Free chapter · Read without an account

Page 2

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1

Page 2

Dariya suke ɓaɓɓakawa tamkar taɓaɓɓu,wanda ke fuskantar sauran ya ɗauki cup ɗin gaban shi ya kai baki,bayan ya ajiye ya sake fashewa da dariya sauran na taya shi.
Cike da farin ciki yace"mission accomplished".
Wolf yayi murmushi yace"shi yafi komai sauƙi Chief,dama wannan ba wani big deal bane da har zai ɗaga mana hankali,gashi cikin ruwan sanyi mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya".
Panther ya ɗanyi gyaran murya, gabaɗaya duk su ka maida hankali kanshi,ya gyara zama yace"wani hanzari ba gudu ba,mu bar ganin munyi nasara,dukkan mu nan mun san dole bincike zai biyo baya..."
Bracket yayi saurin cewa"daga baya kenan Panther,it was a very clean mission,ba mu bar wani room ko clue da bincike zai biyo ta kanmu ba so chill".
Chief yayi murmsuhi yace"so yanzu yaron na gida?"
Dragon ya gyaɗa kai yace"Tun washegari Chief".
Chief ya gyaɗa kai yace"that's awesome,duk ɗan da yace uwarsa ba za tayi bacci ba shima bacci bai gansa ba,kaɗan kenan Lieutenant Umar Sadauki".
Yayi maganar yana kallon makeken hoton Sadauki sanye da uniform dake kafe a bangon ɗakin.

**************

Zaune su ke su huɗu sun zagaye round table dake gabansu,ba ka jin karar komai sai na computers da cameras dake ɗakin.
Bilal ya sauke numfashi yace"this case is so complicated,duk inda aka je aka dawo sunanka na ciki dumu dumu, menene mafita?"
Yayi maganar yana kallon sauran.
Emmanuel ya gyara zama yace"Segun da aka yi amfani da muryar sa wurin magana da kai a wannan daren was not on seat,idan bashi ya kira ka ba then who was that person?"
Adebayo yace"duk wanda yayi wannan aikin yana da nasa manufar either one or two,da farko ya san cewa Segun ba shi zai yi aiki a wannan daren ba,sai aka yi amfani da muryarsa saboda badda sawu".
Bilal yace"ai har shi Segun ɗin is a suspect,shi ya kamata ace ya jagoranci record a wannan daren but he was not,then who was behind all this?"
Sadauki da tunda su ka fara magana bai ce komai ba ya ɗan bisu da kallo,cike da nutsuwa yace"we are just beating around the bush,mun san wanda yayi wannan aikin ya daɗe da shiryawa hakan,kuma ba lallai mu sami traces cikin sauki ba".
Adebayo yace"yanzu menene abin yi?"
Sadauki yace"Segun baya wurin,anyi amfani da muryar sa wurin bani umurni, which was a set up,duk abu ɗaya ne dake da alaƙa da juna,dole koma waye ya shiga communication room before or during the operation".
Bilal yace"ta ina zamu fara Falcon?"
Ya ɗan jingine bayan shi yace"Daga inda wanda ya shirya komai bai yi tsammanin za mu fara ba."
Duk su ka zuba mishi ido don jin abinda zai faɗa,ya kalli Bilal yace"Bilal,i want to know every detail akan inda Segun yake a wannan daren,ba wai iya inda yake ba,ina son sanin wanda ya ganshi,lokacin da ya shiga wurin da kuma lokacin da ya fita".
Ya juya wurin Emmanuel yace"and you,zaka binciki waɗanda su ka shiga communication room before and after the operation,sunayen su,lokacin da suka shiga,lokacin da suka fita da abinda suka je yi,komai ƙanƙantar clue kar kayi wasa dashi."
"Adebayo,kayi bincike akan duka records daya danganci wannan operation ɗin tun daga kan calls or video clip,daga lokacin da aka bamu umurni har zuwa lokacin da aka kai mana hari,ina son timeline ɗin komai".

***********

A ƙofar gida yayi parking ya fito yana bin unguwar da kallo,ya ƙarasa yayi knocking mai gadi ya taso ya buɗe.
Yana ganin shi yayi murmushi yace"a'a soja mazan fama,soja marmari daga nesa,ya ƙarfin jiki kuma?naji abinda ya faru Allah ya tsare ya kiyaye na gaba".
Ya ɗanyi murmushi yace"Mallam Iliya ba zaka canza ba,ya aiki?"
"Aiki Alhamdulilah,gamu muna taɓawa".
"Masha Allah,Allah ya taimaka".
Iliya ya amsa da Amin ya koma ya zauna.
Direct part ɗin Mami ya nufa yayi knocking, Firdausi ta taso ta buɗe,tana ganin shi tace"Yaya F,Ina wuni".
Yace"lafiya ƙalau".
Yabi bayanta ya shigo,Mami dake zaune tace"Faruq,har kaji sauƙi kenan?"
Ya shafa kai yace"Mami naji sauki,ina wuni".
"Da na biye maka da sai abinda hali yayi da hannunka Faruq,ba ka damu da lafiyar ka ba sam,kafi daraja aikinka akan lafiyarka".
Dai dai nan Zarah ta shigo,a hankali tace"ina wuni".
Ba tare da ya ɗago ba yace"lafiya ƙalau".
Mami tace"gashi tuwo mu kayi a gidan Faruq,sai dai Zarah ta shiga kitchen ta samo maka wani abin,yanzu na dawo daga aiki".
Yace"Mami kar ki damu bana wani jin yunwa".
Mami bata saurare shi ba ta kalli Zarah tace"ki duba abinda ke nan da ba zai ɗauki lokaci ba ki dafa masa".
Zarah ta amsa da toh ta bar wurin,ba don ta so ba ta buɗe fridge ta fito da carrots da green peas da kayan miya.
Ta kunna gas ta zuba ruwa a tukunya ta rufe ta zuba kayan miyan cikin bowl ta wanke.
Tayi slicing albasa,carrot da green peas,attarugu da tattasai da ɗan albasa tayi blending dinsu a blender,ganin ruwanta ya tafasa ta zuba spaghetti ta koma ta cigaba da abinda take.
Taliyar bata gama nuna ba tayi straining ta ɗora tukunya ta zuba mai,bayan man yayi zafi ta zuba albasa da tomatoe paste ta ɗan soya su na ɗan lokaci sannan ta zuba kayan miyar data markaɗa.
Ta ɗauko seasoning da maggi ta zuba,bayan ya ɗan soyu ta juye carrot da green peas ɗinta ta ɗan zuba ruwa ta rufe.
A wani tukunyar ta zuba ruwa ƙadan ta wanke kwai guda biyu ta sa a ciki,ta koma ta buɗe tukunyar girkinta ta juye spaghetti da kaɗan ya rage ya nuna ta maida tukunyar ta rufe.
Bayan ƙwan ya nuna ta zuba cikin ruwa ta mishi serving abincin a plate ya ɗora kan tray ta ɓare kwan ta ɗora a kan abincin ta ɗauki bottle water guda ɗaya ta haɗa da cup ta fita.
Parlourn babu kowa sai shi kaɗai yana danna waya,ta wuce dining ta ajiye ta koma ta tsaya jikin kujera tace"ga abincin na kai dining".
Ya ɗan ɗago ya kalleta,a hankali yace "thank you".
Ba tace komai ba ta wuce ciki.
Ya miƙe ya karasa dining ɗin ya na kujera yayi bismillah ya fara ci.
Sudais ya shigo parlourn da sallama,hango Sadauki da yayi yasa ya ɗaga mishi hannu yace"ya jiki?"
A nutse yace"Alhamdulilah".
Ya zauna kan kujera ya fito da wayarsa ya hau dannawa,bai wani daɗe da zama ba ta fito sanye da hijab,da ɗan murmushi ta zauna can nesa dashi tace"ina wuni Ya Sudais."
"Lafiya ƙalau autan Mami,shigowata gidan kenan nace bari na fara ganin kyakkyawar fuskarki kafin na shiga ciki".
Da wani irin ƙarfi aka turo ƙofar parlourn,gaban Sudais ya buga jin muryar mahaifiyarsa tun daga waje.
Tana shigowa ta watsa watsa masa wani kallon banza ta kalli Zarah tace"ina Hafsah?"
Dai dai nan Mami ta sauko,da mamaki take kallonta don tun daga sama take jiyo hargaginta.
Mama tace"gara da Allah ya sauko dake, don a gabanki nake son yin komai babu ɓoye ɓoye,babu ɗana babu ƴarki Zarah,ta fita hanyar Sudais idan ba haka ba wallahi gidan nan sai ya mana kaɗan Hafsah".
Cike da ɓacin rai Mami tace"wani irin zance ne haka,yanzu tsakanin su biyu waye yake bin wani ita dashi,zancen Zarah ta fita hanyar Sudais duk bai taso ba don ɗanki za ki jawa kunne".
Mama tace" wannan kuma ke ta shafa bani ba,wallahi ta gaggauta rabuwa da Sudais kafin ranta ya ɓaci".
Sadauki ya ture plate ɗin gaban sa ya nufi kusa da Mami tace"please Mami,ki yi haƙuri ki koma ciki,bai kamata ki dinga stressing kan ki da magana ba".
Mama ta watsa mishi wani kallon banza yace"kai kuma a suwa kare da gudun layya,bar ganin ka zama mutum yanzu kayi ƙoƙarin ɗaga mana kafaɗa,kar dai ka mance matsiyanka da har masu gida na magana kayi ƙoƙarin tsoma baki".
Sadauki ya zuba mata ido yana wasa da agogon hannun shi.
Mama ta gyara tsayuwa tace"ba shakka,ni ka ke kallo da wannan idanuwan na ka?"
Mami tace"koma ka zauna Faruq,ke kuma ki tashi ki bar nan kafin inyi kwallo da ke".
Zarah ta tashi da sauri ta haura sama Mami ta bita da harara.
Mama taja tsaki ta nunawa Sudais hanyar fita tace"daga yau sai yau idan naga ka taka ƙafafuwanka a part ɗinnan ranka zai yi mugun ɓaci".
Yabi bayanta suka fita har lokacin Sadauki bai daina binta da kallo ba,ya juyo ya kalli Mami yace"ki yi haƙuri Mami".
Tayi murmushi tace"ai ba kai ka min laifi ba Faruq,dama ɗan kuka shike jawa uwarsa jifa,da Zarah na jin magana da ba wannan maganar ake ba,koma ka cigaba da cin abincin ka".
Yace"Na gama Mami,zan tafi".
Tace "to shikenan,gashi Daddy bai dawo ba".
Yace"jiya munyi magana".
Mami tace"to shikenan,Allah ya ƙara sauƙi".
Ya amsa da Amin ya fita daga parlourn,a zaune ya tarar da Mallam Iliya,yana ganin shi yace"har an fito?"
Yace"na fito mal Iliya,sai zuwa gobe idan Allah ya kaimu".
Mal Iliya yace"Allah Ubangiji ya nuna mana".

**********
A nutse yake karanta abinda ke rubuce a takardar hannun shi,Bilal ya ɗauki bottle water ya sha ruwa kaɗan ya maida ya ajiye.
"Cikin binciken da nayi na sami labarin Segun ya kamu da rashin lafiya da yammacin ranar,ya kwana a clinic na headquarter har zuwa washegari da rana kafin a sallame shi,Tunde yayi replacing Segun a wannan daren".
Sadauki yayi shiru yana sake nazarin maganganun ɗaya bayan ɗaya,ya kalli Emmanuel yace"Ema,your findings?"
Emmanuel yayi gyaran murya yace"mutane da dama sun shiga communication room a wannan daren,ciki akwai Tunde,tunda shi ya maye gurbin Segun,akwai Captain Yunus,Ola ma tabbas ya shiga,kuma na sami tabbacin Ola kusan sau uku ya shiga kuma dab da za'a tafi ya shiga sannan ya ɗan jima sosai a ciki".
Sadauki ya lumshe ido jin yadda kanshi ke harbawa,ya juya da kyar ya kalli Adebayo.
Adebayo yace "a wannan lokacin kusan duka cctv footage na communication area were absolutely stopped,sai guda ɗaya da maybe ba'a lura dashi bane a nan na sami Video clip na Ola lokacin da ya shiga communication room,sannan tabbas yana cikin waɗanda su kayi handling kayan aikin da za'a fita dasu kafin a tafi,Captain Yunus ya shiga amma bai wani jima sosai a ciki ba,wanda yafi kowa daɗewa shine Ola, sannan record na instruction da aka bayar a wannan daren duk na samu amma babu inda ya kamata ace an baka wannan umurnin".
Sadauki ya dafe kai na ƴan mintina cike da nazari,can ya gyara zama ya buɗe idanuwan shi da suka kaɗa yace"Segun was absent,duk wanda yayi wannan aikin ya san da hakan ko kuma ya shirya hakan,tunda mai son abinka ya fika dabara,duk da ciwo zai iya kama mutum a kowane lokaci amma still that is also a point".
"Ola ya shiga communication room kusan sau uku kuma ya jima sosai a ciki,me ya kai shi tunda ba unit ɗin da yake kenan ba,hasalima shirin fita muke,dole ya shiga cikin suspect gashi baya raye".
Emmanuel yace"na sami information daga bakin wani wanda ke tare daku a wannan lokacin yace tabbas yaga kaman Ola na magana  amma gaskiya bai san abinda yake faɗa ba".
Sadauki ya sauke numfashi yace"yanzu dole muyi bincike a kan mutane biyu,na farko Ola,dole muyi bincike a kanshi don ta koina he is a suspect,na biyu Tunde,shi yayi replacing Segun,wani lokaci aka sanar dashi zai yi replacing Segun,waye ya bashi wannan instruction ɗin,lokacin da Segun ya fara rashin lafiya akwai Tunde a headquarter ko baya nan,akwai wanda yayi communicating dashi ne kafin operation ɗin,sannan ya san ina cikin operation ɗin ko a'a?"
Dole mu samo amsar tambayoyin nan saboda mu san yadda zamu bullowa lamarin".
Adebayo ya fito da Flash ya ajiye kan table ɗin gabansu yace"wannan na ɗauke da video footage na waɗanda suka shiga communication room a daren".
Emmanuel ya dauka ya jona da daya daga cikin computers dake wurin,duk suka zubawa videos ɗin ido cike da nutsuwa.
Yayi pausing videon dai dai inda Captain Yunus ya shigo ya ajiye wani paper ya fita,ya ɗan ɗago ya kalli sauran yace"wannan papern da Captain Yunus ya ajiye na menene,babu kowa a ciki lokacin da ya shiga,dole shima ya shiga lissafi, sannan Ola zai iya zama innocent,maybe ya taka sawun baro ne,maybe kuma tabbas ya na da hannu,so yanzu ta ina kuke ganin zamu ɓullowa nasa lamarin?"
Bilal yace"koma akwai hanya ba zai zo mana da sauki ba tunda ya rasu, sannan duk kayan aikin shi suna headquarter under restrictions kaga babu yadda zamu sami access da kayan".
Emmanuel yace"then we should meet his family,I think that is the only way".
Adebayo ya gyaɗa kai yace"absolutely,hakan shine kawai mafita".
Sadauki yace"zamu fara bincike akan Tunde for now sannan sai mu sami lokaci mu tafi gidan Ola".
Da haka taron ya watse Emmanuel da Adebayo suka musu sallama suka wuce.
Bilal ya kalle shi yace"ka tafi ka kwanta don wannan idanuwan naka firgita ni kawai suke".
Ya watsa mishi harara ya miƙe ya shiga ciki.




***
Oum Rijalain 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol