Free chapter · Read without an account

Chapter 38

by Sayyada barrister · BIYU A ƊAYA

BIYU A ƊAYA 
    ( Don't judge a book by its cover)



Page 38
Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
The five ink legends



Shirye-shiryen kammala training yasa Dr Waahab a gaba, hakan ya sa ba shi da lokacin kansa, bai zauna ba balantana ya ƙarashe shirya luggage nasa, tun safe suke fita sai dare suke dawowa, baya samun lokacin da zai je Tumbin Giwa wajen Angel. Sai dai ya kirata a waya, wani lokacin ma wayarta a kashe, taxt yake tura mata, daga baya ta yi reply.

Yana barin wajen aiki a daddafe ya iso Tumbin Giwa ya kira ta a waya, ya yi ko sa'a kiran ya shiga, ta ɗauka ya sanar da ita ya iso yana zaune a dakalin da suke hira, da ƙyar Mamanta ta kyaleta ta fito, ta tadda shi yana zaune, ta ƙaraso tare da cewa 

"Sannu da zuwa Yallaɓai likita"

Ya ɗan yi murmushi ya ce

"Yau ba a kira ni da Uncle ba?"

Murmushi ta yi ba ta yi magana ba, ganin haka yasa ya ce

"Have a seat"

Ta zauna tare da cewa 

"Marci"

Ma'ana, thank you, na gode kenan, sannan ta sake cewa

"Bonsoir"

Good evening, ina wuni, ya ɗan sauke ajiyar zuciya, yana jin tsananin farin cikin ganinta, ya amsa da

"Evening mon ange"

Ya faɗa yana kallon fararen idanunta da hasken wutan lantarkin dake bakin ƙofar shop ɗin ya haske mata fuska, jin abin da ya faɗa yasa ta sudda kai ƙasa cike da jin kunya, amma kalmar ta yi mata daɗi

Cewa ya yi, evening my Angel, ta zama Angel tasa kenan, ta ce

"Kwana biyu aiki ya ɓoye ka"

Ya zauna sosai suna fuskantar juna, a hankali ya ce

"Kin yi kewata ne?"

"Uncle"

Ta faɗa a hankali cike da jin kunya, tana murmushi, ya ɗan ɓata fuskar ya ce

"Shikenan zan koma hotel"

"Don mesa?"

"To na yi tunanin kin yi kewata shi yasa nazo"

Ta fahimci yau da rigima Uncle yake a hankali ta ce

"Eh"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Na san an yi kewata, kawai jan aji ake yi min"

Murmushi ta yi, ya ce

"Same here mon ange"

Ni ma haka my Angel, ya faɗa, ita dai kunyarsa take ji, ya sake cewa

"Did you feel that way?"

Ta gyaɗa masa kanta alamun eh, tare da sudda kanta, ya ce

"You always nodded or shook your head when i ask you"

Yana mata magana akan a kullum idan ya tambaye ta bata ba shi amsa da bakinta sai dai ta gyaɗa kanta ko ta girgiza kanta alamun eh ko a'a ba magana, ya matso kusa da ita, ya sake cewa 

"Parle moi, mon ange"

Talk to me my angel, a hankali ta ɗago, ita kanta wani lokacin magana bata wahala take in tana gaban Uncle, bata san dalili ba, ita da take yi wa Mamanta hira har wani lokacin ta cikata da surutu ta korata amma ga shi ta kasa yi a gaban Uncle sai da ya sake cewa 

"Shi kenan mon ange ni ma na yi shiru"

A hankali ta furta 

"I fee that way too"

Ya sauke ajiyar zuciya, cikin farin ciki yake dubanta ita ma ta yi kewarsa, ya ce

"Zan samu time mu zauna mu yi hira kamin na tafi, kin ji"

"To"

"Amma fah za ki yi mini hira sosai"

"Eh"

"Yawwa don ba zayyu na yi ta yi miki hira ba ki yi shiru ki kyale ni"

"To Uncle"

"Babu matsala ko?"

"Eh babu, Mama tana godiya akan kuɗaɗen da ka biya"

"Nupe ba komai ai, da fatan ALAJA bata takura miki"

"Eh bata yi"

"Good, yau a gajiye nake zan wuce masauki na huta"

"Sannu"

Ya mik'e tare da cewa 

"Yawwa sannu, ta shi na yi miki rakiya"

Har ƙaramin ƙofar shiga Tumbin Giwa ta side nasu ya yi mata rakiya, tana shirin shiga ciki ya ce

"Mon Ange"

Ta tsaya, ya sake cewa 

"Prends soin de toi mon ange"

Take care my Angel, ta ce

"Marci"

Thank you, ya matso kusa da ita ya ce

"Me za ki faɗa min kamin na tafi"

Ta sudda kai ya yi saurin cewa 

"A'a mon ange bana son haka, magana za ki yi min"

A hankali ta ce

"You are truly a good person"

"Thanks, ma petite beauté"

Na gode cutie, ya faɗa yana murmushi ta sake cewa

"Bonne nuit"

Goodnight, ya yi murmushi tare da cewa 

"You too, bye"

Yana gani ta shige ciki, ya sauke numfashi yana ƙoƙarin juyowa don tafiya Abraham ya tare masa hanya, Dr Waahab bai ko kalle shi ba, yana ƙoƙari raɓarsa ya wuce amma da yake Abraham ɗan duniya ne ya sake tokare inda yake son bi, sauke numfashi ya yi ya ɗan dube shi tare da cewa 

"What that means?"

Abraham ya fuzdar da iska ya ce

"Ai kafi kowa sanin abin da hakan yake nufi"

"Bani da lokacin wannan shirmen"

"Au haka ma ka ce, to shikenan bari na nuna maka irin nawa ɗanyen kan"

Girgiza kai Dr Waahab ya yi yana ƙoƙarin barin wajen amma Abraham ya riƙo shi ya zai janyo shi baya ya kasa, don kansa ya cika shi ya kalle shi kamar yadda shi ma kallon nasa yake, kamar zai ce komai kawai ya fice daga cikin Tumbin Giwa, yasan rigima yake nema da shi, kuma bayi da lokacin ta...


******************************

Bayan kwanaki biyu 

Bilqees zaune riƙe da wayarta a hannu tana game, tun da ta daina fita restaurant bata da abokiyar hira kamar wayar, wani lokacin su yi texting juna da Uncle wani lokacin su yi waya, ta fara sabawa da shi, ta fahimci shi mutum ne me son in yana hira a kula shi, kuma baya son ɓoye²...

Maman Bilqees ganin fah alaƙa sai sake kulle wa take yi sakanin su yasa hankalin ta ya sake tashi, bata son likita ya aure ƴarta, da farko taso ta sanya ƙarfi ta yanke alaƙar amma ganin yawan tambaya da Bilqees ke yi mata yasa take yin shiru...

"Mama"

Sauke numfashi Maman Bilqees ta yi jin ƴarta na kiran sunanta, ta amsa 

"Na'am Bilqees, menene?"

"Mama kwanan nan duk kin sauya, me yake damun ki ne?"

"Ba komai"

Ta bata amsa, tsoron ta kada ta sake ƙwakulo wata tambayar, Bilqees ta ajiye wayar hannunta ta sake cewa

"Ko dai jikin ki ne mu sake komawa asibiti"

"A'a na ce miki babu komai"

"Mama Yallaɓai likita kusan sau biyu yake so ku gaisa amma ba ki bari ba, ga shi saura mishi kwanaki ya koma ƙasarsu"

"Bilqees kina damuna da yawan tambayoyi, na ce miki ba sai mun gaisa ba"

"To shi kenan Mama"

Daga haka bata sake cewa komai ba, ta ɗauki wayarta ta ci gaba da game....

*******

Dr Waahab ya ɗan sami nutsuwar kwana biyu bai fita ba, yana shirya kayansa, wuni ya yi a hotel yana gyara side nasa, tun da Angel ta daina yi masa gyara komai ya daina yi masa kyau, kawai lallaɓawa yake yi. 

Sai bayan sallar ishai sannan ya samu nutsuwa, yaji yana son sanya Angel cikin idanunsa, ya shirya cikin ƙananan kaya yayi kyau sosai sai ƙamshi da yake tashi a jikinsa kamar kullum. Bai kira wayarta ba sai da ya iso Tumbin Giwa ya zauna a dakalin da suke zama don yin zance, ya kira layinta ya shiga kira na biyu ta ɗauka ya sanar da ita ya iso, ta ce tana zuwa amma sai da ta lallaɓa Mamanta da ƙyar ta barta ta fito, ta tadda shi zaune, ta yi sallama ya amsa ta zauna tare da gaishe shi, ya amsa ya ce

"Mon Ange"

"Yallaɓai likita"

"A'a a sauya min suna"

"Uncle"

"A'a, special name nake so"

Murmushi kawai ta yi, don bata san sunan da za ta ba shi ba, tana ji ya sauke numfashi tare da cewa 

"Yaushe za mu fita tare"

Bata fahimce shi ba, tana kallon shi ya sake cewa 

"Yaushe za ki yi min rakiya na yi siyayya?"

"Sai ka faɗa ranan, ni kuma na tambayi Mamata"

"Hakan gaskiya ne, jibi Sunday ya yi?"

Ta gyaɗa kanta alamun eh, ya ce

"To sai ki tambaye ta, amma tafiyar mu zai kasance Tuesday ko Wednesday"

Jikinta ya yi sanyi shikenan Yallaɓai likita zai tafi ya yi nesa da ita, ta ce

"Har lokacin ya zo"

"Eh kamar yau muka zo, kin ga kuma har lokacin komawa yayi"

"Haka ne Uncle komai in dai da lokaci ne me wucewa ne"

"Ki nema min special name zuwa jibi sai ki faɗa min"

Ta yi murmushi ta ce

"To Uncle"

"Da gaske nake"

"Zan yi ƙoƙari"

Suna hira har lokaci ya ja, sannan ya yi mata sai da safe ya dawo hotel, sai da ya sake watsa ruwa sannan ya yi shirin kwanciya, tunanin Angel fal cikin ransa, baya so ya yi nesa da ita amma ya zama dole sai ya yi hakan...

****************

Kasancewar ranar Sunday ne, kuma a ranar su ka yi zasu haɗu da Uncle da ƙyar Mamanta ta barta ta fito, ta hau mashin ya kawo ta address ɗin da ya tura mata.
Ta iso inda ya ce ta same shi, a wani babban wajen hutawa dage kan hanyar babban titi, tun da take bata taɓa zuwa wajen ba, tana jin dai ana zuwa outing wajen, yara da manya, bata cika yawo ba daga school sai gida ko restaurant, wasu guraren ma ALAJA ke kaita a lokacin da babu aiki amma tun da ta saka dokar aiki a restaurant kullum yasa bata zuwa ko'ina.

Ta yi kyau sosai cikin riga iya gwiwa da wando ta yi rolling da madaidaicin mayafi, sai waige² take yi tana duba Uncle ganin wajen da mutane suna zaune wasu na ciye² wasu na hira amma babu hayaniya sai kalle² take yi ta ji ya ce

"Mon Ange"

Ta juyo da sauri suka haɗa ido ta sauke numfashi, duk ta shiga damuwar rashin ganinsa a wajen, ya ƙaraso kusa da ita ya ce

"Mu je ko?"

Ya faɗa a hankali suka jera suna tahowa zuwa inda aka shirya musu wajen zama, yadda aka ƙayata wajen ya yi matukar burge ta, ya nuna mata wajen zama ta zauna kan kujerar taya, sai yau ma ta taɓa gani, ta lotse da ita kaɗan ta yi ƙauyanci, shi ma ya zauna yana duban ta yaga yau har tafi kullum kyau, a hankali ta ɗago suka haɗa ido, ya sauke numfashi ganin kamar taki sakin jiki yasa ya yi mata magana 

"Yau dai an yi alkawarin yi min hira don haka ki ma saki jikin ki"

Murmushi kawai tayi, ta ɗan gyara zamanta, ya jera mata kayan makulashe a gabanta ya miƙa mata ice cream ta karɓa amma bata iya sha ba, taga shi shan chocolate yake yi hankali kwance, kaɗan ta sha ta ajiye bai takure ta ba, ya miƙa mata chocolate ta karɓa ta riƙe a hannunta, an kira shi a waya, a gaban ta ya amsa OG ne ya ce suna da meeting a hotel da daddare, bayan sun gama magana ya ajiye wayar. 

Ya dawo ya zauna kusa da ita ƙananan kaya ne a jikinsa, sun yi masa kyau musamman riga orange color ta sake haska farar skin nasa mamaki take yi irin bakin gashi dake hannun Uncle ta sudda kanta ƙasa don kada ya gane tana kare masa kallo, murmushi ya yi, aransa ya ce Angel sarkin kunya, ya kalli fuskarta ya ce

"Faɗa min sunan da kika zaɓa min"

Tayi tsilli² da idanu, ya sake cewa

"Mon Ange give me a name please"

"Uncle umm..

Ya riƙe hannunta ya zaunar da ita kusa da shi, ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, ya juyo da fuskarta gare shi yana dubanta a hankali ya yi magana 

"Mon Ange kina so ki hanani bacci ko?"

Ta girgiza kanta alamun a'a, ya sauke numfashi ya kalli siririn wrist watch dake ɗauke a madaidaicin hannunta, ya ce

"Shikenan mu yi zaman kurame"

Ta ɗan yi dariya dimple nata ya lotsa, ya kurawa ramin idanu, abin yana yi masa kyau, ya ce

"Eh mana tun da ba za ki yi mini hira ba"

"Zan yi"

"Yawwa ko kefa, to ki fara da bani suna"

"To"

"Na rufe idanuna bani suna, ina jinki"

"Mon amour"

My love, ta faɗa, ya yi saurin buɗe idanun sa ya zuba mata su, ta rufe fuskar ta da tafin hannun tana murmushi zuciyar ta na bugawa, jikinta har rawa yake bata saba da irin wannan yanayin ba, ita yaushe ma ta iya wani soyayya, tana ji ya sauke ajiyar zuciya, cikin farin ciki ya ce

"Ki maimaita Please"

"Mon amour"

"Uhm ni ce Finally I'm your love"

Ta kasa ɗagowa, ya ce 

"Thanks mon ange da sunan za ki dinga kirana"

"To"

A hankali yake janta da hira, yana bata labaran nishaɗi tun bata sakin jiki har ta fara, tun bata dariya har ta fara yana kallon dimple nata, baya so ta daina dariya yasa bai yi magana akansa ba...

Sun tashi sun zagaye wajen suna hira yana nuna mata abubuwa, sun jima suna tattaki sannan suka dawo wajen zamansu, ya buɗe chocolate ya miƙa mata a ɗan ƙaramin roba, ta karɓa a hankali take sha ba sosai ba, don kada ya yi fushi ne, sosai ya zauna suna facing juna ya ce

"Za ki iya rayuwa dani a kowane irin hali muka sinci kan mu?"

Ta dube shi, kuma sai ta yi shiru, ya riƙe hannunta ya ce

"Ni ɗan babban family ne, ina da ƙanne da ƴan'uwa masu tarin yawa, kuma ko mun yi aure a cikinsu za mu zauna, kin amince duk yanayin da muka tsinci kanmu za mu rayu tare"

A hankali ta sauke numfashi ta ce

"Za ka iya aure na, duk da kasan yanayin gidan mu?"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Eh Angel, na amince zan yi rayuwa dake a duk halin da kika sinci kan ki, ko ta fannin ahali ko wani nakasu na rayuwa"

A hankali hawaye ya gangaro mata, Uncle yana sonta sakani da Allah, tana ji ita ma za ta iya zama da shi a duk yanayin da yake ciki, a hankali ta ce 

"Eh Uncle"

"A'a bana son uncle, da sabon sunan da kika saka min da shi za ki kira ni"

"Mon amour"

"Yawwa ko kefa"

"Kana da ƙanne?"

"Eh ina dasu da yawa amma ƙanwata ɗaya ita ce Hauwa"

"Ka ce Maman ka sunan mu ɗaya?"

"Eh sunanta Bilkisu amma muna kiranta da Mamie, kuma na tabbata in ta ganki za ta so ki sosai"

Ta yi murmushin farin ciki, haka take son ji, bata so ta faɗa a hannun ahalin da basa sonta...

Sun ɗan taɓa hira sannan ta yi masa rakiya ya yi shopping ya yi mata siyayya taƙi karɓa sai da ya yi fushi sannan ta ansa ta ce ai hidimar ta yi yawa, suka fito ya sanya ta a mashin ta koma gida, shi ma ya dawo hotel. Da daddare suka gudanar da meeting nasu akan komawa Nigeria jibi kuma babu fashi...

**********************

WASHE GARI 

Dr Waahab yana zauna a palour ya gama shirya kayan sa, saura tafiya kawai ya rage masa, don ya gama komai, washegari ne tafiyarsu, ya koma ya kwanta akan 2 seater ya lumshe idanunsa, yana farin cikin zai koma gida in ya tuna rabin ransa da zai barta ya tafi sai ya ji wani iri, kiran waya ya shigo ganin Ashfat ce yasa ya ɗauka cike da farin ciki ta ce

"Ya Waahab barka da warhaka"

"Sannu Ashfat ya aiki?"

"Alhamdulillah Yayana"

"To ya yi kyau"

"Yaya gobe za ka taho?"

"Eh in sha Allahu"

"To Allah ya dawo da kai lafiya"

"Amin ya rabbi'

Ta katse wayar, yabi wayar da kallo, ya lumshe idanunsa na wani lokaci sannan ya buɗe ya dannawa Angel kira, sau uku yake kira bata ɗaukawa duk ya shiga damuwa, wuni ya yi jikinsa babu kwari, me yasa Angel bata kira shi ba yasan kuma taga miss call nasa, ya tura mata text akan gobe zai bar Ghana....

Shiru babu reply har ya fito suna ɗan wasu abubuwan da sauran ƴan'uwansa, sai dare ya zauna, ya watsa ruwa ya sanya brown jallabiya, duk jikinsa ya yi sanyi, daga yaji saƙo sai ya duba ko Angel ce, yaso zuwa Tumbin Giwa sai dai ganin bata ɗauki waya ba yake ganin ko yaje ba zai ganta ba...

Nocking aka yi ya basa izinin shigowa, yana daga kwance kan 2 seater, a tunanin Dr Faisal ne kawai sai yaga Angel a tsaye bakin kofar palour tayi masa sallama yana daga kwance ya amsa a hankali ta zauna daga bakin kofa ta ce

"Uncle barka da dare"

A hankali ya taso ya iso ya zauna a gabanta ya kura mata idanu cike da farin ciki, sai ya ji sanyin cikin ransa, ya yi mata magana cikin damuwa 

"Mon Ange na kira ki ba ki ɗauka ba, na yi miki Text message ba raply, are you alright"

A hankali ta danne damuwarta, bata so ya fahimci komai ta ce

"Na tashi da ciwon kai wayar tana cikin jakata na sanya ta a silent"

"Na shiga damuwa da na ji ki shiru, amma na yi farin ciki dana ganki"

Da ya san yadda aka yi ta fito da ya tausaya mata, a hankali ta ce

"Gobe za ka tafi?"

"Eh in sha Allahu jirgin safe za mu hau"

"Allah ya kai ku lafiya"

"Amin mon ange, ki kula min da kanki, kin ji"

Tausayi ya bata, amma ta dake ta ce

"In sha Allahu"

"Mon Ange"

Ya faɗa a hankali, ya riƙe hannunta ya furta

"Je t'aime"

I love you, ya faɗa ta runtse idanunta, tana jin kalmar tana yi mata yawo cikin jinin jikinta, ya sake cewa

"Je t'aime fort"

I love you deeply"

Ta sauke numfashi hawaye suka gangaro mata, bata san ta faɗa a soyayya ba sai yau da safe, a hankali ta ce

"Uncle"

"A'a ki kirani da sunan da kika saka min"

"Mon amour"

My love, ta faɗa, ya ɗan sauke ajiyar zuciya, ya ce

"I'm going to miss you, tu me manques déjà"

I missed you already, ta runtse idanunta tana danne kukan, ya ɗago da haɓarta suka kurawa juna idanu, a hankali ya ce

"Say it mon ange, ki furta min kina so na"

"I love you mon amour"

Kaman ya rungume ta yake ji amma ya kama kansa, wannan kalmar ta fiye masa komai, ya ji zuciyarsa ta yi masa wasai, ya mik'e ya ɗauko wani ɗan ƙaramin kwantaina ya dawo ya zauna kusa da ita ya fiddo da zobe ya sanya mata a yatsanta ya ce

"Ke tawa ce, ki adana min kan ki, da zuciyarki, kada ki bari kowa ya kusanto ki, zan dawo, zan dawo, in sha Allahu zan dawo mon ange"

Ya runtse idanunsa kamar yayi ƙwalla, ya ji saukar siririyar muryarta 

"Je t'attendrai"

I will wait for you, ta faɗa ta runtse idanunta, ya sakar mata da murmushi bayan ya buɗe idanunsa, ta mik'e da sauri ta ce

"Na tafi"

Ya rakata har bakin titi ta hau mashin ta dawo gida dare ya yi...

Dr Waahab ya dawo hotel ya kwana cikin farin ciki suka hau jirgin safe zuwa Abuja Nigeria......









Comment and share fisabilillah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol