Free chapter 路 Read without an account

1

by Asmy b Aliyu 路 OMRI HAYATII

OMRI HAYATII馃┓

by
Asmy b Aliyu....

DEDICATION TO MY SPECIAL PERSON 
(AYUSHERH MUHAMMAD)




1.....

Karfe 8 daidai ya fito daga bangarensa 
cikin fararen kayan da sukayi masa wani irin kyau.ya riqe hula a hannunsa,
gashinsa ya wani irin kwanta tamkar na larabawan maroco tun kafin ya bude bangaren mahaifiyarsa wacce suke kira Mami.qamshin turarensa ya sanar dasu zuwansa ,mai aikinsu ce ta bude masa kofa dattijuwa ce sosai wacce shekarunta Zasu Kai a kalla hamsin da biyar 
cike da girmamawa da fara'a take gaishesa,Shima cike da kulawa da wata irin qamewa yake amsa gaisuwarta,
Kai tsaye bedroom din Maminsa ya nufa,
knocking kofar dakin yayi sai da aka basa izinin shiga ya shiga da sallama,
Sai dai ganin wacce ke kwance a gadon Mamin  yasa ya dan hade rai,
sanin halinsa yasa ta miqe zaune 
Yayanmu ina kwana."tamkar anyi mata dole haka ta gaishesa kallon da taga Yana aikawa ta saitin ta yasa ta qara kama kanta ,bai amsa ba yake tambayarta Mami fa?"
tana kitchen.ke zaman me kike da bazaki bita kitchen din ba,dan marairaicewa tayi
tana yarfa hannunta.banfa da lafia Yayanmu.
ka manta jiya kamun allura."ya qara hade rai,kina nufin tun jiya bakiji sauki ba kenan."itama hade ran ta karayi,
to wai Yayanmu idan na maka Karya ribar me xanci dan Allah."cikin dakin taga Yana shigowa ganin yanayinsa yasa ta miqe 
tsaye tana wani Jada baya tana wani yarfa hannunta."wuce ki tafi ki taya Mami aiki kafin ranki ya baci Fareeda."afusace ta nufi kofa tana masa wani irin kallo tamkar Zata fashe masa da Kuka,Kara daga kafa yayi tamkar zai cafkota ganin haka yasa fareeda ta kwasa da gudu ta fice tana kwalawa Mami kira.kusan cin Karo 
tayi da Mamin,da gudu ta koma bayan Mami.

"ke meya faru?"
wai meyasa bakya da natsuwa ne.
Kafin Fareeda tayi magana ya qaraso wurin Mami ta kallesa ,Kara gaisheda Mamin yayi da respect dukda Sun gaisa da safe,
bayan ya dawo sallar Asuba shida Abba.
Mami ta kallesa,kafin tace har ka shirya kenan.Yana shafa kansa yake fadin na shirya Mami kin manta tafiyar mota zamuyi."Kai dai wallahi yayanmu allah ya dora maka wahala in banda wahala ta Yaya ga jirgi xaka wani dage Sai a mota.
Mami ta juya a fusace tana watsa mata wani irin kallo take fadin"don uwarki zoki wuce kafin ya riqaki Mai masifaffen baki Ina ruwanki."juyawa tayi ta nufi dakinta
batareda ta koma dakin Mamin ba,
zo muje kayi breakfast gayacan na hada maka.dan dukawa yayi ya rungume Mamin,Yana fadamata thank you.

murmushi mamin tayi tana dan shafa kansa,haka tana jin wata irin soyayyar yaron nata na Kara ratsata,
har dinning area Mamin ta jasa tayi serving dinsa.
zama tayi tana kallonsa Yana juya tea da mamin ta hadamasa,
cikin damuwa Mami ke fadin''

mu'azzam!!"
Dan dakatawa yayi jin Mamin ta kira sunansa,Kai baka tsoron yadda hanya ta lalace saboda masu garkuwa da mutane haka zakabi hanya tun daga kaduna har Kano saboda daurin Aure.meyasa bazaka bi flight ba."mami babu abunda zai faru dan Allah kiyi muna addu'a bani kadai zanje ba fa tareda su umar zamuje."
nasan tare Zaku tafi Amman nasan 
Kai  zaka saka su  suyi tafiyar mota 
nafa San halinka,dariya Kawai yayiwa mamin ,yana fadin Mami kiyi muna addu'a in sha Allahu lafia zamuje mu dawo lafia.ajiyar zuciya Mami ta sauke tana fadin Allah ya kaiku lafia."Idan ka gama ka shiga kayiwa abbanka sallama,
in sha allahu Mami."anan Mami tabarsa ta nufi bedroom dinta dan bacci ne sosai a idanunta saboda mu'azzam din ta tashi
sanin halinsa idan ba ita ta saka hannu tayi masa komai ba baci xaiyi ba haka yake tamkar Karamin yaro ko fareeda dake auta bata abunda yake.....Sai da yayi full
ya koma bangarensa ya shiga toilet yayi brush ya dauki suitecase dinsa 
da car key dinsa ya nufi bangaren Abba,
samun Abban yayi anan falo
Yana waya Sai da ya jira ya gama ,
ya Kara gaishesa,ya amsa cike da kulawa Yana tambayarsa har ya fito kenan,
shafa kansa yayi Yana fadin ehhhh Abba."

Masha Allah .allah ya kaiku lafia ya dawo daku lafia."amin ya rabbi abba.abba ya dauki wayarsa nan take yayi masa transfer kudi 500k.kasha ruwa a hanya ,
godiya sosai yayiwa abban nasa. yayi masa sallama,ya fice daga falon ko da ya fita parking lot.buzu Mai gadi ya wanke masa motarsa tas,dan ana gama sallar Asuba ya fara wankin motar koda 7 tayi ya gama
har part dinsa ya tafi ya Kai masa key dinsa,
ya kirgo dubu goma yana baiwa buzu Mai gadi karba yayi Yana washe baki 
Yana yimasa godiya da haka ya bude masa katoton get dinsu ya shiga motar yayi mata key yabar cikin gidan,
a hanya ya kira Omar Yana fada masa gaya ya fito anan yake shaida masa 
suna tareda Anas ,ganinan karasowa
ya fada Yana sauke wayar 
Yana sauke wayar wani Kiran na shigowa
dan duba Mai Kiran yayi,ganin wacce ke Kiran ya dauka.

"malaak  zan kiraki Ina driving......"ya fada cikin natsuwarsa dake qara mata wani irin sonsa,ok bye my love,katse Kiran yayi
koda ya isa kofar gidansu Omar 
bai shiga da motar ba a kofar gida ya tsaya .ya dauki wayar Yana kiran 
malaak. tamkar Wayan na hannunta ta dauka.

Doctor na!!!"
ta fada a shagwabe,
how are you??"
ya fada cike da kulawa a muryarsa
am good...and you?"
Alhmdullahi."
har Kun kama hanya kenan??"
ta fada da wani irin laushi a muryarta
da har ajikinsa yaji hakan,
yanxu dai zamu wuce gani a kofar gidansu Omar.zanyi kewarka ."dan murmushi mai sauti ya saki Yana fadin nima haka,
dan yasan da gaske din zatayi kewarsa.
dan hira suka taba kadan 
kafin tayi masa addu'ar Allah ya
tsare hanya,
jin yayi ana kwankwasa kofar motar adaidai gefen da yake 
Anas ne ya bude kofar motar Yana kallonsa cikin farar shadda Shima da hula akansa,
wane wulakanci ne haka zaka shanyamu muna jiranka."
tun dazu na qaraso na tsaya amsa wayane,
dan tabe baki Anas din yayi dan 
yasan bazai wuce malaak ba wacce suke kira da manyyar mu'azzam,
dan duk yadda mu'azzam yake da ya'mmata haka Yarinyyar nan Zata shiga ta fita ta qorar masa su,
Allah dai ya nuna mana auren nan
kowa ma ya huta ni har yanzu banji a jikina zaka iya auren wannan mai rawar kan ba."kafin mu'azzam din yabasa amsa
Omar ya qaraso da suitscase dinsu shida Anas,mu'azzam ya bude booth din motar 
ya saka.anas ya zagaya ya shiga front seat 
yayinda Omar ya bude back seat ya xauna
kusan lokaci daya suka rufe qofofin motar.
a hankali mu'azzam yayi addu'ar tafiya
kafin yayiwa motar key......Omar ya fashe da dariya Yana fadin"shegen sama
kamar na allah ,Shima anas daria 
ya fashe daita Yana fadin"wannan gayen 
a fuska xaka gansa tamkar idan aka saka masa hannu a baki bazai ce tak 
ba ,nan kuwa shegen sama ne
dan haka malaak din nan ta mace 
a kansa ,Omar ya cafke xance da fadin"ba dole ta mace akansa ba Yana rage mata zafi.wani qallo ya juya Yana yiwa Omar.
ganin yanayinsa ya canja lokaci daya,
yasa suka kama bakinsu.

wani irin shiru motar ta dauka da suka kama hanyar zuwa kano...

######
tana kwance a tsararren dakinta Wanda kallo daya xakayi masa kaga dakin ya'r gata dan dukiya aka narkawa dakin 
sosai tamkar baa San zafin naira ba,
tun da magrib mood dinta ya canja
babu kalar tambayar da mumynta batayi mata ba a falo tace babu komai kanta ke ciwo,haka kawai ta fadawa mumynta ta dawo dakinta,bata hakura ba ta cigaba da Kiran wayar mu'azzam  har lokacin a Kashe ake fadamata duk ta daga hankalinta,musamman da tasan Sai gobe daurin aure.....tasan mu'azzam zaiyi wuya idan  cikin yammatan amarya 
wasu basu kyasa ba dan Allah yayi masa mugun farin jinin ya'mmata ga kyau 
ga wani irin aji .har wani zafi zafi taji zuciyarta nayi mata,
ko kadan bata son Kiran shegun friends dinsa,dan ba wani shiri take dasu ba,
wani irin tururi taji zuciyarta nayi,
haka zuciyarta ta riqa saqamata zaiyi wuya idan ace basa tareda ya'mmata
tana cikin wannan yanayin akayi knocking kofar bedroom dinta.shiru tayi tana jin zuciyarta na tafasa,haka baisa an daina buga kofar ba a fusace ta sauko daga kan bed din ta nufi kofa.

tana bude kofar dakin .fuskarta akan mai aikinsu dauke da tray a hannunta.
kayan abincine da aka shiryo mata kallo daya tayiwa malaak ta saukar da kanta kasa,cikin rawar jiki take fadin ki gafarceni
hajia karama ,hajiya tasa a kawo maki abinci,tiririn da zuciyar malaak din keyi
yasa tasa hannu ta wani kwabar da abinci
haka tray ya tarwatse a tsakkiyyar marbles,cikin rawar jiki maiaikin ke kallonta a tsawace take fadin ki bar nan yanxu kafin ki rasa aikinki......."!
da wata irin rikicewa mai aikin ta duka
tana kwashe kayan da malak din ta tarwatsa a wurin,komawa tayi dakinta gamida bugo kofar......

#OMRI HAYATII 
#HOT LOVE
#LOVESTORY2026/2027
#ASMY B ALIYU 
#***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol