Free chapter · Read without an account
Page 7
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 7
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Da sauri Samira ta dago ta kalle sa cikin damuwa ta rarrafo ta iso gaban Mami itama, hannun ta ta dora akan na Junaid tace "baxan taba barin kaba Hub duk halin daka shiga ni ma shi na shiga ina kaunar ka a haka ina sonka kuma zan zauna da kai a ko wanne hali. Samun miji irin ka kadai ya ishe ni fid dunya"
Murmushi Mami tai tana kokarin mayar da hawayen ta cikin dakewa tace "ku kwantar da hankalin ku yarana Insha Allah za'a dace ma Junaid komai zai zo ya wuce, Allah ya baku ikon cinye wannan jarabawar, mu cigaba da addua don ba abinda yafi karfin Allah”
Shidai Azlan yana zaune ya zuba tagumi yana kallon su shidai har ga Allah baiga wani abun damuwa ba dududu auren Junaidu shekara biyar ne amma ya tayar da hankalin sa sbd ance baya haihuwa ai ya bari ya shekara 20 haka sai ya fara damuwa, Shi Sam yara basa gabansa ma saboda damun sa suke shi kuma baya son hayaniya.
Kallon sa Junaid yai yace "Azlan baka ce komai ba Ka zuba mana ido kawai"
Kankance idonsa yai yace "Junaidu mai zance ma toh addu'a kawai zan taya ka Allah ya kara lafia amma in kana bukatar maganin karfi ne kafada min zan nemo ma"
Da mamaki Junaid yake kallon sa Samira kuwa sunkuyar da kanta kasa tai tana mamakin rashin kunyar Azlan hatta Mami sai da taji kunya ta lullube ta.
A kufule Junaid yace "banson iskanci meye haka wai"
Jingina bayansa yai a jikin kujera yana rungume hannun sa a kirji yace "misali in so daya kake yi kaga sai Ka Kara kaimi kana yi kamar so uku haka koh?shine kawai, kaga in yi dayan ba'a dace ba kasani ko ana biyun a dace don't feel shy Ka fada min zan nemo ma"
Sakin baki Junaid yai ga takaici ga kunya data rufe sa, fahimtar hakan yasa Mami itama ajiye kunyar ta agefe tace "tashi ku tafi Junaid sai da safe Allah yai muku albarka"
A hankali suka amsa suka mike suka fita, da kallo Azlan ya raka su sai dai bai ce komai ba, maida dubansa ga Mami yai yaga ta zuba masa ido hakan yasa shi sosa keya ya saki wani munafikin murmushi yace "Mami ya kinsani Jin kunya, kuma kar ki kawo tunanin komai a ranki nima kawai nasan ana yi fiye da daya ne amma budurcina lau yake"
Girgiza kai Mami tai tace "Allah ya shirya min kai Azlan ya nuna min ranar da zaka yi aure Ka daina kiran wannan budurci"
Dan tsai yai da idonsa yana kallon ta sai kuma ya tsuke bakinsa yace *"MAA* ynxu in nayi aure shiknn kowa ya daina min kallon mai budurci kenan"
Mikewa Mami tai tana cewa "bara na tafi Azlan baza ka samin hawan jini ba, kuma kar ka manta da akwai taron Family karshen watan nan nasan halin Ka zaka iya kin zuwa"
Shidai rakata yai da ido kawai har ta shige dakin ta sai kuma ya mike ya nufi part dinsa, yana isa ya zauna akan lafiyayyan gadonsa, shifa su Abie sun kasa gane sane baya son mace tazo ta ce tana sonsa yana son mace Mai aji matuka, yana fatan ya ga ranar da wata mace zatai masa duba ba irin na soba, yana son ya kasance ko sonsa zai kashe mace ta ja ajinta taki fada masa har sai in shine ya fada mata cewa Yana sonta, Amma Allah na tuba Mai zaiyi da wata Zainab shekarar ta 24 amma kallon kwaila yake mata saboda duk ciko take.
Shi babbar samuwar Sama ynxu wannan family meeting din da za ayi sam baya sonsa sbd wasu dalilai nashi, karamin tsaki yai gashi tunda Mami tace yaje baxai iya musu ba zuwa ya zamar masa dole, kwanciya yai yana lumshe idonsa cikin wani yanayi da yakan shiga.......
********
Dawowa ta kenan daga tahfiz a gajiye nake sosai duk jikina ciwo yake min ma, Zama nai a kasan carpet din palourn mu ina mike kafafuna, cikin gajiya na kalli Umma da take duba littafin Seera turo baki nai gaba cikin shagwaba nace "Umma kina kallo na shigo fah"
Banza tamin sai da ta dau mintuna sannan ta kalle ni tace "toh da kika shigo mai zan miki ne ehe, in zaki Saba ma gwanda ki saba jami'a zaki shiga tohm"
Nidai ban kuma magana ba mikewa nai na shiga kitchen Dan wake na dora mana, ina cikin yi Mimi dasu Kamal suka shigo Suma saida na gama Dan waken na zuba mana a babban plate muka hadu gaba dayan mu muka ci har Umma, bayan mun gama su kamal ne sukayi wanke wanke ni kuma nai wa Mimi wanka, cikin rigunan dana dinka mata na dauki daya nasa mata sai murna take an sa Mata sabon kaya.
Kallona tai tace "Maa unguwa zamu je kin samin sabon kayan da kika dinka min"
Dariya nai ina taje mata dogon gashin ta nace "a'a babban gida zamu gurin yakumbo kinga mun dade bamu je ba ko Babyna"
Daga Kai tai tana murmushin dake kara wa fuskar ta kyau sosai, hula na samata na rufe Mata gashin ta ruf, kallon ta nai bayan na dafa kanta nai mata addu'a nace "Maza jeki gurin Umma ko su Ya Khalil kuyi hira bari nima nayi wanka koh"
Da gudu ta fita na bita da kallo ina murmushi, kayana na cire na sa zanin wanka na na fita don wanka, ban dade ba na shigo dakin mu shiryawa nai cikin riga da skirt simple style ne amma sun kamani, a hankali na taka har gaban Mirrow dinmu na tsaya ina karewa kaina kallo.
Bana cikin jerin masu kiba kuma niba sirirya bace Allah yamin halitta Mai daukan hankali sosai, ina da cikar Kirji sosai haka kuma ina da diri ga hips sai yanayin jikin nawa yasa ake min kallon mai kiba, ina da wani irin jiki ta yadda duk taku daya in nayi gaba daya jikina sai ya girgiza duk abinda zansa kuwa. Saboda yanayin jikin nawa nake sa bra ta kamani kuma nake sa tight a cikin dukkan kayan da zansa amma a banxa shiyasa duk inda zani nake zumbula hijab har kasa duk da shima hijab din ba wai yana hana jikin nawa rawa bane amma yana taimakawa gun rufe min kayan arzikina..
Powder na shafa nasa kwalli da lip gloss, hijab dina dake kan katifar mu na janyo nasa ya fesa turare na mai sanyi oud, Dan kallon kaina nai a mirror naga yadda nayi wani sassanyan kyau murmushi nai na fito hannuna rike da wayata.
Sallama mukai wa Umma bayan na daukar wa Yakumbo zobo, a kofar gidan babban gida mukai kicibus da Shamsiyya yar gidan Kawu Nasiru, kusan sa'a tace sai dai ta girme ni da watanni, kallon kallon mukai kafin na ja gefe don bata hanya ta wuce ina kuma binta da kallo ganin yadda ta tsuke cikin riga da skirt sai wani yalolon mayafi data yafa a kanta, kauda kaina gefe nai ina jiran ta wuce.
Ita kuwa Shamsiyya zuba mata ido tai tana kallon ta cikin bakin ciki ita tana hassada da komai na Batul saboda ta fita komai tafita kyau iya magana sura mai kyau, tsaki taja ta sauke kallon ta akan Mimi cikin tsanar yarinyar tace "ke baki iya gaisuwa bane kina ganin manya"
Turo baki Mimi tai kafin ta waina manyan idonta tace "kema ai bakya gaishe da Umma kullum kullum ina kallon ki"
Zare Mata ido tai tace "ke ni sa'ar kice zaki dinga fada min haka banxa sheg........
Da sauri cikin tsawa nace "kul, na rantse da wanda rai na yake hannun sa in kika karasa sai na fitar Miki da hakori wallahi wallahi"
Ganin yadda nai mata magana ina zare Mata idanuna masu sheki da suka fara rinewa sbd bacin rai yasa ta Jan tsaki ta yi gaba tace "banxa banda lokacin ku ai"
Tsaki naja nima nace "da kin sani kin tsaya ai banxa karamar yar iska daidai nake da ko wacce banza"
Tafin Mimi ne ya sani kallon ta sai gani nai tana tsalle tana tafi, sakin baki nai ina kallon ta nace "ke meye haka"
Washe hakoran ta tai tace "Maa dita hero ce taji tsoron ki ta gudu ai da ta tsaya Maa ki goge Mata bakinta da bango"
Rike baki nai ina gyara tsayuwa ta nace "ban hanaki shiga maganan manya ba uhm"
Hannu tasa ta rike lips dinta tace "na daina Maa dita baxan kuma ba ynxu ma murna ce ta min yawa" ta karashe tana washe kyawawan hakoran ta
Cikin gidan muka shiga ina mamakin yadda Mimi take da matukar wayo kamar ba yar shekara hudu ba ga shegen suruta a cikin ta kamar zata siyar da mutum.
Ban shiga kowanne sassa ba sassan Yakumbo kawai muka nufa, a tsugunne ta same ta tana alwala cikin tsokana nace "ke kuwa wannan tsohuwa sai ynxu kike shirin sallah"
Harara ta galla min tace "ina ruwanki yar sa ido ai ni dake munyi baram baram ja'ira"
Dariya na kwalkwale da ita na zauna akan kujera yar tsugunno Mimi kuma ta zauna akan tabarma tana wasa da zaren tabarmar, muna zaune har yakumbo ta idar da sallah anan muka shiga hira da ita.
Kallon ta nai nace "tsohuwa Mai ran karfe na kusa shiga jami'a fah"
Salati Yakumbo tasa ta ce "kar kice min makarantar gaba da sakandare"
Juya idona nai na ce "hakkun itafa insha Allahu gobe ma zamuje muyi jarrabawa a jami'ar in na haye shikenan na zama yar jami'a"
Tagumi Yakumbo tai kafin ta kalli Mimi ta juyo ta kalle ni tace "ke da nake fatan zakiyi aure abinki ki huta shine zaki wani cigaba da karatu"
Dan hade rai nai nace ni "Yakumbo tunda muke dake kin taba ganin nayi saurayi, nifa baxan yi aure bama gaba daya don bana son Mimi tayi agolanci"
Kallona Yakumba tai tace "ynxu in auren zakiyi da Mimi zaki tafi gidan mijin ai in aure zaki yi ma anan zaki barta"
Hade rai nai sosai na shiga masifa ni ba inda zan bar yata ni auren ma gaba daya baxan ba, itadai yakumbo kyale ni tai kawai tana kallona don tasan ta gama bata min rai daga karshe ma mikewa nai nace mata kuma sai na yi watanni bata ganni ba.
Washe gari muka je mukayi post utme fatan nasara kawai ranar saboda murna na shiga university Naga yadda take har da sadakar zobo nayi wa almajiran layin mu, itadai Umma da Abba dariya kawai suke min.
*******
A hankali muke tafiya nida Cilla ina sanye da dogon hijab har kasa maroon colour ya min kyau sosai duk da ba komai a fuskata, cikin farin cikin da yakasa boyuwa a fuskata nace "Cilla Alhamdulillah mun samu Admission fah"
Shima murmushin yake yace "bari uwar dakina ban taba Jin ina son karatun nan sosai ba sai ynxu"
Murmushi kawai nai ina kallon takardun hannuna da muka je cafe mukai photo copy dinsu don gobe zamu je school mu karbi Admission letter dinmu, muna tafiya muna hira munzo dai dai tsallaka titi knn wata azababbiyar mota tazo a guje saura kiris ta buge min kafa, wani malulun haushi ne yazo ya tokare ni da sauri na sunkuya na dauki dutsen da na kusa bige kafata da shi na wulla wa motar.
Cilla ne ya kalle ni yace "uwar dakina ya zaki wulla musu dutse kin ga motar daga gani wallahi ta masu hannu da shuni ce data fasa musu glass din ya zamuyi"
Cikin masifa na dago xan masa magana saidai maganar tawa ta makale sbd motar data shiga dawowa a hankali, gyara tsayuwa ta nai sosai ina jiran koma waye ya fito ayi ta don ba tsoron sa nake ji ba.
A hankali mai motar ya fito Wanda fitowar sa tai daidai da wani irin bugawa da zuciya ta dake cikin kirjina yai har sai da nai baya zan fadi da sauri cilla da bai taba rike min koda Dan yatsa ba yai hanzarin riko min kafaduna yana gyara min tsayuwa ta, Shi kansa jikin sa rawa ya fara yana kallon Wanda ya fito ya zuba musu lumsassun idonsa yana musu wani kallo...........
Ina Jin dadin comment dinku fans Allah yabar kauna🥰🤝
***
***