Free chapter · Read without an account

THE UNEXPECTED BLESSING

by Nihaal Maalik · KIRAN KADDARA


AMSTERDAM 

Tun lokacin da Maryam ta kammala jarabawarta ta ƙarshen shekara, farin cikinta ya ƙaru saboda dokin hutu, maryam irin mutanen nan che da indai jarabawa na gabansu ko baccin kirki ko cin abincin kirki basu iyawa, yau kusan sati daya da ta kammala jarabawar ta, tanajin jikinta sakayau ba kamar lokacin da tana exams ba da takejin kamar an daura mata dutse a kai ba. Sedai yanayin jikinta da ke mata babu daadi, shima tasan idan ta qara hutawa ze dena, qila rashin chin abnci da rashin isashshen baccee da bata samu ba na tsawon wata daye ne yake tambayar jikinta, Dama ko a sokoto lokacin da tana UDUS indai suka qare semester exams se tayi rashin lfya na kwana biyu. 

Zaid ya dawo daga wurin aiki, bayan ta tarbe shi kamar ydda ta saba cikin fara’a, ta kawo abncin da ta girka mishi suka chi tare sannan yayi wanka ya fito, suna cikin fira yake tuna mata da alƙawarin da ya yi na tafiya da ita cruise, yache mata ya fara clearing schedules dinshi don dan haka itama ta fara shiryawa 

Washegari maryam ta fara shirya kayan su cikin doki da farinciki amma duk lokacin da ta duqa, ko kuma idan ta zauna da zarar zata miqe se taji kamar zata fadi qasa se ta dan tsaya, a ranta take tunanin ko dai zatache a dan daga tafiyar zuwa lokacin da jikinta ze dan sake, amma se tayi tunanin ai kafin ya qare clearing schedules dinshi taji saukee, don haka se tabar zanchen kawae ta ci gaba da shirinta. 

Yau da safe, ta sauko daga sama cikin jin dadin yanayin hutun da suke, sanye da wata doguwar riga mai laushi kalar burnt orange. Ta tarar da Samantha da Rachel a parlour, suna zaune kusa da juna suna magana da yaren Dutch. Tun lokacin da ta fara zama a gidan, ta fara sabawa da su sosai, har suna zaunawa suyi fira tare especially ynzu da take hutu

“Good morning, madam,” Samantha da Rachel suka hada baki wurin gaishe ta suna murmushi.

Maryam ta zauna a kujerar da ke kusa da su.

“Good morning, hope you slept well?”

“Very well, madam. What about you? You look like you just woke up.”

Maryam ta yi dariya a hankali.

“I slept very well. I think I needed the rest.”

Rachel ta kalleta da kyau.

“Are you sure you’re feeling okay? You looked a little unwell yesterday.” Saboda jiya ta lura kamar maryam na ganin jiri lokacin da ta miqe tsaye zataje tayi sallah

Maryam ta gyara zamanta.

“Yea, I’m fine, It was all the stress from exams, Now that I’m done, I’m going to get plenty of rest”

Suka gyada kai a tare

Samantha ta tambaye ta ko tana son a kawo mata breakfast. Da farko ta ce ba ta jin yunwa, amma daga baya tache Rachel kawo mata noodles da black tea 

Sai da aka kawo abincin, Maryam ta dan fara chi se taji duk ta fita kanta. Kamshin omelette da Rachel ta soya mata a gefe daya ya sa cikinta yana dan juyawa. Ta ɗauki cup ɗin black tea dinta, amma da ta ɗan sha sai ta ajiye shi da sauri shima

Rachel ta lura da ita

“Ma, are you feeling nauseous?”

Maryam ta yi ƙoƙarin murmushi.

“Maybe I’m just not hungry.”

Ba ta son ta fara damuwa kar zaid yache batada lfya ze daga tafiyar su. Ta ci gaba da hirar ta da su, tanajin suna rage mata kewa

“Now that you’re on holiday, you can finally relax and rest,” cewar Samantha 

“Exactly. And my husband promised to take me on a cruise for a week.”

Rachel ta buɗe baki cikin mamaki.

“A whole week?”

Maryam ta yi dariya

Samantha da Rachel ma suka yi murmushi suna kallon yadda fuskar Maryam ta haskaka yayin da take gaya musu

“Your husband really cares about you so much, I never thought he can be so caring because he’s always too serious,” cewar Samantha 

Rachel ta qara da cewa “we’ve never seen him smiled before, but when you came to this house everything changed, he smile immediately he opens the door as he enters the house”

Maryam ta ɗan sunkuyar da kai tana murmushi.

amma a zuciyarta ta tuna yadda Zayd ke kula da ita, duk da cewa yanada yawan aiki da ke gabanshi, ya kan tabbatar da cewa ya bata isasshen lokacin shi, kuma yana tabbatar da ba ta damuwar komai 

Bayan sun ɗan yi hira da su Samantha, ta koma sama ta dauki wayarta ta kira zaid, amma bai ɗauka ba. Ta san yana wani abu ne definitely, don haka ta aika masa saƙo.

Maryam: hy, I miss you 

Bai ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin ya amsa.

Zaid: miss you too my haya, give me few minutes please, I’ll call you back 

Maryam: okay rouhi

Zaid: kinyi breakfast?

Ta yi murmushi tana kallon wayar.

Maryam: Yes, sir.

Zaid: Don’t “sir” me when you know I’m already missing you.

Maryam ta yi dariya 

Maryam: Go and work sir 

Zaid: I am working. You’re the distraction.

Ta girgiza kai tana murmushi, sannan ta ajiye wayar, ta miqe zataje bathroom tayi arwallah ganin lokacin sallah yayi, tana miqewa ta sake jin ɗan jiri. Ta zauna a gefen gadon, ta rufe idanunta na ɗan lokaci, tana jiran taji ta dawo normal 

Seda ya lafa bayan ɗan lokaci sannan ta miqe ta wuche bathroom ta fito, tayi sallah ta dauko Qurani ta fara karantawa, se ta fara jin baccee, ta yi ƙoƙarin mai da hankali, amma barci ya fara ɗaukan ta, Ba ta daɗe ba baccee mai nauyin gaske yayi gaba da ita. 


MERIDIAN AXIS GROUP 

A dd wannan lokacin, Zaid ya fito daga meeting yanata kiran maryam amma bata daga ba

Ya shigo office dinshi ya zauna kan kujerar shi yanata qoqarin kiranta ya gani ko zata dauka, a kan table din gabanshi computer che da takardun wani project da ake jiran ya karanta yasa hannu, ga kuma wata paper me dauke da  duk schedules dinshi na ranar, amma ba wannan ba, duk tunanin shi yana wurin maryam

Ya duba agogonsa da ke hannun shi sannan ya sake kiranta, amma still bata daga ba

Ji yayi hnkalin shi be kwanta ba don haka ya kira landline din da ke parlour, Rachel tayi picking, direct tambayar ta matar shi yayi, ta amsa mishi da ta sauko tache a bata noodles amma bata chi sosae ba hakanan ta batta ta koma sama kuma bata sake saukowa ba

“You mean she has not eaten anything since morning?” Shine tambayar da zayd yayi mata a dan tsawace

A rude ta amsa mishi “yyesss sir, i think, i think, she’s sick because she look pale, and and and she was feeling dizzy and light headed”

Kashe wayar kawai zayd yayi da tunanin ko dai baccee tayi don ya lura da yawan baccin da take kwanan nan 

Yana cikin tunanin yaji muryar assistant dinshi 

“Sir, the documents for the afternoon meeting are ready,” ya ce bayan ya shigo.

Zaid ya ɗaga kai ya kalleshi

“Thank you. Put them here.”

Ya ajiye mishi takardun ya juya, amma kafin ya fita, yaji muryar zayd , “tell my driver to be on standby this afternoon. I may need to leave early”

“Yes, sir.”

Bayan ya fita, Zaid ya jingina da kujerarsa ya chigaba da tunani, batada lfya ne? Dazu kafin ya fita yaga kamar batada lfya amma tache mishi lfyar ta qalau stress din exams ne be saketa ba, ynzu kuma anche bata chi abnci ba, Anya ze gamsu da cewa gajiyar jarabawa ce ko dai yaje ya kaita asibiti ta samu proper checkup?

Ya ɗauki wayar ya qara gwada kiranta

A ɗayan ɓangaren, Maryam tana cikin barci, Wayarta seda tayi ƙara ba adadi kafin ta ji ta, ta buɗe idanunta a hankali ta ɗauka.

“Hello, Rouhi.” Ta fadi cikin muryar baccee 

Ya sauke sanyaya ajiyar zucciya “Kin sake komawa baccee ne? Jiya fah tun 9 kika kwanta, da asuba daqyar kikayi sallah sannan kika koma baccee, ynzu kuma kin sake komawa

Ta yi murmushi.

“Eh, Inata huta gajiya ne”

“Haya are you okay?”

“Alhamdulillah, I am”

“Okay Toh, please idan kinji wani abu yana damun ki call me immediately”

“Yes sir, kayi aikinka baccee nikeji”

“Okay Good girl, Zan yi ƙoƙarin dawowa da wuri yau.”

“Toh, Allah ya bada saa my rouhi”

“Ameen, ki huta, zan sake kira anjima”

Bayan sun kashe wayar, Maryam ta tashi ta zauna tana kallon window, tana jin daɗin yadda Zaid yake damuwa da ita, amma a wani ɓangare na zuciyarta ta fara mamakin dalilin da ya sa haryanzu stress din exam be saketa ba

Tun kwana biyu da suka wuche ta ke tsammanin za ta samu sauƙi, Amma maimakon haka, tana yawan jin weakness da baccee koda yaushe 

Daga zaunen da take taji baccin na fizgarta, se kawai ta kwanta ta chi gaba

Da dare a inda tayi sallar magrib nan ta zauna kan carpet tana azkar da niyyar se tayi isha zata tashi, amma batasan ya akayi tayi baccee daga nan ba

Se da zayd ya dawo ya shigo dakin ya ganta a kwanche kan carpet tana baccee, ya tsugunna gabanta yana shafa fuskarta a hankali, bude lumsassun idanunta tayi ta kalleshi, daqyar ta iya furta “rouhi” tana qoqarin komawa baccee

“Haya, kinyi isha?”

Ta girgiza kai

“Toh tashi kiyi sannan kiyi baccee”

Shi ya kaita toilet tayi arwallah suka fito, ya ajeta kan carpet tayi sallah saboda shi ya riga yayi, bayan ta idar yana jiranta ta qare azkar se kawai yaga tana gyangyadi

Tashi yayi ya chire mata hijabi ya kwantar da ita a kan gado yana mamakin wannan irin baccin anya na lfia ne.

Kwana biyu zayd ya kasa gane kan maryam, wani irin baccee takeyi sosai wanda ya fara daga mishi hnkali, se kuma wasu abubuwa da ya lura dasu ynzu, indai be dawo gidan kafin isha ba se ya tarar ta riga tayi baccee amma tana rungume da rigar shi, wai tanajin qamshin jikin shi, ya nuna mata turarukan yache ta rinqa amfani dasu amma tache aa tafi so shi yasa a nashi kayan a jikinshi takeso, idan yana gida kam tana maqale dashi koda yaushe, shi kam wannan abun daadi yake mishi sosai, amma sedai yawan baccin nata yake tunanin ko dai wani rashin lfya ne

Sannan kuma ya lura da yadda take qoqarin nuna mishi lfyar ta qalau, duk da wasu lokutan yana lura kamar tana ganin jiri, ya lura duk da qoqarin boye masa da takeyi ya gane sam batada kuzari yan kwanakin nan 

Yau da safe, suna zaune a dining zasuyi breakfast, zaid ya ɗauki spoon din da ya ciko da oats ya kai shi bakinta, amma kamshin shi da taji yasa ta toshe bakinta da hanci

“Rouhi yau bazan sha oats ba”

“Haya, kwanan nan se zaben abinci kikeyi?”

“Kwanan nan inajin cikina yana mini wani iri, I think I have digestion problem” 

Zaid ya ajiye cokalin hannunsa.

“Kin ga dalilin da ya sa nake son mu je asibiti? Wannan ba abin da ya kamata mu ci gaba da ɗauka da wasa ba ne, what if it’s a big problem?”

Maryam ta yi shiru. A gaskiya, ita ma ta fara damuwa, amma tana jin tsoron asibiti da allura

Ya miƙa hannu ya kama nata.

“Haya don’t worry, kawai ina son Dr ya duba ki, gwara musan minene problem din, tun last week kike chewa stress ynzu ai ya kamata ache kin huta, duk wannan baccin da kike sha these days uhm?” 

Ta gyada kai “Toh, mu je, amma kada ka bari ayi min allura please”

Ya gyada Kai “in shaa Allah”

Zaid ya kira assistant dinshi yasa yayi mishi appointment da wata female dr sannan ya gaya mishi cewa zezo office late ko kuma maybe baze shigo ba gabadaya, depending on abunda ze riqe shi.

A lokacin da suka isa asibitin, wata nurse ta tarbe su ta kaisu office din dr din, Dr ta yi ma maryam tambayoyi game da abubuwan da take ji, yaushe ta fara ji, da kuma wasu bayanai game da lafiyarta, ta debi jini ta bada lab ayi tests, sannan tache su dan jira kafin result ya fito, VIP section nurse dinnan ta kaisu suka zauna kafin tasa aka kawo musu ruwa sa snacks 

Maryam tana zaune maqale da Zayd hannunta a cikin nasa, saboda ynzu indai suna tare ji take kamar zata shige cikin jikinsa

Zaid ya lura da yadda taketa matse hannunsa.

“Haya, muna nan tare, ki kwantar da hnkalin ki, the results will be okay”

Ta ɗaga kai ta kalleshi.

“Idan wani babban abu ne ke damuna fa?”

“Ko minene a tare za mu fuskance shi in shaa Allah, so please don’t worry.” Ya qarasa zanchen yana qara matsowa da ita jikinshi ya rungume ta

Ta numfasa a hankali, sannan ta jingina kanta da qirjin shi

Ba da daɗewa ba Dr din  ta shigo wurin da kanta, ta zauna a gabansu tana riqe da da results na tests din da aka yi. Ta fara yi musu bayani cikin natsuwa, daki daki, chewa tanada low blood count, kuma batada enough nutrients a jikinta, tana buqatar nutrition sosai, sannan ta kalli Maryam tana murmushi.

“And Congratulations. The test confirms that you’re 10 weeks pregnant.”

Na ɗan lokaci, Maryam ta kasa motsi, second daya, biyu, uku..

Ta kalli Dr din, sannan ta juya a hankali ta kalli Zayd, kamar tana son tabbatar da cewa shima yaji abnda taji

“Pregnant?” ta tambaya cikin raunin murya.

Dr ta gyada kai.

“Yes. You’re pregnant. We’ll arrange the necessary follow-up appointments and discuss your prenatal care.”

Maryam ta ɗora hannu a bakinta, Idanunta suka fara cika da hawaye, amma batasan ko ma na miye ba, mamaki? Farin ciki? Ko tsoro?

Zaid kuwa ya yi shiru yana kallon Dr har ta qare bayani, Zaid mutun ne da ke shiga manyan tarurruka da conferences kuma yayi speech a gaban thousands of people ba tare da ko darr ko faduwar gaba ko wani abu ba, bayajin shakkun magana a ko’ina ko a gaban wa, baya jin tsoron komai, babu abnda zeche ya girgiza shi bayan rasuwar mahaifin shi, amma a yau, gashi a zaune ya rasa samun kalmar da zata fito daga bakin shi

Daqyar yaji bakin shi ya furta

“Are you sure?” ya tambaya a ƙarshe, muryarsa ta yi ƙasa tana dan rawa, muryar kamar ba tashi ba, jin yake kamar mafarki yakeyi

Dr ta tabbatar masa da sakamakon, Tana nuna mishi papers din, shi kam baya gane komai a bayaninta bayan da yaji tache she is sure, chi gaba ta yi da musu bayanin matakan kula da cikin da abin da Maryam ya kamata ta kula da shi, ta basu shawarwarin kula da lafiyarta, ciki har da abinci mai gina jiki, hutawa da kuma ranakun da za su dawo a sake duba lafiyarta.

Bayan likitar ta gama bayananta, ta ba su lokaci su fahimci abnda tache kuma suyi digesting don ta lura da irin shock din da suka shiga dukansu 

Maryam ta juyo ta kalli Zaid, Hawaye suka gangaro mata.

“Rouhi…”

Ya matso kusa da ita, yana kallon fuskarta kamar har yanzu bai yarda da abin da ya ji ba.

“Haya,” ya rada mata a kunne

“Da gaske..da gaske za mu… zama iyaye..zan zama daddy da gaske?”

Tayi shiru ta kasa amsa mishi

Ya runtse idanunsa na ɗan lokaci, sannan ya buɗe su yana murmushi. Ya kama fuskarta a hankali, yayi kissing goshinta.

“Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah In sha Allah zamu zama iyaye, ya amsa ma kanshi”

Maryam ta fashe da kuka tana rungume shi da qarfi, Zaid ya rungume ta sosai, yana shafa bayanta, zuciyarsa cike da wani irin farin ciki da bai taɓa ji ba, ya dade yana mafarkin maryam ta haihu tana koya ma yarinyar shi karatu, amma ynzu..a zahiri, maryam tanada ciki..cikin shi..babyn shi..”

Mafarkin samun ’ya’ya wani Abu ne daban, amma ynzu tunanin cewa ɗan ƙaramin mutum yana girma a cikin Maryam, matar da ta sauya rayuwarsa gaba ɗaya, ya sa ya ji kamar duniya ta tsaya mishi na ɗan lokaci.

“Alhamdulillah,” ya furta a hankali. “Ya Allah, ya baki lafiya, yasa wannan babyn ya kasance alheri a gare mu, Allah ya bamu me albarka”

Maryam ta ɗaga kanta daga ƙirjinsa tana chigaba da hawayen ta

“Ai duk kaine, ka tuna abin da ka taba faɗa min? Ka ce kana fatan Allah ya ba ka baby girl da za ta riƙa karanta maka Alƙur’ani.”

Zaid ya yi dariya a hankali, idanunsa har yanzu cike da farin ciki yana kallonta, har zeche bake kikache kinason baby ba? Amma se ya fasa

“Na tuna, Amma yanzu ba zaɓen mace ko namiji nike ba, Abin da nake so shi ne ke da babyn ku kasance cikin qoshin lafiya.”

Ta qara fashewa da kuka ta sake rungume shi.

“Shhshhhh” kawae yaketa rada mata a kunne yana shafa bayanta, yana kissing goshinta yana goge mata hawaye har ya samu ta tsagaita da kukan, suka karbi magani da supplement din da aka bata na masu ciki, ya dauketa har mota ya ajiye ta, ya rufe qofar ya zagaya ya shiga ya tada, se tafiya yake a hnkali ba speed ko kadan don ganin yake kamar idan yayi gudu wani abu na iya samum maryam ko babyn, tafiya yake a hnkali riƙe da hannunta kusan duk tsawon tafiyar, se tambayarta yake ko tana jin jiri, ko tana son ruwa, ko tana buƙatar a tsaya ta huta, Maryam tayi dariya saboda yadda yake jero mata tambayoyi duk se ya rinqa bata dariya ta manta da fargabar da take ciki 

“Rouhi, I’m not made of glass.”

Ya juyo ya kalleta.

“I know. But you’re carrying our baby, Haya. I can’t help worrying.”

Ta dan yamutsa fuska “ka fara ko?”

“Na fara me? Ki jira ki ga abin da zai faru daga yanzu ma”

Ta juya fuskar ta gefe, amma a cikin zuciyarta ta na jin daɗin farin cikin da yaketa nunawa”.

Da suka isa gida, Zaid ya taimaka mata ta sauka daga mota, sannan ya dauketa ya kai ta cikin gida. Samantha da Rachel sun lura da yadda fuskokinsu suka canza ba kamar yadda suka fita cikin damuwa ba, Maryam tana murmushi, Zaid kuma yana kallonta kamar ba ya son ya kau da idanunsa daga gare ta.

“Welcome ma, Is everything okay?” Samantha ta tambaya.

Maryam ta kalli Zaid, sannan ta yi murmushi tana sunkuyar da kai, a take su Samantha suka gane, saboda tun kwanaki suketa ganin symptoms a jikin maryam 

Rachel ta juyo ta kalli Samantha suka rungume juna suna tsalle

“congratulations sir” zayd ya gyada kai yana murmushi kawai

Tare suka matso suka rungume Maryam a hankali suna mata murna, Maryam ta yi murmushi, amma idanunta sun sake cikowa da hawaye, harynzu ta kasa gane hawayen me takeyi 

Zaid yayi ma su Samantha alama da hannu, suka juya suka tafi, ya dauki maryam ya hau sama da ita, ya zaunar da ita a kan kujera sannan ya zauna kusa da ita, ya ɗora hannunsa a kan nata.

“Yanzu dole ne ki kula sosai haya, banason kukan nan please, ko bakison babyn ne?”

Maryam ta yi murmushi a dd lokacin da hawaye suka sauko a Idonta wanda a ynzu ta tabbatar ko na miye

Zayd ya rungume ta

“Daga ynzu za mu tsara lokutan duba lafiyarki kamar yadda dr tache, Kuma ba na son ki yi ta gajiyar da kanki, ki dena aikin komai”

“In shaa Allah ai kaga ynzu hutun school ma mukeyi, banida wani stress”

Ya ɗaga kai.

“ina son mu yi magana game da makarantar.”

Maryam ta kalleshi da kyau.

“Wace magana?”

Ya ja numfashi a hankali.

“Haya, ina son ki dakatar da zuwa school har sai kin haihu, ki huta, ki kula da kanki da babyn a ynzu, bayan kin haihu kuma kin samu sauƙi, sai ki koma ki ci gaba da karatunki.”

Murmushin da ke fuskar Maryam ya ragu.

“Meyasa? Zan iya ai”

“Na san yadda kikeda dagewa da karatu haya, a ynzu banason abnda ze tada hnkalin ki, yanzu abubuwa sun canza, ba na son ki gajiyar da kanki ko wani stress ba wai dole na jiki ba, ko emotional stress yana iya sa wani abu ya faru da ke.”

Maryam ta cire hannunta daga nasa, ba cikin fushi ba, amma don ta nuna cewa bata amince da maganar ba

“Rouhi, ka sani, karatu yana da muhimmanci a gare ni sosai, banason inyi wasa da wannan damar, Ba na so kawai in dakatar da shi, ai ba wai rashin lfya nikeyi ba, kalleni lfya ta qalau”

Ya dan shafa kan shi 

“Ba chewa nayi ki bar karatu har abada ba haya, Na ce ki dakata na ɗan lokaci.”

“Amma ka faɗi maganar kamar ka riga ka yanke hukunci a madadina, baka tambayeni raayina ba” ta fadi hawaye na sauko mata

Zaid ya yi shiru yana lura da ita, sam bata saba yimishi gardama ba, se ya tuna da assistant dinshi na office yana gaya mishi lokacin da matar shi nada ciki yadda kullun take fitowa da sabon rikici kuma in yayi mata magana tayita kuka, akache mishi wai pregnancy hormones ne ya dena bata mata rai, ya fara tunanin ynzu shima haka zeyita rikici da haya har nan da wasu watanni kenan?

Maryam ta ci gaba da taji yayi shiru muryarta a natse amma cike da damuwa.

“Na fahimci kana son ka kareni ne, kuma na san kana cike da farin cikin samun babyn, nima ina farin ciki, amma samun ciki ba yana nufin na daina iya yanke hukunci game da rayuwata ba sedai a yanke min”

Zaid ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli qasa na ɗan lokaci kafin ya sake ɗaga kai.

“Kin san abin da ke bani tsoro, Haya? Ba wai makarantar kanta ba ce. Ina tunanin yadda kike yawan fama da kasala, kina jin jiri, kina jin amai kuma ga yawan baccee, banason ache ki takura kanki zuwa school, kuma kinga idan kina chan duk abnda ke faruwa dake bazan sani ba tunda ina office, ba hukunci na yanke miki kai tsaye ba, ina tsoron kada ki wahalar da kanki fiye da yadda jikinki zai iya ɗauka.”

Ta fahimci cewa a cikin maganarsa akwai tsoro, ba wai kawai son ya mallaki duk shawarar da ta shafe ta bane ko yanke mata hukunci kai tsaye, ta matsa kusa da shi.

“Na fahimci tsoronka, Ni ma ina jin tsoro, rouhi. Wannan shi ne karon farko da wannan abun ya fara samuna so banida experience, amma ina so mu tambayi shawarar dr, mu ga yadda lafiyata take, sannan mu yanke shawara daga nan”

Zaid ya kalleta, yana sauraron kowace kalma da take fadi

Ta chi gaba “Idan Dr tace ina buƙatar hutu, zan tsaya gida in huta, idan akwai damar yin wasu lectures online se inyi abuna daga gida don in rage zaman shuru”

Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya kama hannunta.

“Toh in shaa Allah haya, amma nidai nafison ki huta, kinga idan kina gida ko camera zan iya sakawa ina monitoring dinki daga office kuma kinga su Samantha suna nan, amma idan kina school bazan san me kike ciki ba” 

Maryam ta ɗan yi murmushi.

“Na kasa gane ko kana son ka kula da ni ko babyn ka”

“Duka ku biyu” ya fadi yana kissing hannunta da ke sarqe a nashi

“Fiye da yadda zan iya bayyana miki ma, za mu yi magana da Dr, sannan mu tuntubi school dinku idan ana buƙatar ki huta, za mu tsara yadda za ki ci gaba daga baya. Idan kuma akwai hanyar da za ki ci gaba da karatu a natse ba wani stress, za mu duba ta.”

Maryam ta rungume shi.

“Thank you, Rouhi.”

Yayi kissing goshinta.

“Amma kar ki rinqa hanani in damu da ke.”

Ta yi dariya.

“ba zan ma iya hana ka ba.”

“Good. Saboda na riga na shirya tambayarki ko kin ci abinci sau goma a rana.”

“Rouhi” ta fadi tana kwantar da kanta a qirjin shi

Ya yi dariya, yana shafa gashin ta

Washegari Zaid be fita aiki da wuri ba, ya lura da yadda maryam ke jin daadi baccee maqale cikin jikin shi, kuma yasa a ranshi kullun se idan ta tashi baccin safe a jikinshi sannan ze shirya ya fita aiki, yau bayan ta tashi ta shiga bathroom, ya tuna jiya da suna fira kawai yaji shuru har tayi baccee, ya tuna da yadda ya kwantar da ita sannan ya daga rigarta yana kallon cikinta da ke lafe, ynzu a wannan cikin mutum ze fito? Ya shafa shi a hnkali yana karanta addu’o’in tsari da zuria me albarka, fitowar maryam yasa ya dawo daga tunanin shi, ta shige closet don ta shirya se ya dauko wayar shi ya kira, yayi magana da assistant dinshi ya bashi umarnin yaje wurin dr din da suka gani jiya yayi mata kyautar da seta jijjiga ta, sannan kuma ya sake bashi umarnin gift din da ze kawo ma haya dinshi 

Yana shirin zuwa office assistant din ya kirashi yache gashinan ya iso yana waje, daukar matar shi yayi ya nufi qasa, tanata mamaki se taga ya bude qofar parlor suka fita sannan ya ajiyeta gaban wata rantsatsiyar mota rolls Royce fara qal se interior dinta brown color, ya karbi key din yana miqa mata tareda furta “thank you haya for giving me the best gift of my life” 

Wani irin tsalle maryam ta daka amma zayd ya tallabeta yana fadin “easy, kar ki maidani baya”

Maryam ta kasa magana saboda farin ciki, se kiss kawai ta kai mishi a goshi da kumatu tanata washe baki

A kwanakin da suka biyo baya, Maryam da Zaid suka fara sabon tsarin rayuwarsu, dama ta roqeshi akan kada ya gayama kowa, babu wanda ya sani bayan su dasu Samantha, ko mammi da mama basu gayama ba

Zaid ya tsara ranakun da yake clearing komi ya raka haya asibiti wurin check up, komi dashi akeyi kuma dole yake sata tana bin shawarwarin dr, sannan yana tabbatar da tanada abin da take buƙata koda yaushe

Ta yimishi magana game da tafiyar cruise ɗin da suka shirya, har yanzu tana son su je, yache ta bari se sunyi magana da dr saboda suji idan motion sickness baze jawo mata matsala ba.

Yau da dare, bayan sun yi sallar Isha’i sukayi shirin kwanciya, Maryam ta kwanta kusa da Zaid. Ta juyo tana kallonsa.

“Rouhi”

“Hmm?”

“Ka taɓa tunanin za ka ji tsoron wani abun farin ciki kamar haka?”

Ya yi murmushi.

“Ban taɓa tunanin wani abu zai sa in ji tsoro da farin ciki a lokaci guda ba.”

Ya ɗora hannunshi a kan cikinta.

“Har yanzu ban yarda cewa akwai ƙaramar halitta nan ba, a mini me and mini you”

Tasa hannunta a kan nashi, ya dago yana kallonta cikin tausayi.

“Za mu koyi komai a hankali, Haya, we’ll be fine”

Ta yi murmushi, sannan ta matso ta rungume shi. Ba da daɗewa ba barci ya ɗauke ta.

Yayi murmushi yana mamakim wannan irin baccee nata


Wani sabon babi ya buɗe, babi mai cike da bege, ƙauna da kuma ƙaddarar da har yanzu ba su san irin sauye-sauyen da za ta kawo musu ba. ❤️


Join our WhatsApp group 


Follow this link to join my WhatsApp group: ***

temp_image_10846612-4524-4F8E-A7EF-64A9290B6115.heic

temp_image_4D0AC7B2-0AF4-4A4C-A9D9-FA5BD444A81F.heic

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol