Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Nasreel ML · Furen Zuciya

🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
 Flower of the heart.

   By Nasreel R.L.
      🤍A hausa love story…….

Chapter 3;

Su Layla basu karasa inda takeba Khalisa tayi saurin tsayawa a gabansu tayi musu tsakani, cikin dan daga murya tace “Yane badaku takeyi ba, babu ruwanku da ita”. Wani kallo wanda ke bayan Layla tayi nata sama da kasa kafin tace “ ke yarinya matsa mana anan kafin bakinki yayi jini banason rashin kunya anan niba sa’ar yinki bace”. 

Kallo khalisa tabisu dashi tareda folding hands dinta a kirji tana kara gyara tsayuwanta alaman bafa zata matsa ba. Gaba Layla tayo kamar zata daketa saikuma dayar dabata yi magana ba tun tuni saidai dariya tayi saurin riko ta tana mata kallon warning. Layla sarai tagane me take mata warning akai. Tasan idan har ta taba khalisa toh lallai yau head servant zata nuna musu masifarta na da ba komai bane dan wlh saita sa an kore su. suda samun wani aikin kuma sai wani ikon Allah, sannan ana biyansu sosai anan bakuma wani aiki sukeyi ba. 

Kamar bazata hakura ba dai ganin ita zata chutu hakan yasa kawai ta juya tana ballawa Khalisa harata aranta tana fadin zasu hadu da Miral saita gyara mata zama. 

Khalisa ganin sun koma a hankali ta tsugunna dan nesa da Miral sannan cikin tausasa murya tace “ Miral kiyi hakuri, bansan mena miki ba ni kawai kawance nakeso muyi naga bakida kawa ko daya, amma yanzu kiyi hakuri bazan sake ba idan ma wani abu nayi miki. tashi ki tafi daki kada wayannan marasa mutuncin suyi miki wani abu”. 

Kamar Miral batajita ba dan still girgiza kanta takeyi tana furta abubuwa dabama zaka gane komai daga cikinsu ba. Takai wajen 5 minutes agurin kafin ta dago kanta da fuskar ta tayi sharkaf da hawaye idanunta sunyi ja fatar face dinta shima yayi ja kamar tomato. A sanyaye ta mike idanunta a kasa ta dauki jilbab da rigar daya fadi kasa ta fita daga part din. Dakinta ta wuce ta shanya kayan a jikin kofa sannan ta shige kawai ta kwanta kan bedsheet din tana shasheka tareda maida ajiyar zuciya. 

Ko 15 minutes batayi ba bacci ya dauketa bata tashi ba sai washe gari wajen karfe 6am na safe. Wani irin ciwo jikinta kemata batasan ko dan tun jiya da rana take bacci bane kokuma dan cewa kan cement ne da bedsheet kawai take kwance? Mika tayi sannan ta mike aranta tana fadin yau babu zafi sosai saikuma ta tuna maybe dan safiya ce rana bata kwallo ba. 

Mikewa tsaye tayi tareda jujjuya wuyanta daya sage kamar an buga mata katako a gurin. Wata yauwa ne ta ziyarceta cikinta yayi wani kara tanajin hanjin cikinta kamar an daure mata su. Saurin daukan jilbab daya bushe akan kofa tayi ta zura hannunta nadan rawa kwata kwata batajin kwari a jikinta. 

Kitchen ta nufa ta tarar chefs na cooking breakfast  kanshi natashi taji yawunta yawani tsinke. Kara cikinta yakara yi da sauri ta fita daga kitchen din ta wuce waje ta zauna a terrace dan saita jira sun gama idan da ragowa da ba’ayi serving ba saita dauka. Wajen 10 minutes tayi amma jitake kamar yunwar zata kasheta idanunta sun dan cicciko da kwalla. 

Kamar tayi ihu takeji, a rayuwanta ta tsani yunwa. Zata iya jure komai amma banda yunwa duk kankantan yunwa saita gigitata. Jin an bude gate yasa ta juya don ganin waye, ganin khalisa ne yasa tayi saurin dauke kai tafara wasa da siraran yan yatsunta dake daukeda farata masu kyau daidai hannunta. 

Tanajin yanda ta karaso har inda take saidai bata dago ba harta tsaya dan baya da ita kadan idanunta a kanta. Dan sauke ajiyan Zuciya Khalisa tayi sannan tace “ Hello, Miral”. Tana fadin hakan kuma ta cigaba da tafiya zuwa cikin gidan. Dan dagowa Miral tayi jin tabude kofa a tunaninta ta shige tana kallon kofar kuwa suka hada ido. Taso tadauke kai saikuma tadan yi dan guntun murmushi tareda daga mata hannu tanajin nauyin abunda tayi mata jiya dan ita batamasan tayi bah.

Smile din Khalisa ta mayar mata sannan ta shige tareda rufe kofa. Miral ta juya ta cigaba da wasada yatsunta tana tunane tunanen yanda rayuwa ta kawota nan. Ba uwa ba uba babu ya babu kanwa. Ba kawa babu maisonta, toh inma tanadasu mezasu kara mata banda ciwo? Ciwon da har abada bazai taba warkewa bah? Nunfashi ta sauke tareda mikewa ganin rana yafara dukantanta gari yafara zafi ta shige ciki. 

Kitchen ta shiga wanda ta tarar da head servant a ciki tana ba maids orders din ayyukan da za’ayi, alamun chefs sun gama kenan. Kallo head servant ta wurgama Miral tareda dauke idonta tana yamutse fuska. Babbar matace zatakai maybe 50 years tamada bitch face irin me tsorata yara ga wani black lipstick datasa a bakinta da kwalli daya dambaro batada tsawo ko kadan ranta a hade kamar mala’ikar mutuwa.

Sunkuyar dakai Miral tayi sannan ta nufi side din kitchen da ake wanke wanke ganin har an fitoda plates da mugs da sauran abubuwa na wankewa yasa ta nade hannun jilbab din ta wanke komai tas tas sannan ta sakasu a dishwasher ya gama ta kashe lokacin head servant da sauran maids din duk sun tafi yin ayyukan su. 

Fridge din leftovers ta bude saidai yau babu sa’a dan babu koh faranti a ciki tawani waro ido da nandanan yaciko da kwalla tai narai narai da fuska kenan yanzu bazata samu breakfast ba? Kodai ta duba main fridge ne? Saurin girgiza kai tayi tuna shekaran jiya bazataso a kara kamata tana daukar abinci ba. 

Kamar daga sama taji an kwalo mata kira tayi saurin mikewa daga tsugunnen datake ta mike tajuya inda taji muryan. Daya daga cikin maids din gidan ne tace mata taje ciki Ummi na kiranta. Da ok ta ansa aranta tana tunanin mekuma zatayi ma Ummi? Ko wanki zatayi? Amma kuma ai ko kwana uku batayi dayi mata wanki ba. Kauda tunanin tayi ta wuce palour tana tafiya a hankali dan jikinta babu kwari kwata kwata. 

A kujerar datake zama ta sameta a hakimce fuskarta dadan sarari dan yau ba’a murtuke takeba. Gakuma wata mata gefenta sanye da jeans da blouse ta rufe face dinta da face mask da wani shades a idanunta babu abunda kake gani a bayan wuyanta. 

Gaban Ummi ta tsugunna ta gaisheta kanta a kasa Ummi tayi mata alama ta gaida matar. Juyawa tayi ta gaisheta batareda ta dago kai ba sama sama matar ta ansa sannan ta juya ta kalli Ummi cikin harshen turanci tace “ Can we start? I don’t have time to waste”. Gyada mata kai Ummi tayi matar ta tambaya a Ina zasuyi? 

Dan jim Ummi tayi dan batayi wannan tunanin nan ba, ganin kada ta batama matar lokaci kawai tace suje guest room dake anan kasan. Mikewa matar tayi Ummi ma ta mike tace Miral ta biyosu. Tashi tayi tanajin yanda kirjinta ke bugun uku uku mekuma za’ayi yau? Yanzu tsoro yafara shiganta meke shirin faruwa ne? Me Ummi zatayi da ita? Suwaye wayannan dake zuwa ganinta haka?.

Ganin an nufa guest room yasa taji toh kodai aiki zatayi ne? Questions sunfi dari suke shigo mata gashi babu mai ansa mata. A daidai kofa ta tsaya Ummi ta shige chan cikin ta zauna bakin bed tana nunfarfashi tsabar kiba. 

Wata jaka matar ta ajiye a kan gadon tareda budewa ta fara  fiffito da wasu karafuna da kayayyaki kana gani kasan kayan hospital ne kaman za’a duba mara lafiya. Juyowa tayi ta kalli Miral tace ta cire hijab din jikinta tazo ta kwanta. 

Wani irin faduwa gabanta yayi kwakwalwarta takasa daukar me akece. Wani irin kallo tayi ma Ummi dabata masan tayi ba dayasa Ummi ta daka mata tsawa, batasan lokacinda tazo ta kwanta kan gadon bah. 

Matar tace ta tashi ta cire hijab, jikinta na karkarwa ta mike ta cire hijab din sannan ta koma ta kwanta. Ganin matar ta matso dab da ita sannan tasa hannu ta daga rigarta zuwa cikinta yasata sakin wani ihu ta zabura ta damke rigar ta rufe jikinta dan babu komai a jikinta bayan rigar batada undies. 

Wani gigitaccen mari Ummi tasakin mata dasaida ganinta da jinta gabadaya ya dauke. Duk kawai taji tama kasa motsi dan ba’a taba mata mari irin hakan ba. Hannu Ummi tasa ta damko wuyanta tareda baya da ita ta kifo kan gadon ta kwantar da ita dakyau da saida ta fizge hannun Miral daga jikin rigar ta kwayeshi har zuwa cikinta kafin Miral ta dawo daidai. 

Jin hannun Ummi akan wuyanta kamar zata kasheta dukda ba matse mata wuyan tayi sosai ba amma ta sakin mata nauyin hannunta dayake kamar dutse tsabar nauyi. Dakyar take jan nunfashi tana jin yanda matar tasa hannunta akan naked private part dinta. Mani marayan kuka ta saki tareda fara shushura kafa tana shasheka dayasa Ummi ta shake wuyanta sosai da tuni ta nutsu jin kamar ranta na fita daga jikinta yasa Ummi tadan saki kadan yanda zata ita nunfashi amma bata saki gabadaya bah.

Ko minti daya ba’ayi ba matar ta ja mata rigar tarufe sannan ta kalli Ummi tace “sakin mata Wuya kada ki illata ta nagama, basai nayi wani further examination bah Hymen dinta is intact, dan haka ac….”. Shiru tayi dan ganin sign da Ummi tayi mata tagane ba’aso yarinyar tasani. Dan haka saita chanza maganar kawai tace “ a ina take kwana?” Tafada tana shafa fatar kafar Miral. 

Sakin wuyanta Ummi tayi sannan ta tambayi Miral. Cikin wata wahalalliyar murya datake breathless very soft tace “ A store room na storage area”. Dan shiru Ummi tayi dan batamasan a ina take kwana ba sai yau. A iya saninta a palourn masu aiki da akace mata tana kwana batasan yanda akayi takoma wani store room ba. Gyada kai matar tayi sannan tace “ akwai zafi ne a dakin sosai? Ya ventilation din yake?”. Miral ta ansa mata da cewa akwai zafi sosai sannan babu window.

Kallon Ummi tayi sannan tace “a chanza mata daki, infact ta dawo nan damuke ta zauna na lura babu kowa dake anfani da dakin. Skin dinta is rough duk kananan kurajen zafi kinsan kuma bama daukar wannan koh? Dan haka ta dawo nan da zama in the meantime kuma akwai meal plan da supplements dazata rinka using. Kada ta rinka fita rana sai karfe 6 na safe na 20 minutes kawai bayan haka ta zauna a cikin daki ba aiki na lura hannunta is not as soft as we want alamun tana aiki da ruwa sosai ko wanki. Sannan kayanta might be contributing to rough skin din dikda skin din nata nada kyau dan inba medical professional ba bazaka gane akwai something wrong with it bah. Sannan kwana nawa zaku kara anan din?”. 

Dan gyada kai Ummi tayi dan sam zuciyar ta bata so hakan ba. Tunda dai tana iya kwanan store room din koba window ai yafi ta rabu da ita dai a chan din, amma babu komai. Nanda 1 week zasu koma Ghair muaddal ta yarda kwallon mango ta huta da kuda, dan haka kawai saita ce toh tunda dama babu kowa a guest room din sannan akwai wani koda tayi baki. Dan haka ta ansa ma da matar 7 days zasu kara. 

Da haka matar ta kwashe kayanta ta mayar cikin bag din sannan ta juyo tayima Miral one final look ta cikin shades dake face dinta ta fita. Binta a baya Ummi tayi da sauri dan sauri. Tafiyar nasu ba daya ba. Ganin bazata iya kamo matar bane yasa ta kirata da Miss! Miss! Tsayawa da tafiyar datakeyi matar tayi tareda juyowa ta kalli Ummi ta cikin shades ummi tayi saurin karasawa inda take tana nishi tace “Yanzu tunda kun tabbatar yaushe ne kukeso a kawo muku ita? Nanda 7 days zamu tafi Ghair muaddal shin a airport zaku ansheta? Kokuwa zan tafi da ita har gidan iyayenta ne dan chan muke sauka”. 

Shiru matar tayi kamar bazata ansa ba chan kuma tace “wannan maganar ba’a hannunki yake ba, duk lokacin da muke so zamu zo mu dauketa, bama sa lokaci dan mu mukeda lokaci ba lokaci keda muba”. Tana fadin hakan kuma ta cigaba da tafiyarta. Ummi taso ta tambayeta ta ina zata samesu ko subata number amma sanin bazasu bata ba yasa kawai ta juya. kan sofa ta zauna tana cizon thin lips dinta tana abun sosai yayi mata ciwo sunki su ansa mata kowani question datake musu. Babu wanda yake treating dinta da wannan rasin mutuncin banda su dan kowa yasan waye su a duniya bama guri daya ba. Mijinta nada one of the biggest car manufacturing company a duniya. Kowa cikin respect yake dealing da ita amma su basada wannan. 

Sannan ma babu abunda yafi mata ciwo sai ganin cewa sufa wayannan ma dasuke zuwa kananan rank ne a kungiyar, bama manyan bane amma suna jinsu kamar duniya na juyi ne saboda su. Ita babu abunda ke damunta ma sai alkawarinta, batasan yaushe zasu dauki yarinyar ba dan haka bata san yaushe zai shigo hannunta ba harsai sun dauketa. Kamar tayi ihu haka takeji ta zaro wayarta ta kira head seevant a kawo mata abinci dan wata mahaukaciyar yunwa takeji dukda ko 1 hour da gama breakfast batayi ba.

For more information, contact me via WhatsApp ***.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol