Free chapter · Read without an account

Page 48_49

by Ayshatou Galadima · MISHAL

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 

Page 48_49

‘Dan kallanta yayi kamar bai ji abunda tace ba . 
Ita kuma ta masa tsuri da ido tana rijan jin amsar da zai bata , amma kamar bashi da niyar hakan, wanda yasa tayi saurin judging cewa maganar Zarah kenan gaskiya ne , tunda ya’ki bata amsa.

Hannuwanta ga baki d’aya ta saka ta zare nasa daga jikinta , har sai da ya kalleta ganin abunda tayi. 

Ta mi’ke zata bar wajan. Ya kira sunanta cikin soft bawai da ‘karfi ba “ Mimi come back here 
”

Cikin ‘kun’kuni ta furta “ Bacci zanje nayi, good night
.”

“ In kikai one taku daga inda kike zan ‘bata miki rai , i said come back here, karki bari kuma na sake maimaita miki maganata.”

Komowa tayi wajanta ta zauna , amma bawai kamar yadda suke a da ba wannan ta d’an bada gaf a tsakanin su , sannan ba ma shi take kallo ba wani side d’in take kallo da ban. 

Hannuwansa biyu yasa ya janyota kusa da shi daga inda yake yana fad’in “ I said come back bance ki zauna far from me ba . So now look up ! Kalle ni
”

‘Daga idanuwanta tayi ta kallesa, kana ganin idanuwan kuma kasan kamar daf take da saka kuka anymoment , musamman da ta kalli face nashi sai taji ‘kwalla suna d’an cicciko mata cikin idanu.

“ Mimi repeat what you just said now!
.” 

Shiru Mimi tayi, zata d’auke face nata daga nashi sai yasa both hannuwansa ya talla’be fuskarta , so gentle yadda ba zama taji tsoran yin tanbayar ba . 

And hakan ne bata ji tsoro ba da yayi mata magana sai ma more confidence d’in sake tanbayarsa da taji acikin zuciyarta , hakan yasa ta d’an ja deep breath tana saukewa , duk wannan abun kuma fuskarta har lokacin yana tafin hannunsa. 

“ Uncle Moh dagaske kana san Zarah
?”tanbayar a hankali ta ‘karasa kamar me tsoran jiran amsar da zai bayar. 

Gefen bakinsa ne ya motsa kad’an kamar wanda yayi murmushi sai dai ko kusa babu wani murmushi da yayi , kallan face d’inta yayi sosai , musamman idanuwanta da take ‘ko’karin kaucewa nasa idanuwan. 

Sai ya matso da fuskarsa daf kusa da nata , kamar wanda yake shirin kiss d’inta amma ko kusa baiyi hakan ba “ Mimi who
is she ?”  

Da sauri Mimi ta kallesa jin abunda yace d’in, sai ta had’iye wani abu da yake ma’kogwaranta tun d’azu
 

Bakinta har rawa yake lokacin da take cewa “ Zarah ba, ‘kanwar Yaya Sadiq
”

“ I don’t know her
.” Ya kuma bata amsa .

Yanzu kam d’an ’bata fuska Mimi tayi ganin kamar ma tsokanarta yake ko he’s making fun of her , sai ta saka hannu ta sake same nasa daga fuskarta tana zama sosai, cikin ‘kasa ‘kasa da murya ta furta “ Uncle Moh ka santa ba , nidai shikenan kawai tunda bakasan amsa mun , and kai ne fa kace i can asked but ba komai na ha’kura
.”


“ Do you think ! I will lied to you Mimi?” Yadda yayi maganar so serious with a little bit cool a cikin muryarsa da yasa babu shiri ta girgiza masa kanta alamar a’a ganin yana ‘ko’karin komawa Moh d’insa.

Bakinta yana d’an rawa ta furta “ Ba haka nake nufi ba fa Uncle Moh! Am sorry bazan sake tanbaya ba.”

“ Nasan Sadiq but I don’t know Zarah , or kin ta’ba gani na tare da ita?”

“ No
.” Ta bashi amsa..

“ Kin ta’ba gani nayi magana da ita?”. 

Nan ma still ta kuma cewa “ No
” 

“ Then me yasa kike fushi without even thinking who you really her Mimi?.

Are you trying to make emotions control your sense or brain?

You’re trying to be sad because ba amsa question d’in ki ba , are you trying to be so quick? If one day you have to rule some certain people
. Are you trying to be so quick when judging them?.”

Nan ma Mimi ta kuma ce masa “ No
” sai yanzu ta soma regretting tanbayarsa wannan question d’in da tayi while in the real world ta manta wane ne Moh
.


Ganin ta sun kuyar da kanta ‘kasa ya furta “ Look at me Mimi
” 

Babu musu ta d’ago da fuskarta ta kallesan


“ Mimi why will i ever love a stone while i have a gem with me? ( Mimi, me zai sa in so dutse alhali ina da lu’u-lu’u a tare da ni?)


I have you as my gem ! Who is Zarah ? A stone?
.”

Dif dif Mimi taji hawaye na sauko mata a face nata , zuciyarta tana maimaita last kalamansa da sauri da sauri. 

Taji abunda yace amma kuma wani zuciyar nata yana fad’a mata kamar bata ji abunda yace d’in sosai ba , hakan yasa tayi masa ‘kuri da idanu kamar wacce take neman full bayanin abunda yake nufi da maganar sa , shi kuma sai ya d’an murmusa for the first time, ya d’an hure mata idanuwanta , babu shiri ta kulle idanuwan, tana sunkuyar da kanta akan     hannunsa , shi kuma ya gyara mata zuwa shoulder d’insa, yadda zata zama very very comfortable
 

Sabida yadda jikin su ya d’an  gogu da na juna yana jin yadda zuciyarta take bugu da sauri sauri..

Bai ce mata komai ba , ya bari tayi processing komai da yake zuciyarta , har saida bugun zuciyarta ya ragu sosai , ba kamar da ba , nutsuwarta da ya dad’e da d’aukewa d’azu ya dawo, ta kuma ta zama very relax.

Daga yadda take akan shoulder d’insa, kanta a ‘kasa ta d’an sake sauke ajiyar zuciya tana fad’in “ Uncle Moh?.”

 Shi kuma ya amsa mata da “ Uhmmm?.”

Sai ta kuma cewa “ Uncle Moh
”

A wannan lokacin murmushin gefen la’b’ba yayi mata “ Mimi
” shima ya kirata a hankali kamar yadda ta kirasa yanzu.

“ Haka tace mun wai she likes you, and you will always be hers
 Kuma kome zai faru , sai ta same ka wai kuna soyayya that’s why na tanbaye ka ko kana santa
 but am sorry 
”


A maimakon ya amsa mata maganarta , sai ya canza zuwa “ Do you want a story Mimi?
” 

‘Dagowa tayi ta kallesa da d’an mamaki ta furta “ Uncle Moh , daman ka iya story?”.

“ Answer me , yes or no
”

And she said “ yes
”

“ Let’s go somewhere
” ta mi’ke tare da ita a jikinsa, hannunsa yana cikin nata ya jata zuwa kitchen , ya fito da wannan Juice d’in da ta saka a fridge. 

A frizzer ta saka su, amma tunda ta gansu yanzu a fridge tasan shine ya sa su a wajan kar suyi ‘kan ‘kara . 

Ya mi’ka mata 2 glass of cup, shi kuma ya d’aki juice d’in suka hau sama..

Wannan d’akin da ya ta’ba shigar da ita har ya bud’e mata wani camera da ta ga hotunanta tana ‘karama nan ya bud’e mata suka shiga .

Tana shiga fuskarta ta zama so very excited daman tanasan ‘kara shiga sabida sosai take so taga komai da komai da yake cikin camera d’in sabida she feel so much attach to it
.

Daga inda glass d’in gift d’in nan suke , akwai wani abu me kama da touch a gefen guda d’aya, babu wanda yasan da hakan sai shi da yake da d’akin.

Yana dannawa wannan Glasses d’in suka bud’e , wani waje kamar living room, kamar office , kamar kuma irin wajan hutawa ya fito sosai 
.

A bayyane ta furta “ Wowwww*** tana shiga cikin wajan , shi kuma yana binta a baya, yadda take kallon komai cikin admiration
.. 

Jikin glass wall d’in take shafawa a hankali tana ‘kara kallan cikin wajan, har tazo tsakiyar wajan tana kallan waje, wajan yana saiti da d’akin Mimi, itama kuma sabida wani d’an flower da ta ajje a gane d’akin ta ne , if not ba zata ta’ba kawo hakan ba . 

Sai ta d’an juyo ta kallesa, shi kuma ya d’an d’aga mata girar sa guda d’aya , yana nuna mata wani 2 sitter alamar ta zauna.

Mimi da 2 cup d’inta ta samu waje ta zauna , while shima ya zauna , yana facing d’inta kamar yadda ita ma take facing nashi tana jira ya soma bata labarin
.

“ Mimi do you have any experience stories about families?”. 

‘Dan jim Mimi tayi kad’an kamar me tunani sai kuma tace masa “ A part from my family no Uncle 
”

“ I will tell you a story Little Mimi ! Historical story , zan soma miki from the very beginning, but only some part of the story zan baki, dare ya somayı yanzu
.”

“ Okay Uncle 
” Tayi maganar tana ‘kara bashi ga baki d’ay hankalinta , shi kuma ya ri’ke nata hannunta yana d’an shafawa a hankali,  kafin ya kalleta na ‘yan seconds yana kallan yadda ta nutsu tanasan jin storyn da za’a bata . 

“ Labarin 100 years story ne about a powerful family
..

When I said power, ina nufin real power family da suka had’a both polities, Mulki, Sarauta , Kudi and Say
.

Familyn da they don’t need any one protections , sabida how powerful they’re daga manyan family d’in har zuwa every single person da yake gidan , yana da kud’i
.” Sai yayi shiru for like a second , ita kuma Mimi har wani gyara zama take sabida yadda taji labarin ya soma zama so very interesting
..
Ganin yayi shiru ya’ki cigaba da labarin cikin za’kuwa ta furta “ Uncle Moh please ka cigaba 
..”

“ Okay a peck 
” ya nuna mata gefen kumatunsa . 

‘Dan dariya Mimi tayi har sai da ha’koranta suka fito waje,  ta d’an mi’ke daga inda take zata yi masa peck d’in, sai ya juyo da fuskarsa , a maimakon tayi pecking kumatun, sai lips d’inta ya sauka akan nashi, shi kuma yayi kissing d’insa at the same time. 

Ganin abunda yayi yasa ta furta “ Uncle Moh
” Tana d’an dukan ‘kirjinsa.
Shi kuma sai ya murmushi, yana d’aukar juice d’in nan. 

Mimi tana ganin haka ta d’auko masa cup , bai ce komai ba ya zuba a cikin 1 cup har sai da ya kusa cika cup d’in tukunna ya dakata .

Bakinta ya kai cup d’in, ta d’an sha amma ba sosai ba , shima kuma sai ya sha daga inda ta cire bakinta ya zamto kamar kiss


Yasha more than half d’in juice d’in, Mimi ta amsa cup d’in ta ri’ke tana masa narai narai da ido alamar ya cigaba da labarin 
.

Shi kuma ya d’an lakuci karan hancınta wanda yasa Mimi ta d’an ’bata face nata kad’an
.

Gyaran murya yayi kad’an. 
“ All this Powerful Family is controlled by only 1 person which is the GREAT MOTHER of the Family. 

Ita ce Mahaifiyar Sarki, Mahaifiyar Babban politician, Mahaifiyar Babban Business Tycoon Man da yake da matu’kar kud’i da  shi kansa bai san adadin abunda ya mallaka ba .

Ita ce kuma Mahaifiyar 3 powerful Daughter


‘Daya daga cikin su fitacciyar Business Women ce, da take controlling Business da yawa , ciki kuma tana da companies d’in kaya da har yanzu ‘kasashe da yawa suke anfani da kayan ta , sabida a waje maban banta da ta bud’e companynta.

Middle  sister d’in ta kuma She is a Cardiologist ( Likitan Zuciya ) tana san duk abunda ya dan ganci magani sabida yadda take san associating da different kind of people, hakan yasa ta bud’e Hospital itama da zata dinga bada magani
.

Sai kuma little Sister d’in su, the Apple of the whole family, musamman Great Mother d’in, tana san last born d’in gidan sabida suna kama , kuma tana da sunanta , infact a wajanta ta taso tin tana Baby, yawancin halayenta irin na Great Mother  d’in su ne sabida yadda ta d’auki most of the halinta , sai kuma ra’ayoyin su ga baki d’aya ya zamto kusan iri d’aya , the last born is very supportive of her Great Mother . Itama kuma Great Mother tana supporting duk abunda Little sister d’in su take so ko dai dai tayi ko ba dai dai tayi ba, tana kan  dai dai and babu wanda zai hukunta ta .” 

Yanayin shiru Mimi da tayi matu’kar za’kuwa da labarin ta furta “ Uncle Moh, kana nufin nobody can correct her ? Har Baban su ba zai iya hana su ba  , sabida Great Mother d’in?.” 

‘Dan kallanta yayi kafin ya amsa “ He can try Mimi , Amma tanbayar shine does he have enough courage to stand against VALERIA?”

Fuskar Mimi ga baki d’aya ta nuna confusion, cikin mamaki ta furta “ Wace ce Valeria kuma? I am a little bit confused Uncle 
”


“ I will explain Mimi
.”

Mimi tayi shiru tana jiran ‘karin bayani
.


“ VALERIA HAYES BLACKWOOD shine full name d’in Great Mother, sabida asalin family d’inta ba musulmai bane 
.. 

Akwai sunaye guda uku da ake kiranta da shi. 

‘Ya’yanta suna kiranta da Great Mother 
.. 

Grand Children d’inta suna kiranta da Great Grand Ma . 

A ‘bangaran mutanan da take da iko akan su ana kiranta da MA VALERIA BLACKWOOD 
 that’s 1 thing about Great Ma .

A farkon labarin na fad’a miki tana da maza uku mata uku. 

Her first born , Wanda shine Sarki sunansa KAREEM SULEIMAN AL- QADIR , he’s a muslim , sabida Babansa Suleiman Bin Al-Qadir musulmi ne kuma shine first husband d’in MA VALERIA BLACKWOOD.

KAREEM yana da Brother from the same father sunansa TAIMUR SULEIMAN AL- QADIR, kuma shine Babban Business Tycoon d’in familyn.

Sai third Brother din su which Shine Politician d’in sunansa “ ALEX . His real name ALEXANDER HAYES VICTOR
 shi d’in ba musulmi bane , Sabida Babansa ba musulmi bane , kuma Great Mother ma ba musulmi bane , that’s sunan baban Alex Hayes Victor



Business Woman d’in ’yarta which ita ce first mace a ‘ya’yanta sunanta MARYAM RAYYAN AL- QADIR da sister d’inta Cardiologist  SOFIYYA RAYYAN AL- QADIR 
  the have the same father the two of them . 

Sai the youngest sister d’in ßu Namesake d’in GREAT MOTHER , wato VALERIA HAYES VICTOR , she have the same father with ALEX
” yana kai wa na yayi shiru yana kallan Mimi da yayi tsuru tsuru tana kallansa, ta ma kasa cewa komai.. 

Murmushi yayi kad’an , yasan abunda zata tanbaya, shiyasa ya furta “ Mahaifin MARYAM DA SOFIYYA ‘kanin Suleiman Al- QADIR ne 


Wannan ne yasa Kareem da Taimur Suka zama ‘ Yayan wan baban su , kin fahimta yanzu?”.


“ Uncle Moh but how comes ta auri Yaya da ‘kani? Kenan ‘ya’yanta shida , Kareem da Taimur baban Ɵu d’aya , Maryam da Sofiyya Baban su d’aya , and Also Alex da kuma Valeria baban Ɵu d’aya ? How ? Sau uku tayi aure kenan?.”

“ Yeah
” ya bata amsa kamar wanda bayasan yin magana 
.

Da sauri ta furta “ But as how
.”

Hannu yasa ya d’an dungure mata goshi kad’an “ Story of another day
. Dare yayi Mimi
.” Yana fad’ar haka ya mi’ke .

Ita kanta Mimi batasan lokacin da ta ri’ko hannunsa ba tana fad’in “ Uncle Moh Dan Allah ka ‘karasa mun labarin i can’t wait please! Please
”


“ It’s a long story Mimi, idan na baki yau ba zaki ta’ba fahimtar labarin ba , have a little patience Mimi
”

Kamar za tayi kuka Mimi ta furta “ Toh zaka ‘karasa samun labarin gobe?
.” 

Jin yayi shiru ta furta “ Dan Allah Uncle Moh
. Inaso naji labarin ne 
”

“ I will give you some part of it Mimi
. Karki samun ciwan kai yanzu 
. A talk a lot now
”

Haka Mimi ta sake marairaicewa dan ita ji tayi baccin ma ga baki d’aya ya d’auke a idanuwanta, sabida she already start enjoying the story
.


Badan ta so ba ta furta “ Good night then Uncle Moh bari naje nayi bacci d’in
” zata bar wajan ya furta “ Who asked you to leave Mimi?.”

“ Uncle Moh ai kai ne kace naje na kwanta ai


Bai ce komai ba ya soma tafiya , hakan yasa ta biyo bayansa da sauri , ßuna fita ‘kofar wajan ta sake kullewa kuma, d’an waigawa Mimi tayi ta kalli ‘kofar sau d’aya sannan ta cigaba da tafiya har suka fito daga d’akin. 


‘Dakin kusa da nashi ya bud’e ya d’an matsa mata hanya alamar ta wuce . 

Babu musu ta shiga tana kallansa da jiran ‘karin bayani.

Shi kuma sai ya ri’ko Door d’in , fuskarsa babu alamar wasa , cikin umarni kuma ya furta “ A nan d’akin zakiyi bacci, check the wardrobe akwai kayan bacci , kiyi wanka ki kwanta , if you need anything ina next Door
”

Za tayi magana yayi mata wani irin kallo hakan yasa tayi shiru, shi kuma ya rufo mata ‘kofar. 

Mimi bata tsaya ‘karewa d’akin kallo ba , sabida tunanin labarin da Moh ya bata , da kuma tunanin me zata cewa Mammy idan ta le’ko d’akinta ta tarar da ita bata nan
  lastly kuma maganar Moh da ya sake dawo mata lokacin da yake cewa “ Me zaiyi da stone bayan yana da Gem
” Wannan tunanin su suka cika zuciyar Mimi da take zaune akan kujera , batasan lokacin da bacci ya d’auketa ba , ita bata kwanta akan gado ba , kuma ba tayi wankan ba .


Mintuna 35 , Moh ya shigo cikin d’akin nata , akan kujera da ya ganka ya girgiza kai kawai yana nufarta . 

Wayarta da take ‘ko’karin fad’uwa ya d’auka ya ajje a gefe, sannan ya d’auketa ga baki d’ayanta, yadda ba zata tashi daga baccin da take ba , ya wantar da ita akan gado, ya lullu’ba mata duvet, ya rage mata Ac . Infact sai da ya zauna a wajan yayi kamar 10 minutes ya tabbatar da baccinta ya soma nisa tukunna ya fita daga d’akin. 

________
‘Karfe 2:30am , a part d’in su Mimi
 lokacin dare ya d’an soma yin nisa , kuma kowa ya kamata ace yana hutawa a irin wannan time d’in
. 

A wannan lokacin ne aka murd’a handle d’in d’akin Mimi a hankali, ana turo ‘kofar d’akin, kamar na second biyu. Sai aka dakata na wasu second biyun, sannan aka ‘karasa bud’e d’akin ana shigowa a hankali. 

‘Dakin Mimi is so dummy, babu haske sosai a ciki sabida hasken fitila da aka riga aka rarrage , wacce ta shigo cikin d’akin ba’a ganin ko waye ne sabida kamar last time koma wane ne jikinta a lullu’be yake da ba’ka’ken kaya, ba’a iya ganin single abu da za’a iya sheda ko wace ce sabida har idanuwanta ba’a gani, haka take sad’af sad’af a cikin d’akin.

Kuma babu inda take nufa sai gadon Mimi . 

Abun mamaki gashi nan cikin duvet d’inta kamar akwai mutum da yake kwance akai , dan har ga d’an gashi nan a waje amma ba’a ganin face d’in wacce take kwance sabida duvet d’in da ta saka har wajan fuskarta ne sosai, da kuma yanayin kwanciyar da tayi tana juyawa ‘kofa baya.

Siririn abunda ta ciro last zuwanta shi ta sake cirowa, a yanzu sai da tabi a hankali sabida tasan yadda abun yake da matu’kar kaifin gaske . 

Ta saita komai da komai tayi ready d’insa akan wuyan wacce take kwance. 

Tana daf da sawa a wuya, wacce take kwance a matsayin Mimi ta d’an juya d’aya ‘barinta da yasa wacce take tsaye razana kad’an, sabida yadda tayi tunanin ko tashi Mimi d’in za tayi daga bacci.

A karo biyu ta sake attempting amma abunda ya faru da farko shiya sake faruwa wato motsin da ta kwance tayi , kamar me magagin bacci, sannan ta soma ‘ko’karin tashi daga bacci sabida lalluben abun kunna light da ta
soma. 

Cikin razani ta tsaya , ta ja baya gabaki d’aya ta koma bakın ‘kofa . 

Abun hannunta da take ‘ko’karin sha’ke wuyan Mimi dashi, tayi ‘ko’karin mayarwa inda ta d’aukosa , amma sai dai bata sani ba garin sauri guda  d’aya ya fad’i a wajan , kuma idan har ba shegen ta’be ta’ben mutum ba , yadda ya fad’in nan ba lalle mutum ya ganshi ba sabida it’s very light, kuma it’s not colourful at all. 

Bata ma tsaya wani second tunani ba tayi saurin bud’e ’kofar a hankali without making any some , ta fice da sauri. 

Wacce take kwance akan gadon Mimi kuma ta yaye ga baki d’aya duvet nata tana  kunna haske , Aya ce , ita ce ta kwanta kamar Mimi, idan ba ka kalli face nata d’in ba sai ka d’auka Mimi d’ince , jikinta sanye da wasu ba’ka’ken kaya tana kallan hanyar waje . 

Daga waje kuma lokacin da matar nan ta fito daga d’akin Mimi sai da ta soma dube duben babu kowa a hanya, sannan ta salalla’ba ta  sauka ‘kasa ..

A inda Aya ta ta’ba ‘buya kwanaki Alameen da tun d’azu yake wajan ya fito shima kuma sanye da ba’ka’ken kaya kamar Ameerah, yana kallan yadda take san d’an fita daga cikin falon ‘kasa . 

Sai dai Alameen ya tabbatar ta d’anyi nesa dashi, tukunna ya soma bin bayanta, har zuwa inda ta shiga wanda ita kwata kwata batasan Alameen yana bin ta a baya ba har ta shiga inda take san zuwa .

Aya ta d’auki atleast mintina goma kafin ta fito daga d’akin Mimi .
Shi ma kuma tana fitowa ta d’n dad’e a part d’in, kafin ta fito, ba tare da kowa ya ganta ba , ta shige part d’in su Zarah. 

Ta dad’e sosai a ciki ta fito ta shiga part d’in su Ameerah . 

Nan d’in ma ta d’an jima , kafin ta fito daga cikinsa ga baki d’aya
.

__________________

ISTANBUL

..

8:13pm Ahmet ya dawo cikin gida. Anne tana zaune akan kujera, ta d’anyi crossing leg nata , yadda idanuwan ta suke a rufe kamar me bacci. 

A hankali Ahmet yayi sallama sabida tunanin ko bacci Anne take baya so ya tashe ta a time d’in. 

A hankali yake tafiya zai bar wajan Anne ta bud’e idanuwanta akansa “ Ahmet ka dawo ?”.

“ Anne daman ba bacci kike ba?”

“ Da bacci nake haka zaka wuce kenan ba zaka tashe ni ba?.”

“ Haba Anne ! Taya zan tashe ki kina bacci kinsan bazan ta’ba iya hakan ba .” Yana dawowa ya zauna akan kujera kusa da inda Anne take .

“ Anne na same ku lafiya? Ya gajiyar jiki?”.

“ Lafiya ‘Kalau Ahmet !
Ka tashi dai kaje kayi wanka , already dinner is ready sai ka fito muci
”

‘Dan kallon sakanni yayi wa falon “ Aylin da Nunu fa?”.

“Nunu tayi bacci yanzu ma ita zan je na tasar sabida taci abinci, Aylin kuma na kira number d’inta bama ta d’aga kiran nawa balantana taji inda take 
.”

Kallan Anne yayi ganin tana ‘ko’karin d’orawa kanta damuwa .

“It’s fine Anne ! Zata dawo duk i da take and i promise zamuyi Dinner d’in tare , bari naje nayi wanka ki bar komai a hannu na .”

“ Shikenan Ahmet kaje kayi wankan , nima bari naje na duba Nunu d’in
”

“ Okay Anne
” ya mi’ke ya nufi d’akinsa, ita kuma Anne ta nufi d’akin da Nunu take . 

Yana shiga d’akin sa , wasu ‘yan danne danne yayi kad’an ya ajje wayar a gefe, bayan ya zauna kamar na mintuna goma sha d’aya , ya wuce ban d’aki dan ya shirya shima. 

Cikin mintuna kad’an ya shirya yayi komai, ya sake fitowa falon. 

Anne bata fito ba , sai ya zauna zaman jiranta . 

A wannan lokacin ne Aylin ta shigo cikin gidan, cikin yanga da taku , tana ganin Ahmet sai ta d’an hararesa kad’an , zata yi hanyar d’akinta ya kira sunanta .
“ Aylin?”.

Juyowa tayi ta kallesa ba tare da ta amsa sunan nata ba “ Kiyi maza ki dawo muyi dinner , karki bari Anne tayi complain akan ki yanzu 
”

“ Idan kuma tayi fa ?”

“ Then zaki ga abunda zan iya yi a lokacin Aylin
 rubbish girl
”

‘Karamun tsaki Aylin tayi wanda ita kad’ai taji abunta , bata kuma tankawa Ahmet ba tayi wucewarta d’aki, ‘yar jakar hannunta ta jefar akan gadon , tana faman yin tsaki a jajjere kamar wata tsaka.

Ba ma ta cire kayan jikinta ba ta sake fitowa , lokacin su Anne sun fito suma, Anne bata ce mata komai ba , ta dai kalleta sau d’aya daga nan ta kalli su Nunu “ Ku tashi muci abinci kar yayi sanyi
” ta nufi dinning , suma kuma duk suka mara mata baya .

Ahmet yana ganin abincin da Anne ta girka yayi murmushi “ Jazakallah khairan Anne
”

“ You’re welcome Ahmet..” Anne tayi serving d’insa, ta kuma yi serving Nunu, ta kalli Aylin “ Me zaki ci Aylin?”

Kamar wacce aka ce dole sai tayi magana ta furta “ Just anything is fine 
” kallanta Anne tayi, da sauri Aylin ta sunkuyar da kanta , a maimakon Anne tayi serving nata sai ta ajje serving spoon d’in, ya kalli su Ahmet “ Let’s eat
” Suka soma cin abinci, hakan yasa babu shiri Aylin ta d’auki Spoon tayi serving kanta,tana ci ko d’agowa ba tayi, daman kuma in suna cin abinci baƟa magana , babu wanda yayi maganar har suka gama ga baki d’aya.

Anne ce ta soma fad’in Alhamdulillah.. sai Ahmet da ya gama , amma kuma bai tashi daga wajan ba , sai da Nunu ta gama cin nata ya soma kwashe abubuwan yana shiga dasu kitchen. 

Duk wanda ya d’auka kuma sai ya wanke tukunna yake fitowa , ya gama kwakkwashewa saura na Aylin, ganin plates nata ne kawai yai saura sai ta dakata da cin abincin da take , ta d’an matsar da plate nata yadda zai gani, zata mi’ke ta bar wajan ya furta “ Hey hey 
 wa zai d’auke miki wad’an nan abubuwan da kika bari kuma?”

“ Ahmet kwashe kake , and what’s the problem dan ka d’auki plate d’ina ka wanke?”.

“ Okay kinga na miki kama da wanda zaki aika ko ki saka wani abun? Tun wuri ki kwashe wad’an nan abubuwan ki tabbatar kuma kin wanke su , kar ki bar mana kitchen da datti
”

Kallan Anne tayi ko za tayi magana, amma Anne bata ce komai ba , hakan yasa ta d’an kulu sosai , cikin d’an jin haushi ta soma kwashe plate d’in tana wucewa kitchen dasu, su kuma suka dawo cikin falo 


Nunu tabi ta kai nainaye sa, tana kwanciya akan lap d’insa , shi kuma yana d’an wasa da gashin kanta “ Memet
..” ta d’an kira sunan sa cikin ‘yar muryar yaranta 
..

‘Kara shafa gashin kanta yayi yana fad’in “ Naam Nunu 
.”

“ Memet wasa, ni school babu 
( Memet yaushe zamu fita wasa , ni banasan zuwa school shine abunda take nufi). Already ya gane yanayin maganar ta kuma yasan me take nufi shiyasa ya furta “ Zamu fita wasa Nunu amma ai dole ki dinga zuwa school, ko bakya so ki girma kamar ni?”.

Da sauri ta furta “ Bani so
” Wanda yasa Ahmet yin dariya sosai da sosai, ita kuma ta d’an soma shash she’kar kuka , za tayi kukan ya d’agota sai ga hawaye
Sharrr ya sauka a kan cute face nata .

Hannu ya saka ya goge mata hawayen “ Ya isa haka ! Wa yace miki kiyi kuka kuma? Let’s go out and play
”

Wani irin dariya Nunu tayi me kama da ihu ihu , irin kamar wacce akai wa dariya haka ta soma ‘kyal’kyalewa , shi kuma ya kalli Anne da bama su take kallo ba “ Anne bari muje mu dawo
”

“ Ahmet kar ku dad’e 
” shine abunda tace 


Ya amsa mata da “ Okey Anne , Bye bye 
”

Itama kuma Nunu ta d’aga mata hannu tana fad’in “ Bye- Bye 
.” Ya d’auketa suka fita .

Falon yayi saura Anne. Aylin tana fitowa zata wuce Anne ta kira sunanta “ Aylin
” da wani irin turn , sai da Aylin ta d’an dafe ‘kirjinta da taji kiranta s

‘Dan waigowa tayi ta kalleta “ Naam Anne
”

“ Samu waje ki zauna
..”

Hakanan babu musu Aylin ta samu waje ta zauna tana facing Anne sosai
..

“ A kwanakin nan kin soma canzawa , ba kamar lokacin da kika zo nan gidan ba Aylin, ko me yasa hakan?.”

Babu shiri muryar Aylin ta soma daddare wa , hannuwanta har ya soma rawa rawa , cikin rawar baki ta furta “ Uhm Uhm ba haka bane Anne, ina nan kamar yadda nake ada
”

“ Ki amsa tanbayar da nayi miki Aylin
”

Cikin sauri Aylin ta furta “ Anne, kawai Moody ne kinsan not every day komai yake kasancewa yadda mutum yake so , and kuma am so moody because of my menstrual cycle
.”

“ Dan haka kiyi aiki sosai akan Mood d’in naki. Na kira number d’inki me ya hanaki d’aukar waya na Aylin ?.”

“ Anne wayan yana silent shiyasa ban kula sosai ba
”

“ Baki ga kirana ba , amma ya akai kika ga kiran Ahmet?.”

Aylin tayi shiru sabida bata da abun cewa 
.

Anne bata kuma ce mata komai ba , ta tashi tayi wucewarta d’aki, wanda hakan yasa Aylin ta wuce nata d’akin cikin sauri , tana rufo ‘kofar d’akin ta .

“ Me take nufi dani ne ? Me yasa zata bi ta soma yi mun irin wad’an nan tanbayoyin?Why? Ko ta soma bincike akai na ne ?”. Tayi wa kanta tanbaya kuma babu bai mata amsar tanbayar ta , hakan yasa ta d’auki waya tayi d’an danne danne ta turawa wasu message , sannan ta koma cikin Talk Zone d’in su sabida yadda taga ana magana me zafi a ciki
..

Ahmet da Nunu sun d’an jima sosai a waje , kafin su dawo lokacin dare yayi sosai, har tayi bacci ma a hannunsa, yana zuwa d’akin Anne ya ‘kwan’kwasa , tana bud’ewa sai ta amsa Nunu shi kuma yayi mata good night yana wucewa nashi d’akin.

‘Karfe 3:10am time d’in an kakkashe fitilin yawanci ko ina , sai kad’an da aka bari da alama lokacin da Ahmet zai wuce d’aki ne ya kashe su
.

Fitowa Anne tayi daga cikin d’aki ba tare da ta bari ko sound d’aya na bud’ewar d’akinta ya fito ba . 

Jikinta da ba’ka’ken kaya ta yafa har akanta sabida kar a ganta , sai da ta kuma kashe fitila guda d’aya a cikin gidan , ta hanyar da zata fita tukunna ta fice ga baki d’aya daga cikin sauri
..

Ahmet da yake windown d’akinsa ya ga fitar ta dan tun d’azu ba bacci yake ba , idan sa biyu ga kuma hot coffee da yake hannunsa sai faman turiri yake yi
.

Kamar minti goma da fitar Anne bayan ya gama shan coffee d’in hannunsa ya sauko ‘kasa d’akin Anne. 

Sai da ya sake dubawa Nunu tana bacci babu wani matsala , sannan ya zagaya ta bayan d’akin Aylin yana kallan Windown d’akinta , itama kuma kamar bacci take a wannan time d’in , ya sauka zuwa ‘kasa , akwai wani bookshelves  dogo me fad’i da yake cike da books masu baya a ciki, nan Ahmet ya bud’e , littattafan wajan suka rabu waje gida biyu , ‘kofa ta bud’e wani d’aki ya fito. 

Yana bud’e d’akin shi kuma bookshelves d’in ya sake kulle kansa



Is a very huge d’aki. Yana da matu’kar girma sosai kamar a had’a d’akin mutane hudu a ciki. 

Fitilan d’akin ya kunna ya kalla, teddies ne dayawa a ciki ba na wasa ba , different colours , different size har akan gado akwai teddies kuma babu wacce take a bud’e ko wacce tana cikin ledar ta da ‘yar ‘karamar sticker me rubutu da aka ajje a wuyan ko wacce teddy da take wajan. 

A hankali ya soma takowa cikin d’akin, yana tafiya yana kallan teddies d’in nan , fuskarsa d’auke da murmushin da fuska ba zata iya musaltashi ba sai zuciya sabida shi kad’ai ne yasan ma’ana da kuma dalilin da yasa yake murmushin a wannan lokacin. 

Wata farar teddie da take gefe guda ya nufa, all his knees a ‘kasa ya d’an ta’ba gefen face d’in abun, sai ya sunkuyar da kansa ‘kasa , tunani da yawa suna faman yawo a cikin ‘kwa’kwalwarsa da har sai da ya dafe kansa sosai sabida yadda yaji yana faman sara masa
.

Mi’kewa tsaye yayi ya kalli wani wall da aka saka frame d’in flower a wajan. 

Kuma frame d’in yana da girma sosai , sai mutum ya taka abu tukunna zai iya cirosa duk girmansa kuma yana bu’katar matai maki, sabida yana da nauyi da fad’i , amma haka Ahmet ya cirosa , saura kad’an ya fad’o masa a hannu, kuma da ya fad’o
masan ba ‘karamun yanka zai masa ba sabida akwai glass a jikinsa . 

Yana ajjesa a gefe zaka ga wni d’an digo da yake tsakiyar wall d’in , nan Ahmet ya ta’ba , a hankali wall d’in ya soma jan baya kamar yana ‘ko’karin darewa , yayında wani babban hoto da yake a lullu’be yake faman bud’ewa a hankali, har ya bud’e ga baki d’aya jikinsa . 

THE GOLDEN EYE’s Shine abunda ya soma cin karo dashi. 

Yes pure golden eyes, bayan shi babu abunda ake gani sai zara zaran lashes d’in Yarinyar da take cikin hoton nan, ko ba’a nuna full hotan yarinyar ba , daga yanayin idanuwanta , da kuma lashes nata zasu tabbatar da cewa hotan idan yarinya ne 
.

Daga ‘kasan hotan anyi dot dot dot 
. Babu suna a jiki, sai da ya kalli hotan sosai, har launin idanuwansa yana ‘ko’karin canzawa tukunna ya sauke ajiyar numfashi yana matsar da hotan gefe ta hanyar ta ‘basa, a nanne second picture ya fito, sai dai wannan picture d’in black ne ba’ayisa da colour me haske ba .

Wani huge body builder ne a jikin
Hotan, ba’a ganin fuskarsa, sabida ya bada baya , ta haka akai hotan kuma kanar yana cikin tafiya ne aka d’auki hotan .

Jikinsa sanye da suit amma ba’a gane asalin colour d’in suit d’insa tunda bashi da colour hoton, takalmin ‘kafarsa har a cikin hotan shinning yake .

Hannunsa guda d’aya yana sanye cikin aljihun wandonsa, d’aya hannun kuma lighter ce ya bud’e har d’an wuta ya kunnu a jikinta , babu wani suma sosai akansa sabida ya aske ta , bawai irin askin ga baki d’aya ba , no ya rage kaso kusan 70% cikin 100 % na gashin, ga wani ‘karamun tsaga da gashin yake dashi ta bayansa wajan ‘keya
.

Ya Allah duk da ba’a ganin fuskar me hotan nan, har wani irin Aura da feeling mutum zai dinga ji, uwa uba tsoro kuma kamar wanda ya ga zaki
. 

Hannu Ahmet ya saka ya d’an ta’ba hotan, take a wajan single drop na hawaye ya sauka akan face nasa da yayi saurin sa hannu ya goge
. Sai kuma ya kalli ‘kasan hotan inda aka saka “ EMIR ZAYDAN AL-QADIR
..” anyi rubutun harufan kamar da wani sassa’ken cike, me zallan ba’ki da brown a jikinsa .

Hotan yana da kyau sosai ba kad’an ba , duk da ba’a ga fuskar me hotan ba, amma mutum can easy fell in love dashi dag yanayin bayansa sabida Allah yayi masa ‘kira
. So beautiful ! So Elegant and so Wowwwww
..

Ya dad’e sosai a cikin d’akin yana ‘karewa both hotuna guda biyun kallo, har sai da 4 da wani abu ya gota lokacin da yasan a ko wana time Anne zata iya dawowa , tukunna ya koma nashi d’akin






_____________________

ABUJA 

4:30am ya shigo d’akin da take . 
Ac ya soma ragewa kafin ya kunna hasken d’akin. 

Yana sanye da dogon wando fari, sai ba’kar singlet da ta fito da murd’ad’d’an muscle d’insa, daga jikin singlet d’in ma ana iya ganin packs d’insa sabida hawa jikinsa da tayi sosai


Gashinsa ba a kame suke ba shiysa har a gaban face d’insa sai da suka d’an le’ko time d’in da yayi ‘ko’karin zama a gefen bed d’in. 

Da hannu d’aya yasa ya mayar dasu baya yana d’an tatta’basu, idanuwansa ga baki d’aya akan Mimi da take baccinta so peaceful
.

Gefen pillow d’inta yayi tapping kad’an , tare da kiran sunan ta a hankali “ Mimi!..”

Shiru Mimi bata amsa ba . 
A karo na biyu ya kuma tapping gadon yana fad’in “ Mimi!” 

Sai a time d’in tace “Uhmmm
” Tana ‘ko’karin juyawa wani side d’in, ya hanata ta hanyar ri’ko kafad’unta da yayi kad’an , ya mi’kar da ita zaune a hankali.

Rigar jikinta duk ta zazza me, kafin ma ta bud’e ido ya ja mata rigar ya rufe mata jiki, yana d’an jijjigata “ Bud’e idonki Mimi karki sa na makara sallah, it’s almost time 
.”

Mimi ta kuma cewa “ Uhmm.” Tana ‘ko’karin ’kara komawa 


“ Kinasan ki makara sallah abi? Open your eyes 
” ya kuma magana dai dai kusa da ita 
.

A hankali Mimi ta bud’e idon tana sake rufewa , kafin ta sake bud’e su ga baki d’aya akan Uncle Moh da shima yake kallanta
.

Cikin muryar bacci ta furta “ Uncle Moh?.”

Shi kuma ya furta “ Naam Mimi?”.

The next abunda zai fito daga bakin Mimi shine “ Uncle Moh wai kana san Zarah?”.

Sai da ya d’an d’aga ido ya kalleta sosai, wani murmushi yana saukowa akan la’b’bansa , kuma dagaske baccin ma bai gama sakarta ba , da alama tunani take ko bacci take har yanzu, that’s what makes him ya girgiza mata kanshi, har lokacin kuma murmushin bakin nasa bai tafi ba 
.

“ I don’t know her Mimi! So I don’t like her
”

Cikin muryar bacci ta kuma cewa “ Toh in bakasan Zarah wa kake so? Aunt Aya?.”

Sai da yasa hannu ya d’an ta’ba goshinsa ganin how childish she is now “ No Mimi ! Itama bana santa
”

“ Toh wa kake so ?”

Bai amsa mata ba , ya yaye duvet d’in jikinta ya mi’kar da ita , sannan ya kama hannunta zuwa toilet, sai da yaje har wajan sink ya d’an d’ebo ruwa kad’an ba yadda zai ji’ka mata kaya ba ya wanke mata face.

Taja wani numfashi tana kallansa sosai “ You’re not dreaming Mimi!  Ba mafarki kike ba , lokacin sallah zai iya wucewa 


Ki wanke face d’in ki , ina jiran ki yanzu 
” bai kuma kallanta ba ya fita daga toilet d’in.

Bin bayansa Mimi tayi da kallo yana recalling abunda tayi , dan dagaske batasan ya akai tayi masa wad’an nan tanbayoyin ba . 

Hannu tasa ta rufe fuskarta tana fad’in “ shikenan Mimi kin shiga uku
.” Sai tayi sauri ta wanke face d’inta ta fito, tana faman sun kuyar da kanta ‘kasa , sabida batasan ma su had’a ido kwata kwata 
..

Bai ce mata komai ba suka sauko
‘kasa ya mi’ka mata hijab d’in ta da yake a ninke 


Babu musu ta amsa ta saka hijab d’in ya kama hannunta suka bi ta wannan hanyar, har ya bud’e mata ‘kofa ta’ki kallansa .

“ Mimi..” ya kira sunanta .

Hannu tasa akanta tana d’an sosawa sai ta jiyo ta kalli inda yake amma bata bari sun had’a ido ba 


“ Kalle ni , ba canai ki dinga kaucewa kallo na ba 
”

A d’an shagwa’be ta furta “ Uncle Moh lokacin sallah yayi fa zaka makara
.”

“ I said look at me Mimi
”

Dagowa Mimi tayi ta kallesa, tana tsoran kada yayi mata fad’a akan abunda tayi, fuskarta ya nuna d’an tsoro tsoron nan
.

“ Kin wartsake yanzu?”

Mimi ta furta “Eh ..” a hankali
.

“ Then Banasan Zarah , you can now sleep peacefully
.”

Mimi batasan lokacin da ta furta “ Innalillahi 
” har wani dariya dariya ne yazo mata , kafin yayi magana ta arta a guje zuwa zama


‘Dan girgiza kansa yayi ya juya kawai ko ‘ko’karin tsayar da ita bai yi ba .

Mimi tana shiga d’aki tayi saurin tura ‘kofa kamar ance mata idan ta matsa daga kusa da ‘kofar zata gansa .

Hannuwanta ga baki d’aya ta saka ta rufe face nata , tana maimaita maganarsa , deep down wani irin kunya ne ya kamata , ganin yadda ya ramfo maganarta lokaci d’aya. 

A gefe d’aya kuma she’s happy tunda , irin serious happy d’in nan tunda yace mata bayasan Zarah , and she agreed with him
 

Ganin idan ta zauna za ta cigaba da wannan tunanin nata ne tayi saurin ajje sa a gefe ta wuce toilet , tayi abunda za tayi ta fito. 

Tanayin sallar tayi Addu’a , sai karatun kad’an da tayi , ta wuce  toilet tayi wanka abunta, inners kawai ta saka , ta d’ora doguwar riga a jikinta ta ‘kure Ac d’aki ta shige cikin duvet../ 

Wani irin lumshewa take a cikin pillow tana jin wani irin dad’i da batasan na mene ne ba yana faman yawo a ko wana zazza na jikinta da ruhinta, sai kuma labarin jiya da ya soma bata , she just feels like tanaso taji ‘karashen labarin , she’s having so much interest akai, kad’an kad’an kwa’kwalwarta take sake maimaita mata labarin Valeria, kafin bacci ya d’auke da tunanin last kalmar da ya fad’a mata “ BANASAN ZARAH

”

_____ ‘karfe 12:45pm Ameerah da ta shigo d’akin Mimi ta soma jijjigata.

Mimi tana baccinta me dad’i taji ana faman jijjiga ta , babu shiri ta bud’e ido taga shafaffe da man da ya tashe ta daga bacci , sai taga Ameerah a tsaye a kanta , tana d’an d’age mata gira .

Tsaki Mimi taja , zata kuma jan duvet Ameerah ta ri’ke sa gagam, “wallahi babu baccin da zaki koma , tun d’azu kike bacci sai kace kasa , sau biyu fa ina shigowa d’akin kina bacci sai gaman murmushi kike ke d’aya kamar wacce akayi wa bushara da Aljanna
.

Dallah tashi , d’aya fa ta kusa yı kina ya faman bacci , haka zan aurar dake ?.”

“ Ameerah banasan iska ki kyale ni, bacci nake ji, idan na gama baccin ai zan tashi da kai na ko?”.


“ Wallahi babu baccin da zaki koma lalle ma ‘yar nan, ace d’aya ta kusa kina faman bacci, ke d’aya ce a cikin part d’in nan fa , yau Mommy da Mammy sun fita , already wajan 9:30 su Baffa suka fita su uku da shi da Baba ( Uncle Bashir) da Daddy ( Daddyn Zarah ) sun tafi wata jana’iza , Aunty Shukura kuma daman kinsan ita ce Allaji boka tuni tana makaranta , banga Aunty Aya ba nasan kuma may be itama ta fita , sai ke kad’ai  a part kowa ya fita kina wannan asararran baccin naki ko?.”

Mi’kewa zaune Mimi tayi sosai tana d’anyin hamma “ Yau mutanan gidan duk fita sukai?”.


“ Oho miki, malama tashi kije kiyi bacci , kar na manta labarin da nazo baki dan yau Mama ma itama har ta dad’e da fita tana asibiti, tace mun ko zanje nace mata nahi nahii bacca..” Tana kaiwa nan ta wani irin ‘kyal’kyalewa da dariya har sai da Mimi ta d’an tsargu da irin dariyar Ameerah yau..

“ Wai Dan Allah me ya faru?” Tayi maganar tana mi’kewa tsaye 
”


“ Ki shirya mana , zan baki labari, ina falo dan Allah kiyi sauri kiyi wanka 
”

“ Already nayi wanka Ameerah fuska na zan wanke , na shirya am coming..” Tayi saurin nufar toilet , ita kuma Ameerah ta fito falo. 

Already daman ta d’ora musu d’an wake kafin tazo tashin Mimi. 

Da taje d’an waken har ya d’an soma zuba kuma ya dafu, ta zauna had’a musu Geee ( Gee wani had’i ne mostly ‘yan niger suke a had’a cucumber , tumatur , pabron ( koren tattasai) , albasa , leman tsami, maggi , mai da kuma green Attaruhu da ake d’an sawa kad’an ). Omo gashi kunsan tumatur yana d’an narkewa Hakan yasa G d’in ya d’anyi ruwa ruwa , idan kayi testing zaka ji su ba tsami ba kuma ba za’ki ba , but it’s 100% 
. Ameerah ta had’a musu ta fito dashi falo, akan carfet ta ajje , ta d’auko wani cool 5alive da 2 cups , tana ajje wa Mimi na fitowa , ta saka wata doguwar riga da tazo mata har gwiwar ‘kafarta , red colour da kuma pencil jeans d’in wando , sai d’an kwalin kayan da ta d’aura shima red colour , ta d’anyi baya da d’an kwalin kad’an gashin kanta ya fito. 

Mimi tayi kyau sosai da sosai ga d’an lip balm da ta saka a bakinta sai faman shinning yake 
 

Tana saukowa taga abunda Ameerah tayi musu ta furta “ Awwwwwwn so nice of you
. Sabida kwad’ayi wallahi hannu na har rawa rawa naji yanayi mun
”  ta d’auki bowl d’in Gee tayi 1 spoon kafin ta wani ja nunfashi tana fad’in “ Perfect
” 

Sai ta samu waje sosai ta zauna, Ameerah ta zuba musu d’an waken su a cikin middle tray , ta zuba Gee d’in nan ga yajin su a gefe, Mimi ce ma ta zuba musu 5alive d’in , sabida tafiso tana cin abinci tana shan wani abu me ruwa ruwa , in ba haka ba abincin zaiyi saurin ginsarta neee
”

Ganin zasu soma cin abincin Mimi ta d’an harari Ameerah “ Baki bani labarin da kika ce zaki bani ba fa?”.

“ Saurin me kike , yanzu ai nake shirin fad’a miki 
. Kin gane guy d’in nan da suka zo gidan mu? Shi da sister d’insa? Mahmoud yake kowa? Kin dai gane shi ko?.”

Mimi ta jinjina mata kai alamar “ Eh” tana ‘ko’karin sipping juice d’inta 


“ Jiya aka kira Mama aka ce mata wai yayi accident, yana asibiti ya d’an ji ciwo a face nasa sai kuma?.” Sai tayi shiru tana ‘ko’karin saisaita dariyar da yake ‘ko’karin kwace mata .

Cire juice d’in bakinta Mimi tayi tana fad’in “ Sai kuma?” Kafin ta saka mayarwa tana sipping
..

“ Wai accident d’in, har da Anniniyarsa, amma dai Anniniyar bata samu matsala ba
.” Tana kaiwa nan wani irin dariya ya ‘kwace mata, Mimi da take shan lemo tayi saurin ciresa daga bakinta sabida yadda dariya da ‘kwarewa suka zo mata a lokaci d’aya . 

Kuma ta kasa ha’kura da guda d’aya, tana tarin, tana dariya har da hawayenta sabida yadda wani irin mugun dariya da batasan a ina ta koya ba ya soma ‘kwatarta ta ‘karfin tsiya 
 Mimi har da ajje cup d’inta a ‘kasa ganin lemon yana ‘ko’karin ‘barewa , da sun had’a ido tare zasu kuma ‘kyal’kyalewa da wani saban dariyar duk da basu bud’e baki sunyi magana . 

Sai da sukai mai isar su tukunna sosai, Mimi ta furta “ Amma garin yaya? Astagfirullah wannan tsautsayi haka?”.


“ Bashi d’an iska ba? Ai wallahi Allah shi’kara nayi masa da naji , toh me zai sa nayi wa d’an iska sannu, may be ma alhakin kine ya kama d’an iska ya samu wannan accident d’in, na tabbata ko nan gaba aka ce yazo gidan nan ba zai zo ba 
”

“ Uhmm Allah dai ya kyauta Ameerah , Allah yayi mana tsari dasu
.”

“ Amin Juliet
.”

Wani irin kallo Mimi tayi mata “ Wace ce da wannan sunan kuma ? Who is Juliet?.”

“ Ikon Allah yo ni kuma bazan fad’in sunan da naga yayi mun ba? Ji nayi kawai sunan ya mun dad’i shine na fad’a ko da magana? Muna gama cin d’an waken nan ma zan kunna wa’kar India sabida yau soyayyar Abdul ce a raina
”

“ Wallahi ‘karya kike Ameerah da biyu kika fad’i wannan maganar , me ma’anarta please?.”

“ Yanzu so kike abincin mu yayi sanyi ne ? Yunwa nake ji ki bari muci abincin mu lafiya kar appetite d’ina ya gudu hilis
.” Da haka ta soma cin d’an wake .

‘Dan kallan seconds Mimi tayi mata itama ta soma cin d’an waken ba tare da ta sake tayar da maganar ba 


Sun gama ci sun dawo falo again, Ameerah ganin Mimi na kallanta ba tace komai ba ta d’anyi dariya “ Fine bari na fad’i abunda yake rai na . Dake nake Mimi, your the Juliet
 Omo Mimi daman soyayya kike da Uncle Moh shine ko sau d’aya baki ta’ba fad’a mun ba?.”

Mimi ji tayi zuciyarta ta buga da ‘karfi har sai da ta sake waigawa falon ta tabbatar su biyu ne kawai “ Ameerah ba soyayya muke ba, waya fad’a miki wannan maganar.”

“ Ai nasan haka zaki fad’a , so in kuna soyayya d’in ma mene ne da ba zaki fad’a mun ba ? Like are you serious Mimi?.”

“ Ke wallahi kinji na miki rantsuwa ba soyayya muke da Uncle Moh ba , taya zamuyi soyayya dashi ba ko? Taya zan miki karya ne wai? But in baki yadda ba kuma shikenan , the choice is yours
”

Suprise sosai ya hau kan face d’in Ameerah “ Please are you serious? Like are you really really serious? But scene d’in da na gani fa?”

“ Wana scene and when?”

“ Scene d’in su tafiyar su Mahmoud , lokacin da kika fad’i ‘kasa , irin yadda yazo ya mi’ka miki hannu, kamar sharukan yazo wajan kajol , ai kin gane, and duk wanda ya gan ku at that moment zai ce soyayya kuke, Mimi kinga yadda kika shagwa’be kuwa ? Amma kice mun ba wani soyayya kuke ba, I found myself to hard to believe wallahi
.”


“ So now it’s a crime idan ya taimake ni? Ke yanzu idan ya taimake ki za’a kira hakan soyayya ? I don’t get you
.”

“ Wa ni???????
” Ameerah ta d’an zaro eyes din ta “ Rufamun asiri maza su kai ni ba mata ba , kedai kawai tunda kince ba soyayya kuke ba , idan tayi tsami ai zamuji, nidai in ma gaske ne , am so supportive ya Allah , wai Mimi da soyayya awwwwwn , and 
” 

‘Karamun ‘bari da suka ji a wajan ‘kofa yasa both of them suka kalli junan su, kuma sun san dai babu kowa a falon, hakan yasa duka su biyu suka nufi Door d’in, a lokacin da aka sake wani ‘barin a karo na biyu, kamar ana ‘ko’karin barin wajan. 

Ameerah tayi saurin bud’e ‘kofa, sai kawai suka ga Zarah tsaye a wajan , hannunta da tray d’in juice , which cup d’in sa ne ya fad’i ‘kasa sabida hannunta da yayi ‘ko’karin zamewa , yanzu ma jug d’in ‘ko’karin fad’uwa yake Ameerah tayi saurin ri’ke sa , both da mamaki suke kallan Zarah, most especially Ameerah dan ita yanzu Mimi ta dena bata mamaki sai tsoro.. 

“ Me akai miki kike kuka haka? Har da hawaye , jug a hannun ki, kuma kika tsaya a bakin ‘kofa , Zarah are you okay?.”

A maimaikon Zarahn ta amsa mata sai ta tsaya kallan Mimi, itama Mimi kallan nata take cikin halin ko i don’t care 


Wani hawayen ne ya kuma saukowa a idon Zarah da ta sa hannu ta share sa , tana d’an shigowa falon sosai yadda
Mimi zata ganta , Ameerah da mamaki ta ajje jug a ‘kasa , tana shigowa itama sosai sabida ta fahimci inda abun ya dosa


“ Mimi wai me yasa baki da zuciya? Me yasa ke d’in kamar Mayya kike ne? Ba’ayi dake amma dan naci kice sai kin shiga rayuwar da ba naki ba why why?.”

Cikin d’an sauri sauri Ameerah ta furta “ Hey hey hey me haka? Zarah me haka naji kija fad’a ya za’ayi ki kira ta da mayya , akan wana dalili? Ko me tayi miki ma for example me nakiranta da wannan banzan sunan?
”

“ Kinga yi mun shiru Ameerah wannan karan ba dake nake ba , da ita nake ai duk bakin ku d’aya , kema in banda munafurci babu dalilin da zai sa ai kizo kina ma’kale mata , bayan da ba shiri kuke ba , amma sabida gulma yanzu duk inda take kinanan, sabida san asani so please allow me
”

Cikin sauri Ameerah tayi ‘ko’karin hayayya’kowa Zarahn ,amma Mimi tayi saurin hanata ta hanyar ri’ko hannunta , tana d’anyin murmushi, kafin tacewa Zarah “ Okay tunda waje na kika zo , ina jin ki Zarah ! Sannan mayyar da kika kirani dashi yanzu wa na ta’ba lasa? Or do you think inda mayya ce ni wannan jinin naki mai ‘karnı zai birge ni?.

Malama shiga hankalin ki mana , and for your information, bani da lokacin ni ina da abunyi , ke da naga ko da yaushe kina da so much interest akan nawa rayuwar da bibiyar inda nake bani da aikin yi ne , kuma baki da wannan zuciyar ne shiyasa har yanzu duk inda nake kike ‘ko’karin zuwa 
.

As for Ameerah da kika magana akanta , ko gulma ya kawo ta ko akasin haka, I don’t care ! You don’t have to even judge her bayan ke a karan kanki kin kasa judging banzan halayen ki
 imagineeeeee ! Please we have a lot to dooo
 let’s go Ameerah
” Mimi zata juya , unexpected Zarah ta janyota ta wuyan rigarta, da har sai da Mimi ta kusa fad’uwa , Allah ya temake ta Ameerah kusa da ita da babu abunda ya hana ba zatayi muguwar fad’uwa ba . 

Yanzu ma sai da gabanta ya fad’in sabida ta baki tayi ‘ko’karin fad’uwa , kawai Mimi tana d’agowa, unexpected at the same time Ameerah ta kaiwa kuncin Zarah bari a Right kumatunta, ita kuma Mimi ta kai mata nata marin a Left face nata , kamar had’in baki
. 

Marin yayi mugun shigar Zarah har sai da ta dafe kumatun ta da ‘karfi tana fad’in “ Wayyo Allah na sabida azabar zafin da taji a kumatunta 



Wani irin kuka me zafi ya ‘kwace mata , sai a lokacin suma suka d’an ji guilt ganin sun mareta sau biyu at the same time which ba shine intention d’in su ba kwata kwata 
.

Hannunta dafe a kumatu ta kuma fad’in “ Wayyo Allah na..”
Sabida yadda taji zafin marin kuma sai faman sosawa take da sauri da sauri
 


‘Dan matsowa kusa da ita Ameerah tayi kad’an , cikin rashin jin dad’in abunda tayi mata yanzu ta furta “ Zarah
”

A haukace Zarah ta ‘kwalla ihu tana fad’in “ Don’t you dare Ameerah , don’t you dare 
”

Idanuwan Zarah har yayi ja dan marin ya shiga sosai “  Ga baki d’aya ku kun kiya d’aukar hannu ku mare ni, a fuska at the same time , shine Ameerah har kike da gut d’in ‘ko’karin yi mun magana ?

Wallahi wallahi wallahi yadda kuka mare ni yanzu sai nasa kunyi nadamar da baku ta’ba yi ba a rayuwar ku , musamman ma ke , Mimi
 

Karuwa ‘yar karuwa , wacce ga baki d’aya danginta karuwai ne , har kike da ikon saka hannu akan fuskata da ‘kazamun hannun ki da babu abunda ya sani sai iskanci?.”

Wani ‘karamun dariya Mimi tayi tana kallanta irin up and down d’in nan “ I think Zarah kin samu matsala a kan ki ko? Baki da hankali zaki dinga ala’kantani da wannan ‘kazamun abun, just because kwana biyu idan kikai magana ina d’aga miki , thats what make you ki fad’a mun every rubbish da yazo bakin ki?”

Dariya Zarah ta ‘kyal’kyale dashi, at the same time kuma bata dena kukan da take ba “ Saurin me kike? Ai ban gama ba , bari na koma kan wannan karyar da babu abunda ta sani sai dai ta bi bayan ki, kamar wata mahaukaciya 
”

“ Zarah ni kike kira da karya yau?” Cewar Ameerah tana nunata da hannu 


“ An kira ki da karyar , idan ba ita bace , me za’a kira ki dashi? All the time kina bayan Mimi, kome tace kiyi shi zakiyi, all the time kina ‘bata lokacin ki a wajanta ne ? Idan ba’a kira ki da wannan ba me za’a kira ki dashi ?”

“ Zarah you’re maddd , na yadda kin haukace wallahi, you need some therapy
.” Cewar Ameerah 


Dariyar takaici Zarah ta d’anyi “ Tsakanin ni da ku za’a wa d’an da suke bu’katar therapy, and yes ban gama fad’ar abunda nake san fad’a ba ,  ta kalli Mimi tana yin wani devilish murmushi


“All the time Mimi kina nunawa kamar you’re just the winner , kina yin abunda kika ga damar yi , kuma ana miki duk abunda kike so, babu wanda yake complaining sabida Moh
.

Do you think he even loves you? Fad’amun inda Uncle zaiyi soyayya da ‘yarsa , idan ba iskanci kike so kiyi ba ? You always want to make your self to look like the victim , which you’re not 
 kina abu kamar kin fi kowa gaskiya , ko kin fi kowa sanin abunda yake faruwa , bayan ke a karan kanki baki san wace ce ke ba, you’re just a shadow , or in kira ki da puppet a kowa ya gama damar wasa zaiyi wasa dashi a duk lokacin da ya ga dama , are you even a virgin Mi
”

Hannu Mimi ta sa ta sake wanke face d’in Zarah da Mari , wannan karan both side ta mareta , Zarah kuma ko gezau ba tayi ba , kuma babu ko hawaye a cikin idanuwanta sabida wanda take yin ya d’auke d’if tun lokacin da ta soma yi musu d’iban albarka


“Zarah duk abunda yazo bakin ki fad’a mana kawai kuke, you’re not even thinking twice kafin kiyi magana , kin danganta ni da karuwa me nayi miki haka ? Sabida kawai kinasan Uncle Moh? If you really love him ba zaki zo kina wannan haukan ba , you will fight for his love 
.. Amma kinzo kina zagina , kinzo kina zagin Ameerah, for what reason? Can you just please walk away from here? Just go we don’t need you here 
.”

“Mimi uwata ce ke da zaki dinga bani umarni a duk lokacin da kika ga damar? Kalle ki fa? Ta’kamarki  kina da kyau, that’s all, idan da ace baki da kyawu akwai wanda zai kalle ki ne , yadda you’re not so pure ?”.

“ Zarah me kike nufi she’s not pure ? Kuma wad’an nan maganganun naki ina suke ‘ko’karin dosa? Kawai kije straight to the point ki fad’i abunda kike san fad’a ba wai ki
d’inga kwana kwana ba
.. Idan ba tsoro ba ki fito kiyi magana mana yadda zamu fahimce ki
” cewar Ameerah
.


“ I don’t mind that
 since kunasan jin bayani, then it’s your choice
. Bari na fito dallah dallah yadda zan kashe bosss once and for all
 

Da banyi niyar fad’ar komai ba sabida you guys are my friends, musamman ma ke Mimi, I though you’re my best friend, wacce zamuyi sharing secret d’in mu for life , kuma mu taimaki junan mu as one
.

Amma me ya faru next? Ba kya d’aukata a matsayin da na d’auke ki,  yadda kike d’aukata sai kika soma d’aukar Ameerah hakan , har ya zam to da farko kinfi mu’amala sosai da ita akai na, bayan duk yadda na kaunace ki, na soki as my sister , and also my best friend amma kikazo kina abota da Ameerah kamar ban ta’ba existing ba sabida butulci irin naki.

And again kina da supportive parent , Mammy da Baffa ßuna sanki sosai duk a cikin ‘ya’yan su sun fi kaunarki musamman da ya zamto kece last born d’in Mammy kome kike so shi ake miki, not for once ba’ayi miki abunda bakya so ba , amma me yasa ba zaki ‘kyale mun Moh ba? Kinsan in San shi, babu wanda nake sama dashi a cikin duniyar nan, amma kike ‘ko’karin ’kwace mun shi, a komai Uncle Moh Moh Moh , bakya single magana baki kira sunansa ba alhali kwata kwata bakisan wane ne shi ba , har yau ko sau d’aya bakisan Mamansa ba , bakisan Babansa ba he is not  you partner, kullum
kina zuwa part d’insa  idan ba’a kira ki da karuwa ba wace budurwa ce take zuwa d’akin saurayi wanda bashi da mata cikin dare? And ya kalle ki ga baki d’ayan ki bai miki komai ba , karki rainawa mutum hankali mana Mimi
.”


Mimi da ta gama sauraran maganganunta, babu wani reaction a face d’inta sai ma kallan mahaukaciya da take yiwa Zarah d’in
.
“ Zarah are you done?.” That’s the first statement da ta soma fad’i tun bayan hayagagan da Zarah ta soma .

“ Yes ma gama , idan ban gama ba ai kinsan I will talk because bana jin tsoran ki ko?.”

“ Wowww hakan yana da kyau, yanzu zaki iya tafiya , sabida kina ‘bata mana part
. Banasan too much of zunubi ya zauna a cikin part d’in nan, too much of shouting da kuma haukan ki, mun gode da wanda muka saurara you can go now 
.”


“ And too much of madness
” Ameerah ta ‘kara, tana matsowa kusa da Mimin
. Yadda zata kalli Zarah sosai “ We appreciate your madnesss Zarah , thank you so much wannan kad’ai ya isa ya bamu dalilin da zai sa muyi nesa da ke , aushe kin dad’e kina haushi dukan mu bamu da labari, it’s good da yanzu muka ga side d’in haushin naki ai.. since you’re done with your barking ! You can go and barks along Dogs like you
”


“ Ameerah ni kike kira da Dog?.”

“ Zan kira ki ma da hippopotamus( 🩛 ) if i want, kuma babu uwar abunda zaki iya yi, bani da ha’kuri kamar Mimi, kin sani kuma nima na sani, kika kuma fad’a mana magana yanzu wallahi tallahi sai nayi miki shegen duka a nan wajan , kuma in faffasa miki baki, uban kowa ma ya mutu. A mutu har liman ki gani idan akwai abunda nake tsoro


Aushe wannan haukan kika nunawa Mimi kwanaki, not for once bata ta’ba fad’a mun ba , duk da naga kamar akwai wani abu a tsakanin that seems off
  Aushe matsalar daga kene
 

Kina da 2 option ! Ko ki fita da kanki ko kuma ni na fitar da ke , kuma wallahi da duka zan fitar dake , sai na tabbatar da jikinki yayi luhu luhu , kinga ko bakomai albarkacin Mimi, Uncle Moh zai fito dani , wai tsaya ma , kinga irin soyayyar da sukai jira ? So perfect 
.  Dan Allah baki ga yadda suke kyau ba idan suna tare kamar wasu couple? Kuma munyi matu’kar dacewa da juna both kyawawa dasu? Kinga yadda ya ri’ko mata hannu kuwa jiya? Oh my goodddddddddddd
.. So sexy
.”

Murmushi Mimi tayi tana kallan yadda Zarah take ‘ko’karin tafarfasa kawai daga jin maganar Ameerah , toh ina ga kuma ta fasa mata zuciyar ga baki d’aya?.

‘Dan kallan wayar da yake side d’in Ameerah tayi, da sauri ta furta “ Ameerah please give me my phone 
”

Ameerah ta ce komai ba ta d’auko phone nata ta mi’ka mata , ita kuma Mimi tayi saurin shiga camera, tana shiga abunda take san shiga ta d’anyi murmushi kad’an , tana kallan Zarah da itama take kallanta 


“ Tun d’azu kike faman ihu akan Uncle Moh! I think wannan abun zai iya zama kamar therapy a wajan ki ko?” Mimi ta d’aga mata hotan wayarta 
.

Take hotan da sukai ita da Moh wanda suka kalli juna ya fito akan wayan Mimi
 

Hotan kamar wasu couples da suke ‘ko’karin kissing juna,,,, ya Allah
.

Wani irin shewa Ameerah tasa lokacin da taga hotan , da wani irin guda kamar dangin ‘yan mai duguri sabida yadda gud’ar nata yake , har da wani ‘kara ‘Kara yake fitar wa tana wani zagaye Mimi tana rawa , irin kamar yadda larabawa suke rawa da hannun su, itama Mimi ta juyo duka dinga gud’ar tare ßuna rawar babu kid’a babu komai da bakın su ma suke wa’kar su , sun yi bala’in mayar da Zarah mahaukaciya
.

Ita kuma Zarah tunda taga wannan hotan ta sandare a inda take , kamar system d’in jikinta ma ya dena aiki, ita idanuwanta ma bawai iya hotan Mimi da Moh ta gani Ɵuna kallan juna ba , no nuna mata suke suna kissing juna ne a lokacin


Idanuwan Zarah ga baki d’aya ya rufe , ta soma ganin dishi dishi , zuciyarta tana faman bugawa da sauri da sauri, ji take kamar ta had’iyi zuciya sabida abunda take ji a ‘kirjinta da zuciyarta ba zai bayyanu ba , yau masoyinta kuma mijinta tare da wata har suna kissing d’in juna
.. 


Mimi da Ameerah kuma suna wannan rawar ne sabida kawai su tusa mata ba’kin ciki ko zata tafi ta ‘kyale su , tunda sunga kome suka ce mata ba ta tafiyar kamar anyi mata dole sai ta tsaya , Ameerah har tsayawa ma tayi ta kunna Bluetooth, ta d’an ware volume sosai yadda falon zai cika da music kuma Zarahn tana tsaye har lokacin tana kallan su amma kuma babu komai da yake sarrafuwa a tattare da ita sabida bata gane abunda suke , kuma bata jin ma ‘karar sabida ba shine babban abunda yake zuciyarta ba yanzu
..

Mimi da Ameerah sun shagala da rawar da suke a tsakanin su, ßuna faman yin juyi basu san Zarah ta bar wajan ba.

Kitchen Zarah ta shiga, bata ma dad’e ba ta fito, idanuwanta ga baki d’aya akan Mimi da take dariya, ita kawai take kallo zuciyarta tana fassara mata abubuwa masu matu’kar yawa


Tazo dafff dasu suna cikin rawar nan kawai Zarah ta d’an ta’ba Mimi
. 

Dukansu suka juyo a lokaci d’aya ita da Ameerah


Zarah ta d’aga hannunta zata cakawa Mimi wu’kar da ta d’auko a cikinta , Ameerah da tayi saurin kula da makamın hannun Zarahn tayi mugun hankad’a Mimi gefe wu’kar ta sameta 



At the same time but Mimi da Zarah suka ‘kwalla ihu, sabida Mimi akan center d’in falon ta fad’i while wu’kar ta samu Ameerah
.

(đŸ„čđŸ„čđŸ„čđŸ„čđŸ„čđŸ„čZarah a madadin ‘yan group d’ina muna miki Allah ya isa)

_________________

HAR YANZU ANA KAN FREE PAGES WHICH IS 800 A PAGE 50 KUMA ZA’A TSAYA IDAN AKA GAMA BOOK 1 , KUDIN MISHAL 1k ne . 

ZAKU TURA KUDIN KU TA WANNAN BANK DIN

2681892316
AISHA UMAR 
ZENITH BANK

SAI A TURO MUN SHAIDAR BIYA TA NUMBER TA  ***



_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***


***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol