Free chapter Ā· Read without an account

Chapter 4.

by Nasreel ML Ā· Furen Zuciya

🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
 Flower of the heart.

   By Nasreel R.L.
      šŸ¤A hausa love story…….

Chapter 4;

A bangaren Miral kuwa kuka takeyi sosai ta nade jikinta akan bed din kamar ball jikinta na kyarma brain dinta takasa daukar abunda ya faru.  

Wani irin zafi zuciyarta keyi shin wannan wani irin keta haddi ne? Mezai kawo wannan abun? Meyasa Ummi zatayi mata hakan? Kawai idan ta tuna yanda taji hannun matar akan sirrinta na ya mace harta iya bude baki ta fada ma Ummi wai She’s Untouched saitaji wani ʙuna a zuciyarta kamar ta hadiye zuciya ta mutu. Meke shirin faruwa da itane? 

Saida taci kukanta ta gaji sannan ta mike tareda share hawayen face dinta dayayi ja sabon kumburin mari ya fito akan wanda Hanat tayi mata daya kusa warkewa. Sai a lokacin ta tuna a inda take. Bin dakin da kallo tayi ba yau tafara shigowa guest room dinba saidai duk shigowan datakeyi na gyara ne idan Ummi zatayi baki. Yau tafara mishi kallon kurilla dan kuwa ya hadu dakin sosai dukda interior dinshi is simple.

Komai a dakin brown ne da touch of white. Queen sized bed ne da takejin laushin katifar kamar ta kwanta a kan audiga. Full sized wardrobe ne ta left side, opposite gadon kuma full length mirror ne da dresser da babu komai akai banda lotion biyu dakuma bodywash daya da turaren Reef da duk ba’a taba suba. Ta right side kuma frame ne said kofar toilet. 

Ajiyar zuciya na ba adadi ta sauke tanajin yanda jikinta ke kara lumewa a katifar. Rabon da ta kwanta kan katifa ta manta  jikinta duk sai taji wani iri dan yafi sabawa da kasa. Ga AC dake tashi dakin yayi sanyi dayasa tayi yunkurin janyo white comforter dake folded neatly a karshen gadon. wata zuciyar tace mata kada ta taɓa. Haka tajanyo jilbab data wurgar a gefen gadon ta saka tareda kudindine jikinta a ciki. 

Tunanin maganar matar tayi nacewa a barta anan saboda jikinta yayi kyau. Mezasuyi da kyan jikinta kuma? Tunawa tayi Ummi tace sauran sati daya su koma Ghair muaddal, kenan da ita za’a koma? Me komawar zai haifar mata? Shin zasu karbeta? Bayan duk ab… saurin katse tunanin tayi tasa hannu ta buge kanta kamar hakan ne zai tsayar mata da tunanin. 

Jan nunfashi tayi tareda saukewa kawai ta janyo comforter ta cire jilbab din jikinta ta rufe jikinta da confortern ta daura kanta akan lallausar pillow wani laushi da dumi daga kan confortern har zuwa pillow da katifar ya ziyarceta batasan sanda ta lumshe idanu ba tareda sakin wani moan da saida taji tamanta duk wani matsala datake dashi. 

Wani tunani ne yazo mata toh kodai saboda zasu koma Ghair muaddal ne yasa ta kawo wata ta dubata? Kodai aure zata mata? Dan dariya tunanin yabata dan tasan bazata iya aurar da itaba dan babu wanda zai aureta kowa yasan me babanta yace akan ta dakuma duk wanda ya rabi kanshi da ita. Toh kodai sunce a dawo da ita gida ne? Kodai sun gano gaskiya ne? Kokuma Ummi nason ta maidata ne kada ace tayi abusing dinta? 

Tunane tunane, question bayan question haka suka rinka jerawa a cikin brain dinta batasan lokacin da wani daddadan bacci ya kwashe taba. 

Jin kamar ana bubbuga ta yasa ta mikewa a sukwane tana zazzaro idanu. Layla tagani akanta fuskarta daure tamau kamar ta shanu sai huci take tana harararta. Dauke ido tayi tana sosa kai dan jitake kamar a mafarki take kamar kuma a gaske dan yanda sanyin dakin ke shigarta ya rikita mata brain dinta data riga ta saba da azabar zafi a koda yaushe. 

Tsawa tsawa fada fada Layla ta kira sunanta daya tabbatar mata da ba bacci takeyi bah ta tashi. Dago ido tayi ta kalleta ganin irin kallon datake mata kawai ta sauke idonta cikin muryar jin bacci tace ā€˜na’amā€. Tsaki Layla tayi sannan a kufule tace ā€œakace wai makaho an samu idanu, ga abunci nan da na tabbatar baki taba cin irinshi ba ance ki cinye tas, banmaga dalilin da Ummi zatace a fada miki hakanba dan kowa yasan kedin yar yunwa ce kuma barauniya, dan haka yau ba sai anyi halin beran ba. Sannan ga supplement pill nan kisha daya daga kowanne containerā€. Tana gama fadin haka tay tsaki ta juya ta fice.

Ciccikowa idanun Miral sukayi da kwalla jin yanda ta kirata da barauniya, ita duk zagin daza’ayi mata baya damunta amma sunan barauniya na daya daga cikin abubuwan dake mugun damunta. Gashi wannan tasan tabbas tayi, ta saba daukar abinci, amma Allah na gani sai batada yanda zatayi yunwa zata mata illa take dauka. 

Tuna hakan yasa taji wani zafi a zuciyanta. Yaushe ne wannan rayuwar kunci da kaskanta zai kare? Share hawayen daya zubo tayi tajuya ta kalla tray din abincin da aka ajiye mata a kan side bed drawer. Mashed potatoes ne a plate da chicken soup a bowl sai tiriri sukeyi, ga cup of warm milk a gefe da bottle of chilled water. Saikuma wasu containers da babu label ba komai bare ta karanta da alamun sune supplements din. 

Sosai yawunta ya tsinke takasa dauke idanunta akan abincin rabonda taci abinci lafiyayye daba ragowa ba sannan kuma complete ta manta. Bawai bata samun mashed potatoes din bane ko chicken soup din, kawai dai da wuya tasamu complete food saidai idan tasamu mashed potatoes toh bazata samu soup ba. Saidai kuma tana dadewa bata samu chicken soup ba dan gabadaya akeyi so masu aikin gidan suke ci, kafin yazo kanta ya kare. 

Wai yau ita aka kawoma abinci a cikin daki take kwance kan lallausar gado tanashan  AC? Anya ba mafarki takeyi ba? Jin cikinta yafara murdawa ne yasa ta sauke kafarta kasa sannan ta dauki spoon daga kan tray din tafara tuttura abincin da sauri da sauri kamar mai tsoron a kwace mata. 

Ko 5 min batayi ba tagama ci cikinta ya cika sosai data manta yaushe rabon da cikinta yacika haka, ga abincin da zafinshi da bazama ta iya tuna ya abinci mai zafi ke tasting ba. Madarar kawai yarage half cup bata shanye ba sai supplements din. Tunanin shan supplements din takeyi dan batasan na menene bah. Gashi babu label ko rubutun komai a container. Daukan gudadaya tayi ta bude taga babu wani yawa a ciki basufi guda ten ba kawai ta dauka daya dan za’a iya ganewa idan bata dauka ba dayen ma ta bude ta dau daya tayi ta toilet tay flushing dinsu dan bazatasha abunda batasan mezaimata ba. 

Bin Toilet din da ido tayi bashida girma sosai saidai ba karami bane daidai na guest rooms dai. Ji tayi tanason tayi wanka saidai tuna batada kaya anan yasa ta fasa kawai ta fito tadawo ta kurbe milk din dakyar dan cikinta yacika sosai ta cire bottle of water din daga kan tray sannan ta saka jilbab ta dauki tray din ta fice daga dakin. 

Kitchen takai tray din Sannan ta fara wankewa. ummı ce ta shigo kitchen din da saurı kaman an wurgota.  TSawa ummi ta daka mata "uban waya Saki wanke wanke? neman sai dole anyı mıkı fada koh! zakı ajiye ko sanayı mıkı dukan mutuwa". Saurı mıral tayı ta ajıye tana mamakın yanda ummj ta harzuka akan wanke wanke. Kamar ba ita tasata rinka wanke wanken ba a baya. Wanke hannu tayi.  ummı ta wuce daga kitchen dın, miral Saida tabarı tayı nisa sannanta juya ta nufı dakinta.

Kayanta ta kwaso kaf dinsu dama ba yawa ne dasu ba. batada komaı banda yan kayan Sawan dan haka bata tsaya komai ba ta koma main Part zuwa sabon dakinta aranta tana tunanin ko ıya yaushe zamanta anan dakin zai kasance.
Tana Shiga ta tarar da wata suitcase a gefen gadon dakin. Kamar bazata bude ba kuma ta dagota zuwa kan gadonta ta bude ZiP din. 

Cıke take fam da kayan sawa. Dogosu tafara daya bayan daya. dogayen rıguna ne daidai sıze dinta na pure cotten kusan ırınna jikinta Saidaısu sababbıne gal sannan sunfı najıkınta kyau da alamun kuma sunfisu tsada saboda design dinsu. Wajen guda 12 ne sai wasu abayas suma guda 12 a ciki da underwears bras 12, pants 24. Binsu da ido tayi tans tunanin ina suka san size dinta saidai tuna matar nan babu abunda bata gani a jikinta ba yasa tayi saurin cire tunanin a ranta dan batason kara tuna abun, tasa aranta cewa bai taba faruwa ba bakuma zata sake tunawa ba.

Nunfashi mai karfi ta sauke sannan ta maida kayan ciki ta rufe. Kan bed din ta koma ta kwanta har yanzu ji takeyi kamar a mafarki. 

Haka rayuwa ta kasance mata harna tsawon kwana biyar tana daki bata fita sai safe tayi 20 minutes kachal sannan tadawo cikin dakin gashi kullun ana kawo mata breakfast, lunch, dinner har daki abinci masu kyau da lafiya tareda gina jiki bata komai saidai ta zauna tayita tunani. Ayyukan data sabayi ma yanzu batayi jikinta yayi wani irin kyau fatarta ta kara haske har wani healthy glow takeyi sannan Ummi tasa an fitar da tsofaffin kayanta so wayannan sababbin dresses din take sawa. 

Dukda tanajin kamar kamai ya lafa Ummi sau daya take zuwa dakin ta dubata kota bata umarnin wani abu sannan ta duba ko tasha supplements din wanda har yanzu basha takeyi ba flushing dinsu takeyi amma batajin koda digon kwanciyar hankali a cikin zuciyarta. Takasa tasa ranta cikin salama dan bataga inda wannan chanjin zai kaita ba. Gabadaya Ummi ta chanza mata dukda ba kirki take yi mata ba amma kuma sam bata dukanta yanzu, sannan idan ta shigo saita tsareta da ido sosai tana kallonta, sai taji wani iri dan bata gane kallon menene take mata ba. 

Bakuma ta kara haduwa da Hanat bah shine babban abunda take godewa Allah dashi a cikin zaman dakin datakeyi dan ta tabbatar da tacigaba da aikinta dole su rinka haduwa and haduwa da Hanat bad news ne dan in babu mari akwai duka kokuma ta hada mata su gabadaya. 

Kwance take yau kan gadon dakin ya dauki sanyi da harta fara sabawa da sanyin da dakin keyi dan tarage shigewa comforter all the time. Zaman kadai kwata kwata baya damunta dan inda sabo ta saba. Saidai yau kawai ji tayi zaman yayi mata yawa duk jikinta yayi tsami dan tariga ta saba da ayyuka jikinta na motsawa yanzu kuma banda kwanciya sai zama. 

Tashi tayi tana tunanin ko tayi wanka ne saikuma ta fasa ganin batawani dade dayin wankan ba dan still ma towel ne a jikinta takasa chanza kaya tsabar yanda taji jikin nata babu kwari. Gaban mirror taje ta tsaya tana kallon kanta. Sosai face dinta tadan cicciko skin dinta yana wani glowing kamar wanda akama gyaran amare tayi haske sosai duk wani tan na aiki cikin rana yafita daga jikinta da wayannan kananan kurajen zafin duk sun tafi. 

Idanunta dasuke dan ciki-ciki yanzu sun cicciko sosai daya kara ma face dinta wani cuteness da haiba, brown eyeballs dinta ya kara haske farin dake surrounding idanun nata shima ya washe saidai still oily look dakuma tired eyes din nata nanan. Lips dinta sun kara pink kamar tasa lipstick looking so soft and moist har dan red-red sukeyi. 

Sosai ganin yanda takoma a cikin yan kwanakin nan yabata mamaki dakuma tsoro. Bata cika kallon mirror ba amma tasan dai dole da bahaka take ba, dan zata iya cewa tun bayan tabaro Ghair Muaddal rabon data samu kwanciyar hankali dakuma bukatar ta kalli kanta a mirror ta manta. 

Turo kafar akayi da wani violent push da saida kofar ta bugi bango ta komawa wanda ya turota. Wani razana Miral tayi, tayi saurin juyowa ta kalli kofar dan ganin waye ya bugota haka kamar za’ayi mata sallamar mutuwa.

For more information, contact me via whatsapp ***.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol