Free chapter · Read without an account

The Resignation

by Rabi'ah Shariff · Soyayya Ta

CHAPTER FOUR

THE RESIGNATION

by Rabi Muhammad Shariff 
Ramsha Tales 

Tun daga ranar, rayuwar Hibba a kamfanin Latif ta zama kamar wani sabon yaƙi da take yi a kullum.

Kowace rana, Latif yana ƙara mata nauyin aiki. A duk lokacin da ta gama wani aiki, sai ya sake kawo mata wani wanda ya fi na baya wahala.

Yana ba ta ayyukan da ya san za su iya ɗaukar kwanaki kafin a kammala su, amma yana son ta gama su cikin ɗan lokaci kaɗan.

Duk da haka, Hibba ba ta yanke ƙauna ba.

Ta kasance tana zaune har bayan lokacin tashi, tana aiki ba tare da gajiyawa ba. Wani lokaci har sai dare ya yi kafin ta koma gida.

Ba don tana jin daɗin irin wannan halin ba, sai don tana cikin matsanancin hali sanadiyyar kawunta.

Tana buƙatar kuɗin aikin, kuma ba ta son ta koma hannun mutumin da ya sa rayuwarta ta zama cikin damuwa.

Saboda haka, duk da yadda Latif yake mu'amala da ita, Hibba ta dage da aikinta.

Abin mamaki kuwa shi ne, duk aikin da Latif ya ba ta, tana ƙoƙarin kammala shi a lokacin da ya buƙata.

A wasu lokutan ma, tana yin aikin fiye da yadda ya Latif yayi tunani.

Hakan ya fara ba Latif haushi.

Tun da farko, ya ɗauka cewa zai iya sa Hibba ta gaji da aikin, ta yanke ƙauna, ta bar kamfaninsa da kanta.

Amma duk da ƙalubalen da yake jefa mata, sai ta ci gaba da ƙoƙari.

Abin da ya fi ba shi haushi shi ne yadda Hibba ba ta nuna tsoron sa ko kadan.

Ma'aikatan kamfanin ma sun fara mamakin yadda take gudanar da ayyukanta. Wasu sun fara yabawa ƙwazonta, wasu kuma suna yaba mata a fili saboda yadda take fuskantar matsaloli ba tare da ta karaya ba.

A duk lokacin da ta samu nasara, sai ta ƙara samun kwarin gwiwa.

Amma ga Latif, lamarin ya fara zama kamar raini ne.

Ya saba da ma'aikatan da ba sa kusantar ƙin amincewa da umarninsa. Idan ya ba da umarni, kowa yana yin abin da ya ce ba tare da musu ba.

Amma da Hibba ta zo, sai ya fara ganin kamar komai ya canza.

Yanzu ma'aikata suna bayyana ra'ayoyinsu, suna tattaunawa kan ayyuka, kuma wasu lokutan suna nuna cewa akwai hanyoyin da za a inganta aikin fiye da yadda shu yace.

Hakan yana ƙara ɓata masa rai.

Amma duk da haka, Hibba ba ta damu da abin da yake tunani ba. Ta ci gaba da mai da hankali kan aikinta, tana ƙoƙarin tabbatar da cewa ba za ta bar wata matsala ta hana ta cimma burinta ba.

Sai dai wata rana, wani abu ya faru wanda ya kusan kawo ƙarshen komai.


A wannan rana, Hibba ta shiga ofishin Latif domin kai masa wasu takardu.

Da ta shiga, ta tarar da shi yana nazarin wasu designs a kan system ɗinsa.

Wannan wani babban project ne da yake aiki a kai tare da wasu abokan hulɗarsa daga Amurka.

Aikin yana da muhimmanci sosai a gare shi, domin nasarar wannan kwangila za ta ƙara ɗaukaka sunan kamfaninsa.

Latif yana mai da hankali sosai kan aikin, yana duba kowane bayani da ke cikin designs ɗin.

Da ya ga Hibba ta shigo, sai ya ɗago kai ya kalle ta.

Ya miƙa mata system ɗin, yana nuna mata wasu abubuwan da yake son a gyara.

Hibba ta karɓa cikin gaggawa, domin tana son ta kammala abin da aka ba ta ba tare da ɓata lokaci ba.

Amma a cikin wannan gaggawar, sai aka samu matsala.

System ɗin ya faɗi daga hannunta.

A lokacin faɗuwar, wani abu ya faru da na'urar ajiyar bayanai, wato SD card ɗin da ke ɗauke da muhimman bayanan aikin. Ya faɗi ya karye.

Hibba ta tsaya cak.

Ta kalli system ɗin, sannan ta kalli SD card ɗin da ya lalace.

Nan take tsoro ya kama ta.

Ta san muhimmancin wannan aikin, kuma ta san irin fushin da Latif zai iya yi idan ya ga abin da ya faru.

Latif ya ɗauki system ɗin da sauri, ya fara duba shi domin ya tabbatar da abin da ya lalace.

Bai ce wa Hibba komai ba a farko.

Ya yi ƙoƙarin duba ko yana da wani kwafi na bayanan aikin, amma sai ga shi babu wani copy da ya ajiye.

Wannan ne ya sa fushinsa ya ƙara tashi.

Ya juya ya kalli Hibba cikin tsananin fushi.

"Baki da hankali ne? Me ya sa ba ki yin komai a hankali? Kin san wannan aiki ne da ake san sa da wuri, sati ɗaya ya rage mana a yi finalizing ɗin sa."

Hibba ta sunkuyar da kai.

Hawaye suka fara taruwa a idanunta, amma ta yi ƙoƙarin hana su zubowa.

Ta san kuskure ne ya faru, kuma tana jin zafin abin da ta yi.

Amma kalaman da Latif ya faɗa mata sun ƙara raunana ta.

Ya kalle ta da wani irin kallo na wulakanci.

"I don't know how you will do it, but make sure you make another design before the week, and it should be of standard."

Bayan ya faɗi haka, ya juya ya fice daga ofishin.

Hibba ta tsaya a wurin, ta kasa motsawa na ɗan lokaci.

Ta ji kamar duniya ta tsaya mata.

Ta san yadda irin wannan aikin yake ɗaukar lokaci. Ta san cewa tsara sabon design mai kyau, musamman na irin wannan babban project, ba abu ne da za a yi cikin sauƙi ba.

Amma yanzu, saura sati ɗaya kacal.

Ta zauna a hankali, tana ƙoƙarin tattara tunaninta.

Ta ina zan fara? Ta yaya zan iya kammala wannan aikin cikin sati ɗaya?

Ta share hawayen da suka zubo mata, sannan ta fara tunanin yadda za ta warware matsalar.

Amma abin da ya fi damunta shi ne, Latif bai ba ta wata dama ta bayyana abin da ya faru ba.

Ya riga ya yanke hukunci a kanta.


Bayan Hibba ta fito daga ofishin Latif, sai ta ji muryarsa yana magana da sauran ma'aikatan.

Ta tsaya a wani wuri ba tare da sun lura da ita ba, tana sauraron abin da yake faɗa.

Latif ya bayyana musu cewa babu wanda ya isa ya taimaka wa Hibba wajen yin wannan aikin.

Ya kuma yi barazanar cewa duk wanda ya taimaka mata, zai rasa aikinsa.

Bayan ya gama magana, ya fita daga kamfanin cikin fushi, ya shiga motarsa.

Hibba ta ji komai.

Amma ba ta yi wa kowa magana ba.

Ta tsaya tana tunanin yadda za ta yi, domin yanzu ta fahimci cewa za ta fuskanci wannan ƙalubalen ita kaɗai.

Ta ɗauki jakarta, ta fice daga kamfanin.

A duk tsawon hanyar da ta bi zuwa gida, tunaninta bai bar ta ba.

Tana tunanin aikin, tana tunanin yadda za ta kammala shi, sannan tana tunanin yadda za ta ci gaba da zama a ƙarƙashin irin wannan yanayi.

Amma duk da haka, ta ƙuduri aniyar cewa ba za ta bari wannan matsalar ta karya ta ba.

Idan har za ta iya yin wani abu domin ta gyara kuskuren da ta yi, to za ta yi shi.

Da Hibba ta koma gida, ta zauna ta fara aiki a kan sabon design ɗin.

Ta yi nazari kan abubuwan da take buƙata, ta tsara yadda za ta fara aikin, sannan ta fara aiwatar da shi.

A wannan lokacin ne Aunty ɗinta ta shigo ɗakin, hannunta ɗauke da abinci.

Ta tsaya tana kallon Hibba, wadda take ta aiki ba tare da ta ɗago kai ba.

Aunty ta matso kusa da ita, ta miƙa mata abincin.

"Naga kina ta aiki ko tsayawa ba ki yi kin huta ba, sannan ba ki ci abinci ba. Ki ajiye aikin nan ki ci abinci."

Hibba ta ɗago kai ta kalli Aunty ɗinta, sannan ta kalli aikin da ke gabanta.

"Aunty, aikin nan yana da muhimmanci. Sannan aikin nan zai iya ɗauka ta kusan wata ban kammala ba, idan dai abu mai kyau ake so. Amma Aunty, a sati fa zan gama shi. Gaskiya Aunty, idan na kammala wannan aikin, idan har ya yi, to ni na hakura da wannan aikin. Na san abin da nake samu a wannan kamfanin babba ne, amma Aunty, mutumin nan gaba ɗaya ba shi da kirki."

Aunty ta kalle ta cikin tausayi.

Ta fahimci cewa Hibba tana cikin wani yanayi mai wahala, amma kuma ta san cewa ba za ta iya yanke mata shawara a kan rayuwarta ba.

"Aunty, ki yi haƙuri. Na san kina ta jurar wannan abu saboda mu, amma ba zan hana ki barin aikin ba. Idan kin ga ba za ki iya zama ba, gwara ki hakura. Yanzu ki samu ki ci abincinki."

Bayan ta faɗi haka, ta tashi ta fita daga ɗakin.

Hibba ta kalli abincin da Aunty ta kawo mata, sannan ta kalli aikin da ke gabanta.

Ta san cewa Aunty tana da gaskiya.

Ba ta son ci gaba da zama a wurin da ake wulaƙanta ta, amma kuma ba ta son ta bar aikin ba tare da ta yi ƙoƙarin kammala abin da ta fara ba.

Ta yanke shawarar cewa za ta yi iya ƙoƙarinta a cikin sati ɗaya.

Idan ta kammala aikin kuma ya gamsar da Latif da abokan hulɗarsa, to za ta bar kamfanin.

A wannan lokacin, ta riga ta gaji da halin Latif.

Ba kuɗin da take samu ba ne zai sa ta ci gaba da zama a wurin da ake raina ta.

Amma kafin ta yanke shawara ta ƙarshe, tana son ta tabbatar da cewa ta yi abin da ya dace.


Sati ɗaya ya zama kamar shekara a wurin Hibba.

Kowace rana tana tashi da wuri, tana aiki har dare. Wani lokacin tana mantawa da cin abinci, wani lokacin kuma sai Aunty ta tuna mata cewa jikinta ma yana buƙatar hutu.

Amma Hibba ta ci gaba da ƙoƙari.

Ta yi amfani da iliminta, basirarta da duk abin da ta koya a fannin zane da tsara gine-gine.

Ta duba kowane bayani, ta yi gyare-gyare, ta sake dubawa, sannan ta tabbatar cewa komai ya kasance yadda ya kamata.

A hankali, sabon design ɗin ya fara ɗaukar siffa.

Duk da gajiyar da take ji, ta ƙi yanke ƙauna.

A ƙarshe, bayan kwanaki na wahala, ta kammala aikin.

Ta kalli abin da ta tsara, zuciyarta cike da fargaba da kuma ɗan farin ciki.

Ta yi addu'ar cewa aikin ya gamsar da Latif da abokan hulɗarsa.

Domin a gare ta, wannan ba kawai aikin kamfani ba ne.

Wata dama ce da za ta nuna cewa duk da wahalar da ta sha, ba ta bari hakan ya hana ta yin abin da ya dace ba.

Ranar gabatar da aikin ta zo.

Hibba ta isa kamfanin da wuri, amma jikinta a sanyaye yake. Duk da ta yi iya ƙoƙarinta, har yanzu tana tunanin ko aikin zai yi wa Latif da abokan hulɗarsa kyau.

Ta ɗauki kayan aikinta, ta nufi conference room ɗin da za a gudanar da taron.

Da ta shiga, ta tarar da Latif zaune tare da Alisa da wasu mutane biyu daga Amurka.

Dukansu suna jiran a gabatar musu da aikin.

Hibba ta shiga cikin nutsuwa, ta haɗa system ɗinta, sannan ta fara gabatar da sabon design ɗin.

Ta bayyana yadda ta tsara aikin, dalilin zaɓin wasu hanyoyin zane, da kuma yadda kowane ɓangare zai taimaka wajen cimma burin aikin.

Yayin da take magana, mutanen Amurkan suna kallon aikin cikin kulawa.

A hankali, fargabar da take ji ta fara raguwa, domin ta lura cewa suna mai da hankali sosai kan bayanan da take bayarwa.

Da ta gama gabatar da aikin, ɗaya daga cikinsu ya yi magana yana yabawa ingancin abin da ta tsara.

Sauran ma suka amince da ra'ayinsa.

Aikin ya yi musu kyau sosai.

Har Latif da kansa, duk da ƙoƙarinsa na ɓoye abin da yake ji, ya fahimci cewa Hibba ta yi aiki mai kyau.

Amma saboda girman kansa, bai nuna farin cikinsa a fuskarsa ba.

Ya zauna da fuska a murɗe, kamar babu wani abu da ya burge shi.

Mutanen Amurkan sun tashi, suka taya Hibba murna saboda ƙwarewar da ta nuna.

Alisa ma ta kasa ɓoye farin cikinta.

Ta matso ta rungume Hibba.

"Masha Allah, Hibba! Taya kika yi wannan aikin cikin ƙanƙanin lokaci har ya ma fi wanda muka yi a da, wanda ya ɗauke mu lokaci mai tsayi? Gaskiya na yaba miki."

Hibba ta yi murmushi cikin jin daɗi.

Bayan haka, mutanen Amurkan suka sanya hannu a takardar yarjejeniya, suka tabbatar da amincewarsu da aikin.

Latif ya miƙe tsaye, ya yi musabaha da su, sannan suka yi ɗan murmushi kafin su fice daga ɗakin.

Alisa da Hibba ma suka fito.

A waje kuwa, sauran ma'aikata sun fara taya Hibba murna saboda nasarar da ta samu.

Wasu suna yabawa ƙoƙarinta, wasu kuma suna mamakin yadda ta iya kammala irin wannan aiki cikin ɗan lokaci.

Hibba tana tsaye tana karɓar taya murna, sai ga Latif ya iso cikin kasaita.

Da ya tsaya a gabanta, Hibba ta ɗauki wata takarda ta miƙa masa.

Ya karɓa, ya kalle ta cikin mamaki.

"Wannan na mene?"

Hibba ta kalle shi, ta ce:

"Na san ai ka iya karatu, to ka karanta."

Ta faɗi hakan cikin nutsuwa, amma fuskarta tana nuna cewa ta yanke shawara.

Latif ya buɗe takardar.

Takardar murabus ce.

Ya ɗago kai ya kalle ta, amma kafin ya ce wani abu, Hibba ta fara magana.

"Lokacin da ka buge Aunty na saboda ka fi ba wa aikinka muhimmanci, a lokacin sai ka nuna rayuwarta ba ta da wani muhimmanci. Lokacin da na zo neman aiki a wannan kamfanin, da na ga kamfanin naka ne, ban yi tunanin za ka ba ni aiki ba. Sannan ni ma ba na jin zan iya maka aiki, amma saboda a lokacin ina cikin buƙatar aikin, shi ya sa da ka ba ni na amsa, duk da ina ta tunanin me ya sa ka ba ni aikin.

Hmm," ta faɗa cikin takaici.

"Ashe ka ba ni aikin ne saboda kawai ka wahalar da ni!"

Hibba ta ɗan tsaya, ta kalli Latif cikin ido.

"Na yi matuƙar mamaki yadda na ga ka damu saboda kawai an rasa wannan project ɗin. To, ya kake tunanin ni zan ji da ka buge Aunty na sannan na gan ta a kwance? Na tsaya na maka wannan aikin ne saboda kuskure na ne ya sa ka rasa naka."

Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ci gaba da cewa:

"Ba zan iya ci gaba da aiki a wannan kamfanin ba, shi ya sa na yi resigning. Don haka na gama aikina."

Bayan ta faɗi haka, ta ɗauki jakarta ta fice daga wurin cikin fushi.

Ma'aikatan da ke wurin sun tsaya suna kallon juna cikin mamaki.

Ba wanda ya yi tsammanin Hibba za ta yi ƙarfin halin magana da Latif a haka, balle ta miƙa masa takardar murabus a gaban sauran ma'aikata.

Amma abin da ya fi ba Latif mamaki shi ne yadda ta yi masa magana ba tare da ta nuna tsoro ba.

Ya tsaya yana kallon hanyar da ta bi, fuskarsa cike da fushi.

A duk rayuwarsa, bai taɓa tunanin cewa wata ma'aikaciya za ta iya barin kamfaninsa da kanta ba, musamman bayan ya ɗauke ta aiki kuma ya ba ta damar yin aiki a ƙarƙashinsa.

Shi Latif Abdurrahman, wanda mutane suke tsoron fushinsa, wanda ma'aikata suke ƙoƙarin faranta wa rai, yau wata yarinya ta miƙa masa takardar murabus a gaban kowa.

Ba wai shi ya kore ta ba.

Ita ce ta zaɓi barinsa.

Wannan tunanin ya ƙara kunna masa wuta a zuciya.

Ya naɗe takardar da ke hannunsa, ya haɗe rai sosai.

Hibba!

A karon farko, Latif ya fahimci cewa yarinyar da yake ganin zai iya sarrafa ta yadda yake so, ba ta kasance irin mutanen da ya saba mu'amala da su ba.

Amma abin da bai sani ba shi ne, barin kamfanin da ta yi ba zai zama ƙarshen al'amuransu ba.

Domin kuwa, a wani wuri a cikin zuciyarsa, Hibba ta riga ta bar wani abu da ba zai iya mantawa da shi cikin sauƙi ba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol