Free chapter · Read without an account

Chapter 7

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*













*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)


   



007

Kamar kullum da yamma Hujayrah ta kai ma masu shaguna abinci wa'inda suke a ɗayan layin,har ta kai ta amsa kuɗin za ta tsallaka titi kamar an ce ta wai ga Rasssss!!! Ƙirjinta ya bada ganin Alhaji Sambo Dala ya fito da rantsattsiyar motarsa mai numfashi ya nufa wani babban pharmacy wanda yake a layin da take, sosai hankalinta ya tashi jikinta har jikin ta ya fara rawa, lokaci guda ta rikice ba tare da ta kalli titin ba ta shigo ciki,sai horn ake mata amma ina hankalin ya daɗe da barin jikinta. Ai da wani irin ƙarfi mai motar ya taka birki ji kaka Ƙiiiiiiiiiiiiiiiiiiii, Allah yasa motar ta tsaya wanda saura ƙiris ta bige Hujayrah.

Da sauri mai motar ya fito a fusace yana cewa

"What the hell is wrong with you, makauniya ce ke, bakya gani ne da kawai za ki shigo titi ba tare da kin duba ko akwai motar da take zuwa ba! "

Still jikinta na rawa sannan bata bar yunƙurin tsallaka titi ba ta ce

"Ka yi Haƙuri"

Daga haka ta tsallake titin a guje tsoran kar Alhaji Sambo Dala ya fito daga shago ya sameta.Wawan tsaki mai motar ya ja sannan ya tada motarsa yabar wajen. Hankali tashe Hujayrah ta kaima Hajiya kuɗin abincin,wanda hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Ganin yadda Hujayrah ta kawo mata kuɗi cikin sanyi jiki ga damuwa kwance a fuskarta yasa Hajiya ta tambayeta ko lafiya take ko akwai abinda ke damunta, girgiza mata kai Hujayrah ta yi tana cewa masassara ce take son kamata. Sosai Hajiya ta tausaya mata tare da ɗauko  maganin zazzaɓi ta ce kawai ta wuce ɗaki ta kwanta idan tasha maganin tunda bata da lafiya. Amsar maganin ta yi tana mata godiya tabar ɗakin zuwa ɗakinsu,maganin tasha sannan ta kwanta, don ba ƙarya ta yi ba tabbas masassara ce take son yi mata sallama,don har yanzu jikinta bai bar rawa ba. Nan fa ta fara tunanin anya bazata bar gidan abincin nan ba kar wata rana shi ko yaransa su zo nemanta gidan cin abincin nan,gashi yadda taga Hajiya bata da alamar taimaka mata da kuɗin mota kamar yadda ta ce a baya, kodan taga tana jawo mata Customers ne shiyasa bata son tabar gidan abincin. Matsalar har yanzu kuɗin da take tarawa ba za su isheta kuɗin motar zuwa Kaduna ba. Dole ta samo ma kanta mafita kar mutanan su cimmata tunda har ta iya ganin Alhaji Sambo Dala to yaransa ma za ta iya ganinsu tunda suna da yara ba kuma iya tantance su za ta yi ba.

Tana a kwancen tana tunani ta ji saukar ruwa mai shegen sanyi a jikinta, da sauri ta miƙe daga kwancen da take tana kallon wa'inda suka zuba mata ruwan. Raziƙa, Hajara da Sajida ne tsaye suna cilla mata harara,musamman ma Sajida wacca hannunta ke riƙe da bokiti.

"Lafiya za ku zo har gadona ku zuba min ruwan sanyi a jiki" cewar Hujayrah tana yarfe ruwan dake fuskarta

Dariya suka kwashe suna yi suna kallonta,bata   ce musu komai ba Sai ma zuba musu dara-daran idanunta,sun ɗaɗe suna dariya sai can suka tsagaita suna kallonta.

"Shegiya yau dubunki ta cika, za ki san komu su waye, bake kin mana kutungwila Hajiya ta daina son mu sai ke kaɗai to yau za ki ga ne shayi ruwa ne"cewar Sajida tana dariya

Madadin ta ji tsoro sai ita ma ta kwashe da dariya tana kallonsu har da riƙe ciki,sosai dariyar Hujayrah ta basu mamaki, madadin su ga tsoro da firgici a fuskarta sai ma ta mai dasu ƴan iska tana musu dariya. A zafafe Hajara ta ce

"Ke ƙaramar ƙwaila ce wallahi, Karki maida mu shashasha mana, an faɗa miki ba zamu iya aikata wani abu akanki bane, ko kina tantama ne yanzu kiga cikawa da aiki"

Sai a sannan ne Hujayrah ta tsagaita da dariyar da take tana dubansu ta ce

"Oh ni! jikar Hindatu mai tsoran mutuwa, ku nan takakka kuma min"

Dariyar ta sake kwashewa, sai can ta ce

"Ruwa ba sa'ar kwando bane, duk lalacin zaki yafi ƙarfin namun dawa,hhhhhh! Ku a tunaninku tsoronku zan ji, Cab Allah sittiri-buƙwi,banda lokacinku yanzu da badan haka ba Hmmmmm"

"Oooooh ta ji tsoro" cewar Raziƙa

"Dallah malamai ku ware ku bani waje, ke kuma ƴar rakiya idan baki shiga taitayinki ba wallahi duka tsiya zan yi miki, munafukar banza munafukar yofi"

Tana kallon Raziƙa tana masifa, sosai yadda take masifar ya tsorata su musamman Raziƙa wacca ta kasance matsoraciya sosai. Ganin koba komai sun yi nasara akanta tunda sun zuba mata ruwan sanyi, sai kawai suka juya za su wuce.

"Ke Sajida" cewar Hujayrah 

Juyowa ta yi tana kallonta, sai da Hujayrah ta saki ƙasaitaccen murmushi sannan ta ce

"Kin yi min na sanyi, to ki jira na zafi"

Tana gama maganar sai kawai da shige toilet da kayan sauyawa ta barsu a wurin tsaye suna mamakin maganarta,musamman Sajida wacca ta yi mutuwar tsaye tana tunanin mai Hujayrah take shirin aikawa akanta dole ta kula.Ganin suna ɓata ma gansu lokaci ne yasa kawai suka bar ɗakin zuwa wurin aikinsu,daman fakan idanun sauran masu aikin suka yi ganin Hujayrah ta shigo cikin ɗaki, shi yasa suka biyota amma fa sun kasa aiwatar da ƙudirinsu akanta saboda wani kwarjininta daya shigesu lokaci guda,ga idanunta daya sake sakasu matuƙar tsorata dan dole kowa ya sha jinin jikinsa suka kasa aiwatar da ƙudirinsu .

Koda Hujayrah ta fito daga bayin bata samesu a ɗakin ba, murmushi kawai ta yi sannan ta yi kwanciyarta abinta tana saƙe-saƙe a ranta, bata yi barci ba har aka kira sallar magrib, tashi ta yi ta nufa bayi ɗauro alwala ta fito, kabbarta sallar ta yi, tana cikin sallah  wasu daga cikin ma'aikatan suka shigo ɗakin don yin sallah.

Hujayrah dai bata fito daga ɗakin ba zuwa wurin aiki, har Rabi ta tambayeta ko lafiya, gyaɗa mata kai ta yi ta ci gaba da kwanciyarta amma bacci ɓarawo yaƙi zuwa wurinta har ƙarfe 10:00pm na dare ta yi kowa ya shigo ɗakin don kwanciya wanda har lokacin Hujayrah bata yi bacci ba tana jin motsinsu, sunata hira har ta ji shiru alamun kowa ya yi bacci, ta kai kusan 1:00am na dare bata yi bacci ba, sai can bacci ya ɗauketa tare da mugayan mafarkai barkatai.

Washe gari da asuba Hujayrah ta farka, miƙa ta yi tana addu'ar tashi daga bacci, sannan ta dubi kowa na ɗaki,daman kusanci kullum ita ce ke fara tashi daga bacci, a yanzu baccinsu suke kashirɓin hankalinsu kwance,da idanunta suka sauka akan gadon Sajida sai ta saki wani munafikin murmushi. Jakarta ta ɗauko ta zage zip,wata Leda ta ciro daga cikin jakar sai ta zage zip ɗin, saɗaf-saɗaf! Ta nufi gadon Sajida a hankula ta ɗauko butarta kasancewar kowa a ɗakin yana da tashi butar, sai dai ita da Rabi suke sharing buta ɗaya.A hankula ta buɗe murfin butar sai ta kwance ledar hannunta ta zuba wani abu a ciki wanda bansan me ta zuba ba. Sai ta yi sauri da rufe butar ta maidata inda take, ta miƙe ta nufa bayi. (Allah ya shirya mana ke Hujayrah, ko wace muguntar aka shirya ma Sajida oho😂😂😂)

Alwala ta ɗauro ta  fito daga bayin,Rabi ita ma ta farka ta ɗauki buta ta shiga bayi , haka ɗaya bayan ɗaya suke shigan bayin wanda duk wannan motsin da suke Sajida na kwance tana sharɓar baccinta. Sai kusan bayan kowa ya kammala sallah har wasu sun fita ɗaura ruwan zafi na wanka sannan ta tashi tana miƙa babu salati balle addu'ar tashi daga bacci ta ɗauki butarta ta wuce bayi da ɗan sauri. Hujayrah na zaune ita da Rabi suna hira kafin su yi wanka su wuce wurin aikinsu sai suka ji ihun Sajida a bayi basu ankara ba suka ga ta fito daga bayi da gudu tana ihu.

Tsakiyar ɗakin ta tsaya tana tsalle da ihu tana cewa

"Wayyo Allah na!!! Yaji!!! Yaji!!! A wurin fitsarina!!! Ku taimake ni, fisabilillahi!!! Wayyo Allah!!!"

Da sauri kowa ya matso kusa da ita suna tambayar lafiya, Hujayrah ce a sahun gaba tana tambayarta cike da damuwa shimfiɗe a fuskarta.Babu wanda zai kawo a ransa Hujayrah ta aikata mata hakan saboda duk ta tafi kowa shiga damuwa, har su Hajara da Raziƙa basu shiga damuwa yadda Hujayrah ta shiga ba, har da ƴar ƙwalla. Wasu a cikin ma'aikatan suna tambayarta suna mata dariya domin yadda take ihu tana tsalle dole ya saka ka dariya duk ɗaurewanka.

Ƙafarta a gwale take tana bubbugata tana ihu, fuskar nan ta ƙara ja bayan tasha bleaching fuskarta har ja take,yanzu sai fuskar ta sake ja kamar jan gauta, kamar mai koyan tafiya take yawo a cikin ɗakin, su kuma ma'aikatan suna biye da ita, wasu na dariya wasu na tambayarta,kamar yadda yaro ɗan goyole yake koyan tafiya yana *Ta! Ta! Ta!*  haka Sajida take yi, domin ita kaɗai ta san azabar da take ji,sosai gabanta yake mata zafi da zugi wanda tsakiyar kanta zuwa cikin ƙwaƙwalwar kanta take jin raɗaɗi da zugin.Tun maganar farko bata sake cewa komai ba sai ihu da tsalle.Cike da tausayi Hujayrah ta ce a taimaka ma Sajida da gishiri da ruwan zafi ƙila idan ta yi tsarki da ruwan za ta daina jin raɗaɗin, haka Raziƙa ta tafi kitchen da ɗebo ruwan zafin da za su yi wanka da gishiri,Direct da nufi bayin ta zubar da ruwan butan ta ɗauraye da yake har yanzu gari bai gama wayewa ba, bata iya tantance meke cikin butar daya saka Sajida jin zafi har da ihu.Zuba ruwan da gishirin ta yi sannan ta fito. A hankali Hujayrah ta riƙo hannun Sajida tana mata sannu cike da tausayi ita kuma Sajidar tana amsa mata murya can ƙasa saboda baza ta iya ɗaga murya ba, haka suka shiga bayin da Hujayrah tana *Ta! Ta! Ta!* tafiyar yara. Suna shiga Hujayrah ta sauya fuska daga tausayi zuwa dariya a hankula take maganar tana cewa

"Kaɗan kika gani Sajida har yanzu bakisan wace ce ni ba a gidan nan, wallahi wallahi wallahi rantsuwar musulmi ko!"

Da sauri Sajida ta jinjina mata kai cike da tsoro don sai yanzu Sajida da tuno da maganar Hujayrah ta ƙarshe a jiya *kin yi min na sanyi, to ki jira na zafi* ilai yau gashi tana shan azaba wanda bata taɓa jinsa ba. Sosai ta ƙara tsorata da Hujayrah kai anya mutum ce kuwa, kodai da aljana suke zaune basu sani ba, tunda ta ce kawai ta tsinci kanta a garin nan ne... Bata ƙarasa zancen zucinta ba,Hujayrah ta katseta da cewa

"Ga zuwan zafi da gishiri a ciki ki yi tsarki dashi, idan kin gadama Karki yi, babu ruwan jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa, Ni kinga tafiya sauran ki faɗa ma ƴan ɗaki Kice ni na zuba miki yaji a cikin buta, Hmmmm abinda zan yi miki wallahi sai yafi wannan,ba a takani a zauna lafiya, Ni nan da kike gani na buhun ƙaya ne nafi ƙarfin danna,ƙarin daɗi ni buhun barkono ne duk wanda ya taɓani wallahi sai ya face majina, ki kula ina ƙara faɗa miki"

Jinjina mata kai Sajida ta yi kamar mai ɗaukar karatu ko kuma ƙadangaruwa,sosai take tsoron Hujayrah, haka Hujayrah tabar bayin. Ita kuma Sajida a hankali ta ɗan watsa ruwan zafin a gabanta, babu shiri da saki ihu don wata sabuwar azaba ce wacca tafi ta ɗazun ta ji tana shigarta har cikin tsakiyar kanta yau dai ta ga rayuwa, jin Hujayrah ta ce ita ce kaɗai mafitarta yasa ta sake watsa ruwan, nan ma sai da ta saki ihu, da ƙyar ta iya ɗauro alwala ta fito tana tafiya a gwale kamar mai koyon tafiya, nan take Raziƙa har da Hajara suka tintsire da dariya har da wasu a ɗakin ban da Hujayrah wacca tasha murr! Kamar tasha kunun kanwa. Sosai dariyarsu Raziƙa da Hajara ta kaima Sajida wuya, wani irin malolan baƙinci ne ya taso ma Sajida tun daga ƙahon zuciyarta har zuwa tantani-maƙwallatonta ya tsaya cak! Galla musu wata uwar harara ta yi sannan ta ƙarasa wurin gadonta da ɗauki hijab ta saka ta shimfiɗa dadduma.A zaune ta yi sallar domin bazata iya tsuyawa. (Su Sajida sai a kula kin ji dai Hujayrah tamu ta ce ita buhun ƙaya ce tafi ƙarfin ɗanna🤭🤭🤭😂😂😂)

Ɗaya bayan ɗaya kowa ya shiga bayi ya yi wanka har ya rage saura Sajida wacca ta ce a ce ma Hajiya bata da lafiya, bayanta  tafi wanka lokacin kowa yabar ɗakin har da Hujayrah zuwa wurin aiki, sai ta kulle ɗakin ta kunna fankan sama ta kai ta numban ƙarshe sannan ta hau gado ya buɗe ƙafa isa na shigarta, sai a sannan ne ta fara jin wata sa'eeda(Au na manta ace sunan tauraruwar littafina ne mai suna NACINA Ya JAWO MIN, idan baki karanta littafin ba to ki hanzarta maza kiyi following channel ɗina zaki sameshi tun daga farko har zuwa ƙarshe, Karki manta akwai links ɗin channel ɗina a farkon chapter🤭🤭🤭💃💃💃)

Koda Hujayrah ta fito suna aikin jininta a ƙumba yake,komai take yi da taka-tsantsan take yinsa, har ta fitama yau ta ce babu inda zata je, sai dai wasu su kai abincin.Suna ta aikinsu har bayan sallar Zuhr lokacin kowa ya je ya yi sallah ya dawo. Sai Hujayrah ta fito falon da abinci za ta kai zuwa wani table da suka umurceta, bayan ta kai za ta koma ciki ɗauko wani abincin sai kawai idanunta suka yi arba da wani kyakkyawan saurayi, yana zaune a kujera shi kaɗai yana kallon wani direction, ya saka baƙaƙyen kaya da facing cap, inda yake kallo ta kai idanunta,wasu maza ne suna zaune suna cin abincin suna ƴar hiransu hankalinsu kwance. Taɓe baki Hujayrah ta yi sannan ta wuce ciki don ɗaukowa sauran mutanan abinci. Ta ɗauko musu ta kawo sai ta wuce wurin saurayin fuskarta da murmushi har da zama a ɗayan kujerar dake kusa dashi. Cikin muryarta mai sanyi ta ce

"Dan fari Mai irin  hancin Mammina sannu da hutawa"

Juyowa ya yi ya kafeta da idanu, baƙin glass ɗin daya saka ya hana taga yadda ya kafeta da idanu. Fari ne mutumin sosai wanda har ɗan ja ja jikinsa ya ke, ga sajensa baƙi suɗik! Ya yi luf-luf dashi gwanin ban sha'awa, hancinsa dogon ne har baka, gashi da ɗan ƙaramin baki ja dashi, dole Hujayrah ta ce mai hanci irin na mamminta kasancewar mamminta akwai hanci sosai shiyasa ta ce mishi haka, a duk ɗakinsu  ita kaɗai ce baƙa bai gajeran hanci amma sauran har Haroon autansu fari ne kuma yana da hanci sosai.Jin  bai amsa mata ba yasa  ta ƙara ce masa

"Ammm mai za a kawo maka na ɗan taɓawa a baki mai dogon hanci " 

Nan ma shiru babu amsa,kwaɓe fuska ta yi cike da shagwaɓa wacca bata san ta yi ba ta ce

"Ai daman nasani ƙila a zuciyarka za ka ce wannan ta cika surutu,Ni ma Allah Inaso na daina surutu ma mutane, na daina shiga sharu ba shanu amma naƙi, Ni don Allah ko za ka koyamin yadda ake ɗaure fuska irin yadda ka yi kamar ka ci magani" 

Sa a sannan ne ya saki murmushi, magana ya yi wanda a ka yi masa dole ya ce

"Talkative" 

Waro idanu Hujayrah ta yi har da riƙe baki ta ce

"Laaah mai irin hancin mammi daman kana magana, ai na za ci kurma ne wallahi, Allah sarki Tankative Ashe Sunanka Tankative, Don Allah ka yi haƙuri ina kiranka da mai irin hancin i mammi" 

Mamaki ne ya cika saurayin, ita kuma wannan daga ina haka mai shegen surutu kamar kurna, girgiza kai kawai ya yi yana murmushi, hakan da ya yi Hujayrah ta ce

"Tankative na cika surutu ko?" 

Wannan lokaci dariya ya yi, duk da baya son ya biye mata saboda yana kan aikinsa ne amma ya  zai yi da wannan yarinya mai shegen surutu.Wannan Karon da asalin muryarsa ya yi mata magana

"Ki daina kirana da Talkative, ke ce talkative saboda shegen surutunki ya yi yawa, da alamu baki je makaranta ba ko" 

Nan fa fuskar Hujayrah ta sauya daga farin ciki zuwa damuwa, har da ƙwalla saboda ya tuno mata rayuwarta,ɗagowa ta yi idanunta cike da ƙwalla ta ce

"Ina son makaranta amma ƴan uwan Abbuna suka hanani saboda sun ga Abbuna baya gani, Sannan yaransu basa karatu, Ina son karatu musamman Karatun jarida amma ban samu damar hakan ba a sanadiyyar makantar idanun Abbuna" 

    Wani irin tsantsan tausayi ne ya shiga zuciyar saurayin farar ɗaya ya ji yana tausayin Hujayrah , duk da akan aikinsa yake bazai iya dogon hira da ita ba amma zai dawo nan gaba just because of her. Cike da tausayi yake

"Ya sunanki " 

Cikin  raunin murya ta ce

"Hujayrah" 

"Fine ni Sunana Mas'ud Abdulrahman Saminu Kwankiyal, yanzu ina a kan aiki ne,kinga wa'incan mutanen" 

Nuna mata mutanan nan ya yi wanda sai hirarsu suke babu san da wanzuwarsa ba saboda ɓadda kamar da ya yi. Ci gaba da cewa ya yi

"Ina bikin cike akansu ne, Ni jami'in sirri ne amma zan dawo next time sai mu zauna na ji labarin rayuwarki kin ji, ko da yadda zan taimaka miki, Kin ji Hujayrah " 

Gyaɗa masa kai ta yi, sai ya miƙe saboda yaga mutanan sun miƙe tare da barin gidan cin abincin, sallama yama Hujayrah yana miƙawa ya ajiye mata kuɗi a saman Table masu yawa sannan yabar gidan cin abincin  da  sauri ya shiga rantsattsiyar motarsa ya wuce saboda mutanan suma sun bar wurin da motarsu.Jiki babu ƙwari Hujayrah ta miƙa tabar falon abinci zuwa ɗakin su don ajiye kuɗin koda ta je sai da ta bubbuga saboda ƙofar a rufe take, a hankali Sajida ta sauko daga gadon tana tafiya a gwale ta zo ta zuɓe ƙofar, sai da gaban Sajida ya bada Rasssss! Ganin Hujayrah a gabanta da sauri ta ce

"Na roƙeki da Allah ki yi haƙuri wallahi bazan sake aikata abinda nayi miki ba, yanzu kowani daga yana da niyyar aikata miki wani abu sai inda ƙarfina ya ƙare" har da hawaye bisa kucinta tana ba Hujayrah haƙuri saboda ita kaɗai tasan wahalar da take ciki a yanzu. 

Dariya abun ya so ba Hujayrah ganin yadda Sajida ta zage tana bata haƙuri,murmushi kawai ta yi sannan ta ce

"Nifa ya riga daya wuce bama wurinki na zo ba ai idan kin sa haƙuri, ba komai na aikata miki ba indai akan muguntana ne" 

Waro idanu Sajida ta yi waje tana kallon Hujayrah a zuciyarta tana cewa 'Anya mutum ce wannan, au ma kaɗan daga muguntarta tamin a haka, bala'i '  Katse mata tunani ƙarar faɗowan jaka ta yi,firgigit ta dawo hayyacinta, ashe Hujayrah ma tabar wurin ita take tsaye ƙiƙam! Komawa gadonta a hankali ta  kwanta. Ita kuma Hujayrah ta ajiye kuɗin da Mas'ud ya bata cikin jakarta sannan ta fito daga ɗakin.Yinin ranar Sajida na ɗaki har Hajiya ta zo dubata, sosai ta tausaya mata tare da yi mata addu'ar samun waraka. 

Hujayrah tunda Mas'ud ya ce zai dawo take baza idanu,hakan nan kawai ta ji Mas'ud ya kwanta mata a rai. A tunaninta a ranar zai zo, har aka yi kwana biyu shiru kamar an ci shirwa an sha ruwa,gashi tsoranta ɗaya kar wata rana ta haɗu da Alhaji Sambo Dala ko yaransa ta shiga uku ta lalace. Haka Hujayrah ta ci gaba da zama a gidan abincin tana jiran Mas'ud wanda a ƙarshe ta yanke shawarar komawa garinsu tare da tona ma Baba Zakari asiri a bai nan nasi, kowa yasan halinsa Lokacin da ta faɗa ma Hajiya tafiyarta gobe ne sai bata ji daɗi ba duk da gwara ta tafi gida ko hankalin iyayanta zai kwanta. Sha-tara ta arziƙi Hajiya ta yi mata har da sitiru,ƴan aikin ma wasunsu basu ji daɗi tafiyarta ba musamman Rabi wacca suka shaƙu da juba sosai gashi ba waya balle su karɓa lambar juna. Su Sajida farin cikin ya gaza ɓoyuwa a fuskokinsu ji suke annoba ta kusa barinsu su sarara ko sa ɗan samu masoya don wayancin customers suna son Hujayrah duk da basa samun fuskar furta mata amma suna nuna hakan a fuskokinsu. 

A yau Hujayrah ta shirya tsaf! Zuwa tashar da za ta sadata da Kaduna. Cikin riga da skirt na atamfa wanda Hajiya ta mata da hijab mai shigen kayan sosai ta fito ta yi kyau da ita, har wani sheƙi fatarta take saboda murjewa babu laifi Hajiya na ƙoƙari da ƴan aikinta shiyasa take ganin ci gaba akodayaushe. Har tasha Rabi ta rakata sannan ta dawo. Tana cikin tafiya zuwa idan ake kiran motocin Kaduna sai ta ji wata mata na ƙwalle ihu tana cewa

"Ɓarawo! Ɓarawo! Jama'a ku taimakeni jakata!" 

Da gudu yaron da ya ɗaukema matar jaka ya zo ta gaban Hujayrah zai wuce,Hujayrah bata yi wata-wata ba ta saka mai ƙafa ya faɗi,haba sai suka kacame da kokawa tana jan jakar shima yana jan jakar, da yaga mutane sun kusa zuwa wurin sai kawai ya tura Hujayrah tare da jakar a hannunta ƙasa sai ya ƙara ma motarsa mai a guje.

Matar da sauran mutanen da suke bin ɓarawon suka yo kan Hujayrah suna yi mata sannu, da ƙyar ta tashi tana haki. 

"Ƴar nan sannu zo mu ce Chemis a dubaki " 

A hankula Hujayrah ta miƙe mutanen wurin sai mata sannu suke tare da yaba ƙoƙarinta. Wani Chemis ne a tashar suka nufa aka wanke mata ciwo a gwiwa sannan suka bata magani. Bayan sun fito sai suka samu wuri a gindin bishiya suka zauna. Matar ce ta kalli Hujayrah ta ce

"Ƴata yanzu ina za ki da kika zo tasha" 

"Inna garinmu zani Kaduna" cewar Hujayrah 

"Daman ba a garin nan kike ba" 

Shiru Hujayrah ta yi har yanayinta ya sauya

"Babu damuwa ba sai kin faɗamin komai ba yanzu ya sunanki " cewar matar tana murmushi 

Sosai zuciyar Hujayrah ta aminta da matar sai ta ce

"Sunana Hujayrah ni ƴar Kaduna aure ya kawoni nan" 

Nan take ta kwance ma matar buri har wutsiya har da makantar da ta samu mahaifinta bata ɓoye mata komai ba. Nan da nan ƙwalla ta cika idanun matar har  wani ƙwalla ya fara leƙowa don samun damar gangaro mata bisa kuncinta. Cike da damuwa haɗi da tausayi matar ta ce

"Hujayrah a yanzu ba gida ya dace ki je ba domin idan kin koma gida to tabbas mutumin nan da yaransa za su je farautarki, matsalar yanzu ita ce makantar mahaifinki, idan da yana gani sai ya shigar da ƙara ƙungiyar kare hakƙin ɗan Adam su kuma tai su taimaka miki tare da kareki daga sharrin mutumin da sauran mabiyansa"

Shiru Hujayrah ta yi tana sauraro matar, sai yanzu tunanin nan ya faɗo mata, tabbas! Akwai babbar matsalar idan ta koma garinsu

"Inna to yanzu ya zan yi" 

Murmushi ta sake saki sannan ta ce

"Hujayrah idan kin yarda dani, Kin kuma amints za ki bini inda nake aiki? " 

"Ina ne kike aiki" cewar Hujayrah 

"A gidan wani attajiri ne mai mutunci da karamci, matansa biyu ne suma suna da mutunci sosai, nasan za su ɗaukeki tunda gidan babba ne, mu masu aiki mun kai  mu ashirin a gidan banda masu gadi da masu sharan waje da bama flawowi ruwa,Sannan za su biyaki kuɗi mai tsoka wanda za ki tara ki kai mahaifinki asibiti a yi mishi aikin ido,Kin ga daga lokacin da Allah ya ƙaddara mahaifinki ya fara gani tunda kince da girmansa ya makance sai ya shigar da ƙara a ƙungiyar kare hakƙin ɗan Adam, sai su taimaka mishi, Au! Na manta ban faɗa miki ba, sunana Uwani amma a can suna kirana da Baba Uwani"

Shiru Hujayrah ta yi tana tunani a gaskiya zuciyarta ta aminta ita sosai, amma yaushe har za ta tara kuɗin da zai iya kai mahaifinta asibiti ayi mishi aiki, ƙila idan ta fara aiki ta haɗu da Mas'ud tasan zai taimaketa.Duban Baba Uwani Hujayrah ta yi sannan ta ce

"Shikenan Inna na amince, Allah ya yi mana jagora" 

"Ameen ya Rahman, yanzu taso mu tafi kar dare ya yi mana a hanya, Gida Dubu zamu nufa a can gidan yake,akwai nisa sosai daga nan" 

Miƙewa suka yi tare sannan suka nufi inda zasu samu motar,Direct suka samu drop har zuwa Gubi Housing Estate Wanda ake mishi laƙabi da Gida Dubu. Sun daɗe suna lafiya sannan suka iso bakin gate ɗin estate ɗin. Bayan sun sauka Hujayrah da duba gidajen wajan da kallo, bata san sanda ta furta

"Aljannar duniya" 

"Sai ma kin shiga cikin estate ɗin musamman gidan na nake aiki zaki tabbatar da kin shigo aljannar duniya" 

Murmushi Hujayrah ta yi sannan suka nufa cikin estate ɗin bayan ta sallami mai motar sannan ta nuna I.D ɗinta na aiki s suka barta suka shiga ciki ita da Hujayrah, har Hujayrah na tambayar sai da I.D sannan mutum zai shiga ciki, Baba Uwani ta ce kowani ɗan aiki da masu gidajen suna da  I.D card saboda tsaron ƴan ta'adda da mugayan mutane...✍️

              🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar kwara ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*

A ɓangarensu Hannatu bayan Alhaji Zakari dasu baba Musa sun tafi Giwa wanda yake cikin garin Zaria, sai Hannatu ta fara masifa wai su Mammi da Fatsima su bar mata ɗaki. Taɓe baki Mammi ta yi sannan ta miƙe tana cewa

"Idan kinsa haƙuri dole ce ta saka na zo miki ɗaki amma ba don son raina ba, Fatsima taho mu tafi abin mu, Allah ya kiyaye na gaba ya kuma tsare ƴan baya" 

Miƙewa suka yi tare da barin ɗakin Kakulle ma ta bisu da sauran maƙotan da suka zo ganin ƙwaƙwaf, suna fita Hannatu ta kwance ɗan kwalinta tare da sakin wani sabon ihu tana cewa

"Na shiga ukuuuu! Ni Hannatu na ja ma ɗana na kaina wahala gashi annobar sata ta sameshi rana tsaka, bawan Allah mai tsoran Allah, wayyo Allah naaaa!!" 

Da sauri Murja ta miƙe tana cewa

"Haba Hannatu ki yi shiru abi abun a sannu mu san yadda za mu shawo kan al'amarin tun yanzu" 

"Bazan yi shiru ba! Kin manta ɗan daudu mai zamani ya ce babu makarin asirin? Wayyooo Allah na ni Hannatu shikenan ɗana ya halaka, Allah ya isa tsakanina da ɗan daudu, Allah ya isa tsakanina da matar mai unguwaaaa!!!" 

Saurin rufe ma Hannatu baki Murja ta yi karta tona musu asiri,matan unguwa su samu abin faɗa, cike da damuwa ta ce

" Haba Hannatu ki dawo cikin hankalinki mana, Kin manta boka yana da aljanar da take kai mishi... "

Cire hannun Murja Hannatu ta yi, cike ta masifa da hargagi ta ce

"Na ce Allah ya isa tsakanina da ɗan daudu! Na ce shi ɗan daudun ya ci kazan-kazan ubanshi ɗan hegiya mai sufar mata, mugu azzalumi mai zaluntar bayin Allah na ƙwarai irin ɗana Jamilu, Wayyo! wayyo!! wayoooooooooooooo!!! "

Shiru Murja ta yi tana kallon Ikon Allah, lokaci guda Hannatu ta fita hayyacinta,kamar wata mai tashin jinnu ko kuma mai ƙaramin hauka, idanunta sun yi ja sosai, kwalliyar da ta yi duk ya caɓe kasance Hannatu akwai son gayu duk da ta manyanta, irin matan nan ne wa'inda suke da budurwar zuciya. Murja dai sallama ta yi ma Hannatu sannan ta wuce sashenta. 

Murja na isa ɗakinta ta cillara guɗa tana tafa hannunta ta ce

"Sai ni Murja ta Zubairu mai fuska biyu, ta dangwale-shalele hhhhhhhh! na gama dake Hannatu saura mijinki, da sannu zan janye komai naku ya koma nawa, hhhhhhhh na kusa zama Hajiyar kaina in dinga ji ana kirana da Hajiya Murja mai haƙoran Makka rerasss! Na zinari ,lokacin Izzata da ƙasaita sun kusa Hannatuuuu! Kin kusa zama a ƙarƙashin ikna ke da mijinki, yanzu aka fara wasannnn! "

Ita ka ɗai take magana tana dariya har da canja magana irin da matan manya tana dariya. 

*Waiwaye*

A lokacin da Hannatu ta miƙama Murja jakar zata hau mashin, tana ciki-cikin hawa mashin ita kuma Murja sai ta samu damar canja mazaunin inda ta ajiye magungunan da yake lokacin da suke tsaka da tafiya Hannatu ta ce mata, kowani magani ta saka shi a waje na daban don karta manta ko kuma a samu matsala. Ɗaya cikin jakar ɗaya kuma cikin aljihun waje na jakar. To a nan ne Murja ta fara murna za ta cika aikinta na tsawan shekaru akan Hannatu, wanda ta kasa samun yadda za ta yi sai yanzu da damar ta samu. Wannan kenan

*Cikin labari*

Ɓangarensu Alhaji Zakari da ƙyar aka bada belin Jamilu don ma an san yaron na da hankali kuma ba a taɓa samunshi da case ɗin sata ko makamancin haka ba sai a wannan karon,daman bai saida wayoyin ba mai gadi ya amsa, sai su Alhaji Zakari suka bada kuɗi sannan suka taho gida. 

Basu suka dawo gida ba sai wurin 3:24pm na rana sun gaji sosai kowa sashensa ya wuce. Goda Alhaji Zakari ya shigo ɗakin da sallama Hannatu bata iya amsa mishi ba don har yanzu kuka take. (Ashe ɗa nada daɗi kike son cutar da ɗan wani, mtwsss! 🤔😏😏😏😂) 

Bayan ya shigo sai ya samu wuri ya zauna tare da gyaran murya, sai a sannan ce ta ɗago jajayan idanunta tana kallonsa. Cike da damuwa ya fara bata labarin yadda suka kaya a Giwa har nasarar samun belin da suka yi duk ya faɗa mata. Nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta ya fara dawowa cikin jikin, ɗan murmushi da saki wanda bai kai cikin zuciyarta ba saboda ita kaɗai tasan tashin hankalin da take ciki wanda ba zata taɓa faɗa mai ita ce silar matsalar da ɗansu yake ciki ba, don ba zasu kwashe lafiya dashi ba. Har ƴar hira suka yi sannan ya fita harkokinsa. 

*Bayan kwana uku* 

Da safe Alhaji Zakari ya kammala karyawa sai ya ciro kuɗi masu yawa ya miƙa ma Hannatu fuska a ɗaure ya ce

"Gashi dubu hamsin ne kiba Murja in ji ni" 

Da mamaki Hannatu take kallonshi,miƙewa  ta yi tana kallonsa don taga take-takensa kwanakin nan,baya sake mata kamar da kullum fuska a ɗaure, wani lokaci tada fuskarsa shimfiɗe da damuwa amma idan ta tambayesa sai ya ce mata ba komai.Ɗaure fuska Hannatu ta yi sannan ta ce

"Rigiji-gabji-tabɗijan!!! Me kake nufi da na bata duhu hamsin in jika? ban gane ba? yaushe ka fara bata kuɗi? Bata da miji ne? Ko kuma tana neman taimako ne?" 

Bai tanka mata ba ya zo zai fita sai ya juyo ya ce

"Ina miki kashedi da Karki ce za ki taba hankalinki akan don na bata kuɗin domin... ✍️






*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***














Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol