Free chapter · Read without an account
Page 10
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 10
Bayan sun dawo aka cigaba da karatu kamar yadda aka saba, tsakaninsu dasu Bala sai dai kallo.
Sun dawo da sati biyu aka sace kusan gabaɗaya kayan abincin da ya taho dasu daga gida,lamarin da ya matuƙar girgiza Sadauki.
Sadiq ya dinga kwantar mishi da hankali,dole ya haƙura kamar komai bai faru ba.
Watarana sun fita bara tun karfe takwas amma har sha biyun rana babu abinda suka samu,suna tsaye a bakin titi wata bakar mota tinted ta tsaya kusa dasu.
Wanda ke zaune a gefen mai zaman banza yayi winning glass,yana sanye da wani white top sai black face cap,yayi murmushi yace"sannun ku fa".
Sani da Lawali jiki na rawa su ka ce "ina wuni Alhaji".
Yayi dariya yace "dan Allah idan babu damuwa saƙo za ku miƙa min wancan shagon".
Lawali yace"toh Alhaji".
Yasa hannu a back seat ya ɗauko wani baƙin leda ya miƙa masa yana kallon Sadauki da tunda ya musu kallo ɗaya ya ɗauke kai.
Suna barin wurin mutumin ya sake kallon Sadauki yace"ya sunan ka?"
Sai lokacin ya juyo ya ɗan kalle shi,kamar ba zai ce komai ba ya buɗe baki da ƙyar yace"Umar".
Mutumin ya gyaɗa kai yace "Umar,ya makaranta?"
Dai dai nan su lawali suka dawo,ya ɗauke kai daga kan Sadauki ya musu murmushi yace"kun kai?"
Su ka gyaɗa kai,ya juya ya ciro sababbin dari biyu guda biyar ya miƙa musu,da rawar jiki Lawali yasa hannu ya karɓa.
Still fuskar shi ɗauke da murmushi yace"nagode ƴan samari,Umar a yi karatu da kyau".
Kasa bashi amsa yayi sai binshi da kallo da yake,ya maida windown ya rufe motar suka bar wurin a guje.
Cike da farin ciki lawali yace"mun sami na cin abinci,zamu raba ɗari uku uku harda canji".
Sadauki ya ɗauke kai yace"ku raba ba na so".
Da mamaki Lawali yace"saboda me?"
Yace"haka kawai, ni dai bana so".
Babu yadda ba su yi da Sadauki ba amma yace ba zai amsa ba,ba don sun so ba su ka rabu dashi.
Washegari hakan ta sake faruwa,bayan sun gama yawon barar su suka nemi wuri kusa da inda suka tsaya jiya suka zauna.
Wata farar mota mai daukar ido ta tsaya a dai dai spot ɗin jiya,mutumin ya sauke window suka haɗa ido da Sadauki.
Da sauri Sadauki ya ɗauke kai yana jin yadda ƙirjin shi ya buga instantly.
Sani da Lawali na ganin shi suka miƙe, yana kallon su ya mu su alamar su zo da hannu.
Da gudu suka ruga wurin shi.
Yayi murmushi yace"ƴan samari ya sunan ku?"
Sani yace"sunana Sani, wannan kuma Lawali".
Yace"nice name Sani,tare ku ke karatu da Umar?"
Sani yace"eh"
Ya gyaɗa kai yace"i can see".
Sai kuma yayi saurin ɗauko baƙin leda ya miƙa mishi yace"ka kai shagon jiya Please".
Suna ƙoƙarin juyawa ya dakatar da su ya ƙirga kudi kamar jiya ya miƙa musu,ya sake kirga wani daban yace"wannan na Sadauki ne,ku bashi nashi daban".
Cike da farin ciki suka koma wurin Sadauki dake zaune har lokacin yana kallon su,Lawali na miƙa mishi kuɗin yace"bana so".
Sani yace"me yasa ba ka so Sadauki,ka ga dai ba wani aikin wahala yake samu ba".
Sadauki yayi shiru yana tunani,har ga Allah haka kawai ya ji mutumin bai mishi ba,gashi dai ba wani abu ya haɗa su ba.
Washegari da safe ya tashi da wani irin zazzabi mai zafi,hankalinsu Sadiq ba ƙaramin tashi yayi ba ganin halin da yake ciki.
Haka dai suka lallaɓa suka fita bara,still su na tsaye mutumin jiya ya sake dawowa,da farin ciki suka ƙarasa wurin shi,yana murmushi yace"Sani da Lawali right?"
Suka gyaɗa kai da sauri,
yayi murmushi yace"yau ban ga Umar ba".
Sani yace "ai bai da lafiya yana gida".
Yace"subhanallahi,me ke damun shi?"
Lawali yace"Sadiq yace zazzaɓin cizon sauro ne".
Yace"Allah ya bashi lafiya,idan kun je gida ku ce ina gaida shi da jiki".
Ya mika musu baƙin leda as usual yace"ku miƙa min wannan saƙon,kar ku manta da saƙo na,ga wannan naku ne, wannan kuma na ɗan uwanku".
Yayi maganar tare da miƙa su sababbin ƴan dubu dubu kusan guda goma.
Duk suka zaro ido a tsorace.
Yace"ku karɓa mana,sauri nake".
Sani yace "ai kuɗin da yawa".
Yayi murmushi yace"ai ni na ba ku da kaina ba roƙona ku kayi ba".
Da ƙyar da suɗin goshi su Lawali suka karɓi kuɗin.
Bayan sun isa gida suka tarar da jikin nashi da sauƙi har yaci abincin da Sadiq ya samo mishi.
Ganin yadda suke ta fara'a yasa shi zuba musu ido,duk suka zauna kusa dashi Lawali ya fitar da kuɗin da ya ɗaure a ƙugunshi ya ajiye a ƙasa.
Sadauki ya waro ido da mamaki yana bin kuɗin da kallo.
Da tarin mamaki yace"wannan kuɗin fa Lawali?"
Lawali yace"wannan mutumin ya ba mu".
Yace"wannan kuɗin?"
Duk suka gyaɗa kai,Sadauki ya matsar da kuɗin kusa dashi yace"ku maida mishi kuɗin shi ni dai bana so".
Lawali yace"kamar ya a maida mishi?"
Sadauki yace"kuɗin sun yi yawa Lawali,aikin me ku ke mishi da zai dinga ba ku irin wannan kuɗin?"
Lawali ya miƙe riƙe da kuɗin yace"idan kai baka so mu muna so,so ka ke mu cigaba da zama da yunwa muna wahala?"
Sani ya miƙe ya tsaya kusa da Lawali yace"idan ba ka so ni ina so Sadauki".
Yana gama magana ya juya ya bar ɗakin,da mamaki Sadauki ya bishi da kallo,har lawali ya bi bayan shi kasa kwakwaran motsi yayi.
Tun daga ranar babu abinda ya ƙara shiga tsakaninsu sai dai kallo daga nesa.
Babu wanda ya fi bashi mamaki kamar Sani,idan Lawali ya guje shi dama ba wani abin mamaki bane tunda a makarantar suka haɗu,amma Sani ɗan uwan shi ne da harta bacci tare su ke yi.
Bai ƙara shiga wani shock din ba sai da ya ga sun koma suna magana da su Ɗahiru.
A haka ya cigaba da jinyar shi har Allah ya bashi lafiya ya fara fita bara,Sani da Lawali kam kakarsu ta yanke saƙa don ɗaɗin su suke ci sosai ba kama hannun yaro.
Ana haka watarana ya dawo ya tarar da an zo daga gida an tafi da Lawali,sosai ya ji babu daɗi don har lokacin bai ji wani abu ya ragu daga cikin ƙaunar da yake masa ba.
Bayan sati ɗaya da tafiyar Lawali, Sani ya warware ya cigaba da harkokin gabansa,kusan kullum tare suke fita da Ɗahiru su dawo tare.
Sadauki ya tsaya a bakin kofa ya dinga kallon hanya ganin har ƙarfe bakwai saura babu Sani babu alamar sa,duk da ba magana suke ba amma ya kasa ɗauke idon shi a kan ɗan uwansa.
Jin an kira sallah yasa shi fita yayi sallah amma har suka idar bai dawo ba,zuwa sannan haƙurin shi ya gama ƙarewa.
Ya ƙarasa wurin Sadiq yace"har yanzu Sani bai shigo ba Yaya".
Sadiq yace"da sauran lokaci Sadauki,yaushe ma daren ya yi da har hankalinka zai tashi".
Jin abinda yace yasa ya ji hankalin shi ya kwanta,ya tashi ya fita ya tsaya yana kallon hanya.
Wasa wasa har ƙarfe tara Sadauki na tsaye amma babu Sani balle Ɗahiru,hankali tashe ya koma wurin Sadiq dake rubutu yace"Yaya bai dawo ba".
Da mamaki ya ajiye allon hannun shi yace"har yanzu?to ina zai tsaya haka?"
Sadauki ya juya ya fita Sadiq ya mike ya bi bayan shi,a waje ya tarar da Bala da abokan shi suna shirin fita,da sauri Sadiq yace"dan Allah ko kun san wurin da Ɗahiru yake?"
Bala ya juya baya yace"gashi a bayana".
Sadiq ya ɗaure fuska yace"ba wasa nake ba dan Allah,tun da safe da suka fita har yanzu shiru".
Garba yace"shine don rainin wayo za ka tambaye mu,tare muke fita bara da su ne ko ya ya?"
Sadauki bai tsaya jin ƙarshen zancen ba ya fita da sauri Sadiq ya bi bayan shi,da ƙafa ya dinga bin hanya ko Allah zai sa ya gansu,a haka ya isa wurin da suke zama tare kafin ya kwanta ciwo.
Wurin yayi tsit sai maza biyar dake zaune a kan wani benci suna shanye shaye,zai karasa kusa da su Sadiq ya riko shi da sauri yace"kana da hankali kuwa Sadauki?"
Sadauki ya fincike hannun da sauri,Sadiq ya ƙara riƙo hannun yace"ka kwantar da hankalinka za'a gansu,yanzu ka bari zan musu magana".
A nutse ya musu sallama,duk suka juyo suna kallon shi,a hankali yace"ina wunin ku,dan Allah wasu almajirai nake nema ko kun gansu?"
A fusace wani yace"kai ! Kai bagidajen ina ne,ka ganmu goye da yara ne?"
Sadiq yayi shiru yana kallon shi,Sadauki ya watsa mishi wani banzan kallo,yana ƙoƙarin ɓanɓare hannun shi dake cikin na Sadiq ya ƙara riƙe hannun da kyau.
Wani ya busa hayaƙi yace"easy mana kai".
Ya ɗan ɗago ya kalli Sadiq yace"ya yanayin su yake?"
Sadiq yayi gyaran murya ya mishi bayani yadda zai gane.
Ya gyaɗa kai yace "eh to,akwai wasu da na gani haka ka gane?su biyu haka kusan shekaru goma sha kamar waccan na kusa da kai sai dai kamar zai fisu tsayi haka,na dai gansu da rana ka gane?"
Sadiq yace"dan Allah ba ka san inda su ka bi ba?"
Wani daga cikin su ya daka masa tsawa yace"kai ware dallah,ya ana bin ka ta lallami ka na damun mutane iyee?"
Wani irin huci kawai Sadauki yake cike da bacin rai,ga Sadiq ya riƙe mishi hannu.
Ya ja shi su ka bar wurin cike da damuwa,suna tafe yana duba hanya ko Allah zai sa ya ga Sani.
Sadiq ya juyo ya dube shi yace"idan mun koma zanyi magana da Mallam,Allah yasa lafiya".
Har su lka isa makaranta babu wanda yace komai a cikin su,ko da suka isa mallam ya shiga cikin gida.
Da damuwa Sadiq yace"sai dai zuwa gobe,kafin nan ƙila sun dawo".
Sadauki ya riko hannun shi da sauri yace"dan Allah Yaya ka same shi yanzu,Sani bai saba kai dare haka ba".
Sadiq yace"ka kwantar da hankalinka dan Allah Sadauki,babu abinda zai same su da izinin Allah".
Ba don ya so ba suka shiga ciki,motsi kaɗan zai fito waje.
Har garin Allah ya waye Sadauki bai yi wani baccin kirki ba,Sadiq na ganin shi ya girgiza kai suka fita sallah.
Bayan an idar ya karasa kusa da Mallam ya sanar dashi abinda ke faruwa.
Mallam yace"wannan ba abun ɗaga hankali bane Sadiqu tunda ba yara bane,zuwa anjima za su dawo".
Baki buɗe Sadauki ke bin shi da kallo,bai taɓa tunanin lamarin malamin na su ya kai haka ba.
Daga haka aka cigaba da karatu kamar yadda aka saba amma kwata kwata babu abinda Sadauki ke fahimta har aka tashi.
Ko ciki bai shiga ba ya juya ya bar gidan,lungu da sako da ya san Sani zai iya shiga sai da ya duba amma ko mai kama dashi bai gani ba.
Cike da damuwa ya dawo wuraren ƙarfe huɗu,zuwa sannan ƙarfin shi har ya ƙare ga yunwa yana ji don babu abinda ya ci tsawon wannan lokacin.
Yana shigowa Sadiq ya tare shi a hanya yac"ina ka shiga Sadauki,tun safe nake neman ka".
A galabaice yace"Sani ya dawo ne?"
Sadiq ya dafa kafaɗar shi yace"ka bi komai a hankali Sadauki,bayan fitar ka ni ma ban zauna ba,yanzu na dawo daga wurin Mallam na ƙara sanar dashi rashin dawowar su".
Bai ce komai ba ya wuce ya ja ruwa a rijiya ya shiga wanka.
Har kwana biyu babu labarin Sani da Ɗahiru,zuwa sannan hankalin Mallam ya fara tashi.
Ya shirya ya kai report wurin ƴan sanda,Sadauki ya musu kwatancen Sani da kayan da yasa ranar.
Har bayan sati ɗaya ana investigation amma babu wani labari.
Iya tashin hankali Sadauki ya shige shi,gabaɗaya ya fita hayyacinsa saboda damuwa.
Mallam ya turawa iyayen yaran saƙo tunda babu wani labari.
Inna Yalwati ta fasa wani gigitaccen ihu bayan Mallam ya gama sanar da su abinda ya faru.
Cikin kuka tace"wallahi ba zata saɓu ba,dole ne a fito min da yaro na wallahi,zancen banza zancen wofi".
Mallam yace"menene haka Yalwati,ki kwantar da hankalin ki don Allah,ke baki san ƙaddara ba?"
A fusace tace"na bi ƙaddara da gudu,ba zan yarda da wata ƙaddara ba dole ne a fito min da yaro don wannan tatsuniya ce kawai".
Umma dake gefe hankali tashe tace"don Allah Mallam Sadauki ya dawo,ya haƙura ya dawo gida don girman Allah".
Rai ɓace yace"wani irin magana ne haka Fatime,ya kike magana kamar mara ilimi?ba ki san ƙaddara ba,idan wani abu ya sami Sani shi zai sa ki ce a dawo da Sadauki?shima tsautsayi ne da baya wuce ranar sa kuma in sha Allahu Allah zai bayyana shi".
Inna Yalwati tace"wallahi ban yarda da wani tsautsayi ko ƙaddara ba kawai a fito min da ɗana,idan kuma Allah ya bayyana shi ya gama wannan makarantar kenan billahil azeem".
A can Kano kuwa iya ƙoƙari anyi a kan issue ɗin amma babu wani labari,tun ƴan sanda na wani abu a kan maganar har dai su ka watsar da case ɗin.
Sadauki dai ya kasa sabawa da rashin Sani,gani yake kamar mafarki yake kuma any moment zai iya farkawa.
Oum Rijalain
***