Free chapter · Read without an account

Page 50

by Ayshatou Galadima · MISHAL

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1



Page 50 
 LAST PAGE OF BOOK 1 




__________

“ Wayyo hannu na
!” Mimi tayi maganar a rauna ce sabida bige hannunta da tayi da center , kuma babu abunda ya samu center d’in, sai ta d’an zabura da sauri tana kallan Ameerah , sai faman dube duben jikinta take taga inda wu’kar take. 

Amma babu wu’ka a jikin ta , ta dai ri’ke gefen jikinta , d’aya hannunta akan face d’inta tana ‘ko’karin tsugunna..

Cikin sauri Mimi ta ri’keta tana fad’in “ Ameerah ! Ameerah ? Wayyo Allahna na shiga uku na lallace , dan Allah kar wani abu ya same ki , kinji Ameerah!
” ga baki d’aya a rikice take, bayana sambatu babu abunda take iya yi.

Zarah kuwa a rud’e taja baya tana zazzare idanu , ganin Ameerah na zubar da jini, ga kuma Mimi itama da take ihun hannunta .

Ta kasa ta’buka komai , sai bin su da idanu kawai da take, kuma ta kasa guduwa tananan a inda take .

A d’an raunace Ameerah ta furta “ Mimi ki kaini asibiti , kinji
?” Tana kaiwa nan ta ‘karasa fad’uwa bata ko motsi.

Wani saban kuka Mimi ta saka tana fad’in “ Ameerah dan Allah ki tashi, kinji ki tashi
.” Tanayi tana jijjigata, hawaye da jikin Ameerah da ya d’an ta’bata ya ‘bata fata fuska itama sabida share hawayen da yake sauko mata da take


Hannunta ga baki d’aya rawa suke ta d’auki wayarta .

Sabida gigicewa da ‘kar ta iya bud’e wayar dan gani take kamar an canza mata password d’in wayar ne ma ga baki d’aya .

Babu number wanda tayi dialing sai number Uncle Moh


Just 2 seconds a tsakani akai picking call d’in, sai ta saka kuka sosai tana fad’in “ Uncle Moh kazo ka kai Ameerah asibiti dan Allah kar ta mutu kayi sauri kazo ka kai ta asibiti
.” Tana kai wa nan ta ajje wayar a ‘kasa ko kashe call d’in ba tayi ba , ta cigaba da kuka tana kiran sunan Ameerah akan ta tashi , ta saka hannunta gud’a d’aya tana dafe wajan da jini yake fitowa
.

In ka kalli Mimi kamar wata zararriya, sabida ta fice daga cikin hayyacinta ga baki d’ayanta ma , tayi dame dame da jini a jikinta .

Mintuna 3 ! Just 3 minutes da kiran Moh, suka shigo part d’in su uku, da shi da Alameen da kuma Aya da take bayan su
 

Ganin jinin da yake ‘kasa da kuma Ameerah da Mimi da suke jinin sukai saurin ‘karasawa wajan su. 

Ga baki d’aya su ukun sun ga Zarah da take rawar d’ari amma babu wanda yabi takanta , sabida first priority d’in su yana kan su Ameerah ne ..

Suna zuwa Moh yayi saurin janye Mimi da take ‘ko’karin ’kwacewa dan kamar bata gane mutane, batasan wane ne yake ‘ko’karin janta ba .

Alameen kuma yayi saurin d’aukar Ameerah da shima farar shirt d’insa ta soma ‘baci da jinin, ya samu abu yayi saurin tallafe wajan da jinin yake d’iga, zai fita da ita Mimi ta saka wani ihun tana fad’in “ Zasu tafi da ita ! Zasu tafi da ita .” 

Tana ‘ko’karin ri’ko both Ameerah da Alameen d’in , Alameen yayi saurin fad’in “ Moh ka ri’keta please ..” ba tare da ya kalle su ba , yayi saurin fitar ‘kofar fita .

Mimi tana ‘ko’karin bin su Moh ya ri’ko hannunta , yana kiran sunanta ina gentle way kar ya ‘kara hautsinata “ Mimi
.. ! Mimi
.”

Hajiya Mimi ta’ki kallansa sai faman kallan ‘kofar fita da take , tanasan bin bayan su Ameerahn, amma Moh ya hanata sabida hannunta da ya ri’ko, yayi wa Aya da take ‘ko’karin zuwa kusa da su signal alamar tabi bayan Alameen.

Haka ta fita tana jefawa Zarah wani mugun kallo, ita kuma sai faman zazzare idanuwa take, tama kasayin komai, bayan rawa da jikinta yake , ko ‘kafafuwanta ta kasa takawa balantana ma har ta iya guduwa..

Mimi duk yadda taso ta ‘kwace hannun nata Moh ya hanata sabida mugun ri’kon da yayi mata


A hankali ta soma sauke ajiyar zuciya, tana d’an ta’ba hannunsa da ya ri’ke mata nata hannun “ Uncle Moh hannu na da zafi , na bige dashi da wannan
” ta nuna masa center d’in wajan.

So gentle ya saki hannunta, zai ri’ko d’ayan hannun Mimi kamar wata me iskokai fitt ta ‘bace daga bayansa, ta nufi Zarah da sai a yanzu take ‘ko’karin guduwa ganin Mimi na kusanta.

Mimi tana zuwa daddagewa tayi ta gantsawara Zarah cizo a wuya


Wani irin ihun azaba da Zarahn ta saki sai da ya çıka falon , ga wani fitsarin azaba da ya soma sauko mata babu shiri


Mimi kamar wata zombie , ta’ki sakar mata wuyar sai ma ‘kara daddagewa da tayi a wajan cizonta , da iya ‘karfinta
.

Sai ihu Zarah take tana neman d’auki, tana ro’kan Mimi ta saketa , amma Mimi ta’ki sakinta , tun suna a tsaye kuwa , yadda Zarah ta tsugunna tana kuka da ihu haka Mimi ta tsugunna itama ta’ki sakinta
.

Sai da Moh ya bari kamar mintina biyu, bayan tayi cizonta tukunna ya soma ‘ko’karin zare Mimin. 

Amma to his very suprise mugun kamu tayiwa Zarah , idan yace zai cireta ta ‘karfi zata iya kwasowa da naman wuyan Zarah, which ba fata ake ba wani abun zai iya faruwa, musamman ace fatan wuya akayiwa wannan kamun, gashi Zarahn har ta soma sandarewan bala’i..

Hannunsa d’aya yasa a bakinta kad’an ya matsa, yadda zataci zafi ta saki ha’kwaranta, amma Mimi ta’ki sakin ha’kwaran.

Ya ‘kara matse mata bakin kad’an , still Mimi ta’ki tsakin ta , sai da ya sa hannu sosai a wajan ha’kwaranta ya bud’e bakin sosai ta ‘karfi yadda ba zai hurting d’inta sosai ba ya samu ya bud’e hakwaran Mimin, ita kuma ta soma ‘ko’karin tari, amma ya hanata haka, ya bari ta zubar da abunda yake bakinta ga baki d’aya a ‘kasan wajan, hannunsa d’aya yana bakinta ya wuce kitchen d’in falon da ita , sai da ya wanke mata bakinta sosai, tukunna ya sake ta d’aga ’karfin da ya bata sabida ha’kwaranta har da jini alamu ya nuna mugun cizo tayiwa Zarah..

An gama wannan wanke bakin sun fito, tana ganin Zarah da take kwance hannunta akan wuyanta tana kuka kamar zata shid’e ta kuma ‘kullatan ta , zata nufeta da sauri taji hannunta cikin nashi, tayi tayi ya saketa ya’ki sakinta, shima sai ta soma ‘ko’karin kai masa cizo.

Da yayi wani irin ban’kare hannunta , sai da ta d’anyi ‘kara sabida taji zafi


Sai kuma ya had’e both hannayenta biyu a cikin nasa yana sa’bata a kafad’a , kuma yayi mugun ri’ke ’kafafuwanta , shiyasa ta kasa zillewa da take sanyi, hakan yasa ta soma kuka kamar wacce aka yanka .

Ko da ya shiga part d’insa da ita bai sauketa ba ya wuce toilet da ita , warm shower ya kunna musu ga baki d’aya su biyu, ya sauketa daga kafad’unsa amma kuma bai sauketa ‘kasa ba , tana hannunsa ya’ki sakinta , duk da kokawar da taso yi masa a cikin toilet d’in.

Sai da ya bari ruwa sosai ya soma shiga jikinta , har tana sauke ajiyar zuciya me ‘karfi, hankalinta da nutsuwarta ya soma dawowa jikinta, ‘kirjinta sai faman sama da ‘kasa yake da sauri, kana kallanta kasan a rud’e take ga baki d’ayanta
..

Baice komai ba ya ‘kara bata wani mintina koma a cikin ruwan, har saida completely bugun zuciyarta ya dawo normal which in anyi mata magana zata iya reply 


Hannu yasa ya d’ago ha’banta, duk da shower da yake zuba akanta sai da yaga hawayen da suke sauko mata a idanuwanta sosai


Calmly ya kira sunanta “ Mimi?”

Kamar jira take ya kira sunanta , ta soma shash she’kar kuka, kafin tayi hugging d’insa tana fashewa da saban kukan, shi kuma ya saka hannu akanta yana tapping a hankali cike da kulawa


Sai da tayi kuka mai isarta, ta fitar da duk abunda yake ranta, tukunna ta sakesa tana fad’in “ Zanje wajan Ameerah kaji?”.

“ Zan kai ki, amma sai kin dena kuka tukunna
”

Babu musu ta share hawayenta , muryarta har ya d’an soma dusashewa sabida kuka “ Uncle Moh , Allah na dena kukan kaji, sabida nifa taji ciwon, da bata ture ni ba da ni Zarah zata samu, gashi yanzu taji ciwo sabida nifa, dan Allah ka kai ni yanzu kaji Uncle Moh?.” Ta wani ri’ko hannunsa cikin pleading.

“ Okay ! Kiyi sauri kiyi wanka kinga kayan jikin ki sun ‘baci, sai na kai ki ? Kinjiiii?”.

Ta d’aga masa kai da sauri
 

Ya d’an shafa kanta a hankali “ Good Girl
.” Ya fita ya barta a toilet d’in, ita kuma ta soma saurin yin wanka gashi kanta ya ji’ke da ruwa, shap shap tayi wanka babu wani yanga, sai ma sauri da ta dinga yi, tana gamawa ta d’an matse kayan ta ajje su inda zasu dinga shan iska, ita kuma ta lullu’bo 1 of his bathrobe ta saka , tana fitowa taga sabuwar abaya akan bed , baya cikin d’akin kuma. 

Tasan inda dryer d’insa take , sabida tasan ko tana aljanune ba bazai bari ta fita da kanta a ji’ke ba har ma ta rufeshi. 

That’s what makes her tayi sauri ta d’auko ta , kafin ya shigo tayi drying kanta. 

Da ta tabbatar da ya bushe ta saka Abayan da ta gani and da sababbun pant and bra, da kuma wata rigar mata nauyi me shiririn hannu a ciki duk tasa. 

Kana suna da kyau sosai , amma kuma yanzu ba ta su take ba, ga plat shoe shima da ta gani sawa kawai take , take ta d’an d’auki turaransa guda d’aya shima ta saka kad’an sabida yana da ‘karfi sosai. 

Dama batasan inda ta ajje wayanta ba tunda abun ya faru, hakan yasa tayi saurin fitowa daga d’akin har tana ‘ko’karin yin tuntu’be sabida sauri.

Amma da ta fito falon baya ciki , sabida tana a rud’e kitchen ta soma dubawa ko zata ganshi, baya ciki, babu waya a hannunta balantana ma ta kirasa, babu shiri ta koma sama , d’akin kusa da wanda ta fito yanzu ta bud’e bata ma tsaya ‘kwan’kwasa ‘kofar ba .

Tana shigowa yana daga bakin mirror , jikinsa da black d’in wando da kuma black d’in singlet da ta zauna d’am d’am a jikinsa. 

Za tayi saurin juyawa ta tsinkayi muryarsa “ Bring my shirt Mimi..” ita sauri take kawai su tafi, ba ta ma tsaya yi masa musu ba , ta d’auko rigar ta kawo masa har gaban mirror d’in ..

Yana amsa sai ya ri’ke har da hannunta a cikin nasa, ya saka rigar, already akwai half shoe da take ‘kafarsa, phone da car d’in d’in da yake wajan ya d’auka ya ri’ko hannunta suka fito 
.

Har a fito da wata ba’kar Black Bentley, tsaf tsaf babu ‘kura kwata kwata a jikinta .

Har side d’in da zata zauna ya kai ta kuma ya bud’e mata motar da kansa ta shiga , ya saka mata seatbelt,so gentle kuma ya rufe ‘kofar  ya shiga driver seat , ya soma driving zuwa hospital d’in da Ameerah take , daman hospital d’in da aka kai Mimi kwanaki shine desame hospital da aka kai Ameerah


Mimi was so very quiet a tafiyan dan side d’in ‘kofa ta kwanta, mutum sai yayi tunanin ko bacci take a yadda take , amma idanuwanta biyu, tunani ne kawai yake mata yawo a zuciya sabida yadda take ganin she’s at fault of everything, if not because of her da babu abunda zai samu Ameerah a wannan time d’in


Da wannan thought d’in nata suka shigo cikin asibitin, ita batasan ma sun ‘karaso ba sai da taji yana parking car d’in.

Juyowa tayi ta kallesa kamar yadda shima ya kalletan

Kafin tayi magana ya d’an matso kusa da ita ya cire mata seatbelt d’in da ya saka mata
 

Yana fitowa daga cikin motar, itama tayi saurin fitowa tana binsan da kallo dan tasan shi kad’ai ne kawai zai iya kaita inda Ameerahn take 


Har da d’an saurin matsowa kusa dashi, veil d’inta yana ‘ko’karin fad’uwa ‘kasa , ya d’an gyara mata da hannunsa , ya ri’ko hannunta suka shiga wani part of the hospital


Kafin suje d’akin Ameerah more than 10 Doctors sunyi ‘ko’karin approaching nasa, amma kallan da yake musu yasa ga baki d’aya suka sha jinin jikin su, in as far as sun ganshi tare mace kusa dashi.

Confuse , suprise , scared duk ya bayyana akan fuskokin su
. 

Hanyar d’akin Ameerahn akwai wasu mutane da ba’ka’ken kaya,
amma basa ‘kofarta , shiyasa Mimi bata d’an damu ba , amma ta ri’ke hannun Moh sosai a cikin nata.

Yana bud’e ’kofar d’akin sai Mimi ta   kallesa shi kuma ya bata assurance d’in ta shiga ta hanyar knodding kansa da yayi mata.

A fili tayi ajiyar zuciya, kafin tayi sallama ‘kasa ‘kasa tana shiga d’akin


Tayi tunanin zai biyota ciki, sai taga yaja ‘kofar ya rufo mata door d’in ta waje 
.

Mimi tana shiga d’akin da yake kama da living room, sai ta tarar da Ameerah a kwance , amma an d’an d’ago da gadon da take kad’an kuma idanta biyu, tana kallan kowa har tana magana duk da ba kamar da da take ware baki tayi surutu ba 


Ga Aya da Mama da suke zaune a cikin d’akin , ga kuma Alameen da yake da ya tashi akan kujera fuskar sa a had’e sosai, sabida wannan ne karo na farko ma da zata ce taga ya had’e fuskarsa har haka.

Ya canza shirt d’in jikinsa amma wanda ya saka irin me open d’in nan ce ana ganin ta cikin da har yanzu bai canza ba wacce take da jini a jikinta kamar ta saman kawai ya canza
.
Yazo zai nufi Door ganin Mimi tana tsaye a bakin hanyar that’s the time da ya furta “ Mimi bari na wuce 
”

Babu musu ta matsa masa hanya dan ta kasa magana ma. 

Aya da Mama da sai yanzu suka lura da ita a tsaye Mama ta kalleta da murmushi akan face nata “ Shigo mana Mimi ya akai kika tsaya a bakin ‘kofa?”.

Jiki a sanyaye Mimi ta shigo, daga Ameerah har Aya d’in kallanta suke ganin yadda jikinta yayi wani sanyi sosai kuma ta kasa yiwa kowa magana a wannan time d’in .

“Wai salo salon me kike haka ? Har yanzu fa da rai na ba mutuwa aka ce nayi ba
” Ameerah tayi maganar tana d’an mata murmushi kamar ba itace jikinta yake zubar da jini ba 


Lokaci d’aya Mimi taji ‘kwalla na sauko mata a fuska sai ta sunkuyar da kanta ‘kasa .

Mama da take zaune akan kujera ta mi’ke ta ri’ko hannunta ta zaunar da ita kana kujerar da ta tashi “ Kukan me kike haka Mimi? Ba gashi yanzu dukan ku lafiyan ku ‘kalau ba , kukan me za kiyi kuma?”.


“Amma kuma Mama ta dalili na fa taji wannan ciwan.”

“ Banasan jin wannan maganar mara dad’in ji Mimi. Komai ai baya faruwa da bawa sai Allah yaso , kema kuma baki isa wani abu ya same wani ba wai kuma kiyi tunanin ta dalilin ki ne hakan ya faru ki ma dena wannan maganar, kafin na sassa’ba miki
”


“ Ai shine Mama , daba dan ita ba ai da ina tunanin na mutu ma , sabida nasan ai itace ta kira su Uncle Moh sabida babu kowa a cikin falon sai mu uku, amma kinji maganar da take , kuma nima na turata kan center fa
.” Yanzun ma Ameerah ce tayi magana.

Sai a lokacin Aya tayi magana “ Kinji ciwo ne Mimi?.”

“No babu abunda ya same ni Aunt Aya
.”

“ Glad to hear that Mimi
” 


“ Ameerah ya jikin naki?” Cewar Mimi..

“ Ba wani babban ciwo bane fa , wu’kar bata shiga jikina sosai ba sabida kayan jikina , that’s why am safe now ! Allah ma ya taimaka bai ta’ba komai nawa ba sabida bai shiga can ciki ba , dan haka ki kwantar da hankalin ki, kalli yanda kika wani dawo salo salo ko ni da aka cakawa wu’kar na fiki Energy fa.”

“ Ameerah stop talking karnı fama ciwan ki
.” Cewar Aya..

İta kuma Ameerah ta d’aga wa Aya kai alamar toh, sannan ta d’an rufe idanuwanta tana bud’ewa ahankali akan Mimi cikin yi mata assuring d’in babu wani matsala
.

Mi’kewa tsaye Mimi tayi ta matso kusa da gadon sosai , tana yiwa Ameerah hug yadda baza ta ta’ba ciwan nata ba , ita ma kuma Ameerah tayi hugging nata da one hand ko wannan su sai da ‘kwalla ya d’an tarar masa a ido, amma kuma suna ‘ko’karin  boyeta, da murmushi da suke yiwa junan su.

Aya da kanta ta gyarawa Ameerah gadon yadda zata fi dad’in kwanciya sosai, kuma ko 15 minutes ba’a d’auka ba tayi bacci.

A hankali Mimi tacewa Mama “ Mama ya akai naga ku kad’ai ne a hospital d’in?
”

“ Kowa kinsan ai ya fita , shiyasa ban kira kowa na fad’a masa ba , tunda Aya ta fad’a mun and ba wani babban abu bane kowa dai ta d’an zubar da jini ne shiyasa kuka d’ad’d’aga hankulan ku , amma babu wani abu babba.

Ban dai san lokacin da za’a sallame ta ba , zan koma gıda yanzu na d’an girka muku abunda zaku d’an ci kar ku zauna da yunwa.”

“Mama ki zauna bari naje na dafo abincin na kawo muku..” Mimi tayi maganar tana mi’kewa tsaye .

Itama Aya ta mi’ke tsaye tana mata nuni da ta zauna “ Already Alameen yasa a kawo abinci, any moment from now zasu zo , amma Maman Ameerah kema kına bu’katar hutu, tunda tun safe kika fita , zamu kula da Ameerah anan 
.”

“ Ba’ayi haka ba , d’awainiyar sai tayi yawa .”

‘Kara kallanta Aya tayi“ Maman Ameerah babu d’awainiya, itama ai ‘kanwar muce kamar Mimi , karki damu kije gida ki huta , kar stress yayi miki yawa , tunda an gano matsalar har an magance karki wani damu
” 

‘Dan murmushi Maman Ameerah tayi, tsabar tawakkali irin nata babu wani rud’u ko rikicewa da tayi, she’s calm ba zama kace ‘yarta ta kusa mutuwa yanzu ba sabida yadda take a nutse kamar koda yaushe .

“ Shikenan Aya ! Allah ya baku ladan jinya kema Mimi ya kamata ki huta , zaki zo mu tafi tare ne 
?” Bata ma ‘karasa ba Mimi tayi saurin fad’in “ No zan zauna anan Mama.”

“ Okay Tom shikenan
” Mama tayi musu sallama ta fita daga d’akin. 

Mimi tana shirin kwantar da kanta a gefen bed kusa da Ameerah , Aya ta dakatar da ita ta hanyar fad’in “ Mimi kinyi sallah kuwa?”

Mimi ta girgiza mata kai alamar a’a.

Da hannu Aya ta nuna mata toilet kafin ta furta “ Ga toilet nan kiyi alwala , kar time ya wuce miki.”

Mimi ta sake d’aga mata kai alamar “ Tom.”
Ta shiga toilet tayi alwala, amma a hankali tayi alwalar sabida hannunta da ta bige taji ya somayi mata zafi, sabida kwata kwata bata ta’ba shiba ya soma yin tsami sabida buguwa ce bawai ciwo taji ba , amma sabida hankalinta yana kan rashin lafiyar Ameerah , shiyasa bata ji zafin ba sai yanzu da tazo alwala. 

Tana fitowa ta tarar da Aya har ta shinfid’a mata dadduma, Abaya ne daman a jikinta , so no need ta saka hijab.

A haka tayi sallah, amma duk lokacin da ta d’an motsa hannunta  zata fuskta.

Aya tayi noticing, shiyasa da ta idar da sallar ta kalli Mimi .
“ Mimi me ya samu hannun ki, naga kina sallah kina ‘bata face d’in ki, mene ne a hannun ki?.”

“ No babu komai Aunty Aya , babu abunda ya samu hannu na .”

“ Mimi muga dai hannun ki, in ba zaki fad’a mun ba zan kira Moh Moh sai ki fad’a masa .”

“ Dagaske fa nake miki Aunt Aya , kece dai kike ganin kamar wani abu which ni ban ma sani ba , am okay wallahi trust me .”

“ Hmm shikenan Mimi since you said so, kije Moh Moh yana kiran ki ai zaki iya zuwa compound inda yayi parking ko? Or should I just accompany you?.”


Mi’kewa tsaye Mimi tayi tana ‘ko’karin danne zafin da take ji yana taso mata a hannu, sabida Aya karta gane, tana fad’in “ I will go by my self , ki zauna tunda Ameerah na bacci may be wani abun za’a kawo mata ma I think.” Tana  magana tana bud’e ‘kofar d’akin.

Da ta fita compound inda ya ajje Car d’insa bata gansa ba, bata ga kuma mota kalar tasa ba a wajan, shiyasa tayi mamaki , ta juya zata koma motar Alameen ta shigo cikin asibitin, bata ma gane motar shi bane , that what’s make her to go back to the room and informed Aya cewa bata ga motar Moh d’in ba.

“ Mimi go and check yana nan , may be ko ya canza wajan parking d’in ne , or you should just call him kiji inda yake.”

“ Aunt Aya bansan ina na ajje wayana ba , shiyasa bansan ta ina zan same sa ba
”

“ I will call him now na fad’a masa kin fito , zaki gansa karki bari ya zauna jiran ki Mimi you should start going now 
.”


Mimi ta bud’e ‘kofa zata fita shima Alameen yana ‘ko’karin shigowa ,
Shiyasa ta koma cikin d’akin, both hannuwansa da manyan bags 

A gefe guda ya ajje su da wani babban leda , amma bai ajje ledar a ‘kasa ba , ya mi’kawa Mimi tare da fad’in “ Mimi hold this for you guys
”

Mimi babu musu tayi ‘ko’karin amsar ledar, amma yana saki ta d’an saki wani ‘kara “ Aushhhh 
” Tana ‘ko’karin sakin ledar


Alameen yayi saurin rigewa “ Mimi are you okay ? Ko baki da lafiya ne ?.”

Da sauri bakinta har yana rawa ta furta “ No no am fine babu abunda yake damu na
”

Zai yi maganar Aya tayi gyara murya , kallanta yayi , ita kuma ta girgiza masa kai alamar kar yayi mata magana, tana yi mai wannan alamar tacewa Mimi “ Mimi you can go kar Moh Moh yayi ta jiran ki
” 

Daman hakan take so sabida batasan abunda zata cewa Alameen ba idan ya tanbayeta me yasa mu hannunta , sai tayi saurin cewa “ Okay , bari naje 
” 

Bata jira amsar d’aya daga cikin su ba tayi saurin fita daga d’akin.

Aya kuma ta d’auki waya itama sa sauri tayi d’an typing a wayarta na ‘yan seconds 
.

Time da ta sake fitowa nan d’in ma bata ga motar da, zata juna ta hango kamar motarsa tana fitowa daga wani side . 

She’s not very sure amma haka ta tsaya sabida ta gani shi d’in ne ko wani car d’in ne
. 

Daga gefenta yayi parking , yana d’an zuge window d’in side d’insa kad’an.

“ Come here Mimi..”

Babu musu Mimi ta matso gefen window d’in “ Uncle Moh gani..”

“ Shiga mota muyi magana
”

“Okay
” ta fad’a a sanyaye tana shiga d’ayan side d’in.

Da ta zauna akan kujera sai tayi facing d’insa yadda zata ji abunda zai ce mata..

After kamar 1 minutes of silence , Moh ya d’an juyo saitin ta , hakan ya ‘kara musu kusanci sosai a tsakanin su, Mimi dai rarraba ido take kamar mara gaskiya tana jiran jin abunda zai ce matan. 

Sai ya d’auko 1 big bottle guda d’aya ya mi’ka mata “Bud’e mun Mimi
.”

Amsa Mimi tayi da hannun da yake mata ciwo tana so ta murd’a amma ta kasa, motsi ‘kwa’kwara tayi da hannun sai taji zafi, sai ta mayar da ruwan d’aya hannunta amma shi d’in ma ta kasa, alamar ‘kwalla sun soma taso mata a ido sabida zafi fa hannunta ya somayi..:

Hannunsa ya mi’ka mata alamar ta bashi bottle d’in.

Sai ta mi’ka masa da left hand d’inta da yake normal , right hand d’inta kuma tana d’an faman ‘boyewa kamar tana avoiding ma ya ga hannun ne ga baki d’aya.

“ Shall we go home?” Yayi mata tanbayar all eyes on her .

“ No Uncle nidai ina nan bacci take yanzu fa , idan Doctors sukazo dubata fa ?Inaso na zauna tare da ita Please
.”

“ Kema you’re not feeling fine , yanzu Alameen after 4 za’a dawo da ita gida sai ki ganta a can, shall we?.”

Kamar za tayi kuka ta furta “ Nidai ka barni anan, idan an sallameta sai mu tafi, sabida nifa taji ciwan
.”

“ Okay fine ! Buga hannun ki?”

Lokaci d’aya bakinta ya d’an fara rawa batasan ta soma stammering ba sai a lokacin “ Uncle Moh
 me
me za kayi da hannu
 na
?.”

“ Na soma wasa da ke? Muga hannun ki Mimi
.” Mimi sai ta ‘kara ‘boye hannun kamar shine abunda yace matan


Bai kuma magana ba ya fita daga cikin motar , ita kuma har da saurin saka lock sabida karya bud’e ta d’ayan side d’in
.

Just 5 minutes yayi a waje , ya sake shigowa cikin motar, yana ‘ko’karin tayarwa Mimi tayi saurin yin locking zata bud’e, shi kuma ya sake locking ya tayar da motar, babu fara’a a face nashi ya furta “ Yanzu su Alameen zasu dawo gida suma , idan sun dawo sai had’u da a part d’in su, or will you go will Alameen?”.

“ Noo but kace fa sai bayan 4 za’a sallame su?.”

“ Na canza ra’ayi, zasu dawo yanzu
.” Da haka ya fita daga Asibitin without giving her any chance to argue.

Sunyi nisa sosai da tafiya , wasu manyan Suv ba’ka’ke suka ‘billo ta wani titi, su zasuyi hanyar da su Moh sukayi even though hanya da ban daban, su kuma suna tunkarar hanyar da su Moh d’in suka bari.

A guje motocin nan suke gudu akan titi, amma suna zuwa daff da inda Moh yake sukai slow down da motocin su, suka dawo tafiya a hankali, har saida ya wuce 10 cars d’in wajan, tukunna suka ‘karasa motar wuta suma suka bar wajan a guje
..

Lokacin da suka dawo gida har ta d’an soma magagin bacci, yana parking motar ta bud’e ido tana fad’in “ Thank you Uncle Moh
”
Tana ‘ko’karin bud’e car d’in.

“ Mimi nace ki tafi ne?” 

“No uncle zan tsaya na jira su Ameerah tunda yanzu zasu dawo
”

“Take this file , ki ajje mun a d’akina , I will go somewhere now
”

Jin ba shigowa zai yi ba , ta amsa file d’in hankali kwance , ta shiga part nashi, har ta wuce d’akinsa ta ajje file , zata shigo ya shigo d’akin shima , yana rufe door 
.

Baki na rawa ta furta “ Uncle Moh
 ba
. ba kace fita za kayi ba?Me yasa kazo nan kuma ?.” 

Bai amsa mata ba ya soma takowa inda take , ita kuma cikin tsoro ta soma dube dube tana neman hanyar da zata gudu.

Yana zuwa daff da ita tayi ‘ko’karin guduwa amma ya ri’ke mata hannunta da yake da lafiya 


Cikin tsarguwa ta furta “ Dan Allah karka ta’bamun hannu na Uncle Moh, kaji Dan Allah , zan dena rashin ji ga baki d’aya ! Am sorry 
.”

Da hannunsa d’aya ya soma ‘ko’karin cire mata top abayan jikinta tunda akwai wata rigar a ciki, amma ta cukwikwiye ta hanasa.

Yi yayi kamar zai ta’ba d’aya hannun , sai tayi saurin sakin rigar tana d’an zazzare idanu
.

Ya cire Abaya , ya yar a inda suke ,
Nufi gaban mirror d’insa da ita , hannunsa har yanzu yana cikin nata duk da tayi ‘ko’karin ‘kwacewa, amma ‘kafin su ba d’aya ba .

Wani abu ya d’auko kamar mai jikinsa har rubuta moov.

Mimi tana ganin Moov jikinta ya soma rawa sabida tasan ya riga ya gane hannunta na ciwo kenan.

Da sauri ta furta “ Uncle Moh zanje nayi fitsari kaji.” 

Bai kulata ba  , a gigice ta kuma cewa “ Uncle Moh zanje nayi fitsari , Dan Allah banaso nayi a wando ! Zanyi fitsari please.” Kamar an ta’bata har ta soma kuka.

A gefen bed ya zauna, zata kumayi masa magana ya zaunar da ita akan cinyarsa, kafin tayi wani yun’kuri ya saka both legs d’insa ya ri’ke nata ‘kafafun, ko motsin kırki batayi sabida mugun ri’ko da akai musu


Yana bud’e moov d’in nan ta soma kokawa dashi zata gudu , amma ya’ki sakinsa.

Ta cijesa a hannu, a kafad’a har a wuya, tana ‘ko’karin sake cizansa ya furta “ Mimi kura kika zama yau ne ?.”

Tayi shiru hawaye na sauko mata akan kuncinta..

Yan ri’ke hannun da yake ciwo ta furta “ Aushhhh..” Sabida zafin da taji.
Amma hakan bai hanata soma ro’kon saba “ Dan Allah Uncle Moh kayi hakuri, wallahi na dena maka duk abunda baka so! Na dena ka sakar mun hannu na.”

Yayi mata shiru yana observing d’in hannunta.

Wani waje da ya kama sai da Mimi ta saka azababban ihu , tana fusge fusgen san ‘kwace hannun nata, amma ya ri’ke gam yana ja a hankali , ita kuma zafi take ji sosai , irin zafin da har kayi fitsari bama ka sani ba , dan itama sai da ta somayi a jikinta bata sani ba , kuma tana zaune ajikin Moh ya hanata ko da ‘kwace hannunta , tayi ro’ko tayi magiyar, tayi masa nacin amma ya’ki sakin hannunta .

Fuskarta duk tayi dama dama da kuma


Yana ja tana masa magajiyar dan Allah kayi ha’kuri Uncle Moh, bazan sake duk abunda nake ba , kome kace nayi maka zanyi maka dan Allah ka sakar mun hannu na zaka ‘balla mun hannu, Mamy please kice ya sakar mun hannu na, Baffaaaaaa
” ta ‘kwalla ‘kara jin ya mata wani da hannu har ‘kashin ta sai da ya bada ‘kas
 a wannan lokacin ne taje ajiyar zuciya me azabar ‘karfi kamar zata shid’e, sai ya d’an ja hannun a hankali yana sakin hannun


Cikin jin haushinsa ta mi’ke tsaye, amma kuma sabida ‘kafafuwan su yana cikin na juna ta sake komawa ta zauna a cinyar nasa, hannuwanta both a fuska ta rufe su tana shash she’kar kuka.

Ya ta’ba hannun ta mi’ke su, tana ‘kara rufe face nata.

Murmushin gefen baki yayi kad’an , sai ya saka hannu a wuyanta yana ta’bawa , a hankali cikin cool voice nashi ya furta “ Mimi you’re having fever 
. Bani na duba ki
”

Bata d’ago ta kallesa ba ta furta “ Ni ka ‘kyale ni
.”

“ Okay tashi ki canza kayan ki, kinga kin ‘bata mu 
.”

Yanzu a d’an zuciye ta d’ago, tana wani irin mugun hararansa , a zuciye a zuciye ta furta “ Anyi fitsarin
” ta kuma rufe face nata a dai dai lokacin da ta soma wani kukan
.

Yanzu murmushin da yayi har sai dai ha’kwaransa suka d’an fito, dan ya lura a mugun zuciye take yanzu, kuma ko me zai mata ba zata ji tsoro ba sabida ya gani a idanta fushi take dashi


Ga baki d’ayanta ya d’auketa ya wuce toilet da ita , yau ko zillewa ba tayi kuma ta’ki bud’e masa face d’inta balantana ya kalla .

Banda shash she’kar kuka babu abunda take .

Side d’in toilet d’insa da ya kaita akwai babban bathtub fari me shegen kyau. 

Yana zuwa da ita a hannun ya kunna wani button, wani ruwa ya soma ‘bul’bulowa da yawa a ciki..

“ Mimi can you do it your self ?
Or nayi miki?”

Ba tare da ta kallesa ba ta furta “ I will do it my self 
”

Bai ce mata komai ba ya fito daga toilet d’in.

İta kuma ta dan ta’ba ruwan da ya kunna mata taji da d’umi sosai, hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya , hannunta kuma ya rage mata ciwan sosai kusan 90% ya tafi , taji dad’in hannunta , amma sabida yadda ta dinga ro’karsa akan ya saketan ne yasa take jin haushinsa har yasa tayi masa fitsari a jiki yanzu


Wankan tayi sabida she’s not feeling her self , ko irin wasa da ruwan  da take inda shiga wanka yau ba tayi ba ..

Tana gama wankan ta fito.

Akwai wata doguwar riga ta zaman gıda akan bed , half vest , kuma pant, ta saka su, any moment za’a iya yin sallahr la’asar kuma tasan zuwa dubawa ko su Ameerah sun dawo, taga wajan da suka zauna a gyara alamar an goge wajan, as always d’akin yana nan kamar yadda yake cikin ‘kamshi da kuma tsaftarsa. 

Tana zaune akan bed ta d’an jingina da jikin gadon tana jiran time yayi tayi sallah, ya shigo d’akin shima da alama yayi wanka sabida while jallabiya da take jikinsa
. 

A gefenta ya zauna , ita kuma ta d’an juyar da fuskarta gefe , ta’ki yadda ta kalli side d’in da yake .

Akwai wani medium leda a hannunsa me kyau , ya ajje . 

Bata kula ba sai da ya saka hannunsa a wuyanta yana jin yadda d’imin jikinta yake .

Duk da cewa yanzu ta fito daga wanka jikinta ya soma tayar da d’umin zazzabi, ga la’asar yayi which lokacin ne zazza’bi ma yafi tashi 
..

“ Tazo muje kici abinci Mimi?” A hankali yayi mata magana cikin kulawa, ita kuma ta d’an zame hannunsa, bata kallesa ba ta furta “ Sallah zanyi
.”

“ It’s not yet time Mimi
”

“ Nidai zan soma sallah please
”

Bai sake magana ba , ya d’auko mata hijab da dadduma inda zata gani sai a lokacin ta kalli ‘kofar da ya fita da kallo.

Time d’in sallah nayi, tayi sallah yau ko azkar ba tayi ba ta kwanta akan daddumar sabida sanyi da take ji, kuma ta kasa tashi ta kashe Ac da yake d’akin, amma ta ‘kudun dune cikin hijab nata kamar me bacci.

After 42 minutes ya shigo d’akin , lokacin ‘karfe 4: 23pm , yana zuwa ya d’agata akan daddumar, tana ‘ko’karin sakewa komawa , sai ya d’auketa ga baki d’aya ya kwantar akan gado, ya kashe Ac ya mayar da d’akin so Warming



Ya fita ya dawo , hannunsa d’auke da tray, ga kuma tea half cup me zafi ga food ga kuma bottle water .

Da ya d’auko Tea d’in sai ya d’an kara masa ruwa ya zama me d’umi , ya kira sunanta “ Mimi?”

“ Uhm kawai tace masa a cikin duvet d’in, tashi kici abinci
”

Babu musu ta soma ‘ko’karin tashi shi kuma ya taimaka mata. 
Tea d’in ya mata , duk sau hudu tasha tace ta koshi, sai ya karbi cup d’in ya soma bata da kansa, tasha rabi ta matsar  da kanta gefe alamar ta ‘koshi.

Ya bud’e abincin 2 cup tayi tace ta ‘koshi sabida bakinta har ya soma rashin dad’i babu d’and’ano komai
kamar magani take ji a bakinta. 

Amma haka yayi forcing d’inta tayi 6 spoon daga nan kuma ta’ki yadda ta sake ci.

Zata koma ta kanta ya matso da ita kusa dashi a zaunen ya d’ora kanta a kafad’unsa sabida yadda zataji dad’in zama Abincin da taci kuma ya fad’a .

Ta kwanta a jikinsa kamar me bacci, amma shi a jikinsa yana jin zafin jikinta. 

Sunyi 30 minutes a haka , ya d’an janyo ledar bayansa tunda kamar hugging d’inta yayi ba zata me yake yi ba. 
Tablets ya bud’e ya ciro mata wanda yake so tasha , kafin ya d’agata “ Take some Medicine Mimi
”

“ Uncle Moh ka bari zansha anjima..” kamar me bacci tayi magana.

Gently ya furta “ You will take it now Mimi
 Kisha sai ki kwanta kinji?” 

Ta d’aga masa kai alamar Toh. Ya bata maganin tasha, ya taimaka mata ta kwanta , sai ta d’an ri’ko hannunsa , a hankali take fad’in “ Uncle , Ya jikin Ameerah fa? Sun dawo? Ko naje na ganta?”.

“ Kema you’re not feeling fine Mimi
 ki kwanta idan kin samu sau’ki sai kije ki dubata 
. Kinji?.” 

Ta d’aga masa kai alamar toh, tana rufe idanuwanta amma bata saki hannunsa ba .

Sai ya matso sosai kusa da itan yana zama a gefenta, tare da juyo da ita jikinsa ya zamto half of her body yana jikinsa, ya lullu’beta kuma da duvet d’in tunda ya cire mata hijab d’in jikinta , gashinta kuma da yake ‘ko’karin rufe mata fuska ya mayar dashi baya sosai, ta zama very comfortable numfashi ta yana fitowa a hankali, a hankali, sai da tayi 15 minutes a haka , kafin yanayin numfashinta ya canza alamar bacci ya soma d’aukarta .


_____ A ‘bangaran su Ameerah time d’in da Moh ya fita daga cikin motar nan ya kamata a sallame  su, amma sabida tana bacci kuma ba’a so a tashe ta , yasa basu taho ba sai around 4:30pm , har a lokacin Alameen yana asibiti kuma itama Mama ta koma , sun zo tare da Uncle Bashir , da kana masa kallo d’aya zaka gansa duk a gigice, kamar zai yi kuka duk time da ya kalli Ameerah
.

Mama bata fad’a masa abunda ya faru ba sabida tasan ba ‘karamun rigima za’ayi dashi ba a cikin gidan, tace masa dai Ameerah na asibiti , har suka zo kuma ciki babu wanda ya fad’a komai sabida baiga fuskar haka a wajan Aya ba , Alameen kuma fuskarsa tayi kicin kicin. 

Ya kasa tanbayar Mama sabida tana kusa da Aya shidai ya zauna yayi jigum yana kallan Ameerah gwanin tausayi.

Tana tashi yayi saurin matsowa kusa da ita yana fad’in “ Sannu Ameerah ta , akwai inda yake miki ciwo ne?”

Ameerah ta girgiza masa kai tana d’an masa murmushi “ Naji sau’ki Baba.”

“ Wana irin sau’ki kuma kikaji, bayan ga fuskarki nan ta nuna zallan rashin lafiya kuma kullum sai nace miki ki kula ki kula amma kalli yau keçe a kwance wai asibiti
 me ya faru haka?.”

Shiru Ameerah tayi masa sabida batasan ta yadda zata soma fad’a masa abunda ya faru ba , kuma batasan yaji maganar daga bakinta .

Kallan d’akin tayi da mutanan da suke ciki, ta d’an yun’kura da sauri, sai kuma tace “ Aush
” Tana komawa sabida ta d’anji zafin tashin da tayi da sauri .

Uncle Bashir yayi tunanin hannunta ne yake mata ciwo, sai ya d’an ri’ke hannun a hankali yana fad’in “ Sannu Ameerah , hannunki ne yake ciwo? Ko yayi tsami shiyasa yake miki zafi haka?”.

Ta girgiza masa kai alamar a’a


Matsowa Alameen yayi yana fad’in “ Me yake damun ki haka Ameerah , sai kinje kin faman ciwan da yake jikin ki?.”

Da mamaki Uncle Bashir ya furta “ Wana ciwo kake magana?”.

‘Dan saita face d’inshi Alameen yayi, yana wannan murmushin nasa 
. “Ciwan da yake cikinta mana
.”

“ Kamar ya ciwo ! Nasan lafiya ‘kalau na barta fa
”

“ Yeah ! ‘Daya daga cikin witch ( Mayya) d’in gidan ku ce take so ta illata ta , amma ba wannan ne me anfani ba yanzu.

Doctor zai dubata , if she’s fine za’a mayar da ita gida, akwai Dr da zata zauna tare da ITA for the remaining days sabida ta kula da ita, and yes Plus Aya 
..” yana kai wa nan Ameerah ta furta“ Uhm Uncle Alameen Mimi kuma fa?”.

“ She’s having Fever Ameerah , tana gida yanzu 
. In ta samu sau’ki nasan zata zo wajan ki, but yanzu for now ta lafiyar ki ake kinji?”

Ameerah tayi shiru, tana adduar Allah yasa ba wani abun bane ya sameta , wani zuciyar kuma yana bata turetan da tayi har ta fad’i shiya janyo mata wannan zazza’bin . Ita bama na ciwan jikinta take ba sabida abun it’s not scary yadda ake tunani kawai dan a ciki ne shiyasa yafi komai d’aga hankalin kowa .

Alameen ya fita sabida zai ga Dr d’in kuma yanaso ya basu space suyi magana a tsakanin , sai itama Aya ta fita , making saura su uku kawai a d’akin. 

Da sauri Baffa kalli Mama “ Ki fad’a mun maza maza abunda ya samu Ameerah haka , wana ırin ciwo ne haka a cikinta ?.”

Mama yaja wani dogon ajiyar zuciya , jiki a sanyaye ta furta “ Zarah ce ta caka mata wu’ka, zata caka wa Mimi , Ameerah ta tureta , wu’kar ta d’an sameta kad’an Allah ya taimaka kayan da ta sa masu nauyi ne kuma Zarah bata daddage ba shiyasa kad’an ne ya shiga jikin Ameerah
.”

“Kutumar uba” shine first word da Uncle Bashir ya soma amfata , kafin dai ya sake sassaita kansa yana fad’in “ Wace Zarahn kike magana , kuma dan ubanta wace Mimi da taso cakawa wu’kar?”.

“ Zarah dai da ka sani nake nufi, da kuma Mimi
  sun soma fad’a ita kuma abun ya ‘bata wa Zarah rai ta d’auko wu’ka
”

Wata shegiyar dariya Uncle Bashir yayi, kuma kisan da take ‘ko’karin yi ta rasa akan wa zata soma gwadawa sai akan Mimi? Dan ubanta bata da hankali ko?”

Shiru Mama tayi tana kallansa sai suka ga ya sake wata shegiyar dariyar yana jijjiga kansa, zai juya Mama tayi saurin cewa “ Amma dai ba wani abun abun zaka je kayi musu ba ko?”

“ Wa ? Ni d’an iska? Ai Alhamdulillah tunda babu wani abu da yasa mu Mimi, da wani abun ya same ta daga ni har ke babu wanda zai tsaya yana magana har haka , naji dad’i da Ameerah ta tureta, kema naji dad’i da babu wani serious akan ciwon sosai
..

Ai ni yanzu babu abunda zanyi.
Masu abu da abun su , namu kallo kawai
 zan dai kira na shaidawa ubanta abunda ‘yarsa tayi, idan yana da raban sake jin muryarta sai suyi sallama tun yanzu
.”

“ Mama wai meyasamu Baba ne haka wana irin magana yake ni bana gane wa .” Ameerah ce tayi maganar bayan ta rufe door .

“Hhmmm Ameerah kamar baki san halin mahaifin ki ba? Kinsan shi sarai bau d’ad’d’an mutum ne shi sai dai kawai ka kallesa kayi abunda yace amma bazai fasa ba .

Yanzu dai ki ‘kyale zancen sa ma a gefe , ni yanzu ta lafiyar ki nake , idan yaso koma mene ne , daga baya ayi shi
.”

“ Amma Mama ya banga su Uncle Saleem ba?.”

“ Uhmmm in banda abun ki Ameerah taya zan d’auki wayata nace musu gaki nan Zarah ta caka miki wu’ka kina asibiti? Ni bansan ta yadda zan iya wannan maganar ba sabida abun ya d’aure mun kai
 

Ita kanta Zarahn ina tunanin ko shafar aljanu ne akanta , dan Zarahn da na sani ba zata aikata muku haka ba 
.”

‘Dan ta’be baki Ameerah tayi “ Uhm Ita Zarahn?.”

“ Kodai akwai abubuwan da suka faru a tsakanin ku da ba’a sani ba Ameerah har ta zuciya irin haka take ‘ko’karin illata ku?”.

“Mama dama tun can ai ba tsoran Allah suka cika ba , kin manta lokacin da
.” Ameerah bata ‘karasa ba Mama tayi saurin fad’in “ Ya dai isa haka Ameerah , kiyi shiru tunda ba lafiya ne da ke sosai ba 
 mu bar maganar haka.”

Shiru Ameerah tayi bata kuma cewa komai ba , itama kuma Mama tayi shiru sabida batasan ma maganar da Ameerahn za tayi. 

Minti 5 tsakani duk suka sake dawowa d’akin, ciki kuma har da Dr aka sake duba Ameerah aka tabbatar zata iya tafiya , magunguna and everything an bayar , already ma Alameen yayi komai , zasu koma gida .

Wajan around past  5 suka dawo gida , tare da manya manyan SUV d’in da sukai slow down lokacin da suka ga motar Moh
..

Sun dawo gida , yau har part d’in su Ameerah , Alameen ya shiga amma bai shiga cikin bedroom d’inta ba  yana falon ‘kasa .

Aya , Doctor , Mama sune a cikin bedroom d’in sai Aunt Feedy da kuma Aunty Shukura da tuni suke part d’in dan tun dawowar Mama na farko Aunty Shukura tasan me ya faru , ita ce ta kira su Aunty Feedy ta shaida musu sabida da ta dawo part d’in su ta ganshi a ‘bace da jini , gashi babu kowa a cikin falon, sai da Mama ta fad’a mata abunda ya faru tukunna ta d’an kwantar da hankalinta kad’an , amma tasha muka ta ‘koshi 


Ta kira su Mammy ta fad’a musu ta kira su Baffa suma ta shaida musu, hatta su Uncle Saleem saida ta kira kowa ta fad’a masa gida ba lafiya amma ta kasa fad’o musu komai sai jini da yake falon kawai ta iya fad’a musu, amma babu kowa har Zarah babu ita babu alamarta 
.

Anyi settling d’in komai an bar Ameerah tana hutawa kamar yadda Dr d’in ta bu’kata , su dawo falo su Aunty Feedy duk sunyi jigum jigum an rasa ma me magana sabida nauyi da bakin su yayi duka .

Aya kuma tana wajan part d’in ta fito ita da Alameen da suke magana. 

Sai almost to 6 mazan gidan suka dawo kowa hankali tashe sabida akwai ta zarar inda suke da gida , cikin tashin hankali kuma suka wuce part d’in su Ameerah.

Baffa da Daddy inda suke je ta’aziyya akwai kusan 2 hours gap tsakanin su da gıda, amma yadda sukaji abunda Shukura ta fad’a suna cikin gidan gaisuwar nan suka fito, suka hau motar zasu dawo gida . Sosai suka d’aga hankulan su, idan suka ce zasu sake komawa su bi ta jirgi abun zai ‘kara musu delay shiyasa suka sa driver yaja motar da gudu, kuma yadda ake gudu sosai akan hanya, idan Allah ba kiyayewa yayi ba tsaf zai iya janyo babban Accident.

Mommy da Mammy ma sun fito daga inda suka je sabida abunda Shukura ta ce musu, hankalin kowa ya tashi Mammy tana tunanin halin da ‘yar ta take ciki, Mommy ma tunani kala kala suna ‘ko’karin tarwatsa ta sabida tunanin me ya faru, kuma ina Zarah shine abunda ya hautsina ta, hankalinta yayi mugun tashi dan ita ba wai ta Ameerah ko ta Mimi take ba , gwanda Mammy da ta raba hankulanta gida biyu, rabi akan Ameerah, rabi kuma akan Mimi
..

Lokacin da suka ‘karasa gida , ana yin parking cikin sauri sauri gudu gudu Mommy ta je part d’inta tana neman ‘kwallawa Zarah kira , it’s kuma Mammy cikin sauri ta nufi part d’in Ɵu Ameerah kuma akan idanuwan su Alameen suka shigo cikin gidan.
Wani shegen murmushi kawai yayi yana jinjina kansa
.. 

Mommy tana zuwa taga d’akin Zarah a kulle , ta ‘Kwan’kwasa tayi kiran duniya Zarah bata bud’e ‘kofa ba , har sai da Mommy taje ta kulle part nasu ga baki d’aya .

A d’an rud’e ta furta “ Na kulle ko ina Zarah bud’e muyi magana, wani abun ne ya sa meki?.”

Taji motsi a cikin d’akin alamar ana matsowa kusa da ‘kofar .

Cikin kuka taji muryar Zarah tana fad’in “ Mommy ta mutu ko?”

A rud’e Mommy ta furta “ Babu wanda ya mutu Zarah , nace ki bud’e muyi magana , yanzu haka Ameerah tana part d’in su duk sun dawo gida kinga kenan babu abunda ya faru, so suke kawai su tsoratar dake , ko kuma suyi miki sharri , kuma babu abunda zai faru wallahi bazan ta’ba bari ba 
 bud’e muyi magana.

Bud’e ’kofar Zarah tayi , fuskarta tayi dama dama da kuka har da majina majina , tana ganin Mommy ta fad’a jikinta tana faman sake fashewa da kuka 


“ Mommy nidai wallahi idan suka ce zasuyi mun wani abu zan kashe kai na sabida wallahi bazan yadda ba sharri suke so suyi mun , babu abunda nayi musu.”

“ Me ya kawo maganar kisa ma ana zaune ‘kalau? Keda kike da gaskiyar ki, kada ki yadda kuma kiji tsoro, kome sukai kice baki yadda ba had’in baki sukai miki sabida suna jin haushin ki, kuma kome zai faru Zarah kice ‘ko’kari sukai zasu caka miki wu’ka , Ameerah ta fad’i sai wu’kar ta sameta , kada ki yadda kice kece kikai ko agaban Daddyn ki ne , ai ga su Baffa  bazasu goyi bayan zalinci ba .”

“ Mommy ai sharri suke mun..”

“ Karki wani damu, yadda kike d’aga hankalin ki yanzu shi zai sa suyi miki sharri, amma idan aka ganki normal babu komai a fuskarki za’a fi yadda dake , yanzu kukan da kike shi zai sa suyi miki sharri kuma kinga sunci galaba akan mu


Ki wuce kije kiyi wanka , ki wanke wannan fuskar taki, zan kawo miki shayi kisha mai zafi, karki nuna komai , ai ina nan babu abunda zai faru dake.”

“ Tom Mommy bari naje nayi wanka.”

“ Kiyi sauri ki canza kayan ki sabida nasan duk inda Daddyn ki yake yanzu ya samu labari kuma nasan ßuna yana hanya a yanzu, gwanda ya ganki a cikin nutsuwarki sabida yadda zai fi yadda da maganar ki. 

Idan har baki d’aga hankali ba kika kwantar da hankalin ki waje d’aya , ni zan iya gamsar da Daddyn ki cewa kina part d’in nan babu inda kika je . Ki nutsu kawai , kinji ko Zarah ta?”.

“ Toh Mommy 
”

“ Maza yi sauri ni bari naje na bud’e part d’in kar suyi wani tunani , dan baza’ayi galaba akan mu ba , ina gaf da cikin nasara ta .”

Tana gama fad’ar haka ta wuce ta bud’e part d’in nasu, sannan ta koma ‘kara sanar Zarah cewa tayi zamanta a d’aki kada ta fito har sai idan itace tace mata ta fito.. 
da haka ta fito waje zata je part d’in su Ameerah .

Alameen da Aya suna tsaye , tayi saurin wucewa ta gefen su sabida kada su tsayar da ita 


Kallan juna both Aya da Alameen su kayi, sai kawai Aya tabi bayanta .

Kowa yana zaune a falo har da Mammy, ta shigo Mommy kamar babun ya faru, amma yadda ta gansu kowa fuskarsa gata nan gatanan sai kawai itama ta d’an narke fuskar ta , alamar tsantsan damuwa
. 
Bata ma zauna akan kujera ba ta furta “ ina Ameerahn take naje na dubata ko hankali ya kwanta ya jikin nata ?” Ta tsayar da kallanta kan Mama 


Da hannu Mama ta nuna mata d’aki tana fad’in “ Tana d’aki.”

Ta taka zatayi hanyar d’akin Aya da take tsaye ta furta “Hutawa take yanzu, ba’a bu’katar kowa ya shiga .”

“ Ayyo ! Aikam dai ya kamata na dubata , hankali na bazai ta’ba kwanciya ba idan ban ganta ba , me ya faru haka?” Ta kuma maganar kamar ba ita ce take kitsawa Zarah abunda za tayi yanzu ba .

Shiru Aya tayi mata , ita kuma Mommy tana jiran amsawar nata ne sabida ta wuce zuwa d’akin Ameerahn, amma bata ga fuska a wajan kowa ba , sai kawai ta samu waje ta zauna itama a kan kujera kusa da Mammy kad’an tana observing fuskokin kowa.


_____ Wajan sallar magrib su Daddy suka shigo gida, kai tsaye a part d’in su Ameerah akai parking 
. Kana kallan face d’in su zaka ga damuwa , duk da suna ‘ko’karin danne ran su. 

Suna shiga Baffa yasa akai su inda Ameerah take .

Sunje tana bacci , basu zauna sosai ba , suka fito sabida ana kiran sallah, wani irin kallo da Daddy yake wa Mommy sai da ta sha jinin jikinta amma a haka tana ‘ko’karin nuna kamar babu wani abu da ya faru. 

Alameen da Aya basa cikin part d’in yanzu .

Rai a ‘bace Baffa ya bada umarnin kowa ya dawo falon nan idan anyi sallahr magrib , sabida bazai yu a bar Ameerah ita kad’ai a part d’in ba 


Da ga haka kowa ya wuce dan yayi sallah , sannan su sake dawowa kamar yadda Baffa ya bada umarni.

Ana idar da sallah , su Aunty Feedy ne suka soma shigowa falon, sai su Mammy , dasu Uncle Saleeem , sai su Baffa, Uncle Bashir , da Daddy.

Mommy da Ameerah sune ‘karshen shigowa ,tama ‘ki kallan kowa nacikin part d’in kamar yadda Mommy ta bata shawara , gashi yau tasha wani babban hijabi .

Mimi, Uncle Moh , Alameen , da kuma Aya basa cikin falon. 

Daddy tun kafin ya tanbayi abunda ya faru, ya soma fad’a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sabida yadda ransa yayi mugun ‘baci.

Ya kalli Zarah cikin daka tsawa ya tanbayeta abunda ya faru, amma sai Zarah ta sa kuka , cikin ‘barın rai Daddy ya mi’ke zai nufota, Baffa yayi saurin ri’ke sa yana fad’in “ Me kake ‘ko’karin yi yanzu ? Ta’bata za kayi?”.

“ Yaya ai gwanda na karya mata wuya ko ta bud’e baki tayi bayanin abunda ya faru, in ba iskanci ba ana mata magana tana yi wa mutane kuka, lokacin kuka ne yanzu ?.”

A nutse Baffa ya furta “ Duk bai kai haka ba ai , zauna ayi magana ta fahimta , sannan asan abunda ya faru.”

Babu yadda Daddy ya iya haka ya samu waje ya zauna sabida Baffa . 

Da wuya kaga ‘bacin ransa, amma tunda yau ya fito da ‘bacin ransa an kaishi bango ne




________
Mimi 
.
Bayan an idar da sallar Magrib ya sake dawowa d’akin, har yanzu bacci take , a gefen bed ya zauna yana ta’ba wuyanta, sai ta d’an motsa kad’an hakan yasa yaji temperature d’in ta har yanzu da zafi sosai , ta ya mutsa face nata alamar bacci ba wani jin dad’insa take yi ba .

Ya sake gyara mata duvet d’in sosai , ya kalli time baya san tashinta ya fiso ta tashi da kanta karta samu ciwan kai
.

Yana ‘kara ta’ba wuyanta ta bud’e ido, ganinsa a kusa da ita tayi narai narai da ido , shi kuma ya girgiza mata kai “ Don’t cry okay?”

Ta d’aga masa kai alamar toh, cikin sanyin murya da zazzabi da yake cinta ta furta “ Uncle 
 Moh 
 Ya jikin Ameerah?”.

“ Mimi she’s fine kinji?”

“ Toh zan iya zuwa na ganta?”.

“ No ! Ki bari ki samu sau’ki sai kije , kinji?.”

Yanzu ma ta sake d’aga masa kai.

“ Can you pray?
”

Ta d’aga masa kai alamar “ Eh
” 

Ya taimaka mata ta tashi zaune, da za ta tafi toilet ya ri’ke mata hannun suka nufi toilet


Da tace za tayi fitsari sai yayi excusing kansa ya fita , bayan ya tuntata lokacin da zata gama , ya dawo, lokacin har ta soma alwala ,
Yana tsaye tayi alwalar , suka sake fitowa tare .

Ya d’auko mata dadduma , ya bata hijab tayi sallah , shi kuma ya zauna akan gefen bed yana kallanta .

Da ta idar da sallar sai tayi ‘ko’karin kwantawa a wajan, amma ya hanata 

Ya zaunar da ita kusa dashi “ In kika kwanta zazza’bin zai fi damun ki Mimi, zaki zauna falo ke da Aya? 
”

Ta girgiza masa kai alamar A’a , a hankali ta furta “ Bacci zanyi Uncle Moh..”

Bai musa mata ba ya bari ta kwanta, har zuwa lokacin da Bacci ya sake d’auketa .

      ________________
      Baffa nasiha yayi wa kowa sosai na cikin falon , kafin cikin taushin murya ya tanbayi Zarah abunda ya faru, amma amaimakon ta amsa masa tanbayar sai ta ‘kara fasa wani kukan, har da shash she’ka kamar wacce zata shid’e. 
  Iya sha’kuwa Daddy ya sha’ku da iskancin Zarah , Baffa kuma ya hanata yin magana ganin dagaske so yake ya duke ta . 

Unexpected aka shigo falon, ga baki d’aya suka kalli wanda ya shigo cikin falon. 

Alameen ne da kuma Aya da take gefensa, yau fuskar ko irin murmushin da yake yin nan babu, ga baki d’aya ya rikid’e ya koma real Alameeen d’insa. 

Zarah tana ganinsa ta mi’ke tsaye ,
jiki na rawa ta soma ‘ko’karin ja baya, Mommy tana ‘ko’karin ri’keta ta zauna amma kuma ta rud’e ganin yadda Alameen yake mata wani irin kallo. 

Taku d’aya da yayi zuwa biyu , Zarah tayi saurin fad’in “Ka dena matsowa inda nake , wallahi zan kashe kai na ka sake matsowa .” Ta ‘karasa maganar ta fito da wu’kar da take cikin hijab d’inta
.

Ga baki d’aya aka saka sallallami , Mama da Mammy dama su Aunty Feedy suna ro’kanta akan ta ajje wu’kar , amma ta saka wu’kar a  dai dai wuyanta , tana kallan Alameen , duk da kasancewa hannunta rawa yake, su Uncle Saleem sunyi ‘ko’karin su amsa wu’kar amma tana wuyanta kuma duk ta rikice idan sukai ‘ko’karin cewa zasu ‘kwace da ‘karfi zata iya jiwa kanta ciwo by mistake ..

Uncle Bashir da Daddy suna zaune suna kallanta, kana kallan Daddy kasan dauriya yake, kamar jira yake yazo inda take ya bubbugeta. 

Alameen yayi murmushi, irin shi kad’ai yasan ma’anar murmushin da yayi, yana kallan Zarah a kai kaice , ita kuma sai ‘ko’karin ja baya take , hankalinta yana kan Alameen batasan Aya ta bar wajan ba , ta koma ta bayanta ..

Unexpected Aya da tazo kusa da ita ta baya ta saka ‘kafarta da ‘karfi ta kurfe Zarah
.

‘Kara Zarah ta saki tana sakin wu’kar hannunta at the same time kuma ta saki wu’kar.

A gabansu ga baki d’aya Aya ta janyota kusa da Alameen kamar kayan wanki, kowa ya shiga taitayinsa ganin abun bana wasa bane , dan har Baffa yanzu ya kasa magana balantana ma har ya basu ha’kuri akan abunda yaga suna ‘ko’karin yiwa Zarahn. 

Uncle Baffa kuwa , murmushin yake , duk da yana ‘ko’karin ‘boye murmushin , ya kasa ‘boyuwa ga baki d’aya .

Hannu Alameen ya saka daga inda yake yasha’ko wuyan nata, da ‘karfi, ta d’an soma dukan hannunsa kad’an kad’an sabida kakaki da ta soma na wahala , cikin ihu Mommy ta dinga ro’karsa akan ya saki Zarahn amma kamar ‘kara zugasa take .

The more tana kukan ya saki Zarahn da more yana ‘kara shareta, sha’ka kuma kamar ba ta wasa ba , fuskarsa kwance da murmushi sosai
.
“ Mutuwa kike so kiyi , I can help you with that 
.” Ya kuma sha’kota 
.

Mommy tazo tana ‘ko’karin dukansa , Aya ta ri’ko rigarta , ta soma wanka mata mari, ji kake tasssss tassss tassss tassss tassss , sai da ta wanka mata mari biyar tana hankad’ata ‘kasa 
.

Ga baki d’aya falon kowa ya shig cikin tashin hankali da tsoro, babu wanda bai tsorata da su Aya ba , har Mammy da tasan Aya yau sai da ta d’an tsorata da ita .

Alameen sai da yaga tana ‘ko’karin shid’ewa tukunna ya sake ta ‘kasa , tana faman kakari, hannunta da yake wajan ya taka da ‘karfi yana tsugunnawa , ita kuma ta saki gigitaccen ‘kara tana ‘ko’karin ’kwace kanta


Sai  alokacin Baffa ya mi’ke tsaye shida Daddy ganin yadda Alameen yake ‘ko’karin illata Zarahn a gaban idanuwan su
.

Suna ‘ko’karin magana, wasu manya manyan maza farare tasss dasu suka soma shigowa falon , jikin su sanye da ba’ka’ken kaya, gadai wu’ka da bindigu a jikin su , idanuwan su da ba’ka’ken glasses , gashi babu ko fara’a a tattare da su
.

Lokaci d’aya ’kamshin turarensa ya cika falon, tun kafin gangan jikinsa ta bayyana, Baffa da Daddy da suke tsaye suma suka koma suka zauna



Sanye yake da all black outfit, face d’insa a mugun d’aure babu fara’a kwata kwata a face d’insa , duka falon sai da suka sha jinin jikin su ganinsa a cikin falon, wanda shine karo na farko da ya ta’ba shigowa cikin taran familyn. 

Ga wasu 2 giant guys guda biyu da suke bayansa, d’aya black , d’aya white 
. 

Black d’in ne ya janyo 1 sitter d’in kujera ya ajjewa Moh
.

Moh yana zaune akan kujera yayi crossing legs d’insa waje d’aya , hannunsa d’aya akan goshi yana d’an ta’bawa a hankali, a hankali. 

2 giant guys d’in nan suka koma bayan Moh, Alameen ma da ya taka ‘kafar Ameerah ya saketa yana wani murmushi tare da komawa side d’in Moh shi da Aya .

Hakan yasa familyn ga baki d’aya suke facing d’in Moh
..



__________

ISTANBUL


.
Washe gari ‘karfe 7:06am na safe.

“ NUNUUUU
” muryar Ahmet ta d’an karad’e wajan idan yake a tsaye wato  a bakin ‘kofar d’akin  Nunu, hannunsa ri’ke da wayarsa , d’aya hannun kuma yana kan ‘kugunsa . 

Nunu da take zaune a tsakiyar gadonta, tana ‘ko’karin sanya ‘karamar safa a ‘kafarta, ta d’ago kai ta kalle shi tare da fad’in 
“Memet?” Cikin ‘yar ‘karamar muryarta , tana turo bakinta kad’an.

Rufe idanuwansa Ahmet yayi yana sake bud’ewa akan Nunu “ Yes Nunu ! It’s me ! Now can you please tell me why you’re wearing one shoe and one sock?”

Sauke idanuwanta tayi akan ‘kafarta, tana saurin d’auko d’aya samar, muryarta na ‘yan yara ta furta “ Na manta Memet
 kalli yanzu na saka ya zama two
”

‘Karamun dariya Ahmet yayi “ Allah ya shirya mun ke , wallahi 
” 

Da gur’batacciyar maganarta itama ta furta “ Allah ya shirya kai.” Yanzu kam sosai Ahmet yayi dariya yana shigowa d’akin .

Akan cinyarsa ya d’ora yana gyara mata takalmin nata sosai “ Na kula so kike ki makara a school yau , and kuma kinsan bazan bari ki makara ba ko ?.”

‘Bata fuska tayi “ No school.”

Shiru Ahmet yayi yana kallanta “ No school kuma?”.

Ta d’aga masa kai da sauri.

Shi kuma sai ya furta “ Okay.”

Da sauri ta rungume wuyansa cikin farin ciki tana fad’in “ Memet
”

Shi kuma sai ya ‘kara da Then no toys, no cartoons, and no going out with me.”

Da sauri ta sake sa , tana sauka daga jikinsa, muryarta kamar za tayi kuka ta furta “ Memet you bad !.”

Wani irin dariya Ahmet ya fashe dashi , yana nuna kansa “ Me? Ni ne bad? After  everything I’ve done for you?”

Nunu ta sake d’aga hannunta tana nuna shi da yatsa “ Yes ! You bad !.”

Kamar wani ‘karamun yaro Ahmet daga d’akin ya
‘Kwalla  kiran sunan Anne da ‘karfi muryarsa yana fad’in “ Anneeeee Please come and collect your daughter. This girl has started insulting me!”

Daga can ‘kasa suka ji muryar Anne tana fad’in “ Ahmet Don Allah kar ka soma damuna da sassafe kai da Yarinyar nan ! It’s too early
” 

Kallan Nunu yayi yana d’an bud’e mata hannu tare da fad’in “ You see ! Even Anne tana supporting d’in ki , dan haka be a good girl kinji ?
”

“ Aaaa
.” Nunu ta fad’a da ‘karfi tana dariya da guje guje 
  shi kuma Ahmet ya kamata yana dan mata cakulkuli, ßuna dariya tare . 

A wannan lokacin ne Aylin tazo bakın ‘kofar, jikinta sanye da wata rigar bacci iya gwiwa, gashinta a warwatse a kafad’unta, tana kallon su a kule , fuskarta duk d alamun bacci kamar yanzu ta tashi 
“Can you people please keep it down? Some of us are trying to sleep!”

Ahmet ya juyo a hankali ya kalleta.
“Good morning to you too, Princess.”
“Don’t call me that.”
“Okay, Your Highness.”
“Ahmet!”
“Naam, Aylin?”
Ta yi masa wani irin kallo tare da fad’in “Are you always this annoying?”

“ Only when I’m around people like you
” shima ya bata amsa yana mata banzan kallo. 

Har zata ja tsaki, sai ta fasa , zata juya ya kira sunanta “ Aylin.”

“ What?” Ta bashi amsa tana juyowa 

“ Ki dinga kulle mana wannan gashi me kama da wacce tayi fad’a da kura , kisan yadda zaki dinga rufe mana kai when you’re around people.”

“ Ahmet must you be this annoying? Why do you hate me so much?”

“ Who are you da har zan tsane ki? My friend go and do your business , am busy right now!”

A ‘kufule Aylin ta juya ta bar d’akin bayan ta sakar musu hararar ‘kasan ido su duka. 

7:42am — Dining Room

Anne ta gama shirya breakfast, Nunu tana zaune a kujerarta tana wasa da cokalin hannunta, yayin da Ahmet yake duba wasu sa’konni a wayarsa.

Aylin ta shigo, wannan karon ta shirya tsaf, ta zauna a kujerar da take fuskantar Ahmet.

Kallon shi take cikin jin haushi dan har yanzu bata huce ba akan hanata bacci da sukai shi da Nunu sabida dariyar su.

Sarai Ahmet ya lura da kallon da take masa , amma yayi kamar bai ganta ba , sai ma cewa da yayi wa Anne “ Anne , can I have some tea , please?.”

“ Yeah why not Ahmet
” Anne ta mi’ka amsa cup tea d’in .
Suna tsakiya da sha Anne ta d’anyi gyaran murya “ Ahmet yau zan fita da Nunu, bana tunanin zata je makarantar nan , because am going somewhere with her
.”

“ Somewhere like how Anne?” Yayi maganar yana ajje cup d’in hannunsa


“ Are you questioning me Ahmet? Ko sai na baka cikakken bayanin inda zanje da ita kafin ka yadda?”.

‘Dan murmushi yayi yana girgiza mata kai “ Of course not , Anne
” Sai tayi shiru na seconds , sannan ya ‘kara da “ I was only asking
”


Aylin ta d’an d’aga kai daga kofinta tana kallonsu, amma da Anne ta juyo side d’inta , sai tayi saurin sunkuyar da kanta.

“Ke kuma Aylin, yau kina da wani abu da zakiyi ne ?”

Aylin ta d’auka Anne zata ce zata biyo sune sai tayi saurin cewa “Not really.”


“Good. Then you can stay home and help with a few things.”cewar Anne


Cikin d’an sauri ta ajje cup d’in hannunta tana fad’in “ Sorry?”alamar bata fahimci maganar ba ,

Cikin nutsuwa Anne ta sake maimaita mata abunda tace “ Na ce ki zauna a gida kiyi wasu abubuwan ! You should stay and do something necessary Aylin.”

“ Anne I have something to do..” Aylin tayi maganar tana d’an ’bata fuskarta kad’an 


“ Kamar me kenan?” Anne ta sake tanbayarta .

shiru Aylin tayi na d’an lokaci, kafin ya furta “ Personal things 
”

Wani murmushi Ahmet yayi , tun d’azu da suke magana bai sa baki ba sai yanzu “  Very personal, apparently
 Aylin
”


“ Ahmet can you  please mind your business?”

Cikin I don’t care ya furta “ I’m trying to. Unfortunately, your business keeps announcing itself.”


“Cikin  d’an jin haushi Aylin ta furta “Ahmet!” Shi kuma ya amsa da yeah! What next..”

Aylin za tayi magana , Anne rai a d’an bace ta furta “ Can you guys please shut up?  Safiya ce yanzu amma kuna yin abu kamar wasu yara , If you’re done zaku iya tafiya bawai ku zauna kuna magana irin haka ba .

Ke Aylin if you’re done ki tashi kiyi abunda zakiyi and kai ma if you’re going out ka tashi ka fita , banasan irin haka 
.”

Aylin kamar jira take , Anne tana kawo ‘karshen maganar ta mi’ke tsaye tana fad’in “ Na ‘koshi Anne, zan koma d’aki na .” Da haka tayi hanyar d’akinta .

Tana barin wajan Anne ta kallesa “Banasan irin wannan abun Ahmet, kana sa Yarinyar nan taji kamar she’s not one of us , kuma banasan haka kai ma ka sani.”

“ Am sorry Anne
” daga haka yayi shiru bai ce komai ba .

Itama Anne ta mi’ke tana cewa Nunu “ Let’s go
”

“ Anne ko nazo na sauke ku a inda Kuje?”

“ No need for that Ahmet
”

“ Okay then should I follow you?.” 

“ Ahmet shima nace babu bu’katar yin hakan, do what’s necessary for you okay.?”

Kafin Ahmet yayi magana , wayarsa ta soma ringing


Kamar da wasa ya d’auki phone d’in even though he’s not expecting any call at that time, amma number wanda ya gani ne yasa ya kalli Anne da shock a fuskarsa , yana fad’in “ Anne ! It’s Emir
.” 

Babu shiri Anne ta samu waje ta zauna, Nunu daga ji an ambaci Emir tayi saurin matsowa kusa da Ahmet tana mi’ka masa hannu alamar ya bata wayar.

Answering call d’in yayi , sai dai maganar nashi ko seconds 10 basuyi ba ya kashe call d’in. 

Akan dinning ya bar wayarsa, yana nufar ‘kofar falon da sauri, Anne tana tanbayarsa mene ne amma sam yama ‘ki kulata sai da yaje ya bud’e ‘kofar
..

Da sauri yayi ja baya kad’an lokaci d’aya murmushi ya su’buce masa akan fuskarsa , Nunu da Anne da suke bayan sa . Ita Anne ‘kafafuwanta kasa d’aukarta sukai ta d’an tsugunna a inda take, Nunu kuma ta ‘kwalla ‘kara tana nufarsa a guje
..

Guy d’in ya d’an bawa ‘kofar baya , hakan yasa ba’a ganin face d’insa, amma kuma yana da muscles ya Allah , Allah ya bashi ‘kirar mazan taka. 

Kayan jikinsa idin baggy outfit d’in nanne , baya tara suma sosai , amma kuma akwai gashi kad’an a kansa da kuma wani doguwar tsaga a wajan ‘keyarsa irin na mutumin da Ahmet ya gani a wannan d’akin
.

Ta’bashi da Nunu tayi ne yasa ya d’an jiyo ya kansa

.

Take a wajan fuskarsa ta bayyana
.

“ EMIR
.” Shine first word da Anne ta iya furtawa a wannan lokacin

Sai dai me ga baki d’aya fuskar Moh ne a tattare da guy d’in , banbancin kawai girar wannan guda d’aya a tsage take amma babu wani simple abu da ya rabasu, duk wanda yaga wannan guy d’in zai ce it’s Moh sabida fuskarsa babu annuri kwata kwata , as always kamar yadda yake ada


.


Can it be possible? Mutum d’aya a waje har guda biyu?


______________


END OF BOOK 1
MISHAL IS NOW 1k please 

2681892316
AISHA UMAR 
ZENITH BANK


ALHAMDULILLAH YA RABB ! ALHAMDULILLAH
 Ya rabb yadda ka bani ikon gama book 1 lafiya , Allah ina ro’kanka ka bani ikon kammala book d’in nan cikin Aminci
..


Thank you guys for the love and support .. Farhat A.K.A Shugabar masu commentđŸ˜‚đŸƒâ€â™€ïžâ€Š..Salma yusuf, Teema , Fatimas , Khadija Garba , Ayshert , Saliha , Aisha , Maimouna, zeinab and many more  all masu yi mun comment you guys have special place in my heart..❀ I Love you all Onetiti and wannan page na sadaukar dashi ga duka masoyan MIMIN MU DA MOH MOH 😂😂

_____________
Aysha Galadima đŸ€đŸż
***

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol