Free chapter 路 Read without an account
Chapter 12
*Wasu burukan rayayyu ne, yayin da wasu burikan kuma suke zamowa marigaya, wani burin yakan kai labari, wani kuma ya kan zama tamkar jarumi a filin daga, ya kashe ko a kashe shi, kai kowace rayuwa ma tana da nata burin, sai dai wasu su kan samu kaiwa labari, wasu kuma sai dai a ranar gobe al'kiyama*
_Akwai complete na labarin a documents akan 1k kacal. Ga mai Bukhata yayi magana akan wannan layin ***_
...........Yarima Gibson ya zuba min ido cikin wata irin mayata da soyayya tamkar yaga wata bakuwar halittar da ta bayyana a gareshi yanzu wadda Bai taba gani ba. Abinda ya bakan ta min Rai don bana son wani namiji yana kusanto inda nake bare ya tabani, bare kuma shi Gibson da irin daukar da yayi min har hucin nunmfashin sa najiyo Akan fuska ta
Nima na zuba mishi nawa manyan idanun cikin takaicin abinda yayi min muka SHIGA kallon kallo inda na SHIGA fasalta suffar yarima Gibson kyakkyawan mutum Wanda shima ya fita daban a cikin Ahalin gidan su, duk kuwa da kasancewar kyauwu irin na Ya'yan sarkin to yarima Gibson ya zarta su don shima kamar ba Dan Nigeria ba fari ne tas har yellow yellow yakeyi ga cikakkiyar suffa ta maza da Bakin gashin Kai da kwantaccen saje da manyan idanu da gashin idanu masu kyau. Kai karshen magana dai irin namijin Nan ajin farko da ake cewa first class
A yadda Onye ta tab'a sanar Dani Ya'yan sarakunan da suka so yarima Gibson basa kirguwa, don harda wacce tasha poison wai zata mutu don yace baya son ta, duk dashi a wurin shi mace ba komai bace, baya shiga sabgar mata wai kar su raina shi, ba kowace mace ke burge Gibson ba, yayin da mahaifiyar sa kuma ta shiga Nema mishi yayan manya masu rike da madafun iko dama masu mulki irin su, Amma shi yace duk basuyi mishi ba,
Akwai wata Yar sarkin garin akwai ibom da ta so yarima gibson tamkar zata hadiye shi sai dai kash! Shi bai taba sako ta a lissafin matan da zai iya rayuwa da ita ba, a haka wannan sarauniya take ta wahala wurin Gibson har dai ya fada mata shi fa bai taba son ta ba tayi hakuri, duk yadda akayi da yarima Gibson yace ba zai iya auren ta ba don babu soyayyar ta a ransa. Uban ta yayiwa Gibson alkawarin dukiya da sarauta amma ya kafe akan bakan shi, karshe yarinyar nan bakin ciki ne ya kashe ta, sai dai mutuwa tayi saboda tsananin son da take mishi, kasancewar ta ya daya tilo a wurin Ubanta da ta mutu Ubanta yace tunda yarima yayi mishi sanadin Yar shi zai ga abinda zai faru don ba zai taba yarda son shi ya kashe mishi yarshi ba saboda kiyayyar da Yake Mata to shima zaiga abinda zai faru.
Babu wanda ya dauka furucin wannan sarki zai zama matsala, Dare daya Allah ya hada yarima Gibson da wata yarinya da yaji duk duniya in ba ita ba sai rijiya, da yarima Gibson ya samu yarinyar nan wadda yake masifar so wata yarinya ce itama Yar gidan sarauta wadda suka so juna kamar su hadiye kansu amma abin mamaki ranar daura auren su amarya ta mutu bayan lafiyar ta lau don har shagalin party anyi, kuma ta mutu ne da cikin ta na watanni uku don tazowa yarima yazaman gwaji kuma bata rufe wata guda ba ta samu ciki shine aka tashi maganar aure, sai dai ranar aure aka wayi gari amarya ta mutu da cikin ta,
Wannan tashin hankaki shi ya kusa kashe yarima Gibson don ya kwallafa ransa ga cikin matar sa mai mutywa,
Son da Gibson yake yiwa amaryar shi yasa ya kwanta ciwo Mai tsanani Wanda ya haifar mishi gagarumin ciwon zuciya wanda kad'an ya Rage ya kwanta Dama wato mutuwa
Abinda ya dauke hankalin yarima Gibson daga kan duk wata mace da zai kalla da sunan burgewa ko yaji zuciyar shi ta amsa Akan ta har ma ya Daina tuna zaiyi Aure Nan gaba, tun iyayen sa na magana da kawo mishi yan mata har suka gaji suka kyale shi, sai gashi kwatsam kallo Daya yayi min ya manta da jefarwar da yayiwa mata irin wadda ake watsarwa a maliya
Azahirin gaskiya yarima Gibson bashi da wata makusa ta kowane fuska gashi dai kyakkyawa ajin farko gashi jinin sarauta gashi Kuma Mai tarin dukiya me Kuma yayi saura? A fuskar wasu mutane kenan wasun ma kuwa irin su Amaka da Maazi Nkem Wanda suke cikin farin ciki da murna yau su kuwa wace irin sa a ce dasu da har suka haifo Yar da zata taka gidan igwai sarki da sunan matar yarima Gibson?
Inda Kuma muka samu sabanin Ra'ayi Kenan don Ni ko ga farcen yatsana banji yarima Gibson ba bare ya burgeni a ido har yayi nasarar SHIGA zuciya ta inji Ina son shi, ko kusa Haka Kuma ko Alama Ni ba Zan taba yarda ayi min wannan banzar Al adar da suke tutiya ba badon ba Zan iya yarda ayi min ba tunda Ni dai ko hannu na wani namiji Bai taba Rikewa ba sai dai don kawai ina tare da kawaye Hausawa masu nuna min haduwar namiji da mace ba daidai bane matykar ba aure ne ya hada su ba, bana Jin son yarima Gibson a Raina ba Kuma zan so shi ba ko da kuwa mutanen garin Legos da imo duka dangin sa ne ni dai bai kwanta min a rai ba,
Na zame jiki na daga Rukon da Gibson yayi min na juya zan wuce, Ina Shirin barin wurin ne naji wasu Mata da na lura sune suka daura min murjanan nan a hannu da kafa, da sauri suka biyo bayana suna gaishe ni tare da fada min su hadimai ne a gare ni, ban kula su ba na wuce suka biyo baya na suna yafa min wani mayafi irin na sak'i suna kuma watsa min turare mai kamshi har zuwa cikin gidan sarautar, inda naji haushin su ya Kara kamani Ina Shirin balbale su da masifa ne naga sun shige dakin matar sarkin wato uwar su Gibson da onye har tsakiyar dakin ta Wanda ya gaji da kayatuwa da kayan kawa da ado irin na sarauta
Kan kace me? Suka shigo fito da wasu Kaya na daban suna Shirin saka min inda na Gane sun Raina min wayo tunda har suke Shirin kwabe min Riga gani zaune
Na Mike a fusace Ina zuba masifa suna bani hakuri suna sunkuyar da kawuna kamar wasu munafukai sai ga Mah wato matar sarkin itace ta sani nayi shiru ta Kuma nunawa Matan Nan kofar fita da hannunta suka kuwa fice suna sauri ita Kuma ta Soma saka min kayan Wanda ta Kare da Rataya min wasu murjanai a wuyana da Kuma Dora min wasu a kewayen gashina
Sai ga su Amaka sun shigo wadda ke ta murna da Jin Dadi Ni Kuma na Rasa Gane duk ana me ake min wannan tarairaya?
Haka biki ya Kare Amma ba tare da Ni ba don an hanani SHIGA cikin yan Mata Wai girma ya same ni na fita a layin yan mata zan zama matar yarima Gibson
Ban tsinke da wannan lamarin ba sai da muka tashi tahowa inda aka lodo kayan akwatuna na garari da kasaita wai kyautar yarima Gibson ce zuwa gareni, aka hado mu da kaya tare da dukiya Mai yawa Wai kyauta ce daga yarima Gibson Kuma Yana Nan Zuwa mu gana ko ince mu fahimci juna
Duk wannan Abu da Yake faruwa ban San komai akai ba sai da muka Zo gida naji labarin da Amaka ke fadawa Yan uwana su Sony da Emmanuel Wai Ni din na shigo Duniya a sa a inda yarima Gibson ya ganni ya Kuma zabeni a matsayin matar Auren shi
Su Sony ma murna suke son suna ganin ni kam bayi dace tunda zan auri princess in kuma haifo princess in Kuma aama matar princess 馃ご
Dukan da wannan magana ta Amaka tayi min har ciwon Kai naji Yana sauko min ta Ina Ni zan iya yarda da wannan abubuwan da na Dade da tsana na bikin Auren Yan yaren mu? Kuma ma Ni babu wani Gibson a raina bare kaunar shi, a gaskiya zuciya ta ta jima a cikin abinda Amaka take gudu wato Hausawa da addinin su, zuwa yanzu na soma nutsuwa da Hausawa da addinin da suke bi Don na gamsu mai tsafta ne,
Sai kawai na kudirewa Raina da zuciya ta Koda za ayi me ? Ba Zan taba Auren wani Gibson ba ni ai ba Yar sarki bace su kuwa basa Aure sai Ya'yan sarakuna to yaje ya Nemo wata Yar sarkin amma ba Ni ba don kuwa banayi bana kamar inayi...............
Labarin GARWASHI Nan daban yake da sauran Kar ku sake ayi tafiyar nan babu ku
Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI馃グ
_Masu tambayar farkon labarin suyi following channel namu zasu samu labarin daga farko_