Free chapter · Read without an account

SCARS BENEATH HER STRENGTH 4

by saddiqa.writes · NURI



Har suka qarasa asibitin babu wanda ya sake magana sai saukar numfashin Inna da ake iya ji kawai. Nuri was out of words, bama haka bama tunanin lokacin bata san wanne za tayi ba. Bata san sun qaraso ba sai da mai napep yayi mata magana "hajiya mun qaraso..." Kallon bakin asibitin tayi ganin yadda mutane ke hada-hadar shiga da fita. Miqar da Inna tayi ta taimaka mata suka fita ta sallami mai napep su kuma suka shiga ciki. Tsayawa tayi tana tunanin ina zasu nufa don ba wannan asibitin ta saba kai Inna ba qaramin asibiti take kaita yau tace su gwada zuwa babban asibiti.

Wata ta samu ta tambya inda zasu iya ganin likita ta nuna mata ward din GOPD amman ta tabbatar mata da zata samu layi sosai. Godiya tayi mata suka nufa can inda ta tarar da layi kamar dai yadda aka fada mata haka suka hau layi bayan sun samu wuri sun zauna. Duk motsin da Inna za tayi idonta yana kai duk da cewa itama tana buqatar wanda zai kula da ita don bata da lafiyar ammn no one.

Sun kusa minti talatin kafin akazo aka fara kiransu ciki kowa yaje ya sai kati sannan aka nuna masa dakin likitan da zaije ya gani lokacin magariba ta kusa. Da suka je can dinma wani layin suka tarar daya saka Nuri jin kamar tayi kuka haka dai suka samu waje suka zauna. Basu dade ba magariba tayi haka duk mazan dake wajen masu lafiya da marasa lafiya suka miqe suka bar wajen har likitan da zasu gani daya fito yanzu shima. Bin wajen da kallo tayi tana tunanin a inda za tayi nata sallar da Inna. Daya daga cikin masu aikin asibitin ta samu ta tambya ta nuna mata wata hanya daga can gefen inda suke tace taj tayi alwala acan akwai tabarma tayi sallah.

Dawowa wajen Inna tayi ta kamata suka nufi wajen ya zaunar da ita ta fara yin alwalar kamin ta dawo kan Inna ta tambyeta ko zata iya. One thing da zama da Nuri ya koyawa Inna shine yin sallah akan Lokaci. Hakan yasa ko yanzu da bata da lafiya tace mata za tayi bata sani ba ko itace sallarta na qarshe. Nuri ce ta kaita ta tayata suka yi alwalar sannan suka dawo suka yi sallar nasu sai dai Inna a zaune ta iya yi. Suna idarwa Nuri bata tsaya addu'a ba tace su tashi su koma sanin an dade da idar da sallah.

Suna zuwa suka tarar likitan ya cigaba da duba mutane. Basu suka samu damar ganin likitan ba sai bayan Isha. Tare suka shiga dakin ganin likitan suka tarar dashi a zaune yana danna laptop dinsa. Sallamar da Nuri tayi yasa ya dago kansa ya amsa yana nuna musu waje "Bismillah"

Inna ta zaunar ita ta samu gefen Innan ta tsaya, katin Inna ya duba kamin ya fara rubuta information dinta acikin desktop dake wajen yana tambyar Nuri cikakken sunanta don ba sai an fada ba kowa yaga Inna yasan itace bata da lafiya. 

"Cikinta ne yake ciwo.." ba tare da ya kallesu ba ya sake tambyarta "tun yaushe ta fara?"

"Ta dade gaskiya.."

"Me yasa ba'a kawota asibiti ba?"

"An kaita Kuma har magani sun bata.."

"Anyi mata wani test?" 

Kai ta girgiza tana cewa "an bata amman ba muyi test din ba.."

Bai tambayi dalilin da yasa ba'a yi test din ba ya koma kan Inna "Baba.." kallonsa tayi da idonta da duk ya sauya. 

"Sannu Baba . Wannan 'yar taki dai bata bata miki rai ko?"

Kai kawai Inna ta gyada masa shi kuma ya sake cewa "wajen ina ne yake miki ciwo acikin naki?"

Qasan ribs dinta ta nuna masa ya girgiza kai kawai kamin ya sake tambyarta "sai Kuma Ina?" Kai ta girgiza masa ba tare data bude baki ba, cigaba da typing a desktop dinsa yayi wanda ya daukeshi wasu mintina kamin ya dawo kan Nuri yana cewa "kuje main lab na tura musu tests din da za'ayi mata so samu idan suna nan yanzu ayi mata akawomin yanzu.." Kai Nuri ta gyada masa kawai tana miqar da Inna suka fita. Da kwatance suka je main Lab din ta basu takardar daya bata a reception suka dan tsaya na wasu mintina kamin aka shigar da bayanan Inna aka fada musu kudin tests din guda uku Allah yaso ba tsada sosai ta samu ta biya da kudin wajenta sannan ta kaita waren da za'ayi mata test din. A waje ta tsaya ta jirata har akayi mata. Fada musu suka yi test din ba zai samu ba a lokacin ba hkan yasa ta kaita wajen ultrasound scan shima dai ba laifi she accord the bill. Shima kamar ydd aka fada mata a main lab haka suka fada mata result din nan da kwana biyu zai fito, haka suka fita suka koma gidan cikin daren nan don it's already pass ten.

Agajiye haka suka koma gidan, basu bi takan kowa ba suka wuce dakinsu bayan sunyi shirin bacci suka kwanta. Nuri sai data kwanta gajiya ta fara nuqurqusarta. Bata dade da kwanciyar ba sai zazzabi ya rufeta wanda bai sauka ba sai asuba. Jiki babu qwari ta miqe ta fita taje ta dauro alwala ta dawo ta tada sallah.......

____________

Da sassafe suka fita don yau ya kama kwana biyun da aka fada musu results din su zai fito. Cikin ikon Allah Kuma Inna jikinta kwana biyu ya danyi sauqi don yau Nuri ko taimaka mata ba tayi ba. Ahanya suka hadu da Usman da zaije wajen aikinsa. Har qasa ya tsugunna ya gaida Inna ta amsa masa da sakin fuska kamar ba Inna ba. Nuri dai kamar ta basar dashi ta nuna bata sanshi ba haka dai ta daure ta bude baki kamar yana mata ciwo ta gaisar dashi. Da far'a sosai kan fuskarsa haka ya amsa mata yana yin gaba duk da yana so yayi wa Nuri magana amman ganin Inna yasa ya haqura. A bakin titi daga nesa dasu ya tsaya ya jira har suka tare mai napep sannan ya qarasa kusa dasu ya bashi kudin. Inna ce mai yin godiya Nuri kam kamar bata ga abinda yayi ba. Kawai bata qaunar taga wani ya taimaka mata a al'amuranta san anyi ba taji dadi ba, an barta da jinya a zuciya..

Da suka je asibitin layi Nuri ta fara kama musu suka bi gashi dukda da safe ne still akwai mutane duk da basu da wani yawa. Qarfe takwas akazo aka rarraba kowa zuwa inda zaije yaga likita sai sannan Nuri ta bar Inna a layin taje ta amso test din da akayi mata wanda ya bata mata lokaci sosai ta dawo ta tarar da Inna a zaune tana jiranta layi har yazo kansu an wuce. Sai da suka sake zaman jira sannan ya zaga yo kansu.

Yau ma kamar ranar tare suka shiga office din likitan sai dai bana ranar bane wani ne daban. Tare suka yi sallama ya amsa musu yana nuna musu wajen zama duk suka zauna.

"Sannu Baba.." Kai Inna ta gyada masa tana amsawa.

"Waye baya da lafiya?" Nuri ta nuna Inna ya mai da kallonsa kanta yana sake tmbyarta abinda ke damunta. Fada masa tayi sannan Nuri ta miqa masa results din test din da aka yiwa Inna. Karba yayi yana dubawa, dagowa yayi ya kalli Inna da sauri kamin ya sake maida kansa qasa yana cigaba da duba results din. Mamqki ne ya kamashi sosai haka dai ya dago ya kalli Inna yana cewa "kin taba bada kodarki ma wani?"

Wani kallo Nuri tayi ma likitan kamin ta mayar kan Inna data yi shiru tana dan ware idanunta cike da wani yanayi unreadable. Kai ta girgiza masa ya sake duba result din qarshe y sake dagowa "ammn anan scanning din da akyi mki ya nuna cewa koda daya gareki instead of two..." Shiru Inna ta sake yi na wasu lokaci har likitan ya maida hankalinsa kan Nuri yana cewa "jikarta ce ke ko?" Kai ta gyada masa kawai ya cigaba da cewa "ta dade bata da lafiya ammn baku xo asibit ba ko?" Nan ma ta sake amsa masa da kai, ya girgiza kai yana yin typing a system dake gabansa kamin ya yagi wata takarda ya danyi rubutu ya miqawa Nuri yana cewa "well tana da ciwon koda, kidney stone to be precise, sannan scanning da aka mata has shown that koda daya ne da ita... Sannan akwai alamar an taba mata surgery na koda...shisa na tambayeta ko ta taba bama wani kodarta... Tace a'a but this is so unusual I don't want to pressure her...well ku je pharmacy na tura musu maganin da zaku siya idan bayan kwanaki ba taji sauqi ba ina tunanin sai dai ayi surgery acire stones din. Allah ya bada sauqi.." da Aameen kawai Nuri ta iya amsawa kanta yana daurewa while Inna da kyar ta iya miqewa tsaye jikinta yana yin sanyi. 

Har suka fita suka je pharmacy aka rubuta musu kudin babu wanda yayi magana. Kudin Nuri ta bi da kallo sanin bata da kudin, juyawa suka yi suka fita daga asibitin. 

Har sannan babu wanda yayi magana acikinsu har zuwa sanda suka qarasa gida. Suna komawa Nuri tayi shirin zuwa aikinta duk da tasan ta makara amman haka ta shirya taje.

Duk cin mutuncin da matar tayi mata ta shanye na ranar kawau saboda kanta da take jin kamar ya kulle mata akan lamarin Inna. A iyaka saninta tasan Inna bata taba bawa wani kodarta ba but then...how comes take da koda daya gashi kuma likita ya tabbatar an taba yi mata surgery. Da Yamma ta koma gida sai dai sabon tashin hankali ta tarar. Ciwon Inna ya tashi har yafi da sosai da sosai.

Arude ta qarasa bakin dakin nasu da taga an taru ana kallon Innar kamar basu taba ganin mara lafiya ba. Nabila ta tarar tare da Inna tana mata sannu ammn ganin Nuri yasa ta miqe ta koma can gefe.

"Inna.." dago kanta tayi ta dora kan cinyarta tana goge mata gumin da take hadawa "Sannu Inna bara mu koma asibitin kawai..." Nabila dake mugun tausayin Innan ce ta fruta "naje na samo muku napep?" Kai Nuri ta gyada mata sanin ita ba irinsu Nusaiba bace. Kiciniyar miqar da ita ta fara Inna ta riqeta tana cewa "kiyi haquri Nuratu ba sai kin kaini asibitin ba... Ki barni na qarasa anan... Nasan banda nauyi babu abinda na zamar miki ..." Sai ta dakata tana maida numfashi "an tabamin aiki an cire min qoda sai dai ba wani na bawa ba siyarwa nayi!!!!"


Anya akwai mai son kudi kamar Inna kuwa?????



To be continued....


like, comment and share

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol