Free chapter · Read without an account

Page 9

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1 

Page 9

Garba ya ƙyaƙyale da dariya yace "ka ji rashin rabo,to kuwa a haka za ka cigaba da rayuwa a wahale ka mutu a wahale".
Fuska ɗaure Sadauki yace"ai ba kai bane Allah".
Bala ya ture shi a fusace yace"da ubanwa kake?"
Yace"da dukan ku,bana tsoron kowa sai Allahn da ya halicce ni,kuma da yake cewa zan mutu a wahale sai dai shi ya mutu a wahale ba dai ni ba".
Yana gama magana ya watsa musu wani banzan kallo ya bar wurin.
Sake da baki duk su ka bishi da kallo,Garba ya cije baki yace"ubanwa ya tsayawa yaron nan?"
A fusace Bala yace"babu uban da ya tsaya masa tsabar iskanci ne da tashen balaga kuma zan nuna mishi na fishi hauka wallahi,tun kafin ya san zai fito almajiranci nake garin Kano".
Tun daga ranar babu abinda ya ƙara shiga tsakaninsu,idan ya tashi da safe su fita bara tare da Lawali da Sani,duk abinda suka samu haka zasu raba,idan kuma babu yawa zai hakura ya bar musu.
Cikin watanni shida Sani da Sadauki suka fita hayyacinsu kamar kazar mayu,gabaɗaya sun rame sun lalace sun zama ɗaya da sauran almajiran da ke gidan,ƙuraje ne gabaɗaya jikin su har kai.
Duk tsaftar Sadauki wani abin gagarar shi take,ko sabulun wanka babu balle na wanki.
Bayan sun tashi karatun yamma Mallam ya miƙawa lawali wani baƙin leda yace ya shiga ya kai cikin gida.
A hanya yaci tuntuɓe da wani ƙaton dutse dake gaban shi suka faɗi tare da ledan,mangyaɗan dake ciki ya zube a ƙasa.
Hankali tashe ya fashe da kuka ya rarrafa ya tashi da kyar don ya san yau ya shiga uku.
Sadauki dake riƙe da allon shi ya karaso da sauri ganin yana kuka yace"lafiya Lawali?"
Ya sake fashewa da kuka yace"wallahi Mallam kashe ni zai yi,na shiga uku?"
Sadauki ya bi wurin da kallo,ganin man dake kwance a ƙasa yasa shi fahimtar abinda ke faruwa,kafin ya bashi amsa a kayi gyaran murya daga bayansu.
Lokaci ɗaya kirjinsu ya buga Lawali yayi wani irin tsalle ya koma bayan Sadauki ya ɓuya.
Mallam ya karaso yana gyara babbar rigarsa yace"lafiya ku ka wani tsaya cirko cirko kamar...."
Sauran maganar maƙalewa yayi bayan idon shi ya sauka a kan man dake malale a ƙasa.
Tun kafin yace komai sadauki ya sunkuyar da kai yace"Mallam kayi hakuri,ban sani bane na buge sa ledar ta faɗi a ƙasa".
Mallam ya gyaɗa kai yana ƙara gyara babbar rigarsa yace"to..to..to ..madalllah,sannu da aiki,Bala!"
Ya juya yana kallon Bala dake biye dashi.
Bala ya sunkuyar da kai yace"Na'am Mallam".
"Ku tafi dashi ayi mishi bulala goma tunda shi makaho ne baya gani".
Da sauri Bala yace"yanzu kuwa Mallam".
Ya karaso ya riƙe hannun Sadauki ya ja shi kamar ya riƙe wani ɓarawo Lawali dake maƙale a bayan shi ya fashe da kuka,me yasa ya ɓoye,me yasa yayi shiru alhalin yasan Sadauki bai da laifi.
A can wani lungu Bala da sauran mukarraban shi suka ajiye Sadauki,Bala ya ja kujera ya zauna ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon Sadauki.
Garba ya sa hannu a aljihu ya ciro taba da lighter ya kunna dai dai saitin fuskar Sadauki,sai da ya mata kyakyawar zuƙa sannan ya watsa mishi a fuska.
Sadauki ya watsa mishi wani kallo ya ɗauke kai,Bala ya gyara zama yace"har yanzu kana da sauran dama,idan kana son fita daga wannan ƙangin talaucin da yunwa ba abu bane mai wahala,ka amince ko a'a".
Cikin ido Sadauki ya kalle shi yace"ka daina ɓatawa kanka lokaci,ko yanzu ko anjima ba zan amince ba".
Bala ya gyaɗa kai ya karɓi kara ɗaya a hannun Garba ya kunna idon nan jajir yace"shikenan zamu gani,na san ba kai kayi wannan laifin ba,amma ka je ba zan dake ka ba saboda na san komai daren daɗewa idan yunwa ta ciyo ka zaka dawo ka same ni".
Da sauri Sadauki yace"babu wannan ranar".
Garba ya ƙyaƙyale da dariya yace"ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare Sadauki,za ka iya tafiya".
Ya mike ya kaƙƙabe rigar jikinsa ya bar wurin,Bala da Garba suka raka shi da kallo.
Garba ya sauke wani ajiyar zuciya yace"yaron nan akwai taurin kai".
Bala yace"shi yasa nake son ya amince,irin su idan zasu yi abu da dukkan zuciyar su suke".
Su Sadauki na da watanni takwas aka fara shirin tafiya gida,Mallam yasa kowanne yaje yayi aski kafin a zo ɗaukar su,su Lawali suka fara tafiya don motar su ta iso da wuri su ƴan Sokoto saboda nisa.
Sai washegari motar su Sani ta iso,wani irin farin ciki mara misaltuwa ta lulluɓe Sadauki.
Yana sa kafar shi cikin motan ya sauke wani ajiyar zuciya,addu'a yake Allah yasa ya tafi kenan don ko mai Baba zai mishi ba zai dawo ba sai dai ya kashe shi.
Tunda suka fara tafiya yake kallon waje har sauran su kayi bacci kamar waccan karan sai shi da Mallam Ɗanjuma da driver.
Ƙarfe biyar suka isa ƙofar gidan Mallam Ɗanjuma,cike da zumuɗi yaran ke fitowa,Sadauki ya fito hannun shi riƙe da Sani yana wani irin murmushi cike da farin ciki.
Ɗauke da sallama suka shiga gida, Umma dake durƙushe gaban murhu tayi saurin ɗagowa tana binsu da kallo.
Ya sake hannun Sani ya ruga da gudu ya rungumeta, Umma ta ƙanƙame shi da sauri hawaye na bin fuskarta.
Inna Yalwati ta fito daga ɗaki riƙe da zani lami biye da ita jin muryar Sani yana kwala mata kira.
Ta rapka salati ta fashe da kuka tace"Sani kai ne haka?na shiga uku na lalace".
Umma ta ajiye maficin hannunta ta riƙo hannun Sadauki suka shige ɗaki,a bakin gado ta zaunar dashi ta ɗauki kofi ta ciko ruwa a randa ta miƙa mishi,kallo ɗaya zaka mata ka hango farin cikin dake kwance kan fuskarta.
Ta juya ta fita ta haɗa wani murhun tasa ruwan wanka ta dawo ɗakin ta ɗauki hijabi.
Sadauki yace"Umma ina za ki je?"
Ba tare da ta juyo ba tace"ina zuwa".
A bakin kofa ta tarar da yaran dake wasa,ta kira wani daga cikin su ta miƙa mishi kuɗi ta faɗa mishi abinda take so ta dawo gida.
Bokitin ta dauko ta juye ruwan ta kai mishi banɗaki ta yaye labulen ɗakin tace"fito kayi wanka".
Ya mike yana kallonta yace"to Umma".
Ta sake labulen ta koma bakin murhu ta hau haɗa sanwa,nan da nan yaron ya dawo riƙe da baƙin leda ya miƙa mata tare da canjin Naira ashirin,ta karbi ledar kawai tace"tafi da canjin Iro,nagode sosai".
Yayi godiya cike da farin ciki ya juya ya fita.
Bayan minti talatin Umma ta sauke tukunyar taliyarta ƴar hausa da ya sha kifi ta juye a plate ta wuce ta kai tsakiyar ɗaki ta ajiye,ta ɗauki kofi ta ɗebo ruwa ta ajiye ta koma waje.
Sauran dake cikin tukunyar ta juye a plate ta ƙarasa bakin kofar Inna Yalwati.
A nutse tayi sallama ta kira sunan Sani,Inna Yalwati ta yamutsa fuska tace"lafiya dai ko?"
Umma tayi murmushi tace"lafiya ƙalau yaya,wurin ɗana na zo,ya fito ya karɓi abinci".
Lami ta miƙe da sauri ta fita tun kafin Inna tace wani abu tasa hannu ta karɓa Umma ta juya ta koma ɗaki.
Inna Yalwati ta watsa mata harara tace"shegiya uwar kwaɗayi,na aike ki ne?"
Ta turo baki ta dire plate ɗin a gabanta tace"to naga dai abinci ta kawo ba wani abu ba".
Inna Yalwati ta ja tsaki tace"munafurcin banza munafurcin wofi,ko ina ruwan ta da Sani wai ɗana,ko da yaushe ya zama ɗanta oho".
A ɗaki ta tarar da Sadauki yana jiranta,ta zauna kan tabarma tana kallon shi tace"ba ka ci abincin ba?"
A hankali yace"zan ci Umma,ina Baba?"
Tace"ya na gona bai dawo ba".
Bai ƙara cewa komai ba yayi bismillah ya fara cin abincin, Umma sai kallon shi kawai take ganin yadda ya rame yayi baƙi kamar ba Sadaukin ta ba.
Ya ɗago ya kalleta yace"Umma ke ba za ki ci ba?"
Ta girgiza kai tace"ka ci Sadauki,ni a ƙoshe nake".
Silently ya cigaba da cin abincin, har sannan Umma ba ta ɗauke idonta a kanshi ba.
Kiran sallar magrib yasa shi miƙewa ya fita da kayan da yayi amfani dasu ya ajiye a waje.
A kofar gida ya tarar da Sani suka ƙarasa masallaci.
Sai da aka idar da sallahn Isha sannan ya nufi gida,tun daga waje suke jiyo muryar Inna Yalwati da Baba.
Inna ta buga shewa tace"babu inda Sani zai koma ni dai na gama magana Mallam".
A fusace Baba yace"sai kuma kiyi Yalwati,ki gama barazanar ki dole ne Sani da Sadauki su koma karatu,ni banga dalilin dawowarsu ba kwata kwata,suyi zaman su a can tunda abinda zai dinga faruwa kenan idan sun dawo,duk lokacin da nake son ganinsu da kaina zan shiga mota tunda ni ba makaho ba ne".
Yana gama magana idon shi ya sauka akan su biyun,ya nuna su da yatsa yace"kun aiki iyayen ku su same ni ko?to ku sani babu abinda hakan zata canza,karatu yanzu kuka fara,ko kunga sauran ƴan uwan ku a gidan nan?"
Sani ya girgiza kai da sauri,Sadauki kam kanshi na ƙasa,shi kaɗai ya san yanayin da yake ji a zuciyarsa.
Ya gama maganar da zai yi ya shige ɗaki, Umma dake zaune kan darduma ta sauke numfashi ta ɗaga hannu tace"Ya Allah,ga bawan ka nan,ka tsare min shi a duk inda yake,ka tsare shi daga sharrin mutum da dukkanin abin halitta,Ya Zul Jalalu wal Ikram,kai mai ji ne kuma mai gani,idan wannan zuwa karatun shine mafi alkhairi Allah ka dafa mishi,ka tsare shi daga dukkan sharrin zamani,Ya ubangiji ina tawassali da sunayenka kyakyawa da siffofinka maɗaukaka ka tsare min ɗana Umar kasa wannan zaɓi ya zama mafi alkhairi a gare shi".
Ta shafa addu'ar tana jin wani nutsuwa na sauko mata.
Da safe ta dama mishi koko ta aika aka siyo mishi alalen manja,sosai ya sha kunun don yana so sosai.
Baba na fitowa daga ɗaki Sadauki ya gaishe shi da ladabi,ya ɗan kalle shi yace"ina ɗan uwanka,ya fito mu tafi gona,tunda Allah ya kawo ku dole ku yi aiki".
Sani ya fito daga ɗaki Inna Yalwati biye dashi,ya karasa ya duƙa ya gaishe shi.
Inna Yalwati tace"ba gara min zuwa gona da wannan tafiyar ba,Allah ya gani ba son tafiyar nan nake ba,in ban da zalinci babu abinda yake,yaro dai yace wahala kawai suke sha wallahi".
Sani ya sunkuyar da kai da sauri wani zufa na keto masa.
Mallam ya mata kallo ɗaya ya maida kan Sani,bai ce komai ba ya kalli Sadauki yace"idan kun gama ku same ni a can tunda kun san hanya,kuma kar ku ɓata min lokaci".
Daga haka ya sa takalamansa ya bar gidan,Inna Yalwati sai mita take cike da baƙin ciki.
Tun daga ranar tare suke tafiya gona da Baba,idan sun fita da safe basa dawowa gidan sai magriba.
Kafin su fita za su karya,da rana akan aiko musu da abinci daga gida,idan sun dawo kuma su ci na dare.
Duk da yawanci tuwo ake yi da daddare amma kullum sai Umma ta ajiye mishi wani abin daban.
Sosai yanayin yake musu daɗi, a zuciyar su fata kawai su ke Allah ya kawo dalilin da zai hana su komawa Kano.
Sai da aka fara cire amfanin gona sannan suka fara shiryen shiryen komawa,zuwa sannan duk sun dawo hayyacinsu sun murmure,Umma tun da daɗewa take tanadinta a hankali.
Cikin ƙaton jaka take shirya mishi duk wani abu da zai buƙata,duk da ba son tafiyar take ba amma ta san tashin hankali ba zai hana komai ba.
Ranar asabar Mallam Ɗanjuma ya karaso ƙauyen da ƙaton Bus da zai kwashi yaran,Baba ya haɗa su da wake da masara kamar waccan lokacin,Sadauki ya sha nasiha sosai a wurin Umma.
Cike da kewan gida suka ɗauki hanyar dawowa Kano.




Oum Rijalain 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol