Free chapter · Read without an account

Page 9

by khadijah danasabe · TASWIRAR KADDARA



*TASWIRAR KADDARA*




  DijahAM(Oum Amani)





Page 9







BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






  Dan yatsina fuska nai nace "Umma wani ne ya kusa markade min kafafuna fah, kuma wai sbd mugunta ni ban masa rashin kunya ba amma ya nemi ya zage ni"




Kura min ido Umma tai cikin rashin yadda da abinda na fada mata tace "anya Batul, ke dama ana ka da ke a magana ne? Me kika ce masa don nasan halin ki"




Turo baki nai nace "Umma kawai fa daga nace masa ya kula sabods gaba in ni ya kusa kade ni banyi magana ba wasu in ya musu sai sun zage sa shikenan ya fara zagina"




Girgiza kai Umma tai tace "da ban sanki badai Batul amma na tabbata kin masa rashin kunya ne ko kuma kin fada masa maganar da bata yi masa dadi ba wallahi ina hanaki wannan tsiwar taki amma bakya ji"




Langwabe kai nai nace "ynxu Umma da an kawo miki ni ranga ranga fah ya take min kafa fah"




Tsaki Umma tai tana juyawa cikin kufula tace "Allah ya nuna min ranar da zakiyi hankali"




Sakin baki nai ina kallon Umma, sai kuma na mike na fita kitchen don dora abincin dare.








**********




Junaid ne ya mike da sauri yazo ya janyo Azlan yace "baka da hankali Azlan me kake shirin yi taya zaka cire wandon ka?"




Kasa kasa da murya Azlan yai ta yadda Junaid ne kadai zai jisa yace "kai mai Ka maida ni ne, ina da hankali fah taya zan cire wando na barazana ce kawai, ai ko aure nai kafin na cire wandon nan sai an hada da nasiha"




Ajiyar zuciya Junaid yai don shifa lamarin Azlan tsoro yake basa mutum kamar aljani don da ya fara tunanin ma ko aljanu ne da Azlan din sai daga baya ya fahimci cewa kawai tsabar tsageran cine.




Dan daure fuska Azlan yai yace "Ka barni Junaidu na cire mata wandon na nuna mata budurcina da nake tana dawa iyalina" ya karashe yana kamo hantsar wandon sa yana wani zunkuda kafada.




Abie ne ya mike yace "in baka daina wannan shirmen ba sai na Saba ma wallahi mara kunyar banza da wofi"




Murmushi ya saki yana maida zip dinsa, juyawa yai ya kalli Baffa yace "tsoho zan iya fece wa duk baka ji yadda nake ji a zuciya ta ba kasan ba abin da ke saurin bata min rai kamar a ce ana shakkar budurcin dana ke ta tashi fadi wajen ajiye wa iyali na"




Baffa da tunda yai magana sau daya ya zubawa sarautar ALLAH ido yana mamakin shakiyancin jikan nashi ya daga masa kai kawai yana binsa da addu'ar shiriya.




Cikin takunsa ya karaso kusa da Mami ya tsugunna yai mata kiss a kumatu yace "sai anjima MAA" daga haka ya juya ya fice daga palourn.




Mummy ce ta kalli Baffa cikin rawar murya tace "ynxu baffa kana kallon yaron nan abinda yai min amma baza ka masa fada ba"




Murmushi baffa yai yace "Hafsatu kenan ai dama koda kika zo da maganar wannan hadin a take a gurin nace Miki ba lallai ne wannan abun ya yiwu ba, sbd sanin halin sa danai amma kika dage akan a tuntunbe sa aji gashi ynxu ai ya fada bashi da ra'ayi kuma gaskia ni bazan masa dole ba tunda ya fadi dalilin sa"




Abie ne yace "Amma Baffa ai mune muke gaba dashi kuma duk abinsa haihuwar sa akai shekarar sa 33 amma har ynxu yaki hankali ni a yadda nake ganin take taken Sama ba aure sam a gaban sa"




Dan hade rai Baffa yai ya kalli Uncle M da yai shiru yana kallon su yace "Mustapha rufe mana taron da addua"






*********




Washe gari muka je muka karbi Admission dinmu inda zan karanta architecture shi kuma cilla zai karanta library science, sosai muke murna don mun fara jin kamshin Zama cikakkun yan University.




Da daddare muna zaune ina bawa Abba labarin yadda Makaranta take Mimi na kwance akan cinyata tana bacci.




Murmushi nai na ce “Abba nan da wata daya fah zamu fara zuwa koh, wallahi na matsu sosai”




Murmushi Abba yai ya ce “Allah yasa ku fara a sa'a Batul, ki maida hankali sosai ba ruwanki da biye wa kawayen banza, dama nasan Alhamdulillah ke ba mai biye biye bace, amma ina Kara tuna Miki bake ba lecturers tsakanin ki dasu karatu. Ban yadda ki dinga zuwa office din lecturer ba ke kadai ko kiranki yai kuje keda wasu ki kama mutuncin ki Batul, kuma kiji tsoron Allah a duk inda kike, sannan ki maida hankali akan karatu don Allah duk da baki da Wasa amma still ina kara tuna Miki wannan karatun ba irin Wanda kika saba bane sai kin dage sosai Allah ya bada sa'a.




Kaina a kasa na amsa da "Ameen" sai kuma naji jikina yai sanyi. Kallon Umma Abba yai yace "Umma baki ce komai ba"




Dan murmushi Umma tai tace "ai Ka gama fadin komai Abba sai dai kawai Nima nace ki kula sosai ki rike mutumcin ki Banda kawayen banxa sannan ki dage da karatu, jami'a ba wajen wasa bane. Allah ya baki sa’a yasa ki fara karatun cikin nasara ya kuma kare ki daga dukkan sharri.”


“Ameen” duk muka fada.


Daga Kai nai na kalli Abba nace "Abba ni kun fara tsorata ni in kuna cewa na dage da karatu Allah"




Dariya Aisha tai tace "tun da kika ji tsoro mu kuma fah Ya Batul, ai sumu inaga tun ranar da muka samu admission zamu fara zawo har ranar da zamu fara lecture"




Hararar ta nai kawai na juya gurin Abba daya miko min kudi, kallon sanai ganin haka yasa shi fadin "ungo dubu talatin ne kiyi siyayyar hijabai da takalmi sai jakar makarantar da zaki yi amfani dasu".




Cikin farin ciki na karbi kudin nace "angode sosai Abba Allah ya kara arziki ya Kara lafia da nisan kwana mai albarka ai kuwa gobe Insha Allah zanje kasuwa na siyo yadikan hijabai guda da kuma material ko Umma sai na siyo jaka a gwanjo mai kwari wacce zata dinga dauke min komai guda biyu" 




Khalil ne yace "Ya Batul zan raka ki don Allah"




Da sauri kamal yace "ni zan raka ta ai ba Kai ba"




Tabe baki nai nace "ba wanda zanje da shi ni kadai zanje na dawo"




Kallon Umma nai nace "Umma wannan kudin da nake ajiye wa  a gurin ki don Allah in zan samu sai na hada dasu goben na siyo material da dan yawa Wanda zan na Sawa dama nai WA Aunty Zainab magana Zan dinka abina da kaina"




Gyada kai Umma tai tace "mai zai hana ki samu kuwa, suna nan na ajiye miki dama ai, goben in Allah ya kaimu sai na baki"




Murmushi nai cikin Jin dadi na mika mata kudin da Abba yaban nace "Toh gashi Umma ki ajiye min wannan ma"




Mikewa nai na dauki Mimi na kwantar da ita, Nima kwanciya nai don gobe da wuri nake son zuwa kasuwar, lumshe idona nai saidai kuma duk yadda naso baccin ya dauke ni ya kasa zuwa saboda fuskar wannan mutumin kawai kemin yawo, a hankali na bude idona na zuba akan fuskar Mimi gani nake kamar Mutumin ne kwance a gefena.




Mikewa nai na zauna ina kallon Aisha dake shirya littafan ta acikin jaka nace "Aisha kinsan me?"




Dan juyo wa tai tace "A'a Ya Batul"




Ajiyar zuciya na sauke nace "wani abin mamaki na gani wallahi jiya nida Cilla bayan mun fito daga cafe wani ya kusan take min kafa, kin san Mutumin yana kama da Mimi sosai kamar yayi kaki ya tofar har yadda yake magana da yadda yake bata fuska duk irin na Mimi ne"




Waro ido Aisha tai tace "kuma kin fadawa Umma Ya Batul"




Girgiza kai nai nace "ban fada mata ba bana son na fama Mata ciwon da take kokarin rufe wa ne"




Zama tai a gefena tace "Ya Batul kina tunanin zai iya zama baban Mimi?"




Da sauri na yatsina fuska nace "Allah ya kiyaye insha Allah ma ba shi bane babanta, toh meye ma ya dame ni da sanin ko waye baban nata, bana ma fatan sanin sa don duk ranar da muka hadu nida shi Allah ne kawai zai kwace sa a hannuna"




Tagumi Aisha tai tana kallo na ganin yadda nake faman tsinewa baban Mimi Wanda ko kalar fatar jikin sa ban sani ba.




Haka nai bacci saboda sa abin a raina har mafarki nai wai mutumin dana hadu dashi yazo yace na basa Mimi yar sa CE, ai kuwa haka na tashi raina duk a bace, da kyar naje kasuwar na siyo duk abinda zan bukata na tahowa da Mimi dogayen rigunan Yan gwanjo guda uku na siyo mata sabon takalmi.






Kwanci tashi har mun fara shiga university muna bude file nida Cilla muke tafiya komai tare muke yi kafata kafarsa har muka gama, gobe Insha Allah dukkan mu zamu fara lecture gaba daya cikin zumudi muke koda aka ban time table sai da naje nai photo copy daya na barsa a cikin jakata daya kuma na sa salatif na manna a jikin bangon dakin mu.




Yau saboda zumudi da wuri nai bacci bayan na shirya kayana dazan sa goben in Allah ya kaimu..














*********




A hankali yake gyada kansa kamar salihi yana Jin abinda Abie yake cemasa.




Girgiza kai Abie yai yace "don Allah Azlan Ka dinga zuwa duk ranar da kake da lecture kar kasa shiririta kuma Ka dinga suturta jikin Ka kaji"




Daga Kai yai yana lumshe idon sa sam wannan lecturing din da zai fara kawai don ba yadda zai yi ne amma ayyukan office kadai ma aka barsa dasu ma sun ishe Shi ga kuma wannan nauyin an Kara dora masa.




Shiru yai yana jin Abie da Mami suna masa nasiha Shi dariya ma suke basa yadda suke wani lallabasa akan lecturing din toh sun san halin sa a goben da yake da class zai iya kin zuwa ya kwanta yai baccin sa hankalin sa kwance.


 


Sai da suka gama masa nasihar sannan ya mike ya fita bayan yai musu sai da safe


















***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol