Free chapter · Read without an account
Page 2
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 2
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Sai da yakai bakin kofar palourn sannan ya juyo ya Abie yace "baxan taka dokar kaba Angon Mami," daga haka yasa kai ya fita.
Da sauri Abie ya mike har yana kokarin kifewa yabi bayansa sanin dayai masa tunda har ya shirya zai fita sai ya fitan kuma ba ta gate zai bi ba, bin bayansa Junaid yai shima da sauri yana girgiza kansa, a ran sa yana nema wa biyun nawa shiriya wajen Allah.
Shi kuwa Azlan yana fita daga palourn bayan gidan yaje ya dakko ladder ta karfe cikin zafin nama, ya rike ta da hannu daya kamar ba abin nauyi ya dakko ba, ware ta yai ya saita a jikin bangon gidan yadda zai mai daidai, su dai masu gadi suna zaune sai satar Kallonsa suke ba halin su bari ya gane suna Kallonsa.
Cikin sassarfa ya shiga takawa hana hawa sai da ya Kai karshen sa yadda zai dira daga gidan sannan ya juyo ya kalli Abie da Junaid, shafa gemun sa yai kafin ya saki wani murmushin gefen baki daya bayyana dimple dinsa guda daya na bangaren dama, hannu ya daga musu alamar bye sannan ya juya ya dira daga gidan.
Da sauri Abie ya dafa kirjin sa tare da rintse ido yana addu'ar Allah yasa bai ji ciwo ba, maganar da Azlan yai da karfi ne yasa Abie sauke ajiyar zuciya.
Shi kuwa yana dira mikewa yai ya karkade jikin sa sannan ya kalli dogon ginin daya diro, shafa gemun sa yai yana lasar lips dinsa wayar sa ya zaro a aljihun sa, wata number yai dialing bata dade tana ringing ba aka dauka.
A kausashe yace “zo mu hade ina kofar gida” daga haka ya kashe wayar, bai dade sosai a wajen ba wata lafiyayyar mota ta shigo layin, a daidai kusa da shi ta tsaya bai wani tsaya jiran komai ba ya bude gurin mai zaman banxa ya shiga suka figi motar a guje suka bar layin.
Abie kuwa girgiza kai yai kawai suka koma palourn, Mami ce ta kalle sa fuskar ta cike da damuwa tace "ya fita koh Abie?”
Zama Abie yai yana ajiyar zuciya yace "don na ce masa baxai fita ta gate ba shine ya haura katanga ya dira"
Lumshe idon ta Mami kawai tai tana binsa da addu'a duk da ya kasance mara Jin magana amma shidin mafi soyuwa a gare tane baya Wasa da duk abinda ya shafe ta kuma baya mata karya.
Mama kuwa ajiyar zuciya ta sauke cikin Jin dadi sbd dama ita duk ranar da yazo suka zauna da shi takura mata yake, ta rasa mai yasa yaron ya raina ta tunda take dashi bai taba ce mata Mama ba sai dai Hajia da Yaya ma yake ce Mata saida Abie da Mami suka dinga masa fada sannan ya fara ce Mata Hajia.
Haka suka ci abincin bayan sun gama aka shiga hira, sai wajen 10 sannan Junaid ya mike kallon Abie yai yace "Abie bara na tafi zan biya na dauki Samira a gidan su"
Murmushi Abie yai cikin kauna yace "Allah ya tsare ya cigaba da kare mana ku Allah ya warware muku dukkan matsalolin ku"
Fuskar sa cike da murmushi yace"Ameen"
Kallon Mami yai cikin nutsuwa yace "Mami sakon samiran tace min kin ce zaki bada sako in taho mata da shi"
Mike wa Mami tai cike da tausayin yaron nata ta ce "muje na baka dama dambun naman da nai ne nasan tana so sosai shine na zuba mata"
Tabe baki Mama tai tana yatsina fuska itama ta kusa aurar da Yusuf dinta tayi sirikar dai, duk abi a wani damu mutane.
Bayan sun shiga part din Mamin Mika masa leda mai dan girma tai wacce take dauke da dambun naman a cikin, sai da ta kara masa nasiha sosai akan yadda da KADDARA sannan ya tafi.
Binsa tai da kallo cike da tausaya wa shekarar sa biyar da aure amma har ynxu matar sa ko bari batayi ba, duk inda suka je kuma matsalar daga gare sa ne amma matar tasa lafiyar ta Lau, da farko da aka gane matsalar daga gurin sane yaso rabuwa da samiran amma ta dage ita akan ta yadda da KADDARA zata zauna da shi ko da baxa ta taba haihuwa ba har karshen rayuwar su..
***********
Kallon cilla nai dake zugar sigarin sa cikin kwanciyar hankali, tsaki nai cikin fada fada nace "wallahi cilla in baxa ka rage shan sigarin nan ba zamu raba hanya haba, ayi mutum bashi da aiki kullum sai banka wa kan sa hayaki, kai ko tausayin lungs dinka baka yi koh?"
Yar da sigarin yai a kasa ya murje ta sannan ya kalle ni yana murmushi cikin muryar sa da kana ji kasan an taba daba a da yace "afuwan aminiyas xan kiyaye Insha Allah tun safe ban sha ba fa, ai aha ka ma ina kokari, eh wallahi”
Tsaki na kuma ja kafin nace "cilla so nake ka targada min Manniru dan gidan kawu nasir, yaron nan dan baya jin magana shine zai zagi Mimi"
Ashar ya saki yana jan kafar sa baya kafin yace "kika ce zagin shalele yai wallahi sai na karya sa don uwataii"
Gyada kai nai cikin takaici nace "ba sai ka karya saba kawai kasa amasa shegen duka yadda gobe ko wani ya gani zai zagi Mimi sai ya kwabe sa"
Murza kafa a kasa Cilla yai yace "cau cau, an gama aminiya ta kuma abokiyar shawara ta muje in taka miki ki karasa gida sbd yan jagaliya"
Jera wa mukai muna tafiya yana ban labarin yadda zai casa Manniru har muka karasa kofar gidan mu, sallama nai masa na shiga gidan, ba kowa a tsakar gidan hakan yasa na nufi palour don nasan suna zaune ynxu tunda an kawo wuta.
Da sallama na shiga palourn duk suka amsa min, Zama nai a gefen kafar baba ina cire hijab din jikina.
Kallona Umma tai tace "kin biya gurin cilla neh koh don nasan yadda kika dade din nan sai dai in kun hadu dashi"
Sosa keya ta nai nace "Umma a kofar gida muka hadu fa shine kawai muka gaisa"
Girgiza kai Umma tai tace "ni na rasa me yasa kike Kula wannan yaron wallahi sam baya ji, na miki fadan amma a banza. Sbd Allah Batul meye hadin ki da dan daba"
Abba ne ya ce "A'a Umman Aysha ki bisa da addu'a kawai shima dane Allah ya shirye sa da dukkan zuri'ar musulmai baki daya"
"Ameen" muka hada baki gaba daya muka ce, mike wa nai ina fadin "sai da safe Baba gobe da school kuma ina son na fara shiga school din su Mimi"
Khalil ne yace "Ya Batul zan raka ki in zaki kaita"
Hararar sa nayi sannan na juya na nufi dakin mu nida Aysha, akan katifar mu 6 by 6 na samu Mimi tana sanye da rigar baccin ta kanta sanye da hula, murmushi nai na karasa gurin wardrobe dinmu, kayan bacci na dauko masu nauyi saboda yanayin garin nasa sannan na hau kan katifar addu'a na fara ma Mimi kafin nima nayi, janyo ta jikina nai na rungume ta hawaye masu dumi suna zubo min a gefen fuska tatabbas a duniya Mimi ce rauni na ita nake kallo nake tuna *TASWIRAR KADDARAR* data same mu shekaru 5 baya, wata Kaddara mai matukar munin data tafi da kaso mai yawa na farin cikin ahalin mu.
Lumshe idona nai ina ina tuna abubuwan da suka faru shekarun baya lokacin ina da shekara 14 gashi ynxu ina 18 amma abun kamar ynxu ya faru......
**********
Kallon Haidar Azlan yai yana tabe jajayen lips dinsa yace "in baxa ka kaini club dinba sauke ni in karasa ai ina da kafa"
Girgiza kai Haidar yai yace "Azlan kayi ma kanka fada wallahi Kai ynxu ya dace ma ace kullum kana hanyar zuwa club gurin Yan mata, kwata kwata hakan ba tarbiyyar da addinin mu ya mana bane”
Shafa gemun sa yai yadan lashi jajayen lips dinsa wanda hakan ya zamar masa al’ada kafin yace “ina ruwan Ka Mata ai abin nishadi neh kuma don naje ai ba budurcina zan basu ba, kai fa kafi kowa sanin yadda nake taka tsantsan da wannan budurcin nawa”
Tsaki Haidar yaja mai karfi yace “budurcin yaci uban sa”
Da sauri Azlan ya ce “zan ci ubanka wallahi, samartakar tawa kake zagi?”
DijahAM(Oum Amani)
***