Free chapter · Read without an account
EP_________ 2️⃣
🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️ QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
EP_________ 2️⃣
"Wai ku mata Meysa idan kuna tuqi bakwa amfani da hankali da tunani ne? Ni ban ma san dalilin da ya sa ake ba ku license ɗin tuƙi ba, dan duk inda zaku je babu alheri a tare daku. Duk abinda zakuyi saikun haifar da matsalar kamar abokan shaidan. Useless set of humans kawai". Ya Ƙarashe yana jan wani zazzafan tsaki.
Ɗayan mutumin ne ya ce, "Haba Aryan, meke damunka ne? Ai ba ta sani ba ne, kuma ma duk laifina ne".
Katse shi yayi ta hanyar faɗin, "Shut up Mansur! Ba da kai nake magana ba".
"Saboda ba ka son gaskiya ko Aryan. Abun da ya faru duk muna da laifi a ciki, amma kana ganin yadda ta tsaya tana ba mu haƙuri, alhali mu muka yi mata ɓarna ma".
"Kai, dan ubanka wuce ka shige mota, an fasa zuba man ma". Ya faɗa a fusace.
"Eh?". Mansur ɗin ya tambaya kamar baiji ba.
"Eh, ai kaji abinda na faɗa, Idan kuma ba za ka tafi ba, ni zan shiga in ja in wuce".
Murmushi kawai Mansur yayi kafin ya juya ya kalli Faryal, wadda tayi tsaye kamar mutum mutumi tana kallon Aryan da ya buɗe ƙofar ɓangaren me zaman banza, ya shige sannan ya rufo ƙofar da ƙarfi, kamar zai cire ta daga jikin motar.
"Please I'm sorry on his behalf, haka yanayin sa yake".
"Ba damuwa". Ta amsa, jikinta a sanyaye. A tsawon rayuwarta, ba ta taɓa cin karo da mutumin da ya gaggaya mata Maganganu san ransa ba kamar Aryan. Ba ta saba faɗa da mutane ba, domin duk inda ta je, ƙauna da tarairaya take samu. Amma shi wannan, a farkon haɗuwarsu, ta hango ƙiyayyarta me tsanani a idanunsa ba tare data san me tayi da zafi haka ba.
Haka tayi tsaye har ta daina hango tayar motarsu, kafin ta juya da niyyar komawa motarta, amma sai idonta ya sauka akan wallet ɗin dake jefe a ƙasa, daidai inda Aryan ɗin ya tsaya. Ji tayi kamar ta ƙyale tayi wucewarta, amma sai zuciyarta ta tunatar da ita faɗin ALLAH maɗaukakin sarki a cikin suratul fussilat aya ta 34
وَلَا تَسْتَوِي الْحَسَنَةُ وَلَا السَّيِّئَةُ ۚ ادْفَعْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ فَإِذَا الَّذِي بَيْنَكَ وَبَيْنَهُ عَدَاوَةٌ كَأَنَّهُ وَلِيٌّ حَمِيمٌ
Sai kawai ta karasa tasa hannu ta ɗauka sannan ta koma motarta domin ta gyara parking ɗin nata.
Ana gama zuba mata man kuma, ta nufi gidan Auntynta ta. Tana ƙarasawa ta danna horn, mai gadin ne ya leqo dan ganin waye. Yana ganin motarta ya koma ciki da sauri ya wangale mata gate ɗin ta shigo. Sakin gate ɗin yayi a bude ya rufawa motarta ta baya da gudu yana faɗin, "ALLAH ya taimaki uwar masu gida! Gimbiya sarautar mata. An buga da ke an barki, an sake bugawa da ke an barki. To, sun ga ba haza ehhh! Fara mai farar aniya, sukari baki farin banza ba. Ehhhh! ALLAH ya ƙara girma uwar ɗakina. ALLAH Ya sa ki daɗe kiyi ƙarko".
Dariya Faryal tayi bayan ya gama kirarin nasa, sannan ta sa hannu a jaka, ta ƙirgo kuɗi ta miƙa masa tana faɗin, "Baba Adamu namu, to ga wannan ba yawa, ka sha ruwa".
Ɗurkusawa yayi ya karɓa, yana ci gaba da yi mata kirari da addu'ar gamawa da duniya lpy har ta fito daga motar ta nufi entrance ɗin gidan.
Knocking tayi taji shuru, tana ƙoƙarin sake knocking ɗin ta jiyo taku alamar ana tahowa, dan haka ta tsaya.
Wata yarinya ce ta buɗe ƙofar, tana ganin Faryal ɗin kuwa, ta faɗa jikinta cike da farin ciki ta shiga ihun faɗin Ga Aunty Faryal ga Aunty Faryal, tana yi tana kiran sunayen yan uwanta ɗaya bayan ɗaya, "Kainat, Shaima, Warda".
Da gudu suka fito kamar wadanda kura ta biyo su, suka rungume Faryal ɗin suna tsallen murna.
Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga wani ɗaki, riƙe da lotion a hannunta, alamar bata jima da fitowa daga wanka ba. Kallonsu tayi ta jinjina kai tare da faɗin, "Ai na san babu wanda zai zo yasa a cika mana gida da hayaniya sai ke". Ta faɗa tana zama a kan ɗaya daga cikin sofas ɗin dake falon.
Riqo hannun kananan Faryal tayi, suka karasa kan sofar da Manira ke zaune tana shafa mai a tsintsiyar hannunta. Cikin barkwanci Faryal ta ce, "Madam Chef, yanzu haka ake tarbar baƙi? Saboda Allah, baƙonka annabin ka fa".
"Ke kika san hakan". Manira ta faɗa tana taɓe baki.
"Au too, ya miki kyau kinji". Faryal ta faɗa, sannan ta juya ga yaran. Ta zaro packets na chocolates ta rarraba musu, wanda yasa suka shiga tsalle suna murna, suka sake rungumeta suna mata godiya.
"Kainat, ina Ammi?". Faryal ta tambayi babbar cikinsu.
"Ammi ta samu kira daga hospital. Tana da patient, amma baza ta daɗe ba, dan muna dawowa daga school ta tafi".
"To, Allah Ya dawo da ita lafiya. Manira na zo ɗaukan ki ne ki raka ni wani wuri, amma tunda Ammi ba ta nan, ba za mu bar gidan ba wani babba ba ai".
"Kainat za ta iya kula da su". Manira ta amsa.
Juyawa ga Kainat ɗin Faryal tayi kafin ta ce, "Kainat, zamu ɗan fita ni da Manira. Amma ba zamu daɗe ba. Dan Allah ki kula da ƙannanki har Ammi ta dawo kinji ko?".
"Kar ki damu Aunty Faryal. Babu abin da zai faru, in sha Allah". Kainat ta amsa.
"Man...". Maganarta ta katse saboda juyowar da tayi inda Manira ke zaune ta ga wayam. Ɗaukan jakarta tayi tabi ta ɗakin tana faɗin, "Wai ni, me na miki ne tun a waya kike ta cimin magani?".
Taɓe baki Manira tayi, tana ci gaba da gyara ɗankwalinta, ba tare data ce komai ba.
"To ni dai yanzu ki shirya, ma yi Magana a hanya. Ana jirana ne yanzun". Faryal ta sake faɗa, saidai still Manira bata amsa mata ba sai ma wucewa da tayi wurin wardrobe ɗin su, ta buɗe ta zaro jilbab ɗin ta, ta sanya a kan Summer dress ɗin dake jikinta. Ta zura takalminta, ta ɗauki wayarta ta yi waje ba tare da ta furta uffan ba.
Biyo bayanta Faryal tayi amma bata tarar da ita a falon ba, sai kawai ta yiwa yaran sallama tayi waje. A jikin motar ta hango manira tsaye. Bata ce da ita komai ba ta buɗe motar ta shiga, itama maniran ta buɗe passenger front seat ta shige. Tada Motar Faryal tayi ta danna horn, Baba Adamu ya buɗe musu gate ɗin, suka fice yana daga musu hannu tare da addu'ar isa lpy.
Saida suka hau titi sannan Manira ta ce, "Ke yanzu kina ganin abin da kike yi daidai ne?".
"Well, fara faɗa min abin da na yi ɗin tukunna, sai inji ko daidai ne ko kuma akasin sa". Faryal ta amsa hankalinta akan tuqin da take.
"Barr Hashim!".
"Barr Hashim! Barr Hashim! Ya Allah, wai meysa mutumin nan yake ƙoƙarin takurawa rayuwata ne haka? Na gaya masa cewa ina da wanda nake so, in ma latsi yake ai zuwa yanzu yaci ace ya hakura ya kyale ni ko". Ta faɗa cikin ɓacin rai, wanda ya bayyana har a fuskarta.
"Amma ai ya kamata ki saurare shi, ko dan ni, tunda yayi kamun ƙafa dani. Ko kuwa so kike ki nunawa duniya cewa bani da daraja a idonki?".
Yar dariya Faryal tayi Kafin ta ce, "I don't care. Abin da na sani kawai shi ne, ba zan yaudare shi ba, tunda na riga na gaya masa gaskiya, kuma ya ƙi fahimta, that's his own cup of tea".
"To sai ki gaya min ai, uban wa ya kawo shi gidan mu?".
"Ƙafafunsa! Ƙafafunsa ne suka kai shi".
"To, kin san Allah, ba zaki cigaba da ɗora min aiki a kai ba. Nan gaba idan kika fita wani wuri kika lura wani yana bin ki, to ki canza hanya ko kuma ki nufi gidanku. Kuma ma ai ke kika so".
"Me kike nufi da ni na so? Ni mutum ɗaya nake so, and that's Hamdan".
"Naji da Allah. Amma a lokacin nan me kika cewa Barr Hashim?".
"Manira, bafa wani yaren nakeyi na daban ba. Na gaya masa cewa inada wanda na tsaida nake so, ha'an".
"Kin gani ko, wato baki san mazan wannan zamanin bane. Sau da yawa, idan suka ga macen da suke so, to sai sunyi iya yinsu wurin ganin sun sameta ko da kuwa ce musu kikayi akwai ranar wani a kanki, as long as ba'a ɗaura auren ba gani zasuyi wannan ma wata dama ce a gare su. To abinda wasu ma ko matan auren suka gani in dai sun musu sai sun bibiye su. Su kuma mayar da tunanin su gabaɗaya kan yadda za su fito da ita daga gidan mijin. Despite seeing that Barr Hashim bai yi kama da irin waɗannan mutanen ba, amma da tun lokacin da ya biyoki kawai kin shaida masa ke ɗin matar aure ce, tunda har bai sanki ba bazai yi jayayya dake ba zai haƙura ne kawai ya tafi".
Harararta Faryal tayi kafin ta ce, "Na miki kama da matar aure ne?".
Dariya Manira tayi kafin, ta ce, "Shikenan ki ci gaba. Sai ki san yadda za ki yi da shi. But spare me from this ".
Dan tsaki taja Kafin ta ce, "Manira please be serious, taya zan iya yakice shi daga rayuwata ne?".
Numfashi ta furzar kafin ta ce, "Za mu yi tunani a kai. Dan gsky wannan zamanin abun tsoro ne".
"Ai dole ma ya rabu da ni whl, tunda ba gware muka yi muka zo duniyar ba". Faryal ta faɗa, tana danna horn daidai lokacin da suka tsaya a bakin gate ɗin gidan senator ɗin.
Saida aka bincika motarsu kafin a bar su su shiga, bayan sun kira matar sanatan a waya sun haɗata da Faryal.
Alhamdulillah, an tarbe su cikin mutunci da girmamawa, ba kamar yadda ake yi a wasu gidajen masu kuɗin ƙasar ba. Faryal ta sa ido kan ma'aikatan nata sosai, ta gyara musu wasu abubuwan. Bayan ta tabbatar da cewa komai ya daidaita, sai ta sallame su domin su koma can Brand ɗin nasu. Ita kuma ta yi wa Hajiyar sallama, wadda ta haɗo su da kyaututtuka da kayan ciye ciye aka kai musu har mota, saboda Hajiyar ta dage cewa sai sun zauna sun ci abinci, amma suka ƙi, shi ne ta sa aka musu packaging ɗin sa dan su wuce dashi.
Ko da suka isa parking lot ɗin, sai gani sukayi wata mota ta rufe su ta baya, ba yadda za'ayi su fitar da tasu motar.
Manira ce ta ce, "To yanzu ina za mu ga mai wannan motar?".
"Ai ba za mu cigaba da tsayuwa a nan ba. Dubawa zamuyi ko Allah zaisa baiyi nisa ba a masa magana".
Daga bayansu suka ji wata murya na faɗin, "Akwai wanda kuke jira ne?". A tare suka juya, inda sukayi tozali da wani matashin saurayi tsaye a bayansu.
Faryal ce ta ce, "Mun zo tafiya ne, to sai kuma muka tarar wani ya rufe mu ta baya da motarsa".
Kallon motar Matashin yayi kafin ya ce, "Tabbas wannan motar Jalal ce. Babu wanda zai yi parking irin haka sai shi".
"To dan Allah tunda ka san shi, ko za ka iya yi masa magana ya zo ya gyara parking ɗin sa?". Ta faɗa Muryarta ɗauke da damuwa, dan dare ya fara yi, ga kuma gidan da ya fara cika da mutane yan biki.
"Okay bari in kira shi". Ya faɗa, yana zaro wayarsa daga aljihunsa.
Kiransa yayi, amma bai same shi ba. Kallonsu yayi da ɗan damuwa Kafin ya ce, "Ban same shi ba whl, amma kada ku damu. Ku ɗan jira ni kaɗan, bari in duba ko baiyi nisa ba". Ya faɗa yana barin wajen.
Suna tsaye suna jira, har kusan mintuna goma kafin Faryal ta ce, "Ya shiga ya duba shin ne, ko kuwa yayi tafiyarsa ne ya manta damu?".
Kafin Manira ta bata amsa, sai ga shi ya dawo da sauri, yana faɗin, "Ku yi haƙuri fa na bar ku tsaye. Whl banga inda yayi bane ina ta duba shi. But let me have the key, bari in gwada ko zan iya fitar muku da ita".
Miqa masa Faryal tayi, ya karɓa ya shiga motar ya tada, cikin dabara da kuma gogewa a tuqi irin na namiji sai gashi ya yi nasarar fitar musu motar.
Fitowa yayi daga cikin motar ba tare da ya kashe ba, ya kalle su yana murmushi ya ce, "Magana ake ta tsohon driver, to me ya wharu".
Dariya Faryal tayi, kafin ta ce, "Gsky kam ba duk kai ba. Mun gode sosai, sakallahu bi khair".
Manira ce ta ce, "Kuma ba dan kai din ba da whl ni da Faryal dai bamu isa mu fito da motar nan ba".
"To ai ke dama ba ki yi kama da wadda ta iya tuƙi ba". Ya faɗa da sigar zolaya yana kallon Maniran.
Harararsa Maniran tayi kafin ta ce, "Eh ban iya tuqa mota ba amma zan iya tuƙa jaki ai". Ta faɗa cikin shaguɓe.
Dariya ya fashe da ita kafin ya ce, "To ai wannan ne ya dace da ƙwarewar tuƙinki dama. Da kin harare shi, yayi tutsu ki faɗo".
Faryal dake Murmushin dramar su ta nufi motar amma sai yayi saurin shan gabanta tare da faɗin, "Ban san ko zan iya samun number ki ba, saboda duk lokacin da kuka sake maqalewa irin haka sai dai kawai ki danna min kira". Ya faɗa cikin barkwanci.
Ba musu Faryal ta karanto masa ya shigar a wayarsa, sai kuma ya ɗago yana kallon ta ya ce, "Kin tabbata number ki ce dai? Kada ki sa ni in je in kira yan cult, dan baka neme su bama nemanka suke ballantana kuma an kai kuka gidan mutuwa!".
Dariya sukayi gabaɗaya kafin Manira ta ce, "Ko kan kowa zai kawo kuɗi, ai banda naka".
"Ba komai, na gane yar adawa ce ke. Zanji dake". Ya faɗa yana murmushi, daidai lokacin da kiransa ya shigo wayar Faryal.
"Yauwa to yanzu kin ga naga Dahir. Za ki ga kirana, in sha Allah. Nagode ". Ya faɗa yana wucewa sai kuma ya dawo da baya tare da faɗin, "Emm, Sorry. Fayyad by name and you?".
"Faryal". Ta amsa a taƙaice, tana sanya gear.
"Wow! Nice name. Allah ya kai ku gida lafiya". Ya faɗa yana basu hanya suka wuce.
*** *** ***
A kan hanyarsu ta komawa gida kuwa in banda zancen kirkin Fayyad ba abinda sukeyi, Faryal ta ce, "Gaskiya yana da kirki sosai. Dan ba dan shi ba, inajin da saidai mu kwana acan kaw......". Kiran wayarta ya katseta.
A tare suka kai kallonsu kan wayar kafin Manira ta ce, "Walida ce".
Hankalinta ta maida kan tuqin tana faɗin, "Amsa ki sa min a handsfree".
Muryar Walida ce ta cika motar inda take faɗin, "Faryal, how you dey?".
"I dey Fine Walee. Wby? Kwana biyu kin ɓuya, ko a media ba'a ganinki, hope all is well?".
"Ba za ki gane ba. Abubuwa ne suka min yawa, bana nan ma naje Abuja, sai jiya na dawo. Na zo gidanku Maama ke gaya min kin fita aiki".
"Omoo! This girl's chilling, so what's up? Ya rayuwar Abujan?".
"Labari ne mai tsawo. Ke dai sai mun haɗu".
"I can't wait girly. In sha Allah i will visit you tomorrow if my schedule allows".
"Alryt see you yah". Daga haka sukayi sallama ta kashe.
Bayan sun isa gidan su Manira, sallar magriba suka fara gabatarwa. Suna idarwa sai ga kiran Barr Hashim ya shigo.
Qin ɗauka Faryal tayi har kiran ya katse wani ya sake shigowa, ajiyar zuciya ta sauke, wadda ta sa Manira dan kallonta ta ce, "Lpy?".
"Barr Hashim ne".
"Ɗauka mana. But don't act like you are with your boyfriend, it will only make him more interested". Ta faɗa cike da zolaya, tana me kashe mata ido ɗaya.
Ɗaukan wayar Faryal tayi amma kafin ta kai ga cewa wani abu Barr Hashim ya katseta da faɗin, "Faryal, dan Allah ki tsaya ki saurare ni. Ki ba ni dama, wallahi tun ranar da na dora ido na a kanki, ban sake samun sukuni ba, ki tausaya min mana". Ya Ƙarashe muryarsa ɗauke da damuwa.
Jikin Faryal ne yayi sanyi, ta ɗan saci kallon Manira, wadda ta kasa kunne tana saurarensu kafin ta ce, "Barr, ina ganin girmanka. And kana da duk wasu qualities da mata ke nema a wurin ɗa namiji. Amma na riga na faɗa maka game da wanda nake so. Imagine mutumin da ka yi shekara biyar tare da shi, har kuna shirin aure, sai kwatsam wani ya shigo tsakaninku. Idan kai ne yaya za ka ji?".
Barr Hashim ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce, "Gaskiya ba zan ji daɗi ba".
"To, ka ga kenan, Idan muna son yin wani abu, ya kamata mu fara sanya kanmu a matsayin mutumin da abin zai shafa".
Jim yayi har tayi tunanin ko ya kashe ne kafin taji ya ce, "Na fahimta Faryal, amma ina neman wata alfarma a wurinki".
"Wace irin alfarma?".
"Lets be friends please". Ya faɗa kamar zai yi kuka.
Faryal ta yi murmushi, kafin ta ce, "Ba damuwa Barr. Na gode da ka fahimce ni". Godiya sosai Barr Hashim ya mata, kafin su dan taɓa hira sannan suyi sallama ta kashe.
"Hmm. Manira bari kiga in tashi in wuce gida. I have a meeting with some guests around 9am tomorrow, kuma ya kamata in dan samu hutu". Faryal ta faɗa tana miqewa tsaye.
Tashi itama Maniran tayi suka fito tare. Faryal ta yi wa Ammi sallama, sannan Manira da sauran yaran suka rakata har mota, saida suka ga tafiyarta sannan suka koma ciki.
A gajiye ta isa gida inda ta tarar da Daadee da kannenta biyu suna kallo a falon. Kayayyakin da matar senator ta hado su dashi wanda suka raba da Manira ta dire musu a tsakiyar falon kafin ta zauna gefen Daadee tana amsa musu sannu da zuwa da suke mata, ta miqawa Daadee ledar goronta da basbousar data bata sallahu da zata fita.
Maama ce ta shigo falo, tana fadin, "Beta, Aapake Pita Aapako Bula Rahe Hain". (Your Appa is calling you).
Wata yarinya da baza ta wuce 9 years ɓace ta miqe ta bar falon da gudu.
Maama ta juya ta kalli Daadee da Faryal, kafin ta ce, "Faryal, yaushe kika dawo?".
Daadee ta amsa da, "Yanzu yanzu nan ta shigo. Kin ganta nan diyar albarka".
"Kawarki ta zo nemanki ɗazu bakya nan". Maama ta faɗa.
"Oh yeah, Waleeda ce, Munyi waya ma yanzu da ina tahowa". Faryal ta fada tana miƙewa tsaye ta daɗa da faɗin, "Yau ba dan ina tunanin aiki ba, da in na kwanta bacci sai gobe da yamma zan tashi".
Wani an samari da shekarunsa baza su wuce 15 bane ya ce, "Ke dai ki bar wani kame kame, kawai kice kina so ki shige daki ne kiyi zaman waya da Hamdan saboda bakyaso a dameki shi ne zaki fake da gajiya".
Tsayawa Faryal tayi ta juyo ta kalle shi, a fusace ta ce, "Maama, whl ki shiga tsakanina da Nasar. Ni fa ba sa'ar wasansa ba ce".
Daadee ce ta shiga tsakani, tare da faɗin, "Rabu dashi Faryal. Zan miki maganin ɗan banza yanzun nan". Ta faɗa tana ɗaga sandarta ta buga masa a ƙafa.
Nasar ya yi saurin tashi ya sauya wurin zama, yana dariya. Ƙwafa Faryal taja kafin ta wuce ɗakinsu tana kiran sunan Hadiyyah.
Maama ce ta ce, "Hadiyyah tana falon baƙi, tana da baƙo ne". Da Okay ta amsa kafin ta shige.