Free chapter · Read without an account
Chapter 3
Ƙazafi
Page 3
By
Ɗan Bugaje
Tunda ta shiga unguwar ta sheda ta baro yankin talakawa ta shiga layin masu hannu da shuni, saboda wata irin sanyayyar iska da ta ziyarceta sakamakon manya -manyan shukokin dake zagaye da kowane gida, masu ƙamshi da kyau gwanin birgewa, kowane gida fayau da haske kamar ba dareba, domin kuwa duhu yayi sosai wani waje anngama sallar issha'i wani wajan kuma yanzu akeyi.
Unguwar shiru tayi tsit babu kowa kuma kowane gida akulle yake gam, haka kawai sai taji ƙirjinta yana bugawa Dam! Dam!! Da ƙarfi kuma da sauri, amma sai ta aro jarumta na yafama kaita ta soma buga ƙofar wani gida mai kyan gaske, bugu biyu tai mai gadin yazo ya buɗe yana cewa “waye a nan”
Kuka sireenah ta fashe da shi inda ta kuma miƙamasa takardar tana cewa "Baba don Allah ina neman taimako ne mahaifiyata ce wallahi aka kwantar da ita Asibiti bamuda abin sai mata magani, kuma ance zata iya mutuwa idon ba akawo magungunan ba, kaiman rai na shiga cikin gidan nan nasar dasu halin da nake ciki inga ko zan sami wani abu awajan su.......... "
"ke imana shiru munafukar banza da wofi duk irin salon makircinku da yaudara babu wanda ban haddaceba, da irin haka kuke isa wajen masu gida kuna lashe masu yara, to ba anan ba wai baisan mabaratan nan duk mayuneba, haka simi -simi dake kamar ta Allah yanzu ƙarfe takwas na dare kina bin gidan mutane, sai kin samu mai yimaki dukan tsiya a daren nan maza ware bar nan tun kafin na ɓaɓɓallaki,. "
Ya kai ƙarshen maganar yana nufota kamar zai daketa yana mai zare jajayen idanuwansa, da sauri ta matsa ta bar wajen har tana haɗa hanya, haka tadinga bin gidaje tana bugawa amma ko ɗaya bata samu nasarar shigaba bare har ta samu taimakon da ta fito nema, zaunawa tayi a ƙofar wani gida mai kama da ginin turawa tana mai da lumfashi da huta gajiya domin ƙafafunta sunyi sanyi ta gaji lakwas.
Batai minti biyar da zamaba sai ga wasu samari su ukku sun iso wajen masu kyau da kwarjini ga hutu da naira da suka saka fatarsu wani sheƙi na daban ga wani ƙamshi da suke na manyan turaruka da yagama gauraya da ƙamshin arziƙi, bita suke da wani irin kallo mai kama da na sha'awa da birgewa kallo ba na wasaba tsuru sukai mata kamar zasu lasheta.
Cikin ɗaga murya da faɗa faɗa ɗaya daga cikin su yace "ke mekiki anan? Waima daga ina kike? ".
Take tsoron su ya kamata sakamakon jin dakakkar murya mai firgita ƴan mata mai sanyi da daɗi irin wacce hutawa ke haifarwa, sai kawai ta zube gabansu tana mai ɗimaucewa tace "Don Allah ku taikakeni ku ceci rayuwar mamana tana asibiti kwance babu rai ajikinta kuma bamuda kuɗin maganin da za'a dubata ".
Wani shu'umin murmushi ɗaya daga cikinsu yayi kafin ya motso kusa dani sosai ya duƙa kamar yarda nake duƙe a ƙasa har ina iya jiyo fitar lumfashinsa kafin yace
" ƴar kyakyyawa kina sona? "
Dam! Dam!! Ƙijina ya hau luguden bugun ukku ukku na zaro idanuna waje tare da miƙewa, nace "ina ina da wanda nakeso, ta ƙarashe cikin in ina,
"Wanda kike so baida wani amfani agareki tunda bazai iya fitar dake amatsalaba don haka sonsa babu riba kirabu da shi kawai ni zan maki komai kikeso kinji. "
" Don baisaniba shiyasa amma da nasanar dashi zaiman ko".
"To asanar da shi mana , ko da yake manta da shi kawai ni zan maki komai rabon mu haɗune yasa kikazo ki aminta da ni kawai zaki zama zinariya acikin ƙawayenki ina da kuɗi kuma antaraman kuɗi zaki shana, zan baki lambar wayata da adreshina duk sanda na buƙaci ganinki sai kizo kawai muji daɗinmu zanso ganinki kusa dani akeɓance kina da kyau my pretty. "
" inna lillahi wa inna ilaihir raju'un Allah yayiman tsari da aikata saɓon ubangiji, kuma zan maku addu'a Allah ya shiryaku ku gane gaskiya amma ni ba irin matan da kake nufi bace don haka kurabu dani "
Takai ƙarshen maganar tana yin baya da su, tafiya da ta fara itace ta ida hargitsasu domin ko ina najikinta motsawa yake, hakan yasa sukai saurin zagayeta ɗaya na cewa" wallahi bazaki bar nan ba sai kin gamsar da mu koda ta ƙargin tuwo ne, don haka zaɓi na gareki ko ki karɓi kuɗin mu ko karki karɓa mudai abinda mukeso shi zamuyi kuma babu wanda ya isa ya hana".
Rasss! Gabanta ya buga tsoro ya sake mamaye zuciyarta, tashin hankali ya baibaye kwakwalwarta ta rikice ta rasa abinyi.
" Ai khamis baka san wani abuba yadda nakeji ajikina idon har ban kasance da wannan yarinyarba to yau sai nayi zazzaɓi. "
Ɗayan da bayi magana ba yafito da kuɗi ya miƙa mata yana cewa " ga wannan ki rage zafi ki bamu haɗin kai muyi abinda zamuyi salin alin ki tafi tun kafin muyi da ƙarfi mu illataki".
"Don Allah kuyi haƙuri wallahi bazan sake zuwa nan ba banason kuɗin gida ma zan koma dare yayi. "
" Ai ko baki buƙatar kuɗi mu munada buƙatarki don haka dole ki barmu muyi abinda mukeso, sauban wane gida zamu kaita? ".
"Mukaita gidan su fahat don naga mai gadinsu bai dawo daga masallaci ba. "
Jin haka yasa jikin sireenah ya fara rawa kamar ana kaɗamata gangi ta buɗe baki da nufin rafka ihu, sauban yayi sauri ya toshe bakin suka ɗauke ta taga- taga sukai cikin gadan da ita, sai mutsu -mutsu take amma ta gaza kwacewa kuma bakinta rufe bare tai ihun neman ɗauki, suna daf da shiga cikin wani lungu da yake acikin harabar gidan sukaji anyi (hon) abakin gyat.
Cikin tashin hankali da tuɗewa fahat ya kalli sauban yace "sauban ga dady nan ya dawo ".
Khamis zaiyi magana sukaga kan motar ya fara shigowa babu shiri suka ajiye sireenah suka shige cikin lungun aguje suka ɓuya,
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya sireenah ta sauke tana mai godiya da hamdala ga Allah da ya kawo mata ɗauki, ta gyara tsayuwarta tare da gyara hijabinta, dai dai nan dalleliyar motar tayi fakin a tsakiyar gidan, wani hamshakin mutum ne dogo baƙi mai ƙiba da tunbi ya fito da ga motar, fuskar sa ɗauke da glass fari, fuskarsa ɗauke da mamakin ganin sireenah a cikin gidan da wannan daren don haka inda take ya nufa.
Atake tsoron sa da shakkunsa suka kama sireenah ta ruɗe tana neman abin yi da kalaman da zata furta su kareta.
" ke wacece nan, daga ina, mikike man acikin gida cikin wannan daren?,. "Sune tanbayoyin da aAlhajin ya furta baki daya yana mai kafeta da ido irin na rashin yarda.
" um, um in aiyi, haka tafara in ina kafin dabara ta zo mata tai sauri miƙamasa takardar Asibitin tana cewa “ina neman taimako don Allah ka taimakeni ina cikin damuwa da tashin hankali mamana zata mutu ina buƙatar taimako tana gadon Asibiti ayanzu haka,
Bai amsa takardar ba kuma bai yadda da abinda tace ba sai kallon tuhuma da zargi yake binta da shi, kafin ya hau kiran sunan mai gadin gidan "sanbo! Sanbo!! Sanbo!!! ".
Haka ya dinga kiran sunan mai gadin cikin ɗaga murya, take mai gadin ya iso yana faɗin " gani Alhaji Allah kasa dai lafiya ranka ya daɗe. "
" Taya kabari wannan ta shigoman gida acikin wannan daren ", yakai ƙaishe yana nuna sireenah dake ta rawar jiki
" wallahi Alhaji basan ta shigoba dawowa ta kenan daga masallaci ".
" To har sai yaushe zan ɗinga shedama ka kulle mani gida idon zaka sallah ".
"Dama Alhaji fahat ne yace nabarshi buɗe zai rufe idon ya shigo don zaune na barsu aƙofar gida suna fira shida su khamis. "
" To adai ƙara kiyayewa inba hakaba kayi ta aikinka, ni wannan yarinyar ban yarda da itaba, yakai ƙarshe yana nuna sireenah kafin yaci gaba da cewa kakorata har sai kunbar layin nan kafin ka dawo, kasan almajiran nan duk ƴan leƙen asirine da sunga sirrin ka sai dai kaji da dare an hauromaka, ko idon sunga wawuyar ajiya su ɗauka, sam ni banyi amanna da itaba. "
"To ranka shi daɗe, ya faɗa yana tasa ƙeyar sireenah gaba,
"Ke kuma na haddace fuskar ki idon wani abu ya faru agidan nan sai na ganoki ko ina kika shiga na ɗai ɗaita rayuwar ki, maza bacceman da gani ".
Fahad ya kalli sauban cikin wata kasalalliyar murya da tai wani irin yanayi yace "sauban ya zanyi banaso ta bar gidan nan batare sa na cika burina akantaba, ina jima ni sonta nake don wani irin bugu zuciya ta keman saka kunnanka kaji, idon ta fita bansan inda zan sake ganintaba kuma zan wahala wallahi. "
" Ai kawai musata a tsaka mai wuya "cewar khamis yana wani shu'umin murmushi kafin yace kunsan yadda za' ayi?
" A'a sai ka faɗa "
"Ku kawo kunnaku kuji, " nan yayi masu raɗa a kunne.
Atare suka fashe da dariya suka tafa hannayensu sauban yace " nike da kai ina tsoron ka khamis gida biyu ne kai maganin gobara.
Da sauri fahat ya fito daga maɓuyarsa ya kwanta ƙasa bayan wata mota, sauban kuma ya ɗaura hannu aka ya fasa ƙara yana cewa" inna lillahi wa inna ilaihir raju'un Dady ku riƙeta mayiyace ta kama kurwar faha".
Cak suka tsaya daga ita har mai gadin dake ta yimata surutai na jan kunne
Dam! Gaban Alhajin yayi wani irin bugu zuciyarsa ta hau harbawa da sauri wani irin yar yaji wani abu yana masa yawo ajiki kamar tafiyar maciji, " riƙeta sanbo muguwarce mayiyace dawo da ita. "