can ya tsagaita yana kallonsu, fuskarsa a ɗaure ya fara magana cikin muryarsa ta asali na matsafa

"Wannan aikin mai sauƙi ne sai dai ba a takamin doka a zauna lafiya, idan na sharɗanta ma mutum abu ya kuskura ya taka dokata, to aikin zai dawo garesa babu shamaki, Abi doka a zauna lafiya" 

"To Boka mai Zamani zamu bi komai daka gindaya mana ba tare da an samu tangarɗa ba" 

Muryarsa ce ta sauya kamar almara, ta dawo irin ta ƴan daudu, cike da kashe murya ya ce musu

"Kamar kubi dokar wallah ubanku zaku ci, Eheh" 

Miƙewa tsaye ya yi tare da nufar wata jakar fata wacca take a rataye ya ɗauko, sai a sannan ne na dubi ɗakin da kyau,ɗan ƙarami ne ɗakin, bangon ɗakin an yi masa baƙin fenti complete, sai aka yi rubutu da farin fenti wanda ba iya gane me aka rubuta na yi ba,a gefen hagu tiraran wuta ne wanda bai da daɗin ƙamshi yake tashi sai kace turaran ƴan bori,a ta gefan dama wata ƙatuwar randa ce mai baƙin fenti da rubutun farin fenti. Su Hannatu dai sun yi shiru suna kallon Ikon Allah don duk zuwa yawan gidajen bokayan da suke, basu taɓa ganin boka ɗan daudu ba sai akan wannan bokan, komai da yake iri ɗaya da mata har yana son zaƙewa da yawa. 

Bayan ya ɗauko jakar sai ya dawo inda yake ya zauna har da cewa 

"Wasshhhhhh!" 

Su Hannatu na ganin Ikon Allah.Buɗe jakar ya yi sai ya saka hannunsa ciki ya ɗauko ƙullin magani har biyu wanda kalarsu kusan iri ɗaya ce,With serious tone ya fara magana yana dubansu. 

"Kunga wa'innan magungun kar ku yi wasa dasu, yanzu ma dai wace ce take son aikin ko dukkaninku ne" 

da sauri Murja ta ce

" A'a ita kaɗai ce za a ma aikin ni ƴar rakiya ce"

Kallon uku saura quater Hannatu ta yi ma Murja, ƙwafa kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Kallon Hannatu boka mai Zamani ya yi sannan ya ce

"Kar kiyi wasa da wannan maganin,duk abinda na sharɗanta miki shi za ki bi ba naki ra'ayin ba,ko kuma ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya" 

"To Mai Zamani zan yi yadda ka ce" cewar Hannatu

"Idan kun koma gida, sai kin tabbata yaron na nan sannan ki fito da maganin ki zuba cikin abinci, kinga wanda za ki saka mishi cikin abinci nan" 

Miƙa mata maganin ya yi, ta duba da kyau sannan ya ci gaba da cewa

"Sai wannan ki zuba cikin abin sha kowani iri ki bashi ya sha, to da zarar ya ci abincin ya sha ruwan shikenan ƙurunƙus-kankusu, an yanka ta tashi, babu shi babu barin sata har abada, duk malamin duniya da za su je wurinsa neman taimako ba zasu taɓa yin nasara ba ko ni banda makarin maganin, amma fa ki kula sosai"

Amsar ɗayan maganin ta yi da murna jin haƙarta tana gab da cimma ruwa, sai jera masa godiya take tare da bashi sadakar kuɗi. Murja dai bata ce komai ba sai ma shiga kogin tunani da ta yi tana ayyana abubuwa da yawa a ranta, nan take da sake wani munafikin murmushi. Miƙewa suka yi tare da barin ɗakin sai suka bar gidan. Takawa suke a hanya suna hira,cike da farin ciki Hannatu ta ce

"Kinsan da farko da muka shiga ɗakin na yi tunanin mahaukaci ne"

Da sauri Murja ta ce

"Umm Umm  Ummmmm babu ruwana a wannan zancen ko kin manta ya ce ya ji duk abinda muka faɗa ɗazu a gida ta hanyar aljana, wallahi babu ruwana don ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba" 

Nan da nan Hannatu tasha jinin jikinta har tsoro ya fara ɗarsuwa a cikin zuciyarta,gum ta yi da bakinta sai suka ci gaba da tafiya,suna fitowa daga Layin sai ga masu mashina har biyu, hawa mashin ɗin suka yi sai gida. Kasancewa akwai ɗan nisa shiyasa basu isa garinsu da wuri ba, lokacin ƙarfe 5:00pm ta gota, bayan sun sauka sun shiga gidan sai kowa ya yi hanyar sashensa.

Bayan Hannatu ta shiga ɗaki, cire gyalenta ta yi sannan ta faɗa kitchen don girka abincin dare haɗe da maganin da za ta saka ma Salim a cikin abinci. Girki mai rai da lafiya ta yi,cooler my kyau ta ɗauko da jug, abincin ta zuba ta saka maganin kamar yadda mai zamani ya ce,zoɓon ma ta zuba mai maganin.Wata sabuwa in ji ƴan caca, yanzu ya za ta yi abincin ya kai da Salim har ya ci,akwai chakwakiya, lokaci guda wani tunani ya zo mata, wayarta ta ɗauko ta kira numban Gudidi autar Kakulle wacca suke ɗasawa da ita sosai.Gaisawa suka yi sannan ta ce ta zo tana son ganinta. Amsa mata ta yi da to.

Jiki na ɓari Gudidi ta shirya duk da ana kiran sallar magrib amma haka ta shiryo zuwa gidan saboda kwaɗayi.Kasancewar gidan Gudidi babu nisa  yasa ta iso da wuri,bayan ta zauna sai ta ce mata, ta kira Salim gidanta ta bashi abinci, kar ta bari yaranta suci abincin nan, jinjina mata kai ta yi sannan ɗau cooler da jug ɗin.Kuɗi Hannatu ta miƙa mata masu yawa, jiki na rawa Gudidi ta amsa kuɗin tana mata godiya sannan tabar gidan. 

Gudidi na fita ta haɗu da Salim da Haroon sun dawo daga masallaci,da fara'a a fuskar Gudidi ta ce 

"A'ahh Salim ashe ku ne" 

Cike da mamaki Salim ke kallon,matar da take nuna ta tsanesu, yanzu take sake mishi fuska Ikon Allah, cike da girmamawa ya gaisheta, sai ta sanar mishi tana nemanshi idan ya fito, da mamaki ya amsa mata da "To" 

Koda ya shiga gida ya sanar ma Mammi bata kawo komai a ranta ba ta ce, ya shirya ya je, fita ya yi zuwa gidan. Sallama ya yi a ƙofar gidan sai yaran da gudu suka ce an ce ya shigo, da sallama ya shiga gidan, sai tsallake kwanuka yake a tsakar gidan,gidan ya yi baza-baza da datti,kasancewar akwai wutar lantarki yasa yaga gidan da kyau,har ɗaki ya shiga da sallama a bisa labɓanta, wuri ya samu ya zauna, bayan sun gaisa ta ce ma yarinyarta ta kawo masa abinci a cooler, ɗaukowa yarinyar ta yi har da jug ɗin da Hannatu ta bata,sakar mishi murmushi ta yi tana cewa 

"Bismillah Salim ga abinci fa" 

"Gwaggo ai naci abinci a gida kafin na zo nan" cewar Salim yana kallon cooler da jug ɗin

"Haba Salim ai koda ka ci a gidanku ka ɗan ci nawa koda ƙaɗan ne" tana ƙara sakar mishi murmushi 

Buɗe cooler ya yi tare da ɗaukar cokali bakinsa ɗauke da bismillahi ya fara cin abinci,cokali biyar ya yi ya ce ya ƙoshi,sannan ya ɗauki kofi ya zuba zoɓon shima yasha da bismillah.Duk abinda yake tana satar kallonsa tana murmushi duk da bata san abinda Hannatu ta saka a ciki ba, amma ta san ba abu bane mai kyau.Janshi ta yi da hira har aka kira sallar Isha'i sannan ya yi mata sallama yabar gidan,da murna ta kira Hannatu take shaida mata ya ci abincin har da zoɓon ya sha, sosai Hannatu ta shiga farin ciki don haƙarta ta cimma ruwa. Aikawa Faisal autanta ta ce ya kira mata Innar Balki. 

Rai ɓace haka Murja ta taso ta zo sashenta duk da wani ɓangare na zuciyarta tana farin ciki. Bayan ta shigo ko zama bata yi ba Hannatu ta ce

"Innar Balki!!! Mun yi nasara Salim ya ci abincin" 

Ko ɗar! Gabanta bai faɗi ba sai ta ce

"Shikenan kin cika sharudɗan mai Zamani sai mu jira nashi aikin zuwa gobe" 

Cike ta farin ciki Hannatu ta miƙe tana taka rawa tsofai-tsofai da ita.Murja sai  dariya take mata, sun ɗan taɓa hira daga bisani ta wuce sashenta, koda Alhaji Zakari ya dawo sai da ya tambayeta me take ma farin ciki haka, bata sanarsa komai ba sai dai ta ce zai ji koma mene ne gobe. Shima farin cikin ya shiga duk da bai san wani abu ne ya saka ta farin ciki ba. Cike da farin ciki ya Allah ya nuna ma. 

                🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Koda Salim ya dawo gida lokacin Fatsima ta shigo sashensu tana sanar mata faɗan da Baba Musa ya yi saboda  ta yi mishi maganar auran Hujayrah, da yake tun da rana ta so zuwa Allah bai yi sai kawai ta fito da daddare tun da mijinta yana majalisar layi suna hira, shima Abbu yana tare dasu a wajen suna hira tare,idan Baba Musa na gari yakan shigo har sashensu Abbu ya taimaka mishi su fito majalisar layi su sha hirarsu har dare, Sannan ya komar dashi sashensa tare da yi mishi sallama. 

Sosai maganar Fatsima taba Mammi mamaki, ta rasa wani irin hali Alhaji Zakari yake dashi, a ce ɗan uwanka na jini kake ma asiri,damuwa fal! Ranta ta ce

"Kwantar da hankalinki Innar Nazira, Ubangijin daya haliccemu ba bacci yake ba,yana kallon duk abinda ke faruwa  bai manta damu ba, da sannu sai saka mana,alhaki kwaikwayo ne, duk abinda mutum ya shuka a sannu zai girba da hannunsa, a da nake damuwa da halin  Zakari wanda  yake nuna mana ni da mijina har da yarana, amma yanzu ko a jikina wallahi, har da Innar Harira da Innar Balki yanzu banda lokacinsu,komai za su yi su da Allah,hausawa sun yi gaskiya da suka ce idan za ka gina ramin mugunta to ka gida ƙaɗan don wataran kai za ka faɗan cikinsa,su je su yi ta gina mana ramin mugunta a ƙarshe su za su faɗan,don *Bamu  da Madogara sai Allah* shi kaɗai ne zai taimake mu a halin da muke ciki"

Sosai maganganun Mammin Hujayrah suka ɗarsu a zuciyar Fatsima, sosai ta burgeta har tana cewa cikin ranta 'Da ana samun mata da maza masu hali irin na Zaytuna da kuwa duniya za ta zauna lafiya'  tana wannan tunanin Salim ya shigo ɗakin da sallama. Amsa masa suka yi, sai ya samu wuri ya zauna tare da gaida Fatsima. Cike da kulawa da amsa masa

"Har ka dawo daga wurin Innarsu Badi'ah" cewar Mammi tana karantar yanayinsa

"Eh Mammi, surutu kawai ta cikani dasu, ni na za ci wani laifi na yi" yana dariya ya yi maganar

" Innar Badi'ah kuma, ita da kanta ta ce ka zo gidanta"cewar Fatsima tana mamaki

" Eh Inna ni ma na yi mamaki don tun da nake ban taba zuwa gidan da sunan ziyara ba, sai dai aike "

Riƙe baki Fatsima ta yi tana cewa

"Anya babu wata a ƙasa kuwa" 

"Idan ma akwai Allah ya fisu,lokacin daya sanarmin na yi mamaki sosai" cewar Mammi

"Allah ya mayar musu da aniyarsu, ko wace iri ce" cewar Fatsima tana gyara zama

"Mammi ina Haroon?" 

"Yana tare da Abbunku, ya ce yau dashi za a je majalisa don yasha shayi" 

Dariya Salim da Fatsima suka yi, suna cewa Allah ya shirya Haroon da shagwaɓa. Haka suka ci gaba da hira, daga bisani Fatsima ta yi musu sallama,Salim ya tafi ɗakin kwana kasancewar ƙarfe 10:12pm ta yi, su Baba Musa na gab da shigowa. 

              🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Washe Gari*
*Ƙarfe 9:15am na safe*

A ɓangarensu Hannatu da mai gidanta Alhaji Zakari suna zaune suna karyawa, Faisal na gefe yana cin nashi abincin, hankalinsu kwance suke karyawa sai wayar Hannatu ta fara ringing, har ta kai ƙwan bakinta za ta ci sai wayar ta fara kukan agaji,ajiye ƙwan ta yi tana kallon screen ɗin wayar, an rubuta *UWATA* shiru tana kallon screen ɗin gabanta na faɗuwa ta rasa dalili ga wayar sai ringing take,Alhaji Zakari ya ce

"Ki ɗauki kiran man ko sai ya yanke ne" 

Jiki ba ƙwari ta ɗauki kiran lokaci guda gabanta ya yanke ya faɗi har tsuma jikinta yake,bata san sanda ta ce

"Innayi Mutuwa a kayi" 

A can Innayi wacca take kuka ta ce 

"A'a Hanne, mu shiga uku mun lalace Jamilu na police station" 

Daramm! Dam! Dammm! Ƙirjin Hannatu ya bada lokaci guda ta miƙe daga zaunan da take har tana kaɓe kofin shayin,duk ilahirin jikinta rawa yake, idanunta sun kaɗa sun yi ja,jijiyoyin kanta sun yi raɗo-raɗo sai motsi suke, Tashin hankali wanda ba a saka mai rana,cike da tashin hankali Hannatu ta ce

"Innayi mai Jamilu ya yi da za a kai police station!" 

Ai da wani irin ƙarfi zuciyar Hannatu ta buga wanda idan mutum na kusa ya ita to babu makawa zai iya tsinkaya, ji kaka Dummmmmmmm! Jin abinda Mahaifiyarta ta ce Jamilun ya yi,sake maimaitawa ta yi ma Innayi 

" Innayi kika ce SATA Jamilu ya yi, SATA fa Innayi kodai baki ji da kyau bane" 

A can Innayi ta ce

"Da gaske sata Jamilu ya yi, nima na yi mamaki sosai don bai taɓa ɗaukar koda tsinke ne da sunan sata tun yarintarsa har girmansa,gashi da ƙwazo a karatu, gobe fa zai ta fi Lagos bautar ƙasa a can suka tura shi, amma da safe muka tashi da mummunan labari an kama shi hannu dumu-dumu ya saci manyan wayoyi a har takwas a wani babban  shagon saida wayoyi a cikin kasuwa, mai gadin kasuwar ne ya kamashi"

Nan take Hannatu ta saki wayar tare da ɗora hannu akai tana fasa uban ihu wanda babu wanda bai ji a gidan ba,Alhaji Zakari sai tambayarta yake lafiya meke faruwa, shi daman tunda yaga ta miƙe shima ya miƙe, jira kawai yake ya ji abinda ke faruwa, ihu kawai take saki tana cewa

"Na shiga Uku na lalace! Wayyo Allah ni Hannatu!!" 

Tana wannan ihun ne sai Murja ta faɗo ɗakin a gigice ita da mijin suna tambayar lafiya, meke faruwa, Kakulle, Fatsima da Baba Musa da saurinsu suka shigo ɗakin a gigice, don yadda take ihun da kururuwan dole ya tsorata ka matuƙa ainun, har maƙotansu ma sun fara shigowa don kashe kwakwatar idanunsu,sai daga baya Mammi ta shigo bayan Abbu ya matsa mata akan ta je ta ji ko lafiya, meya faru. 

Sai tambayarta suke amma taƙi basu amsa sai ihu take tana cewa ta bani ta lalace,ɗaukan wayarta Alhaji Zakari ya yi yana duba wanda ya kirata na ƙarshe, *Uwata* yaga an rubuta yana kyauta zaton rasuwa akayi mata, sai kawai ya danna kira, bugu ɗaya-biyu a na ukun sai Innayi ta ɗauka tana sallama, Alhaji Zakari ne ya ce 

"Innayi meke faruwa ne, na yi-na yi Hannatu ta sanarmin abinda ke faruwa amma taƙi, sai faman ihu take ta tada hankalin kowa a gida" 

Bata tsaya wata-wata ba ta sanar masa abinda ke faruwa,Haba wani irin gumi wanda bai san da zuwansa ba ya fara masa ambaliya a jikinsa,duk ilahirin jikinsa ya jiki sharkaf! Sai maimaita 

"Wa'innahu min Sulaimanu Bismillahir rahmanir rahim!!! Wa'innahu min Sulaimanu Bismillahir rahmanir rahim!!! Innalillahi! Innalillahi!!" 

Sosai Alhaji Zakari ya sake tada hankali su Kakulle,da ta gaji ta ce

"Wai meke faruwa ne ɗan Inna, kun sakamu a duhu kuna ƙara tada mana hankali, ba kai ba ita ba, Haba don Allah ka fito fili ka yi mana bayani" 

Sharce zufa yake amma ƙara tsattsago mishi take, cike da damuwa da tashin hankali Alhaji Zakari ya ce

"Inna! Inna! Ɗana Jamilu aka kama yau da safe a shagon saida waya hannu dumu-dumu, gashi jiya ya kirani ya ce gobe zai tafi Lagos bautar ƙasa, Wa'innahu min Sulaimanu Bismillahir rahmanir rahim" 

Lokaci guda ɗaki ya kaure da salati da sallallami,cike da tashin hankali Baba Musa ya ce

"Zakari zama bai gammu ba,taho muje Giwan a samu ya fito kafin goban kar ya samu matsala a karatun sa" 

Da sauri ya shiga uwar ɗaka ya ɗauko key ɗin motarsa ya fito, a nan aka fara drama da Hannatu tana cewa  ita sai ta bisu, sai haƙuri ake bata amma amma taƙi sauraronsu, sai da Alhaji Zakari ya daka mata wata uwar tsawa sannan ta shiga taitayinta tana gunjin kuka. Haka ta haƙura suka wuce, Alhaji Zakari, Baba Musa da Baba Zubairu su uku suka shiga motar suka nufi Giwa local government kasancewa acan Jamila ɗan Alhaji Zakari ya taso kuma acan ya yi secondary daga bisani ya tafi jami'ar Ahmadu Bello ya karanci ɓangaren Agriculture wato harkar noma, yana zauna da kakarsa ce mahaifiyar Hannatu, yanzu haka ya za da shekara 30 da haihuwa, duk wani so da buri Hannatu da Alhaji Zakari sun ɗorama Jamilu, sosai suke Alhaji Zakari yake biya mishi kuɗin karatu don gaba ya taimakesa. Wannan kenan... ✍️

                     🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Bauchi State.Nijeriya*

Sosai Hujayrah take huci tana kallon matar wacca ta yi mutuwar tsaye tana kallonta,Hujayrah na huci ta ce

"Kika ce inna isa, to na isa har nafi isarma isa!!! Ke har wani ƙarfi kike dashi da zan ji tsoro ko shakkar tun kararki, wa'inda suka fiki jiki mun yi karan-batta balle ke karan kaɗai miya, jiki Duk ƙashi" 

Sosai take masifa kamar ta ari baki,ɗaya a cikin ta riƙo Hujayrah ta baya, da wani irin sauri ta kai mata duka, wacca aka mara ma dukan ta kai ma Hujayrah nan take suka kacame da dambe ji kake tim! tim! ƙush! ƙush! Hujayrah wannan damban da suke Hujayrah bata bari sun yi galaba akan ba, sosai take kai musu duka, idan kuma sun ka mata duka sait ta zille, suna cikin damben sai ga Hajiya ta zo wurin babu ko hijab hankali tashe. Tsawa ta daka musu lokaci duka suka tsaya da faɗan sai faman huci suke suna harar junansu.Juyawa Hajiya ta yi sai ta ce 

"Ku biyoni ciki" 

Biyota suka yi a baya, ita Hujayrah sai ta tsaya ta jira Rabi wacca take duƙe tana kuka, suka biyosu daga baya.Ɗakin suka nufa kasancewa kowa can ya nufa. Zama suka yi a ƙasa Hajiya na saman kujera tana kallon, ɗakin shiru ya yi kowa na saƙe-saƙe a zuciyarsa,gyaran murya Hajiya ta yi tana kallon kowa,sake shiga taitayinsu suka yi musamman matan don ita Hujayrah wani ciccin magani take tana musu harar ƙasa ido,bata so Hajiya ta zo a lokacin ba, ta so ta ci ubansu lakada a waje su goge raini. 

"Raziƙa meya haɗaku faɗa  da baƙuwa?" cewar Hajiya tana kallon matan. 

Wacca aka kira da Raziƙa daman ita ta kaiwa Hajiya gulmar ana dambe da baƙuwa ta ɗan kalli Hujayrah sannan ta gyara zama ta ce

"Hajiya baƙuwa ce bata da gaskiya, kawai daga fitowa taga Rabi na kuka sai ta shatata ma Sajida maruka har biyu, hagu da dama ji kake tasss! tasss! Ba tare da ta tambayi ba'asi ba, sannan ta kaiwa Hajara duka, nan fa suka kacame da dambe" 

Ƙarya ce tsagwaro Raziƙa ta shatfa tana magana tana kallon Hujayrah duk da ta ji tsoro yadda ta kafa mata kaifafan idanunta ta kallon.Bayan ta saurari Raziƙa sai ta tambayi su Sajida da Hajara kamar yadda Raziƙa ta ce mata haka suka sanar mata har da ƙara gishiri don ta yi zaƙwai-ƙwai.Bayan ta ji ta bakinsu sai ta dubi Hujayrah wacca ta kafesu da ido babu ko ƙyaftawa ta ce

"Hujayrah shin abinda suka faɗa hakane" 

Sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce

"Hajiyarmu mai share kukanmu, mai yin hukunci tsakani da Allah ba tare da banbantamu ba,mai faɗin gaskiya duk ɗacin sannan kuma mai ƙaryata Ƙarya duk daɗinta,idan na faɗa miki tsakani na da Allah za ki yarda?" 

Jinjina mata kai Hajiya ta yi don Hujayrah na matuƙar birgeta saboda iya kalamai. Gyara zama Hujayrah ta yi sannan ta ce

" Hajiyarmu mai share kukanmu kamar yadda na sanar miki ni na tsinci kaina ne a garin nan bansan Kowa ba haka-zalika bansan sunan garin nan ba sai daga baya,To bayan na zo gidan abincin nan mai albarka wurin matan nan na je na yi musu sallama, ciki-ciki suka amsamin, Hajiyarmu ban damu na sake cewa ina da tambaya, amma babu wanda a cikin ya kalleni illa Rabi wacca fuskarta da fara'a ta tako har wurina na shaida mata abinda ke tafe dani, sosai ta yi murna da zuwa, har waccan "

Nuna Hajara Hujayrah ta yi sannan ta ci gaba da cewa

"Buɗar bakinta ta ce wai Rabi ta zo su ci gaba da aiki ta ƙyaleni, don ba za su yi aikin jaka ba, su ci abinci iri ɗaya sannan a basu kuɗin iri ɗaya, ni kuma sai na jayota zuwa wurinki kasancewar ita ta san inda kike,bayan kin min tarba mai kyau tare da ɗaukana aiki har kika bani masauki mai kyau da tsafta tare da haɗadɗan abincinki mai rai da motsi,ga wasali har biyu sai kabbara sukemin,baki barni haka ba kike haɗamin da ruwa mai sanyi wanda ya sanyaya zuciyata ya hanata ƙunci da damuwa,bayan na kammala jan girkinki har na wanko hannuna sai na ji hayaniya a bayan ɗakin,da yake nasan wurin wanke-wanke ne kawai na saka hijab na fito wurin, koda na zo na samu Rabi a tsakiyar matan nan tana duƙye sai kuka take, ban ce dasu komai ba sai na dubi Rabi na tambayeta meke faruwa,kawai waccan mai ƙarmasasshen jikin"

Nuna Sajida ta yi sannan ta ci gaba da cewa

"Ban fa sato bakinta ba ta ce da gadara da izza tana wani jijji da kai ta ce 'Ni na mareka ko za ki... Hajiyarmu ban bari ta ƙarasa maganar na cika aiki,ba a taɓani ba ya na cika balle an taɓoni,ita kuma waccan Hajarar ta Jani ta baya kawai muka kacame da dambe" 

"Zabiya uwar zance, wannan zance haka babu ko ɗigon aya Hujayrah" cewar Hajiya tana murmushi

Taɓa kumatunta Hujayrah ta yi tana murmushi ta ce 

"Ai Hajiyarmu na daina surutu ba kamar da ba"

"Sannu da ƙoƙari Aku, yawwa Rabi faɗa mana meye dalilin daya saka Sajida ta mareki" 

Nan Rabi ta sanar mata akan meyasa ta raka Hujayrah zuwa wurinta shi ne dalilin haka, Hajara har da zagin mahaifiyar wacca take kwana a ƙabari.Sosai ran Hajiya ya yi matuƙar ɓaci don ta tsani zalunci da mugunta,faɗa ta hau su dashi babu ji babu gani, sai daga baya ta koma musu nasiha tare da ce musu su ba Rabi haƙuri akan zalintarta da suka yi.Ransu ba ya so ba haka suka bata haƙuri.

Bayan sun fito dukkansu sai Hujayrah ta yi gyaran murya hakan yasa suka juyo suna kallonta.Murmushi ta sakar musu ta fara musu waƙa tana cewa

" *_Kun yi abun ya sha muku kai Chasss! Wai ya akayi wanka yabi jiki Chasss! Ku ya kuka ga Hujayrah ta ci gari chasss! Chassss! Chassss! Chassss! Chassss!!!_* " 

Rawa take har da juyi tana waƙar har abun yaso ba Rabi dariya don yadda take yi dole mutum ya dara. Harara suka cilla mata sannan suka wuce cikin babban falon don taya sauran ma'aikatan aiki ba tare da sun tanka mata ba, amma kowa na ayyana abubuwa marasa kyau akanta tare da alwashi mai girma akanta.

Haka Hujayrah ta ci gaba da rayuwa a wannan gidan abincin har mafi wayan customers sun gane ta saboda ban dariyarta, har sun fi son ta kawo musu abinci akan wasu su kawo musu. Sosai su Sajida suka kullaci Hujayrah a rai ganin daga zuwanta ko sati baya yi ba har ansanta,kowani customer ya zo sai dai ka ji ya ce Ina Hujayrah, Hujayrah dai Hujayrah hakan ya ƙara musu tsanarta sosai. Ko shagunan saman layi sun fi son Hujayrah ta kai musu abinci ko don su ci dariya da barkwancinta, sosai hakan Kema Hajiya daɗi a rai don New customers ta ƙara samu a dalilin zuwan Hujayrah har take tunanin anya za ta bari Hujayrah ta koma gida. 

Kamar kullum da yamma Hujayrah ta kai ma masu shaguna abinci wa'inda suke a ɗaya layin,har ta kai ta amsa kuɗin zata tsallaka titi kamar an ce ta wai ga Rasssss!!! Ƙirjinta ya bada ganin Alhaji Sambo Dala ya fito da rantsattsiyar motarsa mai numfashi ya nufa wani babban pharmacy wanda yake a ɗayan layin, sosai hankalinta ya tashi jikinta har ya fara rawa, lokaci guda ta rikice ba tare da ta kalli titin ba ta shigo ciki,sai horn ake mata amma ina hankalin ya daɗe da barin jikinta. Ai da wani irin karfi mai motar ya taka birki ji kaka Ƙiiiiiiiiiiiiiiiiiiii... ✍️




*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***


















Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol