Free chapter · Read without an account

Chapter 8

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*















*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)




 

008

Da mamaki Hannatu take kallonsa,miƙewa  ta yi tana ƙara kallonsa da kyau don ta ga take-takensa kwanakin nan,baya sake mata kamar da kullum fuska a ɗaure, wani lokacin sai  ta ga fuskarsa shimfiɗe da damuwa amma idan ta tambayesa sai ya ce mata ba komai.Ɗaure fuska Hannatu ta yi sannan ta ce

"Rigiji-gabji-tabɗijan!!! Me kake nufi da na bata dubu hamsin in jika? ban gane ba? yaushe ka fara bata kuɗi? Bata da miji ne? Ko kuma tana neman taimako ne?" 

Bai tanka mata ba ya zo zai fita sai ya juyo ya ce

"Ina miki kashedi da Karki ce za ki tada hankalinki akan don na bata kuɗi domin ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba, ki yi yadda na ce sannan har ɗaki za ki sameta ki bata" 

Yana gama maganar ya ficewarsa abinsa,Wata uwar ashar Hannatu ta saki tana riƙe ƙugu,sai jijjiga kai take tana cewa

"Kutumar dumadu yau ake yinta a gidan nan,ni Hannatu zan ɗauki kuɗin mijina har naira ɗai ɗai har naira dubu hamsin na ba wata tsinanniya, har yana cewa “ki je har ɗaki ki bata in ji ni” hahaha, bara na je har ɗakin na bata na ji ita kuma me za ta ce shegiyar" 

Fitowa daga uwar ɗakin ta yi sai ta ɗauki hijab ta saka sannan ta jawo ƙofarta da sashenta ta wuce sashen su Murja.Ta ɗaɗe rabonta da sashen Murja, a ƙiyasi za ta iya  cewa tun lokacin da Murja ta yi rashin lafiya ta je sashenta gaidata rabonta da sashen. Buɗe ƙofar sashen ta yi bakinta ɗauke da sallama har ciki ta shiga. Murja dake zaune tana hutawa bayan ta kammala karyawa ta amsa cike da mamaki, yau Hannatu ce cikin sashenta Ikon Allah. Cikin ɗakin ta shiga fuska a ɗaure bayan ta zauna ta dubi Murja a gatse ta ce

"Alhajina ya ce na baki dubu hamsin" 

Tana maganar tana miƙo mata kuɗin, Murja bata amsa kuɗin ba sai ma da mamaki a fuskarta ta ce

"Ni kuwa Innar Harira anya ni ya ce kiba kuɗin, anya ni Murja, a'a sai dai idan wata  ya ce kiba mai sunana amma bani ba, don ban ga abinda zai sa ya ce a bani kuɗi har dubu hamsin ba, Kema ki yi tunani mana Innar Harira" 

Shiru Hannatu ta yi don yanzu kanta ya ƙara  ɗaurewa, shi ya ce ta bata ita kuma yanzu ta ce ba ita ba ce sai dai idan wata mai sunanta ya ce ta ba amma ba ita ba, akwai ruɗu a cikin wannan al'amarin. 

"Amma ni ya ce min har ɗaki zan kawo miki sannan na ce inji shi, lissafina ya ɓace Innar Balki" cewar Hannatu tana dafe kai

murmushi Murja ta saki tana cewa

"Ba ke kaɗai ba nima nawa lissafina ya ɓace,abin da rikita ƙwaƙwalwa sosai,haka nan ya ce a bani kuɗi inji shi, tun can da hakan bai taɓa faruwa ba sai yanzu, Kema ki yi tunani mana" 

Shiru kake jin ɗakin baka jin motsin komai sai saukar numfashi su kaɗan-kaɗan, kowa yana nashi zancen zucin.Sun kai kusan minti biyu a haka, Hannatu ta katse shirun da cewa

"Bara na kirashi na sake tabbatarwa ko bake bace, ko ni ne ban ji da kyau ba" 

"Yawwa hakan da yafi gaskiya" cewar Murja

Wayar ta buɗe sannan ta kirashi,wayar nata ringing har ta kusa yankewa sannan ya amsa kiran. 

"Assalamu Alaikum" 

A can ya amsa mata yana cewa lafiya take kiransa sai kace ba yanzu yabar gidan ba.Shanye ɓacin ranta ta yi ta ce

"Alhajina mun shiga ruɗu ni da  Innar Balki, ta ce ba ita ka ce na ba kuɗin ba" 

A can ya ce

"Ita na ce kiba kuɗin ba kowa ba sannan ba sai lalle kin ji dalilin da yasa na bata kuɗin ba, karki ce mata komai ki kawai miƙa mata kuɗin ki taho, Ina ƙara nosar dake Karki ki ce za ki tada balli akan bata kuɗin da na yi don yin hakan ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba,ki yi abinda na saka ki kawai ki bar ɗakin"

Wani irin ɗaci take ji a maƙogaronta, sosai maganarsa take sukarta kamar ana caka mata mashi a ƙahon zuciya. Sake danne ɓacin ranta ta yi ba tare da ta ce ma Murja komai ba ta ajiye mata kuɗin tabar ɗakin fuuuu! Kamar wacca aka kora. Wata bazawarar dariya Murja ta saki, sosai take dariyar, ɗaukan kuɗin da Hannatu ta ajiye Murja ta yi tana ƙirgasu har da saka miyau a yatsun hannunta don ta ji daɗin ƙirga kuɗin da kyau, ƙirga take tana murmushi har ta kammala ƙirgan ta ce

"Dubu hamsin cif-cif! Hejiya naira mai maganin matan zamani, wayyo Allah daɗi kasheni ni Murja, komai yana tafiya a yadda na tsara, hhhhh Hannatu kenan baki ga komai ba wallahi yanzu za ki fara gani, Izzar da mulkin sun kusa dawowa tafin hannuna ta yadda zan juya ki ke da shegen mijin naki, kuɗi kuma yanzu na fara cin su har sai naga abinda ya ture ma buzu naɗi, hhhhhhh"

Dariya take sosai har da jijjiga ƙafa, ƴar ƙaramar wayanta ta ɗauko ta kira wata numba, bayan sun gaisa ta ce

"Ke dai bari komai ya fara tafiya yadda ya kamata" 

Saurarawa  Murja ta yi tana jin mai take cewa, sai  ta saki ƙayattacan murmushi har da gyara zama ta ce

"Me kike ci na baka na zuba, ai kin kusa shigowa ciki ki yi yadda kike so,Kema ki kwasa romon da take kwasa wurinshi,shegiya sai mulkin tsiya da jijji da kai ita ga mai miji mai kuɗi bayan nasan komai! matsalata ni da ita shi ne shegen maƙo tsiya daga ita sai yaranta duk taimakonta da nake yi na tsawan lokaci ban ƙaru da ita ba sai ma raguwa,Ina faɗa miki kar ki ji komai aure kamar an yi an gama,dole yabi duk abinda nace mishi don yasan nasan komai, kar tasan kar"

Sake natsuwa Murja ta yi tana sauraron abinda matar take cewa, sai sakin murmushi take tana yaƙe jajayan haƙoranta kamar mai tallar makilin. Sun ɗaɗe suna wayar daga bisani suka yi sallama,miƙewa Murja ta yi tana taka rawa tana cewa

" *_Naira Zainabu Abu mai maganin matan zamani! Naira Zainabu Abu mai maganin yaran zamani! Kuɗi!!! Kai! Kai! Kai!_* " 

Zama ta yi tana sakin wata dariyar tana cewa

"Shikenan na tsinci dami a kala bara ma na kira Hadiza, da Balki su zo  har da Aliya na ƙara musu jalin sana'ah" 

waya da ɗauka ta kira Babbar ƴarta Hadiza ta ce ta aika yaranta su kira Balki da Aliya  da ita su zo zuwa anjima,sai suka ɗan yi hira har tana tambayar lafiyarta da abokan zamanta,ce mata ta yi maganar bata yawa ba ce sai ta zo daman yau take da niyyar zuwa gidan daga haka suka yi sallama. 

             🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Bayan Hannatu ta koma ɗakinta sai ta kasa zaune ta kasa tsaye,sai faman safa da marwa take a ɗakin ta rasa meke mata ɗaɗe a rai, me mijinta yake nufi da ita ne, ya sauya mata baya sake mata fuska, wani sabon iskanci yanzu ace ita ce za ta kai ma wata Kuɗi har dubu hamsin in ji shi, lallai kam wai tukunna, Cak! Hannatu ta tsaya wuri ɗaya tana tunani can ta ɗauki hijab ɗin da ta cire ta maida shi, ta shiga cikin uwar ɗaka da ɗauko ƙaramar jakarta ta fito ta saka key a kubar sannan ta rufe sashenta ta fito daga gidan. 

Tafiya take tana tunani har ta isa gidan aminiyarta matar mai unguwar garin uwar gidansa, da sallama ta shigo gidan kai tsaye ta nufi sashen aminiyarta. Ita kaɗai ce a ɗakin tana zaune a bisa kujerar mutum biyu tana latsa wayarta, da sauri ta ɗago ganin aminiyarta ta shigo babu sallama  fuskarta shimfiɗe da damuwa. Da sauri ta miƙe tana kallonta cike da mamaki  ta ce

"Aminiya lafiya kika shigo babu sallama?, meke faruwa ne? " 

Bata amsa mata ba sai ma zama ta yi  saman kujera tana kafa tagumi. Gyara labule aminyar ta yi sannan ta dawo ta zauna kusa da ita tana sake tambayarta lafiya. Still babu amsa sai ma wasu zafafan hawaye  suka shiga gangaro mata a bisa kuncinta, cike da damuwa Hannatu ta dubi aminiyarta ta ce

"Yanzu abinda Zakari zai sakamin dashi kenan Aminiya " 

"Ban gane abinda zai saka miki ba, mai ya faruwa ne" 

Numfashi Hannatu ta sauke sannan ta zayyane ma aminiyarta abinda ya faru tun daga zuwa wurin boka mai zamani,matsalar da ta samu aiki bai yi akan Salim ba ya dawo kan ɗanta, canjawar mijinta da kuma abinda ya faru yau na kuɗin da mijinta ya ce taba Murja bata ɓoye komai ba. Sosai Aminiyarta ta shiga tsantsan mamaki har ta jinjina tana riƙe baki, sai da ta sauke ajiyar zuciya kamar wacca ta yi tseran gudu sannan ta ce

"Kayya! Innar Harira abinda na yi ta miki gudu  kenan yanzu ya faru dake,a zamanin nan ba a yarda da mutum kuma koda muke a ƙauye baka yarda da mutum duk shekarun da za ku yi, ɗan Adam! Ɗan Adam butulu ne,tuntuni nake hankaltar dake akan Innar Balki amma kin kasa fahimta,saboda kin yi amanna ba zata munafunceki ba,wallahi Innar Balki munafuka ce ta ƙin ƙarawa, Kinsan barewa baza ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba,munafunci tsotsanshi ta yi daga nonan uwarta,kinga ke ba ƴar garin nan bace auroki aka yi baki san komai anan  ba, mu da aka haifa a cikin garin mu muka taso cikin sa sannan muka yi aure cikinsa mu muka san komai a cikinsa,kinga uwar Murja har ta koma ga Allah bata bar munafunci ba da shegen son Kuɗi,idan kinga tana naniƙe da mutum to abin hannunsa ta gani idan taga da damar  iya ƙwacewa to ƙwacewar za ta yi wallahi jinta take kamar bakanuwa wasu sun ce tafi Kanawa son kuɗi, koda ya ke ance mamanta asalin ƴar Kano ce,gata da annamimanci, kinga kuwa taya za ta haifi yara basu yo gadonta ba,ita Murjar tasan nasani sau nawa lokacin tana budurwa samari suke tattaɓa mata nonuwa a lungu suna bata kuɗi, to daya ya ta auri Zubairu ai duk munsan komai, abar kaza kawai cikin kwancinta amma idan da za a fara tone-tone wallahi kare ba zai ci ba, kar tasan kar ne, shiyasa idan kun zo tare take yin shiru kamar wata ta annabi"

Ta natsu ta yi shiru tana sauraran aminiyarta wanda sai yanzu ta fara tunanin ashe ta ɗaɗe da kwance zani a kasuwa bata sani ba,tana mata kallon biri ita tana mata kallon ayaba, lalle akwai matsala babba kuwa.Cikin sanyin murya Hannatu ta ce

"Aminiya ni abinda yake ɗaure min kai yanzu shi ne, dana kai mata kuɗin sai ta ce wai ba ita ba ce sai dai idan mai sunanta ya ce akai mata,dana kirashi don na sake tabbatarwa faɗa ya hauni dashi wai yaushe yabar gidan da zan dameshi da kira, wallahi faɗan nan daya min ya yi matuƙar ƙona min rai amma na shanye na tambayasa akan ta ce ba ita bace, buɗar bakinsa sai ya ce na ajiye mata kuɗin na baro ɗakin, Sannan kar nace zan tada balli saboda babu abinda zai haifar min illa ɗa marar ido "

" Kambatasiiii! Au haka ta ce miki wai ba ita bace! Lallai Murja sheɗaniya ce taƙin ƙarawa, wallahi tallah bazan yi kaffara ba duk wannan matsalar da kike samu da mijinki duk kitumurmurar ta ce, haddasana ce sosai, lokacin muna ƴan mata munsha zuwa har gida mu turketa idan ta haɗa faɗa,aminiya kinsan Allah rashin aikin maganin nan duk ita ce sannan akwai abinda take shiryawa akanki tunda ta fara haka, Allah yasa bata faɗama mijinki ke ce silar kasancewar ɗanki ɓarawo ba, don komai za ta iya inda dai za ta samu kuɗi"

Dafe ƙirji Hannatu ta yi tana salati, cikin raunin murya ta ce

"Wayyo Allah da na shiga uku na sake lalacewa ni Hannatu, anya bata faɗan mishin bama, don tun bayan faruwa al'amarin ya canjamin, kai amma Allah ya tsinema Murja, Allah ya isa tsakanina da ita, aminiya don Allah ki taimake ni" 

Shiru aminiyarta ta yi tana tunanin sai can ta dubi Hannatu ta ce

"Aminiya abu ɗaya zamu yi mu kama shegiya shi ne Karki nuna mata kinsan halinta, idan mijin naki ya ce ki bata kuɗin Karki mishi musu ki bata, Sannan dole mu sake sabon shiri babba akanta, Ina so ki canja malami tunda tasan duk malaman da kike zuwa wurinsu, keda kike ƴar Zaria a faɗa miki malamai, kawai mu koma KUSFA inda asalin malaman suke, amma kafin nan dole mu sake komawa ƙauyan Ciri-tawa wurin boka mai zamani, nasan za mu sha wahala kafin ya karya sihirin, amma mu yi ta bashi haƙuri har Allah ya ɗoramu akansa ya karya sihiri kinga shikenan ɗanki zai dawo daidai, sannan shawarata a gareki yanzu ki ajiye duk wani makaman faɗa da Zaytuna don yanzu abar a tausayi ce ita da mijinta, koda kika faɗamin Salim za ki ma aiki wallahi sai na ji tausayin Zaytuna ya ɗarsu a raina"

"Hmmmm Aminiya ai ni yanzu anshani na warke, yanzu bata baiwar Allah Zaytuna nake ba ta Murja nake sheɗaniya,naga ishara akan ɗana to mai ya rage illa miƙa wuya, faɗin hausawa da suke cewa *kukan kurciya jawabi ne mai hankali ke ganewa* ni nan na gane komai, kuma in shaa Allah daga yau ni da Zaytuna sai zumunci na daina biyewa mugun mijina da Murja har ta yarana zuwa gobe zan kirasu na shaida na daina faɗa da Zaytuna, su dinga zuwa wurinta sannan su ja yaranta a jiki, Kinsan Allah aminiya duk muguntana bazan taɓa yi ma Zaytuna abinda Murja ta aikata mata a shekarun baya ba"

Gyara zama Matar mai unguwa ta yi saboda ta gaji da zaman ta ce

"Wani abu ta aikata mata aminiya ? " 

"Sirri ne mai girman gaske, matsa da kunnanki ki ji don ko ƙuda bana so ya ji" 

Babu musu da masu da kunnanta, sai Hannatu ta faɗa mata ma matar mai unguwa lokaci guda ta waro idanu waje da sauri ya juyo tana kallon Hannatu ta ce

"Da gaske aminiya !" 

Jinjina mata kai Hannatu ta yi, ai nan take matar mai unguwa ta fara tafi tana salati da sallallami, ɗumbin mamaki ne ya cikata

"Lallai Murja ta kai ƙarshe a mugunta, kai ina bazan iya aikata haka ba ko akan kishiyoyina ne, bar ni na mallake miji amma ba irin wannan aika-aikar ba, da sauran imanina gaskiya " 

Miƙar da ƙafa Hannatu ta yi sannan ta ce

"ke dai bari aminiya ai ina jiran wata rana za to a yi ƴan tone-tone za ta sha mamakina wallahi, bara na koma gida, yanzu dai yaushe zamu ƙauyen Ciri-tawa kinga Jamilu an ɗaga tafiyarshi zuwa Lagos saboda nace ma Innayi kar a barshi ya je ko ina sai na zo, gwara mu je a karya asirin sai ya samu damar tafiya don tsoro nake kar ya je can Lagos ya yi sata su ƙonashi tunda haka suke ma masu sata"

Ɗan tunani Matar mai unguwa ta yi sai ta ce

"Ko zuwa gobe sai mu je kinsan da zafi ake bugun ƙarfe, Sannan Karki nuna ma Murja kinsan komai  ku ci gaba da kasancewa kamar a da, mu kuma sai mu san abun yi, Sannan ki dinga taimaka ma Zaytuna don Allah kinga mijinta ba gani yake ba" 

"Zan yi kamar yadda kika ce da yardar Allah, ai ba yanzu zan taimaka mata ba sai bayan na gama da wannan shegiyar, bara na wuce gida sai goban mu tafi" 

Sallama suka yi sannan tabar gidan, a hanya sai saƙe-saƙe take a zuciyarta ,duk shawarar da aminiyarta taba babu wanda bazata ɗauka ba illa taimaka ma Zaytuna don a jininta  tsanar Zaytuna take, ta dai faɗa ma aminiyarta za ta nemi yafiyar Zaytuna ne don ta ji daɗin taimaka mata.Da Zarar ta koyama Murja hankali za ta dawo kan Zaytuna da yaranta wannan alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta babu gudu babu ja da baya. A haka tana tafiya tana zancen zuci ta iso gidansu.

Koda Alhaji Zakari ya dawo gidan da yamma bata nuna masa komai ba ko kuma fushinta sai ma tarbarsa da ta yi da fara'a kwance a fuskarta, shima sakin tashi fuskar ya yi har suka ɗan taɓa hira amma kowa cikin zuciyarsa da abinda yake rayawa... ✍️

              🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangarensu Mammin Hujayrah basu da wata matsala a yanzu sai ma farin cikin da suke ciki na albishir da baba Musa ya yi musu akan zai tafi da Salim can garin Zaria ya tayashi kasuwanci sannan ya ci gaba da Karatunsa a can tunda ya kammala JSS3. Sosai su Abbu suka shiga farin ciki mara misaltuwa har da ƙwalla Abbu ya zubar don farin ciki, yanada burin yaransa su yi karatu mai zurfi, amma Allah ya yi ikonsa babu yadda ya iya da hukuncin Allah, ƙaddarar zamantowansa makaho yasa wasu abubuwan sai dai ya ji amma bashi da Ikon aikata wani abu a kai. Allah kenan mai yadda ya so ga bawinsa.... ✍️

                🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida Dubu-Gubi Housing Estate,Bauchi State. Nijeriya*

A ɓangarensu Hujayrah bayan sun shigo cikin estate ɗin babu abinda take sai kalle-kalle, ta taɓa can ta duba can ta leƙa can, kai har da ƙwanƙwasa wani gate Hujayrah ta yi saboda tsokana, sai da baba Uwani ta yi mata magana sannan ta natsu suka ci gaba da tafiya. Sosai estate ɗin ya haɗu baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye masu daɗin sauraro,ga bishiyu sai kaɗawa suke suna bada sassanyar iska mai daɗi. Sun ɗaɗe suna tafiya daga bisani suka tsaya a wani gate wanda yafi kowanne gate kyau da tsaruwa a wannan estate ɗin,baba Uwani ce ta kalli Hujayrah ta ce

"To Hujayrah Allah ya yi mun iso gidan, Ina so ki shiga da ƙafar dama bakinki ɗauke da bismillah, Allah ya haɗaki da alkhairan dake cikin gidan nan ya kuma kareki daga sharrin dake cikin gidan nan" 

Hujayrah da ta tsaya tana  kallon gate ɗin gidan bata san me yasa ba zuciyarta ta yi Na'am da gidan sannan bata jin ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi,   murmushi ta saki lokacin da baba Uwani ta kammala mata addu'a ta ce

"Ameen ya Allah, zuciyata ta yi Na'am da gidan nan Baba Uwani" 

Ƙarasawa wurin gate ɗin suka yi sai baba Uwani da ƙwanƙwasa, can bayan minti biyu sai aka buɗe ƙofar gate ɗin, wani mutum ne baƙi hannunsa riƙe da carbi ya buɗe musu, yana ganin baba Uwani ya washe baki yana cewa

"A'aaahhh ƴan tafiya ne suka dawo har da wata ƴar budurwa mai kyau, sannunku da zuwa" 

Matsa musu ya yi suka shigo cikin gidan, kamar yadda baba Uwani ta ce Hujayrah ta shiga da ƙafar dama haka ta yi bakinta ɗauke da bismillah, a nan baba Uwani ta tsaya suna gaisawa da mai gadi ita kuma Hujayrah ta tsaya kallon gidan da mutanan gidan, maza da  sai aikinsu suke kowa bai shiga harkar ɗan uwansa. Gidan babba ne sosai don har yanzu akwai tafiya kafin su Ƙarasawa cikin gidan, bayan baba Uwani sun gaisa da mai gadin sai suka ci gaba da tafiya, kamar waje haka Hujayrah ta yi ta kalle-kalle, sosai gidan ya burge Hujayrah har ta kasa haƙuri ta ce ma baba Uwani

"Baba Uwani anya ba a wata ƙasar muke ba?" 

Dariya baba Uwani ta yi don taga alama Hujayrah akwai ta da ɗankaran surutu, suna tafiyar ta ce 

"A'a muna cikin ƙasarmu Nijeriya Hujayrah da alama ke ƴar fari ce ko" 

Da sauri Hujayrah ta ce

"A'a Ni ce ta biyu a ɗakinmu Yayana Mansur ya rasu wurin almajiran,mammina ta ce ta ji mutuwarsa sosai lokacin, duk a yaranta tafi sonsa,amma Allah ya karɓa abunsa, ni kuma Abbuna yafi sona kuma nima nafi sonsa akan mammina saboda ɓata biye min wai na cika surutu, amma Kinga Abbuna hahaha! Yana matuƙar son surutuna shiyasa wani lokacin idan na ce zan daina surutu na koma shiru-shiru sai na tuna Abbuna yana son surutuna sai kawai ci gaba da abuna, Kinsan baba Uwani lokacin da Abbuna yake gani har faɗa yake taremin ba kamar mammi ba, cewa take su dukan tunda nina tsokanesu"

"Ruwan sama kenan wannan zuba haka shaaaaa! Shaaaaaaa! Sai ka ce zuban ruwan sama babu ko ɗiga aya Hujayrah dole mammi ta ce kin cika surutu, wannan shi ake kira da faɗi ba a tambayeka ba, tambaya ɗaya na miki amma kin kawo min wasu abubuwan da ma ban tambayeki akai ba"

Dariya Hujayrah ta yi sai suka ci gaba da tafiya, wani gate suka gani ƙarami bai kai na farkon ba,ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin baba Uwani ta yi sai wani mai gadi ya buɗe amma wannan yafi ɗayan mai gadin yarinta, shiga suka yi sai baba Uwani ta tsaya gaisawa da mai gadin, ɓata fuska Hujayrah ta yi cikin ranta ta ce 'wannan baba Uwanin ta cika son gaisuwa wallahi, ni ga ƙosa mu shiga ciki naga daular dake cikin gidan amma ta tsaya faman gaisawa dasu' ci gaba da tafiya suka yi wanda basu ɗaɗe ba suka shigo cikin gidan,gidan sama ne mai hawa ɗaya da ɓangarori biyu sai gidan ƙasa guda biyu fenti iri ɗaya ne a gidan ga flawowi masu kyawun gaske wasu maza biyu suna saka almakashi suna gyara flawowin sai suka bada wani shape mai kyau, a tsakiya gidan wani katafaran wuri ne an ginashi a cikinsa ruwa ne, ga wani dogon ƙarfe mai huji-huji yana fitar da ruwa. 

Direct baba Uwani ta ce su fara wucewa masaukinsu tukunna idan sun yi wanka sun sake kaya sai su shiga ciki. Rai bai so ba haka Hujayrah tabi baba Uwani sashensu na masu aiki, babba ne sashen nasu masu ɗakuna da yawa mata ne sai shiga da fice suke a sashen, wasu ƴan mata wasu masu shekaru irin zawarawa wa'inda suka taɓa aure suka fito. Sai gaida baba Uwani matan suke da alama ita ce mai shekaru a cikin masu aikin, wani ɗaki suka shiga ita da Hujayrah nima na bisu da kayan ɗaukar rahotona, ɗan madaidaici ne ɗakin da bayi a ciki, zama baba Uwani ta cema Hujayrah ta yi sannan ta fita ba jimawa ta zo musu da abinci,cin abincin suka fara yi sai baba Uwani ta shiga wanka babu daɗewa ta fito Hujayrah ita ma ta shiga wankan, bayan ta fito sun shirya sai Baba Uwani ta dubi Hujayrah ta ce

"Hujayrah bara na fara baki ɗan labarin matan mai gidan nan sai mu ta fi wurinsu muga wacca za ta ɗauke ki a aiki, matan Alhajin biyu ne uwar gidan Sunanta Hajiya Izzatu Allah bai bata haihuwa sai dai tana riƙon yaran ƴan uwanta guda uku, namiji ɗaya sai mata biyu dukkaninsu basu yi aure ba, sai ta biyun Hajiya Mubina ita ce mai ƴaƴa, haihuwanta uku da Alhaji namiji ɗaya wanda baya ma ƙasar amma ana saka ran sati na sama zai dawo, sai mata biyu amma autarta ce take hannunta bai bima namijin tana wurin ƙanwar Alhaji kasancewa ita ma bata da yara duk sun koma. Duka matan Alhaji suna da kirki sosai musamman uwar gidan, itama ta biyun tanada kirki sai dai bata cika son mutane kamar uwar gidan ba, Sannan muna kiran uwar gidan da Hajiyan Sama, amaryar muna kiranta da Hajiya Momma, yanzu taso mu je na fara kai ki wurin Hajiyan Sama ko za ta ɗaukeki "

Miƙewa a tare suka yi, baba Uwani na gaba Hujayrah na biye suka bar sashen,gidan saman suka nufa Hujayrah na biye da ita. Da sallama a bakinsu suka shiga falon, matar dake cikin falon tana goge-goge ta amsa. Baba Uwani ta ce

" Zainu Hajiyan Sama na ciki ne?" 

Wacca aka kira da Zainu ta ce

"Eh Baba Uwani ashe kun dawo" 

Fuskarta da murmushi Baba Uwani ta ce

"Eh ga ƴar ɗan uwana na zo da ita" 

"Allah sarki to sannu da zuwa" 

Murmushi Hujayrah ta mata, hankalinta na ga kallon dukiyar da aka kashema ɗakin kamar ba za a mutu ba, falon babba ne sosai ga royal cushion milk da ratsin gold sun yi circle Sai center table da flower a sama, ga plasma TV babba an kunna kallo, a nan idon Hujayrah suka shantake tana kallo, Baba Uwani ta ce ta biyota, babu musu kamar raƙumi da akala haka suka haura sama, wani sashe suka nufa da sallama a bakunansu, wata babbar mace ce ta amsa musu lokacin da za ta kai ayaba a bakinta, ta ɗan manyan amma akwai gayu a zuciyar Hujayrah ta ce'Ga irinsu Innar Harira da Innar Balki sai shegen son gayu' Fuska Hujayrah a murtuke hakanan zuciyata taƙi aminta da matar saboda kallon farko da ta mata ƙirjinta ya yi mugun bugawa. A ƙasa suka zauna baba Uwani na gaisheta, ita ma ta gaidata tana russunar da kanta. Babu yabo babu fallasa Hajiyan Sama ta amsa mata, cike da girmamawa Baba Uwani ta ce

"Hajiyan Sama ga ƴar ɗan uwana na kawo aiki, idan da hali a ɗauke ta" 

"Babu wuri a nan Uwani sai dai ko wurin Hajiya Momma" cewar Hajiyan Sama tana ƙarema Hujayrah kallo nan take ta ji yarinyar bata yi mata ba. 

Miƙewa suka yi Hujayrah ce farkon fita tana murna don bata son matar, sai baba Uwani ta fito ta kalli Hujayrah ta ce

"A'ahhhh ya naga fuskarki da fara'a madadin naga damuwa don bata ɗaukeki aiki ba" 

Wani murmushin ta saki sannan ta ce

"Ai daɗi na ji da taƙi ɗaukana aiki wallah Hajiyar nan batamin ba, zuciyata bata sonta, kawai ki kaini wurin Hajiya momma, Ina ji a jikina za ta soni " 

Sheƙeƙe Baba Uwani ta tsaya tana kallonta, kai wannan yarinyar akwai daru, ci gaba da tafiya suka yi, wani ɓangaran suka nufa har ƙofar falon, sallama suka yi sai aka amsa musu murya ciki-ciki, shiga ciki da wata sallama a bakin, wata kyakkyawar mata ce fara tas kamar balarabiya hannunta riƙe da jarida tana karantawa, idanunta da ƙananun tabarau don ƙara ƙarfin ido fari tar dashi ta sake amsa musu sallamar, a ƙasa  baba Uwani ta zauna amma Hujayrah Direct wurin da Hajiya momma take zaune  a saman kujera ta  samu wuri ta zauna Fuskarta ɗauke da murmushi (My Esteem fans Pls ku jama Hujayrah kunne kar ta ce za ta yi ɓarin zance a nan, don yadda take murmushin nan akwai abu a bakinta🤭🤭🤭)

Hajiya momma murmushi ta sakar ma Hujayrah sai ta dubi Baba Uwani ta ce

"Ina muka samu ƴar budurwa yarinya mai kyau haka Maa shaa Allah Tabarakallah" 

Sai a sannan ne hankalin baba Uwani ya kwanta jin furucin Hajiya momma don da farko gabanta ya faɗi sosai saboda yadda Hujayran ta yi ya tsorata ta, ita a tunaninta ƙila Hajiya momma ta koresu tunda bata son mutane saboda yadda Hujayrah ta yi, fuska ɗauke da murmushi baba Uwani ta ce

"yarinyar ɗan uwana ne" 

Duban Hujayrah Hajiya momma ta yi tana cewa 

"Beauty queen ya sunanki?" 

Zama Hujayrah ta gyara don ta ji daɗin bada labari ta ce

"Mammi ni sunana Hujayrah ɗiyar Abdullahi jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa" 

Haba mai Hajiya momma za ta yi inba dariya ba, cikin dariya ta ce

"Yau naga Ikon Allah ni Mubina Hujayrah yaushe zan iya riƙe sunayan nan,kenan kakarki tsoran mutuwa take" 

Za ta fara magana sai ga sallama mai gidan, juyowa ta yi tana kallonsa da murmushi a fuskarta ita dai ta rasa meyasa take kallonsu kamar iyayanta, kujerar da Hajiya momma ta zauna shima nan ta zauna tana cewa

"Meya sakaki farin ciki haka tun daga waje ake jin dariyarki" 

Murmushi ta yi tana duban Hujayrah ta ce

"Ai ɗiya na samu mai barkwanci yanzu take faɗamin sunanta, her names were too long har da cewa jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoron mutuwa shi ne ya sakani dariya" 

Shima dariyar ya yi yana cewa 

"To fa tsoran mutuwa kuma wa kenan kakarki?" 

"Eh Abbu ai Abbu ina faɗa maka Kakulleta akwai tsoran mutuwa,akwai wani lokaci ana hira ake zancan mutuwa buɗar bakin Kakulle ta ce ai ita bata tsoran mutuwa ko yanzu ta zo a shirye take, habawa alla-alla nake dare aya yi na yi shigar fararan kaya na zo na ji da gaske take ko kuwa a fatar baki ta tsaya, kasan me Abbu"

Girgiza mata kai Alhaji ya yi yana murmushi ita ma Hajiya momma girgiza kan ta yi. Sai Hujayrah ta ci gaba da cewa

"Hmmmm farar hodana mai kyau na ajiye, daman Mammina ta ɗinka sabon hijabinta fari na ɗauko, a ɗakin Kakulle nake kwana tun da rana na samu buhu dogo na cusa tsumma da yawa sai ya yi kamar mutum, sai da na fakaici idonta sai na kai buhun ɗakinmu a ƙarƙashin ƙaramin gadon da nake kwana na ɓoye, hahahaaaa! Cikin dare Kakulle ta yi nisa a baccinta har ta fara waƙarta na mutan da ji kake ƙhurrrrr!!! Ƙhurrrrr! Sai na tashi daman ba bacci nake ba na lallaɓa na ɗauko buhun a hankali na ɗora a inda nake kwana, sai na ɗauki farin hijab ɗin Mammi na saka, na shafa hodana na koma wata iri dani, saɗaf-saɗaf na fita daga ɗakin, daman a ƙa'idar Kakulle cikin dare tana tashi fitsari, sai da na bari ta fito fitsari sai na yi sauri na shiga ɗakin na kunna wutar ɗakin bayan na yamutsa fuskanta, na ware idanuna da haƙorana wa je, da sallama a bisa labɓan Kakulle ta shigo ɗakin Haba ai cak! Ta tsaya jininta  ya fara rawa, Abbu ina faɗa maka wata kalar murya na yi amfani da ita na ce *Yake Bil Adama lokacin tafiyarki ga mahaliccinki ya yi* , ai nan take na ji ƙarar tusa,ji kake ɓar! Ɓar! Ɓaɓarrr!!! Nan da nan ɗakin ya turnuƙe da waru, Kakulle birkicewa ta yi tana don Allan da ya aikoka ka yi haƙuri wallahi ina son raina! Ka taimake ni don Allah, wayyo Allah! Ƙara ɗaya muryana na yi ina cewa *bake kika ce a shirye kike ba* *to yanzu mun ɗaukarki tunda kin shirya* , murya na rawa Kakulle ta ce wallahi suɓutar baki ne, duk don hirar ta yi daɗi ne yasa na ce haka amma har cikin raina wallahi ba haka bane, kashe wutar ɗakin na yi ai nan take Kakulle ta tsandara ihu, ni kuma da sauri na cire hijab na tura ƙarƙashin gabo na jaye buhun tsumman na maida ƙarƙashin gado kafin mutanen gidan su zo na kunna wutar ɗakin ita lafiya Kakulle mai ya sameki, kasan abinda na gani kuwa Abbu"

Alhaji ta girgiza kai, sai ta ci gaba da cewa

"Wallahi Kakulle na gani kwance cikin kashi male-male tana iyo ga shegen ɗoyi, tun daga ranar idan an fara maganar mutuwa tashi take tabar wurin" 

Dariya sosai suka tuntsire suna yi, ita Hajiya momma har da riƙe ciki har ta baba Uwani sai da ta dara, suna cikin dariya a banko ƙofar, da sauri suka waiwaya ganin waya buɗe ƙofar haka, wata kyakkyawar yarinya ce wacca bazata gaza shekara 15 ba ta shigo da uniform a jikinta, fara ce sosai kana ganinta kaga Hajiya momma, cike da shagwaɓa ta tako har inda iyayanta suke, za ta zauna saman kujera sai ta yi saurin Miƙewa tana kallon Hujayrah ta ce

"Ammie ina muka samu model" 

"Aiki aka kawota gidan nan, she is so friendly Razina, you will like her" cewar Hajiya momma tana kallon Hujayrah da murmushi 

Buɗar bakin Razina ta ce... ✍️





*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***














Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol