Free chapter · Read without an account
Page 5
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 5
Da safe suka yi shirin makaranta kamar yadda suka saba,a hanya suka dinga haɗuwa da sauran yaran ƙauyen sanye da uniform irin na jikin su.
Har sun gota wani makeken gida mai ɗauke da shuke shuke tamkar ba'a ƙauyen ba Sani ya tsaya da sauri yace"mu shiga mu tsinko mangwaro Sadauki".
Sadauki yace"ka bari idan mun taso anjima".
Ba don ya so ba ya haƙura ya na turo baki.
Har sun iso kusa da makarantar wani yaro Ɗahiru ya jefi Sani da ƙaton dutse,Sani ya fasa ihu ya riƙe ƙeyar shi dake malalar da jini.
Ɗahiru ya tsaya yana huci yace"ai na faɗa maka sai na rama".
Sadauki ya juya a fusace ya nufe shi,Ɗahiru na ganin shi ya ruga da gudu, Sadauki ya jefar da jakar da ke goye a bayan shi ya rufa mishi baya.
Ɗahiru ya zube a ƙasa yana sauke numfashi a wahale,Sadauki na isa inda yake ya hau dukan shi kamar Allah ya aiko shi,sai da ya mishi lilis sannan ya tsaya a kan shi yace"na sha sanar da kai ka fita hanyar Sani amma ka ƙi ko?gobe ma ka kuma".
Ya juya ya nufi inda Sani ke kwance yana ihu sauran ɗalibai kewaye dashi,ya nemo takarda cikin jakar shi ya goge masa jinin da ya wanke masa ƙeya su ka shiga makaranta.
A hanyar su ta dawowa duk da halin da Sanin ke ciki suna isa wannan gidan yace"mu shiga mu samo mangwaro".
Sadauki yace"ka bari gobe,ka ga ba ka da lafiya".
Sani yace"ni dai sai na shiga".
Babu yadda Sadauki ya iya ya bi bayan shi don ba zai iya barin shi shiga wannan gidan shi kaɗai ba.
Sani dake gaba ya nufi makeken gate din gidan,ya na taɓa ƙaramin kofar ya ji ta a buɗe,yayi murmushi ya na kallon Sadauki.
A hankali suka sa kafar su cikin gidan,ko'ina tsit ba ka jin motsin komai sai na tsuntsaye.
Cikin sanɗa suka isa bayan gidan dake dauke da bishiyoyi daban daban,gaban dwarf mango tree su ka isa.
Sani ya dinga tsinka yana sa wa cikin jakar sa,sai da ya zuba kusan guda goma yana shirin tsinko na sha ɗaya su ka ji wani gigitaccen murya yana cewa"who is there?"
Sadauki ya riko hannun Sani ganin zai cigaba da tsinka yace"ka zo mu tafi Sani".
Sani zai fincike hannun shi ya janyo shi suka nufi gate da sauri,wani gabjejen mutum ya fito daga ciki sanye da kakin soja riƙe da bindiga.
Cike da masifa yace"surrender,you little rascals!"
Da gudu su ka bar gidan,ba su tsaya ba sai a ƙarƙashin wani bishiya su ka zuɓe a wurin su na maida numfashi.
Sani yace"na tsani mutumin nan wallahi".
Sadauki ya zauna kusa da ɗan uwan shi yayi dariya yace"ni kuma ya na birge ni sosai,ina son kayan jikin shi".
Sani ya taɓe baki yace"Allah ya kiyaye wannan mugun?"
Sadauki yace"dama zan zama irin shi watarana in dinga sa irin kayan jikin shi,ka ga harda bindiga ya ke dashi".
Sani yace"ni dai mai kuɗi nake son zama,in gina ƙaton gida irin wanda yake ciki,da ƙaton mota".
Sadauki yace"umma tace idan mun yi karatu za mu zama watarana".
Sani ya turo baki yace"ni dai bana son karatu,kawai in zama mai kuɗi ba sai nayi makaranta ba".
Sadauki yace"kai dai ba ka son karatu Sani".
Sani yace"ai karatu akwai wuya shi yasa bana so".
Sadauki yace"zan dinga koya maka,ina so muyi karatu tare mu zama sojoji".
Sani yace"ni dai bana son zama mugu,ai sojoji mugaye ne kaman wancan mugun da ya hana mu tsinko mangwaro".
Sadauki ya mike yace"wa ya ce maka mugaye ne,kawai dai ƙila shine mugu amma ni ba zan zama mugu ba".
Sani ya miƙe ya bi bayan shi su ka wuce gida.
Suna zaune karkashin bishiyar kukan dake tsakar gidan da daddare mahaifin su ya shigo,su ka mishi sannu da zuwa ya amsa ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin Yalwati ya yaye labulen yace"ki same ni a ɗakina yanzu".
Bayan ya wuce Yalwati ta taɓe baki tace"kuma dai,Mallam da feleƙe kala kala,to muji alheri".
Ya karasa ya yaye labulen ɗakin Umma yace"Fatime,ki same ni a ɗakina yanzu".
Umma tace"to Mallam".
A ɗakin ta tarar da Ummah,ta wani taɓe baki ta nemi wuri ta zauna.
Malam yayi gyaran murya yace"kun san dalilin tara ku a nan?"
Umma ta girgiza kai,Yakwati ta wani ɗauke kai ta turo ɗankwali gaban goshi.
Ya cigaba da cewa"Malam Ɗanjuma ya dawo ƙauyen nan ɗazu da rana,kuma yana sa ran komawa nan da sati mai zuwa,don haka wannan karon tare da Sani da Sadauki zai tafi can birni su samu ilimin mahammadiyya kamar yadda na samu,don shi kaɗai ne gatan da zan iya ba su".
Gaban Umma ya yanke ya faɗi,Yalwati ta miƙe tsaye tace"wa?wani Sanin,to wallahi ban yarda ba,ba za'a ɗauki ɗana namiji kwara ɗaya tak a ɗuniya kamar tsoka ɗaya a miya a kai almajiranci ba".
Malam ya ce"to sai ki hana mu gani Yalwati,idan kin isa sunan ki Yalwati ki hana ni aiwatar da ƙudiri na".
A sanyaye Umma tace"dan Allah Malam ka yi hakuri,kwata kwata yaran nan guda nawa su ke da har za'a tura su almajiranci?"
A fusace yace"wai menene kuke kiran almajiranci kamar wani mugun abu,da iyaye na ba su rufe ido sun kai ni ba zan samu wannan ilimin da nake taƙama dashi yau?"
A hankali Ummah tace"ba za ka haɗa lokacin ku da yanzu ba,yanzu komai ya canza, ita kanta rayuwar ta lalace,dan Allah malam kayi hakuri".
Yalwati tace"ki tsaya maƙale murya ke matar ƙwarai,ni da ki ka ganni ba yarda zanyi ba,babu inda Sani zai tafi sai dai ko Sadauki".
Malam ya mike ya ɗauki babbar rigar sa ya nufi ƙofar fita yace"sai kuma ku yi,ni dai na gama magana,nan da wani sati zasu tafi karatu."
Umma ta miƙe da ƙyar ta koma ɗaki,tunda ta shiga take maimaita innalillahi wainna ilahiri raju'un.
Ta na zaune Sadauki ya shigo,kallo ɗaya ya mata ya zauna kusa da ita yace"Umma me ya faru?"
Ta sauke tagumin da tayi ta zuba mishi ido,lokaci ɗaya hawaye ya cika idonta,hankalin Sadauki yayi mugun tashi ya matso ya riƙe hannun ta yace"Umma kuka ki ke?ki yi hakuri kar ki yi kuka".
Umma ta ƙirƙiro murmushi tace"ba kuka nake ba Sadauki,idona ke ciwo".
Ya zuba mata ido ba don ya yarda ba,ta miƙe ta nufi gaban samirunta dake jere tace"ka tafi ka kwanta sai da safe".
Ya miƙe jiki a sanyaye ya bar ɗakin.
Da asuba Malam na shiga ɗaki Umma ta bi bayan shi sanye da hijabi,ya mata kallo ɗaya ya karasa ya zauna kan tsohuwar tabarmar dake ɗakin fuska ɗaure.
Ta zauna kusa dashi tace"ina kwana Mallam".
Yace"an tashi lafiya?".
Umma tace"mun gode Allah".
Daga haka su kayi shiru kowanne da tunanin da yake,Ummah tayi ƙarfin halin cewa "don Allah malam ka soke maganar da ka yi jiya,ban iya bacci ba wallahi har gari ya waye,idan karatu ne ko a garin nan za su yi".
Ya ɗaga mata hannu yace"Fatime ! ki fita idona in rufe,kun fini son yaran nan ne ko me? karatu kamar sun tafi sun gama,ba zan zuba ido yara su tashi babu ilimin mahammadiyya ba".
Umma ta durkusa ta fashe da kuka tace"dan Allah Mallam,dan Allah ka yi hakuri".
A fusace yace"tashi ki bar ɗakin nan Fatime,babu wanda ya isa ya hanani aiwatar da abinda nayi niyya".
Umma ta miƙe ta bar ɗakin ta koma nata ta zauna a bakin katifarta ta hau kuka.
Da daddare ta nemi izinin barin gidan,bayan an shiga masallaci ta ya shirya ta fito.
Sadauki dake tare da Sani ya rugo da gudu yace"Umma ina za ki tafi?"
Umma tace"ba ku shiga masallaci ba?"
Sadauki yace"munyi alwala za mu shiga kenan".
Tace"ka wuce ka yi Sallah yanzu zan dawo".
Ya koma bakin masallaci Umma ta bishi da kallo har ya shiga sannan ta sauke ajiyar zuciya ta tafi.
Da sallama ta shiga gidan su,Inna Mairamu dake zaune saman tabarma bayan ta idar da sallah tace"waalaikumussalam".
Umma tana duƙa kusa da ita tace"Inna ina wuni?"
Inna mairamu tace"Lafiya da wannan daren?"
Umma tace"bari inyi sallah".
Ta cire hijabinta ta rataya kan igiyar tsakar gidan ta ɗauki buta ta karasa bakin kwararo tayi alwala.
Kusa da Inna mairamu ta shimfiɗa darduma tayi sallah,bayan ta idar suka sake gaisawa da Inna.
Yayan ta Buhari ya shigo gidan ɗauke da sallama,ta gaida shi cike da girmamawa.
Ya zauna kusa da Inna yace"ya na ganki a nan,ince ko lafiya?"
Inna mairamu tace"ni kaina jira nake ta idar da sallah in tambaye ta sai ga ka".
Umma sai wasa take da bakin hijabinta,lokaci ɗaya ta fashe da kuka.
Yaya Buhari yace"menene haka Fatime,ko wani abu ne ya faru da Sadaukin?"
Ta girgiza kai da sauri tace"babu abinda ya same shi Yaya, wai birni zai kaisu shi da Sani karatun allo,babu yadda ban yi ba amma ya ƙi hakura yaya".
Lokaci ɗaya Yaya Buhari ya ɗaure fuska yace"yanzu karatun allon kike wa wannan kukan Fatime?shi mahaifinsu bai san abinda ya dace da yaran sa bane,karatu aka ce za'a tura su ba wani abu ba".
Cikin kuka Umma tace"na sani,amma Yaya ko anan su na iya yin karatun,tarbiyyar yaro ko a gaban ka yake sai a hankali ballantana baya kusa da kai,duniyar ta lalace yanzu,dan Allah ka same shi da maganar yayi hakuri".
Yace"a can malamin su zai sa musu ido Fatime,kiyi hakuri kowa da kike gani da haka yayi karatun nan ai ba sabon abu bane,kawai ki dage masa da addu'a Allah ya tsare maki shi a duk inda yake".
Inna mairamu ta gyaɗa kai tace"nima haƙurin zan baki Fatime,ki yi haƙuri ki yiwa mijinki biyayya da yardar Allah za mu ga alheri,shi kuma Sadauki ki bishi da addu'a, addu'ar uwa bata faɗuwa ƙasa banza".
Umma ta jingine bayanta ta lumshe ido,hawayen dake maƙale cikin idonta su ka gangaro,babu wanda ya fahimce ta,an kasa gane me take ji a ranta.
Tun daga ranar Ummah ta rasa duk walwalarta,haka zata dinga binshi da kallo,idan ta shiga ɗaki ta zauna ta ci kuka ta gode Allah.
Ranar da ta sanar da Sadauki zuba mata ido kawai yayi,lokaci ɗaya yanayinsa ya canza.
A hankali yace"Umma inda aka kai su Jamilu?"
Ta gyaɗa kai a sanyaye,ta riƙo hannun shi tace"ka natsu da kyau ka ji abinda zan sanar da kai".
Ya zuba mata idonuwan shi da suka kaɗa lokaci ɗaya.
A hankali tace"a duk inda ka tsinci kanka ka zama mai gaskiya,ka riƙe tarbiyyar da na baka,duk abinda ka san babu kyau kar kayi Sadauki,zan dinga tayaka da addu'a,Allah ubangiji ya tsare min kai a duk inda kake."
Ya sunkuyar da kai yana jin yadda wani abu mai ɗaci ya tokare mishi maƙoshi.
Cikin sanyin murya yace"bana son zuwa Umma."
Tace"nima bana son tafiyar ka Sadauki,babu yadda zanyi ne kawai saboda anfi ƙarfi na".
Tun daga ranar Umma ta fara haɗa mishi ɗan abinda zai tafi dashi,a ɓangaren Inna Yalwati itama ganin duk haukarta da borinta bai canza komai ba ya sa ta saduda.
Ana gobe zasu tafi Inna mairamu ta aiko da nata saƙon,cikin ƙaramin ghana most go Umma ta haɗa mishi kayan sawar shi da kayan abinci irin su garin rogo,ƙuli,yaji,gishiri,barkono,cokali da kwanon cin abinci,ta ɗauko tsohon zanin gadonta ta haɗa mishi cikin kayan.
Mallam ya shigo da sababbin alluna guda biyu da butar alwala sai garin rogo mai ɗan yawa ya miƙawa kowacce na ɗanta.
Ya shiga rumbu ya fito da babban buhun masara,gero da wake ya ajiye a tsakar gidan.
Inna Yalwati tace"wannan fa?"
Ya karasa ya ɗauki buta ya wanke hannun shi ya koma kan tabarmar dake shimfiɗe a tsakar gidan yace"kayan da zasu kaiwa malamin su ne".
Ta taɓe baki ta ɗauke kai,Umma ta miƙe ta koma ɗaki inda Sadauki ke cigaba da gyara kayan.
Ta karasa wurin jerin kayanta ta sauke akwatunan ɗaya bayan ɗaya ta buɗe na karshen ta fito da wani baƙin leda ta koma ta zauna.
Sadauki dai sai binta da kallo kawai yake.
A hankali ta fitar da kuɗin dake cikin ledan ta ƙirga kusan dubu biyar ta ajiye a gefe ta ƙulle ledar ta miƙe ta maida cikin akwatin ta dawo ta zauna.
Ta ɗago ta kalle shi ganin yadda yake binta da kallo,ta mishi alamar ya zo.
Sadauki ya miƙe a sanyaye ya ƙarasa inda take ya zauna.
Ta daure kuɗin cikin baƙin leda tace"zan sa maka wannan cikin kaya ka lallaɓa dashi babu yawa,kayan abincin da na sa maka zasu ishe ka kwana biyu kafin wani lokaci,zan rubuta lambar Yaya Buhari a takarda duk abinda ka ke buƙata sai ka kira ko da wayar malamin ne idan ya na dashi ka sanar,banda ɗaukan abinda ba na ka ba,daka ci abinda babu wanda ya ba ka gara ka kwana da yunwa Sadauki,duk rintsi ka zama mai gaskiya,Allah ubangiji ya tsare ka ya maka albarka a duk inda ka shiga".
Ya sauke kai ya amsa a hankali.
Cikin sanyin murya yace"Umma na gama karatun boko?
Tace"kayi hakuri Sadauki Allah yana tare da kai".
Oum Rijalain
***