Free chapter 路 Read without an account

2

by Asmy b Aliyu 路 OMRI HAYATII

OMRI HAYATII馃┓

by
Asmy b Aliyu
 
2.....
daren ranar malaak kasa bacci tayi 
har kuma lokacin wayar mu'azzam din a Kashe Sai wurararen qarfe 7 tana kwance ruf da ciki akan bed dinta tayi nisa da tunanin da take wayarta dake hannunta har lokacin ta fara ring.da wani irin yanayi ta kalli wayar tana jin bugun zuciyarta na canjawa,sunan dake yawo akan wayar  ta qurawa ido tamkar mai son gano wani abu cikin sunan da wayar,wani nauyi da kirjinta yayi taji Yana ragewa a hankali murya can ciki 
take fadin mu'azzam!.....
kifar da wayar tayi tana kasa daukar wayar duk da yadda take tsananin jin kewarsa da son jin muryar tasa,har ta katse bata dauka ba ,kira ukku yana yimata ajere.
kalmar plsssssssssss!!!
kawai ya tura mata,kafin ya sake Kiran
daga wayar tayi a Karo na hudu,
tana jin yadda yake jan numfashi Yana saukewa.
beb!"shiru tayi masa dan har lokacin ranta a mugun bace yake ,yasan bazata iya bacci batareda ta ji muryarsa a kunnenta ba meyasa yake azabtar da zuciyarta.
saboda kana da kyau zaka rika azabtar da zuciya ta ,saboda duk maccen da zaka hadu daita duk kamewarta Sai kayi mata ko yayane, meyasa mu'zzaam?wannan qaron tayi maganar muryarta na dan rawa.wani irin abu yakeji Yana taba masa zuciya.ko kadan bayason jin muryarta haka.

malaak mana!........
da sauri ta dakatar dashi.ka rantse da Allah baka kula wata macce ba.
nasan duk yadda kake qame kanka 
ko waya'nnan shegun friends din naka Zasu ingizaka ka kula matan,saboda basa kaunata dakai."Runtse idonsa yayi
Yana jin yadda take fitar da kalamanta axafafe ,am sorry kinji nayi laifi Kaina bisa wuyana."

batayi magaba sai saukar numfashinta da yakeji cikin wayar.bazaki mun magana ba."
nan ma dai shirun tayi masa dan wani irin haushinsa takeji.meyasa zaka Kashe wayarka?"
muna tareda ango malaak na manta nabar wayar a mota ,koda muka dawo a hotel wayar ya riga ya mutu Sai kawai ban kunna ba na saka caji.
Really mu'zzaam???
ta fada da wani yanayi a muryarta,
jin yayi kansa ya fara ciwo duk yadda zai yiwa malaak bayani bazata yadda ba 
Yana daya daga cikin babbar matsalarta rashin yadda dashi ,ga zafin kishi
kusan abunda ke hadasu fada daita kenan.
"ki kwanta kiyi bacci Kaina Yana mun ciwo 
idan na tashi Karfe 10 zan kiraki ,bude baki tayi Xata qara yimasa wani qorafin
malaak please.........a zafafe ta katse Kiran tun kafin ya katse,runtse idonta tayi 
tana jin wani sabon sonsa na huda dukkan jininta.ga wani irin zafi zafi da radadi da zuciyarta keyi lokaci daya,

#######
da ya tashi qarfe 10 na safe kamar yadda yayi alkawari ya kirata wannan qaron korafin komai batayi masa ba suka Sha hirarsu ta masoya ta tambayesa qarfe nawa Zaa daura auren.ya fadamata qarfe biyu ne,allah ya kaimu.na matsu gobe tayi ka dawo."shafa sumar kansa ya shigayi Yana sakin murmushi, murmushin da malaak din ta jisa har cikin zuciyarta,
jin nake tamkar banda lafia bakaji yadda nayi kewarka bane....."nima nayi kewarki."
ya fada sounding so very care a muryarsa,
sunfi awa daya Suna wayar kafin su sauke wayar,ya kira maminsa suka gaisa,
bayan yagama amsa dukkan wani calls,
ya aje wayar duk da yayi wanka kafin yaje sallar asuba,wani zafi yaji Yana ji
Yana gama breakfast ya qara shiga wani wanka,sha biyu daidai sukabar hotel din,
suka nufi inda ango yake.

kasancewar ranar jumu'ane ana saukowa daga massalaci aka daura auren.kuma a Ranar zasuyi diner shiyasa suka zama busy ,tun safe da yayi waya da malaak basu qara magana ba Sai bayan ishaai ana shiryen shiryen wucewa diner,Yana zaune akan bed Yana daura agogon Rolex a hannunsa.wanda ya wani irin zauna a fatar hannunsa,yayiwa wani irin hannun kyau
saboda haske fatansa.a natse yake sauraren malaak din da take masa rigimar yayi zamansa basai yaje dinner party ba.ya fadamata idan baije ba haisam baxaiji dadi ba tayi hakuri zai kula mata da kansa
ya fada mata a natse da wata irin kulawa cikin muryarsa.Yana jin numfashin da take saukewa ta cikin wayar.

haka ta sakasa a gaba yayiwa kansa pics har kalla 3 ya tura mata,Sai da zuciyarta ta tsaya da bugun da take na kusan sakanni 
ganin irin mugun kyan da yayi mata,
tamkar balarabe haka ya fito cikin bakin yadin filtex dake jikinsa,anyi masa wani irin dinki,kusan friends din ango shi suka sanya,Sai dai kowa da kalar dinki da yake raayi.

"Doctor!!!"
ta fada da wani irin karyewa murya tana jin wani irin tashin hankali na mamayarta,
kyan yayi yawa."
murmushi ya sauke Yana dan ware idonsa
tamkar tana gabansa.da gaske din malaak rigima takeji.
jin sautin murmushinsa ta qara cewa 
dan Allah!""""""""
qofar room din yaji ana knocking haka ya samu damar kaucewa rigimar malaak din
owk bye beb sai munyi waya.
ya fada Yana aika mata da wani zazzafan kiss ta cikin wayar da taji tsikar jikinta ta tashi.kafin tace komai ya katse Kiran
Sai kawai ya mayarda wayar a silent 
ya sakata a aljihunsa.
a haka ya nufi kofa cikin nutsassen taku mai daukar hankali Yana bude kofar fuskarsa cikin ta Anas da Shima da kalar shigen mu'azzam din.

"Masha Allah 
"Masha Allah!!!"
Anas ya qara kallon mu'azzam
juyawa mu'azzam yayi ya koma cikin dakin ya dauki kalar turarrukan da yake using ya shiga fesawa Yana jin tsiyarda Anas din keyi masa,Omar ne ya qaraso ya kallesu
kafin ya tsayarda kallonsa akan mu'azzam din,dolema ne wannan malaak din ta mutu akan wannan gayen,ya fada da murmushi a fuskarsa haka Yana kallon cikin fuskar mu'azzam din da yayi kamar bai gane abunda yake fada ba..

#######
dinner party akayi mai cike da wata irin natsuwa da aji kusan ya'yan manyya ne a wurin babu wata hayani,haka aka riqa daukar pics.sai kusan qarfe 1 suka koma hotel din da suka sauka dukansu a gajiye suke dan haka kowa ya nufi nasa dakin,
ido rufe mu'zzaam yayi nufi bathroom wanka yayi Yana jin yadda idonsa sukayi masa wani irin nauyi bacci yakeji sosai,
bai jimaba ya fito daga wanka ya tsane kansa da towel din dake jere cikin hanger,
masu matuqar kyau da tsari,kayan bacci ya saka ajikinsa ya fesa turare ya nufi 
bed Yana duba wayarsa lokaci daya 
ya ware ido Yana kallon wayar,sai yanxu ya tuna a silent ya sakata,
kiran malaak yagani kusan 10 miss call
kwantawa yayi gamida jawo qaramun
pillow ya mannesa cikin kirjinsa,
kafin yayi dialling number malaak din,
tana shiga ta daga kamar jiran Kiran nasa take.sai dai tayi masa shiru ba tareda ta furta kalma ko daya ba. Yana jin yadda take sauke masa numfashi yasan baxatayi magana ba,

"malaak!!!
ya fada sounding so very tired a muryarsa,
kin kira wayar na silent am sorry...........bamu dade da dawo ba gani har nayi Shirin kwanciyya. yanayin muryarsa ma da taji ya tabbatar mata da ya kwanta din haka bacci yakeji.hira ta farayi masa Cike da kulawa da wani irin masifaffar kaunar da take yimasa tamkar karamun yaron dake shan nono.wata hirar ya amsa mata wata yayi mata shiru,saboda mugun kamewarsa da miskilancinsa a hakan ma 
ganin ake ita kawai yake sakewa haka daita yayi hira mai tsayi.sai da taji saukar numfashinsa Wanda yake saukesa cikin wani irin nutsuwa da kwanciyyar hankali,
murmushi ta saki kafin ta furta kalmar 
I love you!!!"ta fada cikin muryar a hankali mai dauke da wani irin aji kafin ta mannawa wayar kiss Sai Kuma ta katse Kiran ,tana jin wani sabon sonsa na qara huda zuciyarta......
a ranar dakyar ya iya tashi sallar asuba saboda gajiyar dake lullube dashi ,bayan yayi sallar anan cikin hotel room din
ya cire jallabiyyar jikinsa,ya Kara bin gado,
duk da a ranar Zasu koma bai tashi ba Sai kusan qarfe 9 Wanda bugun kofar da Ake yimasa ne ya tashe sa.yasan Kuma baya wuce su Anas .addu'ar tashi daga bacci ya Karanta
Sai da yayi minti biyu kafin ya miqe daga kwanciyyar ya nufi kofar cikin nutsassen takunsa,
Yana bude kofar suka hada ido da Omar,
juyawa yayi ya koma batareda ya masa
magana ba cikin dakin Omar ya shiga,
bacci ma kake kasan ko Karfe nawa?"
dan dage kafada yayi Yana nufar hanyar Bathroom,baki Omar ya saki 
Yana binsa da kallo.kaifa dan iska ne."
Yana juyo Omar din ya tura kofar bathroom din,Shima omar fita yayi daga dakin daman zuwa yayi yaga ya tashi
ya shirya.koda ya fito daga wanka waya 
yayi aka kawo masa simple breakfast,
koda Omar ya dawo dakin wannan qaron tareda Anas suke ,cikin shirinsu tsaf da alamar shi kadai suke jira.cigaba da danna wayar hannunsa yayi.kafin Anas yayi magana wayar dake hannun mu'azzam din ta fara ring ganin sunan Mamin sa 
cike da natsuwa ya daga dauke da sallama a bakinsa.bayan Sun gaisa da Mami ta tambayesa ya hidimar bikin?"
ya fadamata Alhmdullahi."

nan ta tambayesa da yaushe Zasu baro kanon ya fadamata zuwa anjima kadan,
addu'a tayi masa akan Allah ya tsare hanya,ya amsa da ameen 
kafin suyi sallama.

#OMRI HAYATII 
#LOVE/ROMANCE
#MALAAK MADAWAKI
#MU'ZZAM MARAFA
#ASMY B ALIYU.
#***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol