Free chapter · Read without an account

Page 3

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1

Page 3

MILITARY HEADQUARTERS - BRIGADIER GENERAL'S OFFICE

Brigadier General Ibrahim Abubakar ya cigaba da nazarin takardun gaban sa,ya sauke numfashi a nutse ya ɗago yace"sojoji arba'in da bakwai suka fita operation a wannan daren,shida sun rasa rayukansu,sha ɗaya sun jigata,kuma har yanzu bamu sami clear explanation yadda akayi hakan ta faru ba".
Da sauri Colonel Hafiz ya buɗe file ɗin gaban sa yace"with due respect Sir,
we do have an explanation. Lieutenant Sadauki changed the team's direction."
Colonel Musa ya juya ya kalle shi yace"Based on an order he received through the official communication channel."
Colonel Hafiz yace"which a cikin records ɗinmu babu wani abu mai kama da hakan".
Brigadier General ya gyaɗa kai yace"exactly,abinda ya tara mu a nan kenan,ina ya samo wannan false instruction ɗin?"
Colonel Barau yace"Sir,the fact remains that Sadauki was responsible for his men at that moment. He gave the order to move east."
Colonel Musa ya ɓata fuska yace"saboda yayi tunanin hakan umurni ne daga sama".
Colonel Barau yace"a matsayin sa na soja,kamata yayi ya tabbatar da ingancin umurni kafin ya aiwatar".
Musa yace"taya ka ke tunanin zai tsaya tabbatar da ingancin umurnin da ya fito direct daga communication channel da aka bashi umurnin ya bi?"
Colonel Hafiz yayi saurin cewa"ba defending wani ya kawo mu nan ba, sojoji shida suka rasa rayukansu".
Colonel Musa yace"kuma ba ɗorawa wani laifi ya kawo mu nan ba, saboda sojoji shida sun rasa rayukansu".
Brigadier General ya buga table ɗin gaban sa yace"Enough!"
Duk suka yi shiru kowa na sauke numfashi,ya nuna file ɗin yace"Someone gave Lieutenant Sadauki an order that Command says it never gave."
"Kafin mu yanke hukunci dole muyi bincike,dole ne cikin biyu a sami ɗaya,ko dai Lieutenant Sadauki bai da gaskiya,ko kuma wani ne ya shirya hakan".
Da sauri Colonel Barau yace"ko da wani ne ya shirya komai,still Sadauki shi ya bada last command".
Colonel Musa yace"shi yasa za'a yi bincike idan har ana son kamo bakin zaren".
Brigadier General ya rufe file ɗin yace"a binciko min wanda yayi duty a wannan daren,su waye suka shiga communication room a ranar,and most importantly,wanene yayi magana da Lieutenant Sadauki".

**********

Bilal ya gyara zama yace"a bisa binciken da mu kayi,Tunde bai san da batun replacement ba sai dab da operation ɗin, sannan yana cikin headquarter a dai dai wannan lokacin".
Emmanuel ya cigaba da cewa"Captain Yunus shi yayi replacing Tunde saboda rashin lafiyar Segun all of a sudden".
Adebayo yayi gyaran murya yace"bayan Captain Yunus babu wani da ya sake magana da Tunde a headquarter,kuma tabbas ya san kana cikin masu leading a wannan daren".
Sadauki yayi shiru na ɗan lokaci cike da nazari,yana ɗan buga table ɗin gaban shi yace"Tunde bai san da batun replacement ba sai dab da operation, sannan Captain Yunus ya zaɓe shi saboda rashin lafiyar Segun,tambayar a nan shine,me yasa Captain Yunus yayi replacement instead of higher officers,sannan me yasa aka zaɓi Tunde,wani takarda Captain Yunus ya ajiye a communication room before the operation?"
Adebayo yace"zai iya yiwuwa Captain Yunus yayi replacement ɗin ne saboda babu yadda za'a bar wurin empty a wannan lokacin".
Sadauki ya gyaɗa kai yace"hakan na iya zama dalili,amma me yasa bai sanar da manyan officers ba kafin yayi hakan?"
Bilal yace"maybe yana ganin hakan bai da wani amfani tunda replacement din na ɗan lokaci ne".
Emmanuel yace"amma me yasa ya zaɓi Tunde among hundreds of officers?"
Bilal yace"wataƙila shi yafi kusa a wannan lokacin kuma yafi dacewa da aikin".
Sadauki ya lumshe ido yace"duk hakan na iya yiwuwa,bamu da tabbacin Captain Yunus nada hannu ko babu, from all angles he's a suspect".

**********

Su shida ke zaune a makeken office ɗin, Brigadier General, Colonel Musa, Colonel Hafiz,Colonel Barau, Captain Yunus da Lieutenant Sadauki.
Brigadier General ya maida hankalin shi kan Captain Yunus yace"Captain Yunus,me yasa aka yi replacing Tunde instead of Segun?"
Captain Yunus yace"Sir,Segun ya kamu da rashin lafiya a wannan lokacin,sanin muhimmancin aikin kuma bai kamata a bar wurin haka ba shi yasa nayi assigning Tunde".
Brigadier General yace"akwai officers da yawa a cikin headquarter ranar,me yasa ka zaɓi Tunde?"
Captain Yunus yace"yana kusa a wannan lokacin Sir,sannan ya san kan aikin,na kuma tabbatar zai yi aikin yadda ya dace".
Colonel Musa yace "amma me yasa baka sanar da manyanka ba kafin kayi hakan?"
Yace"Segun ya kamu da rashin lafiya dab da za'a fita,idan nace sai na tsaya sanar da manya za'a iya ɓata lokaci wanda hakan zai iya haifar da matsala,kuma banyi tunanin abu ne da dole sai manya sun sani ba".
Colonel Musa ya sake cewa"lokacin da ka sanar da Tunde batun replacement,ka sanar dashi akwai Lieutenant Sadauki a ciki ne?"
Da sauri yace"eh na sanar dashi Sir,saboda dole ya san Unit ɗin da zai yi aiki dasu".
Brigadier yace"bayan kayi assigning Tunde,kun sake wani magana ne dashi?"
Captain Yunus yace"munyi magana amma akan abinda ya shafi aiki ne Sir".
Colonel Hafiz yace"Captain Yunus,kafin a fara operation,ka shiga communication room?"
Sadauki ya zuba mishi ido.
Ya ɗanyi jim sannan a nutse yace"eh,na shiga".
Colonel Musa yace"saboda me?"
Yace"saboda akwai document da zan ajiye Sir".
Colonel Barau yace"wani irin document?"
"Yana ɗauke da replacement statement ɗinsa da Segun".
Colonel Barau yace"ka nada abinda za ka iya faɗa akan communication da aka yi ranar?"
Yunus yace"an sami matsalar network ranar Sir,so the communication wasn't stable".
Brigadier General yace"Lieutenant Sadauki,yace ya sami order daga communication unit akan canza direction,me za ka ce a kan hakan?"
"Saboda rashin stable network a ranar, za'a iya samun wannan matsalar,ko kuma call yayi diverting,ba za mu iya detecting kiran ko muryar ba saboda rashin network".
Dakin yayi tsit kowa da irin tunanin da yake, Brigadier General ya dubi Sadauki yace"Lieutenant Umar Sadauki".
"Yes,Sir".
"Daga bayanan da muka samu zuwa yanzu,babu wata hujja da za ta tabbatar da ka yi sakaci ko kayi watsi da umurni da gangan,saboda haka,za ka koma bakin aikinka with immediate effect,amma hakan ba yana nuni da cewa mun rufe case ɗin bane,dole muna bukatar sanin abinda ya faru har ka sami wannan umurnin".
Sadauki yace"Thank you Sir"
"Za ka iya tafiya ka cigaba da aikinka kamar yadda ka saba".
Sadauki ya miƙe yayi saluting yace"Yes,Sir".

**********

The Dark Network 

Suna zaune gabaɗaya zagaye da round table,Chief yayi gyaran murya yace"kana ganin a hakan ba za'a sami wani matsala ba?"
Yace"wannan case ɗin ya rufu kenan illa ma sha Allah,ko da sun cigaba da bincike babu wani hujja da zasu samu".
Chief ya gyaɗa kai cike da gamsuwa yace"interesting,shi yasa nake son aikinka sosai,you're very clever".
Bracket yayi murmushi yace"sosai kuwa Chief,sai dai wani hanzari ba gudu ba,idan sauran manyan sunyi shiru da al'amarin kuna ganin wannan yaron zai haƙura kuwa?"
Hunter yace"total nonsense,ƙaryar shi ta sha ƙarya,shi a suwa?"
Chief yayi murmushi yace"mu zuba ido mu ga menene next step ɗin shi,idan ya san wata bai san wata ba,yaushe ya zo duniyar da har zai nuna mana taurin kai?"

**********

Cike da nazari ya ke duba takardun gaban sa,yayi sipping coffee dake riƙe a hannunsa sannan ya maida ya ajiye.
Motsin da ya ji ya sa ya ɗan ɗago kai,bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake.
Adeyemi Idayat ta ƙarasa shigowa bakinta ɗauke da sallama,ba ta 
da tabbacin ya amsa ko bai amsa ba.
Ta ajiye basket dake riƙe a hannunta tace"Good afternoon Umar".
Ya buɗe baki da ƙyar yace"afternoon".
"Please come and eat,tun safe ka ke aiki".
Ya cigaba da flipping takardun yace"thank you,you can leave please".
Idayat tayi shiru tana kallon shi,Ita kam ya za tayi,Allah ne ya ɗora mata soyayyar shi menene laifin ta.
Bilal ya turo ƙofa ya shigo,yana ganinta ya kashe wayar dake kunnen shi ya ƙaraso yana cewa"love birds ne ashe,ko in koma ne?"
Sadauki ya mishi banza tamkar bai san da shigowar shi ba,kallo ɗaya ya yiwa Idayat ya san abokinsa yayi tsiyar.
Ganinta riƙe da basket yasa ya zauna yana shafa ciki yace"kamar kin san wani ɗan banzan yunwa ke damuna anan Adeyemi".
Ta ɗan sassauta fuskarta tace"to bari in zuba maka".
Sai a sannan ya ɗago,ya kalli Bilal yace"aiki nake anan Bilal,ku yi hakuri ku fita dan Allah".
Bilal yace"idan ka ga na fita a office ɗin nan sai wani ikon Allah Falcon,wallahi ba zan fita ba sai na gama cin abinci,kowa fa na da aikin nan amma sai ka bi ka hana kan ka sukuni".
Sadauki bai ce komai ba ya rufe takardar ya ɗauki wallet ɗin shi ya fita.
Bilal ya taɓe baki yace"kai ka jiyo,mutum sai baƙin taurin kai".
Idayat ta ajiye abincin ta zauna kusa da Bilal ta kurawa waje ɗaya ido.
A hankali yace"Idayat".
Ta ɗago a nutse tace"na'am".
Ya sauke numfashi yace"na san ba zai wuce issue ɗinki da Sadauki ba,kin san halin shi tun ba yau ba,bai kamata hakan ya dame ki ba,you're very beautiful Idayat, i assure you watarana zai so ki In Sha Allah".
"Sai yaushe Bilal? I'm not getting younger,ni mace ce,ka san irin pressure da ake bani a gida kuwa,gani ake auren ne bana so, sannan yawancin mutane a can garinmu gani suke rayuwata kawai nake shi yasa bana son yin auren".
Bilal ya girgiza kai yace"idan kin ce za ki damu da abinda mutane ke faɗa a kan ki you're not ready to live in this life,ba za ki taɓa burge su ba,tunda dai mun san babu abinda ki ke hakan ya wadatar,so chill baby girl".
Ya kai ƙarshen maganar tare da kashe mata ido.
Ta watsa mishi harara tare da ɗaukar pillown kusa da ita ta jefa mishi.
Dai dai nan Sadauki ya shigo,kallo ɗaya ya musu ya taɓe baki,ya tattara takardun wuri ɗaya ya adana su cikin drawer ya sake fita.
Bilal ya shafa kai yace"to ni dai ki barni in ci abinci,tunda kin hana ɗan uwana sakewa shi da office ɗinsa".
Da sauri tace"babu ruwana wallahi,ban hana sa ba".

***********

Bayan sallar Isha ya nufi gidan Mami,babu kowa a parlourn sai TV dake aiki,ya ciro waya zai kirata Zarah ta buɗe ƙofa ta shigo.
Suna haɗa ido tace"ina wuni".
Bata tsaya jiran amsarsa ba ta juya zata tafi,ya ɗan bita da kallo yace"ki sanar da Mami ina ƙasa".
A hankali ta amsa da toh ta haura sama.
Yana danna waya Mami ta sauko,ta zauna tana kallon shi tace"ashe ka shigo Faruq,da yake zazzaɓi ke ɗan damuna shi yasa na shige ɗaki,ko asibiti ban leƙa ba yau".
Yace"subhanallah,amma da sauki ko?"
Tace"da sauƙi,na sha magani".
Yace"Allah ya ƙara sauƙi,dama so nake in sanar da ke zan tafi Zaria gobe idan an sauko daga masallaci,zuwa Sunday sai in dawo".
Ta gyaɗa kai tace"ya kamata kam,ka yi kwana biyu rabonka da zuwa gaskiya,idan da hali sai ku tafi da Zarah,kusan kullum sai ta tambayi takwararta".
Ya ɗan shafa kai yace"dama tare da Bilal zamu tafi a motarsa,ta shirya sai mu tafi".
Mami tace"to shikenan,Allah ya kaimu,idan ka isa sai ka sanar da ita bikin Zeenah,Naima, jamila da jidda".
Yace"ashe an sa bikin?"
Tace"ashe ban sanar da kai ba?last week aka kawo kuɗin kowaccen su,idan yaso sai su ƙarasa karatun a ɗakunan su,yanzu daga Firdausi sai Zarah,itama Firdausi saboda babu tsayayye ne da tare za'a haɗa da ita,ita Zarah har yanzu da sauranta bata gama hankali ba,ga rashin son aiki,kwata kwata Zarah bata son aiki,tafi son ta kwanta bacci idan ta tashi taci abinci ta koma ta kwanta tana danna waya,ni kuma ina da ƴaƴa mata ba zan ɗauki mai aiki ba wallahi,wani namiji ne zai ɗauki wannan shirmen".
Yayi murmushin da shi kanshi bai shiryawa hakan ba don sosai Mami ta bashi dariya,wai bata gama hankali ba.
Mami tace"dole kayi dariya Faruq,wallahi na kusa mata shegen duka a gidan nan,ba ranar kana nan uwar Sudais ta shigo ta gama rashin mutuncinta ba?to albishirinka har yanzu bata fita hanyarsa ba wallahi,ko kuma da kaina zan miƙa maka ita ka wuce da ita barrack a lakaɗa mata na jaki lokacin zata fahimci abinda nake nufi".
Har lokacin Sadauki bai daina murmushi ba,ya ɗanyi dariya yace"Allah ya huci zuciyarki Mami,yarinta ce watarana zata daina".
Cike da ɓacin rai tace"wani irin yarinta Faruq,shekararta ashirin shine za'a kirata yarinya?,sai dai iskanci wallahi".
Haka dai ya cigaba da bata hakuri har dai ta haƙura.
Firdausi ta fito daga ɗaki sanye da hijab, Mami tace"Ina zuwa haka?"
"Wurin Hajja zan tafi Mami,na bar iPad ɗina a can"
Mami tace"wuce ki kawo masa abinci sai ki tafi".
Ta juya ta gaida Sadauki don dama bata lura dashi ba ta shige kitchen.
Mami tace"Faruq,kafin ka wuce ka shiga ka gaida Hajja".
"In sha Allahu Mami".
Rice and stew Firdausi ta zubo mishi,sai kunun aya mai sanyi.
Bai wani ci da yawa ba sai kunun ayan da ya shanye duka yayi sallama da ita ya fita.
Direct part ɗin Hajja ya nufa,tana zaune saman darduma ya shiga da sallama.
Ta shafe addu'ar da take ta amsa sallamar,ya zauna kan carpet yace"ina wuni Hajja".
"Ashe ana ganinku,haka za ka shigo gidan nan ka wuce wurin Hafsah tunda ita kaɗai ka sani,mu ba mutane bane ko?"
Yace"ki yi haƙuri Hajja,ban cika shigowa sosai ba saboda yanayin aiki,zan dinga shigowa in sha Allah".
Hajja tace"to yanzu naji zance,ga tuwo nan yanzu na gama tuƙe abina tas saboda na gaji da shinkafar da matan gidan ke dafawa kullum kamar ibada".
Sadauki ya ware ido da sauri ganin ta turo mishi kular gabansa.
Da sauri yace"na ƙoshi Hajja,yanzu na gama cin abinci".
"Wannan ne kuma ba ka isa ba,da Hafsah ta dafa ta baka dole ka ci ko da kuwa ka ƙoshi".
Salati kawai Sadauki ke yi a zuciyarsa,yanzu ya zai yi da wannan tsohuwar ta fahimci abinda yake nufi,duk da AC dake parlourn amma har wani zufa ke gangaro mishi.
Ya ciro handkerchief ya share fuskar shi yace"ki yi haƙuri ba na cin tuwo Hajja".





***
Oum Rijalain 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol