Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by Abdulhakim Umar · ƘAZAFI Book One

Ƙazafi
Page 4
By 
Ɗan Bugaje
Wani irin abune yasoki zuciyar sireenah take jikinta ya fara kyarma da mazari tamkar an joganamata shoking na wutar lantarki, wani irin abu ya fara yawo ajikinta tundaga ƙarƙashin ƙafarta har zuwa cikin kwakwalwarta, zufa ta fara tsatssafomata a kowacce gaɓa ta jikinta, kanta ya ɗau wani irin turiri tamkar garwashin da yake karɓar zuga acikin ramin maƙera, tashin hankali wanda ba asamasa rana. 
Kafin tayi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ga Alhaji a gabanta yayima hannunta wata irin cafka yajata ƙeeeee! Har gaban fahat. 
"Maza tsallakashi muguwa kawai". 
" wallahi tallahi ni ba mayiyabace sharri sukai mani kuma..... 
Kif taji saukar wani zazzafan mari akuncinta wanda yasa maganarta tsayawa tai luuuu! Taga -taga zata faɗi amma sai mai gadin ya tarota yana faɗin " maza kiyi abinda akace ". 
" wallahi tallahi ni ba mayiya bace Allah ma yasani...... 
Kafin ta ƙarasa taji saukar maruka tas! tas!! haggu da dama, zafi, zugi, azaba sune suka ziyarci zuciyar ta a lokaci guda ta ruɗe ta dabarbarce sai tashiga daka tsalle tana dawowa ƙasa tsabar kiɗima. 
Tas! Ta sake jin saukar wani marin wanda mai gadin ne ya batashi yana cewa " cire takalminki ki tsallakashi akace. "
Kamar dama anyita don bin umarnin sa take ta cire takalmin ta hau tsallaka fahat ɗin, wani irin mamaki ne ya ziyarci zuciyarta ganin fahat ya tashi zaune yana tari da mai da lumfashin kamar gaske. 
Jikake dam! Dadyn ya kai mata duka abaki take bakin ya fashe jini ya fara fita juwa da hajijiya suka ɗauke ta tafara ganin mutane dishi-dishi. 
Alhaji ai ba haka ya kamata kayi mataba banni da ita ai mugu shi yasan makwantar mugu, iya ruwa fidda kai, kiɗa a ruwa mai tada haukan dodo, ni nake da maganin ta, duk lalacewar tsohon zaki yafi ƙarfin saurayin kare, kifin fadama bai gasa da na gulbi, kai da kake da ni agida ai kai agwagwane baruwanka da tsafi, nasan yadda zanyi da ita ina zuwa. "ya kai ƙarshen maganar yana nufar ɗakinsa dake liƙe da gate ɗin gidan. 
Wani irin kallo Alhajin yake bin sireenah dashi irin na zaki sani. 
Ita ko sireenah jikinta rawa kawai yake ta kasa cewa uffan saboda rawar da bakin ta yake, wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubomata jitake ina ma tana da damar ɓaccewa ta yi tsuntsuwa ta ɓacce, ko ace tana da damar canza marecen yau ya zama tarihi ba ayishiba, amma ina ƙaddara ta riga fata Alƙalamin ƙaddara ya riga ya gama rubuta komai. 
 Mai gadin ne ya dawo yana cewa kash "Alhaji na baro kayan aikina gid, amma bari nasa igiya na ƙulleta muje sitasion ahukuntata ayi mana tsakani da ita. 
Ha kawai sireenah tanaji tana gani akasa igiya aka ƙulleta akasata bayan mota, Dady yaja suka fice sai sitasion. 

Da sauri sauban ya fito da motar fahat suka maramusa baya.
Suna isa Dady yasa aka kulle sireenah bayan yayi ma yan sanda bayanin komai kafin ya tafi da niyyar zai dawo gobe.
Dady na fita suna shigowa, fahat ne ya zubema ƴan sandan kudi masu yawa ya ce 

“yallabai wannan yarinyar za abani gidan sarkin mayu zan Kaita don cenne yafi dacewa da ita.”
“amma kayi hauka ko taya zan barku da mayiya ta illataka”.
“yallabbai kenan ai mu shirye muke kudai nake tausayamawa shi yasa na zo na rabaku da ita don mu munfi karfin ta kurwarrmu tafi madaci daci muda maye sai gani sai hange, amma munfi karfinta.”
Ganin manyan kudi asaman tebir ne, da kuma kalaman khamis yasa hankalin ’yan sandan ya fita jikinsu suka fito da sireenah, inda wani daga cikin yan sandar ya kamo hannun ta har cikin motar su sauban, sauban ɗin ne a mazaunin direba sai fahat da khamis sun sata a tsakiya domin kuwa duk gidan baya suka zauna, a cewarsu zasu riketa ne don kartai masu hauka a mota sai matseta suke suna taba jikinta.
don kawai cikar burin su, sireenah ko tuni ta shiga tunanin yadda zata kwaci kanta ta koma gida take , domin yanzu duk hankalinta ya koma gida ko wane hali mama take shin ko wane irin hali su salima suke ciki, oho shine kawai abin da take son sani, kuma ta dau alwashin daukar fansa middin suka rabu to sai ta dau fansa akan KAZAFIN da sukai mata.
Kiyi Aljannun karya wani sashe na zuciyarta ya gayamata don shine kawai mafita a iya tunaninta, ta zurfafa a duniyar tunanin yadda zatai abin ya zama kamar da gaske sai ga wata bakar katuwar mota tasha gabansu. dai dai sadda suka hau titi.
Ji kake Kiiiiii! Karar jan burkin da sauban ya yi da karfi don gujema yin karo da motar gabansa, dukkan su sai da sukai gaba sukai baya kafin sauban ya juyo cikin firgici yace “fahad Abbanmu ne.”
“la’ilaha illallahu Allah kasa Dady bai sanar masa halin da ake ciki ba?”.
Amin suka ce su duka cike da alhini.
Cikin tashin hankali da tsoro Abban sauban ya fito daga motar sa ya tunkarosu, ya isa ya buɗe motar da sauri ya ɗauke sauban da mari kafin ya fara magana cikin zafin rai “ku mahaukatan ina ne da baku da hankali ban saniba mayiyar zaku dauka a mota kuna yawo da ita sai wani abun ya sameku, zata illata rayuwar kune a banza da wofi ko baku san irin hatsarin da yake tare da mayuba.”
“Ayi hakuri Abba” cewa sauban.
“Dama zakace haka tun da kuruciya na dawainiya da kai baka san ciwon jikinka ba bare ka kula da lafiyar ka, kassan kai kadainake da, bazan lamunci wani abu ya samekaba, Dadyn fahat ya sanar dani komai hankali tashe naje sitasion aka ce wai kun fita da ita, cikin firgici... na biyo hanyaku aguje har nai nasarar samunku."
Sai da ya mai da kallon sa kan sireenah kafin ya ci gaba da cewa “ke kuma munafukar banza da wofi yau taki ta kare maza fito nan don yau idon duk Ahlinku mayune to sai na karar da su, ke dai taki ta kare sai dai muyi fatan Allah ya kara nauyin kasa don kasheki zan saka ayi yanzu ba sai anjimaba”. 
Ya kai karshen maganar yana kokarin fizgo sireenah waje.
Rudududum! Zuciyarta tai wani irin mummunan bugi take jikinta ya fara rawa hankalinta ya kai kololuwar tashi,
ahankali ta furta na shiga ukku yau naga ta kaina lallai ina acikin tsaka Mai wuya, sai ta hada hannayenta waje daya tana fadin “ya rabbi ya rabbi Allah kana gani Allah kaine ka halicce ni kassan ni wacece Allah ka kawoman dauki da agajin gaugawa na samu na fita daga cikin wannan tsaka mai wuyar da na fada Allah ka bayyana gaskiya su san cewa ni ba mayiya bace”, sai ta fashe da kuka mai tsuma rai zuciyarta na mata wani irin zafi da zugi Ashe haka sharri yake da ciwo Ashe haka KAZAFI yake da cin rai Allah gani gare ka Allah ka sanar da su gaskiya.
“wallahi Abba ba mayiya bace KAZAFI kawai mukai mata.”
Da sauri kuma da azama sireenah da fahat suka dago kai atare suna kallon sauban, kallo na mamaki da al’ajabi, bakin fahat har ruwa ya ke wajen fadin “sauban ka haukace ne kasan abinda kake fada”.
Sireenah ko wani sanyin dadine ya ziyarceta sakamakon jin abinda sauban ya fada tasan tabbas ya gama wanketa addu’ar ta amsu,
Mulmushi sauban ya yima fahat kafin yace “kwantar da hankalinka abokina nasan abinda nake fada”.
Bai jira cewar fahat ba ya faru ya sanar da Abban nasa, sanin irin so da kaunar da mahaifin nasa yake masa bazai ga wani laifinsa ba.
cikin wani irin yanayi fahat da khamis suke kallon sauban cike da tsana da jin haushin tona masu asiri da yayi.
“kai amma kunban mamaki ku yanzu haka yara da ku har kunsan yadda zaku daurama yarinya wannan sharrin, kun san yadda KAZAFI yake barema na maita lallai kun isa.”
“Abba bamu sani ba sai dai munsan cewa zaka fitar da mu ko a inane cikin kasar nan, shi yasa muka aikata, ballema wannan yar matsiyatan da ke neman na abinci, ai ko kusa bazasu iya shari’a da muba, kudin magani ma sai anyi bara atiti kafin a samu.”
“Dadina da kai sauban akwai hangen nesa, yanzu ya ku keso akwai wanda zai iya auren ta acikin ku, ko kuma kuna da wata manufa ne a kanta.”
Wata irin aziyar zuciya fahat ya sauke har sireenah na iya jiyo sautinsa, sakamakon jin abinda Abban yace.
Ita ko sireenah mamaki ne ya mamaye zuciyarta wannan wane irin ubane haka ai so ba hauka neba kauna kuma ba rudu ceba……
Cak tunanin sireenah ya tsaya jin irin kalan da sauban yake faɗa “haba Abba kamar ni zaka hada da wannan yar matsiyatan yar talakka kaskantacciya ai zaren ba kalar yadin bane wutsiyar rakumi tai nisa da kasa, kawai dai muna son rage dare ne da ita saboda ta burgemu za mu hutane kawai mu biyata”.
Mamaki al’ajabi masu tarin yawa suka cika zuciyar sireenah ta yadda ta ji ɗa na sanar da mahaifinsa wannan kalamai.

babu kunya bare tsoron Allah......
Ai duk wani mamaki da Al'ajabi tuni suka kaura daga zuciyar sireenah jin irin amsar da Abban yake bama sauban din.
“Ga kudi nan dubu dari biyu ne kai maleji da su, bazan hana kaba tunda kana so sai dai zai zama karo na karshe don aure zan ma wannan ba rayuwa bace ina tsoron bacin ranka shi yasa na barka kayi din amma zai zama na karshe, ka kula da kanka, ke kuma ki basu hadin kai domin kin warke daga talauci zaki sami kudi mai yawa, idon ko naji labari wani abu ya faru ga yarona sai na daureki har igiya tai rara don zaki kare rayuwarki ne a gidan kaso.”
Yana gama maganar ya koma cikin motar sa ya ja yabar wajen, Ashe ba sireenah kawai ke mamaki ba har da khamis don cewa yai “abokina anya Abba yana cikin hayyacinsa kuwa, abin ya yi yawa.”
“Haba kaima kasan bazai yuyu ba ace mutum mai hankali da nutsuwa ya fadi irin wadannan kalamai ba, sanin cewa ni daya ya haifa ne yasa na dau burin more rayuwa da jindadi inyi wadaka da duniya, sai hakan ta kasa Faruwa don burin Abba na zama na gari mai addini, da nayi dan karamin laifi sai asanar da shi yai taiman fada, ni kuma bazan juraba sai nasa wani malam ya rufe man bakinsa sai abinda nace shi za’ayi babu jayayya bare gardama, ni kaina ina mamaki idon ina sanar masa da wani abun, amma bai ganin laifina komai zanyi yana bayana sai dai ina lura dashi idon nai wani abun yana masa ciwo sai dai bazaiyi magana ba.”


> Ya kai ƙarshen maganar yana ƙoƙarin tayar da motar, ya yi mata key suka soma ratsa kwalba. Ƙaraf idon Sireenah ya sauka a kan Yaya Najeeb da yake zaune bisa mashin na aƙaba. Ai take Sireenah ta wāge baki ta ce, "Yaya Najeeb ka taimaka min za su lalata min rayuwa." Ai ƙaraf sai a kunnansa, cikin ruɗewa ya sa mai aƙabar ya biyo bayansu har cikin GRA. Ba ƙaramin artaɓu aka sha ba kafin Najeeb da mai aƙabar suka yi nasarar tafi da Sireenah suka bar wajen a guje, saboda mugun dukan da suka yi masu don kuɓcewa suka bar su. Amma fa sun sha wuya don har ciwo suka jima, Yaya Najeeb a goshi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol