Free chapter · Read without an account

Page 11

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1 

Page 11

Shekaru uku kenan da ɓacewar Sani amma har yau Sadauki ya kasa sabawa da hakan,ji yake da zai samu wani opportunity da babu abinda zai sa ya samu saɓani da ɗan'uwan shi.
Yayi kewar yadda su ke cin abinci tare,su yi wasa tare gashi yanzu ya tafi bai ma san inda yake ba.
Ya kan ɓuya yayi kukan rashin ɗan uwan sa kusan kowanne dare.
Ranar yana tafe a hanya sanye da suɗaɗɗen takalmin shi da kusan rabi ya cinye zafin rana na dukan ilahirin jikin shi,yana sanye da wani koɗaɗɗen shuɗin yadi da wani wandon uniform da su ke samu wurin jama'a.
Taron mazan da ya gani ya sa shi ƙarasawa kusa da wurin,sai da ya fahimci abinda ke faruwa sannan a hankali ya taɓa na kusa dashi yace"dan Allah nima zanyi aikin".
Kallon sama da ƙasa ya watsa mishi sannan ya tsartar da yawu yace"shine sai ka taɓa ni,ƙazamin banza ƙazamin wofi".
Na kusa dashi ya ce"haba dan Allah,ka dinga hakuri mana,menene a ciki don ya taɓa ka?"
Yace"da wannan dattin jikin nashi zai wani taɓa ni?bana son irin haka gaskiya".
Wani mutum ya ƙaraso ya mu su kallo ɗaya bayan ɗaya yace"za'a buɗe gate yanzu sai ku fara shiga da kayan,banda hayaniya don oga na ciki,ayi komai cikin nutsuwa".
Cike da girmamawa kamar za su kwanta su ka amsa shi,nan da nan aka wangale makeken gate ɗin sabon ma'aikatar da ake kan aikin shi.
Kusan maza ashirin su ka fara sauke kwalayen da ke cikin manyan trailoli dake wurin,da farko hana Sadauki aikin su ka yi ganin ƙanƙantar shi,da ƙyar da suɗin goshi bayan wani ya sa baki aka ƙyale shi.
Sun kai kusan awa uku kafin su gama sauke kwalayen, gabaɗaya kowa ya Jigata don ba ƙaramin aiki ba ne.
Bayan sun gama aka zauna zaman jiran wanda zai biya su,sai da su ka shafe kusan awa ɗaya a zaune sannan ya fito riƙe da wani envelope yace su yi layi.
Babu musu duk su ka aikata abinda ya umurce su,yana tsaye za ka karaso ya kirga kuɗin ka ya miƙa maka.
Dai dai Sadauki ya karasa kusa dashi wani mutum ya fito securites biye dashi,kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar kuɗi sun zauna.
Suna haɗa ido da Sadauki ya ɗauke kai,sauran ma'aikatan suka ɗurƙusa ƙasa cike da girmamawa su ka hau gaishe shi.
Da mamaki yake bin Sadauki da kallo ganin shi kaɗai ke tsaye,bai ce komai ba ya karasa gaban motar shi driver yayi saurin buɗe mishi kofa,har zai shiga sai kuma ya juyo still su ka sake haɗa ido da Sadauki da ya bishi da kallo.
A nutse yace"Musty!!
Da sauri wanda ke rabon kuɗin yace"Yes Sir".
Cike da girmamawa ya bar wurin da sauri ya ƙarasa gaban shi,bayan wani lokaci ya dawo wurin yana kallon Sadauki yace"oga yace kar a biya ka,za ka iya tafiya".
Sadauki ya juya ya bi motar da kallo har ya fita aka rufe gate ɗin.
Sauran dake tsaye su ka dinga kallon Sadauki cike da tausayi amma babu halin nuna hakan,ganin bai motsa ba ya sa shi cewa"ka fita daga nan kuma kar ka ƙara tako kafar ka".
Sadauki ya ɗago ya kalle shi da idanuwan shi da su ka kaɗa,bai ce komai ba ya juya a nutse ya fita.
Tafiya kawai yake ba tare da sanin inda yake jefa ƙafafuwan shi ba,sai da yayi tafiya mai nisan gaske sannan ya nemi gefen wani gida ya zauna jikin flowers.
Kanshi ya cusa cikin cinyoyin shi,tunda yake abu bai taɓa tsaya mishi a rai kamar abinda ya faru yau ba.
Rabon shi da abinci tun jiya da rana tunda tuwo a kayi a gidan Mallam da daddare kuma ba ci yake ba.
Wata farar mota ta karyo kwana ta tsaya dai dai gate ɗin gidan da Sadauki ke zaune, driver yayi horn aka wangale makeken gate din ya shiga yayi parking kusa da sauran motocin dake wurin.
Wata farar mata ta fito daga baya sanye da blue hijab sai black handbag rike a hannunta,ta kalli mai gadi dake zaune kusa da gate tace"Iliya".
Ya taso da sauri yace"na'am Hajiya".
Tace"akwai wani almajiri dake zaune a waje,kace ya shigo".
Yace"to Hajiya".
Ya juya da sauri ya fita, Sadauki na zaune yadda yake mai gadi yace"ɗan Mallam,ka shigo ana neman ka a ciki".
Sadauki ya ɗago a galabaice ya kalle shi,a hankali ya miƙe tsaye ya kakkaɓe jikin shi ya bi bayan shi har cikin gidan.
Babban gida ne dake ɗauke da kusan part huɗu,tana tsaye jikin mota mai gadi ya ƙaraso yace"Hajiya gashi nan".
Tace"Nagode Iliya".
A hankali Sadauki da kallo ɗaya kawai ya mata ya sunkuyar da kai yace"ina wuni".
Tana bin jikin shi da kallo tace"lafiya ƙalau,ya sunan ka?"
A hankali yace"Sadauki".
Matar tace"Sadauki ba suna bane ai,asalin sunanka nake tambaya".
A hankali Sadauki yace"Umar".
Tace"masha Allah Umar Faruq,akwai ɗan aikin da nake son ka min idan babu damuwa amma bari ka fara cin abinci tukun,ka zauna ga kujera can zan aiko maka da abinci yanzu".
A hankali yace"nagode".
Ya karasa kan kujerar da ta nuna mishi yana bin gidan da kallo.
A parlour ta tarar da ƴan matanta kusan su huɗu su na kallo,suna ganinta duk suka tashi zaune banda ƙaramar da gabaɗaya hankalinta ke kan kallon da take a Ipad dake hannunta.
Babbar cikinsu tace"Mami sannu da zuwa".
Da gudu wacce ke kallo a Ipad tayi wurgi dashi ta rugo da gudu ta rungumeta tace"oyoyo Mami".
Ɗayar ta tashi ta ƙarbi handbag dinta tace"Mami welcome,ya aiki?"
Ta zauna kan kujera ta amsa gaisuwar su ɗaya bayan ɗaya tace"duk kun gama aikin dake gidanne ku ka zauna kallo?"
Babbar wacce zata kai shekaru goma sha takwas tace"Mami duk mun gama, babu wani aikin da ya rage".
Mami ta gyaɗa kai tace"yayi kyau".
Wacce ke rungume da ita har lokacin sanye da wani pink gown fara sol kamar mahaifiyarta don gabaɗaya ita ta dauko hasken uwar an raba mata dogon gashinta gida biyu da pink ribbon ta riƙo hannun Mami tace"Mami ! Aunty Zeenah bata haɗa min cornflakes ba".
Mami tace"me yasa ba'a haɗawa Zarah na cornflakes ba?"
Zeenah ta watsa mata harara tace"wallahi ƙarya take Mami,sau biyu ta sha cornflakes yau".
Mami ta juyo ta kalleta yace"kin sha cornflakes ko ba ki sha ba?"
Ta turo baki tace"to Mami taƙi ta ƙara min".
Mami ta buge bakin tace"ban hana ki ƙarya ba?"
Zarah ta miƙe da sauri kusa da ita ta fashe da kuka,a fusace Mami tace"zaki rufe min wannan bakin ko sai na zo wurin?"
Da sauri ta haɗiye sauran kukan sai hawaye da ke gangaro mata.
Sauran sai ƙunshe dariya su ke sanin halin Mami,ta miƙe za ta shiga ciki sai kuma ta juyo da sauri tace"subhanallahi,Zeenah me ku ka dafa?"
Zeenah tace"jollof rice".
Mami tace"dan Allah ki zuba abincin a plate akwai wani almajiri da zai min aikin bayan nan ki kai masa ,idan ya gama ci sai yayi aikin".
Zeenah ta miƙe tace"to Mami".
Zarah dake tsaye a gefe ta bi Mami da kallo dake ƙoƙarin hawa stairs,tana ganin ta haura ta fashe da kukan dake cinta.
Na'ima wacce ke bin Zeenah a shekaru ta watsa mata harara tace"tashi ki bar nan,yarinya ba ki da wani aiki sai kuka".
Da gudu tabi bayan Zeenah dake kitchen,tana ƙoƙarin zuba abincin ta shigo ta rungumeta ta baya.
Da sauri Zeenah ta ajiye plate ɗin hannunta tace"lafiya Chu Chu?"
Cikin kuka tace"Kin ga Aunty Nai'ma ko?"
Zeenah ta shafa kanta tace"yi haƙuri auta,zan kama Aunty Na'ima,yanzu haura sama ko dauko min hijab sai ki raka ni mu kai abinci waje".
Da gudu ta juya ta fita Zeenah ta girgiza kai,bayan wani lokaci ta sauko riƙe da wani farin hijab ta miƙa mata.
Zeenah tayi murmushi tace"thank you Zarah na".
Ta riƙo hannunta ta buɗe kofar baya su ka fita,yana zaune yana wasa da yatsun hannun shi Zeenah ta ƙaraso.
Tun daga nesa take bin shi da kallo har ta isa kusa dashi.
Tayi sallama ya ɗago a hankali ya amsa mata,ta miƙa mishi plate ɗin hannunta tace"gashi Mami tace a kawo maka".
Yasa hannu ya karɓa a nutse yace"nagode".
Zarah dake bin shi da kallo ta juya ta kalli Zeenah tace"Aunty Zeenah,his clothes are old".
Zeenah ta watsa mata harara tace"keep quiet Zarah,you talk too much".
Sadauki ya ɗan ɗago ya kalli wacce aka kira da Zarah,sai kallon shi take kamar ta ga sabuwar halitta.
Kasa ɗauke idon shi a kanta yayi ganinta kamar ƴar turawa.
Zeenah ta riƙo hannunta su ka bar wurin,har sun yi nisa ta juyo ta kalle shi su ka haɗa ido,da sauri ta ɗauke kai ta dubi Zeenah tace"Aunty Zeenah".
Zeenah tace"yes, Zarah".
"Why is he looking at me?"
Zeenah tace"looking at you?"
Zarah ta gyaɗa kai, Zeenah tayi dariya tace"because you talk too much Zarah,dan Allah ki barni in huta".
Sadauki yayi shiru yana kallon abincin,tunda su ka shigo garin Kano da sunan karatu bai taɓa ganin abinci makamancin wannan ba kusan shekaru uku kenan,in fact ba'a taɓa karrama shi haka ba.
A hankali yayi bismillah ya fara cin abincin,sai da ya cinye abincin tas sannan ya karasa gaban tap dake gefe ya wanke hannun shi da kyau sannan ya tare hannun ya sha ruwan ya koma ya zauna.
A can ciki bayan sun koma parlour Zarah ta haura sama ta buɗe ɗakin Mami bayan tayi sallama,Mami dake zaune tana duba wani file ta ɗago ta kalle ta.
Zarah ta zauna kusa da ita tace"Mami".
Mami tace"yes darling".
"His clothes are old Mami".
Mami tace"wa kenan?"
Ta nuna mata waje tace"ba kin ce Aunty Zeenah ta kai mishi abinci ba,tare mu ka kai da ita but Mami why are his clothes old?"
"I don't know Zarah,stop asking silly questions please".
Bayan kusan minti biyar ta ajiye papers ɗin hannunta ta miƙe tsaye ta shiga wanka,ta ɗan jima a ciki sannan ta fito ta shirya cikin wani cotton Abaya baƙi ta shafe jikinta da turaruka ta zura dogon hijab ta riƙo hannun Zarah su ka sauko ƙasa.
Babu kowa a parlour sai tv dake aiki shi kaɗai ta buɗe ƙofa ta fita,yana zaune ya hango fitowarta,ya tashi tsaye da sauri ya sunkuyar da kai.
Mami tayi murmushi tace"Sadauki ka gama?"
Cike da girmamawa yace"na gama Hajiya,na gode Allah ya saka da alkhairi".
Mami tace"sunana Mami ba Hajiya ba,mu je in nuna maka aikin da zaka min".
Ta nufi bayan apartment dinta ya bita a nutse.
Flowers dake wurin ta nuna mishi tace"sun yi yawa sosai,ga scissors can ka rage min su don Allah kafin in kira wanda ya saba gyara min".
Sadauki yace"toh".
Mami ta ja kujera ta zauna Zarah ta zauna kusa da ita.
Ya karasa ya ɗauki scissors ya fara aikin a nutse,Mami na zaune tana sauraron hiran Zarah lokaci lokaci ta kan ɗago ta kalle shi.
Wayarta dake riƙe a hannunta tayi dailing numbern Zeenah tace ta kawo mata handbag dinta.
Bata wani ɗauki lokaci ba ta kawo jakan ta koma cikin gida,bayan ya gama yace"ina za'a zubar da sharan Hajiya?"
Mami tace"ka bar wannan kawai,kayi mai wuyar ai,zan sa Iliya ya kwashe".
So yake ya ce mata zai kwashe amma kamar wadda aka ɗinkewa baki don wani irin nauyin matar ya ke ji.
Ta buɗe jakarta ta ƙirga kusan dubu uku ta miƙa mishi,Sadauki ya ɗan ja da baya ya girgiza kai.
Mami ta watsa mishi harara tace"meye haka?"
Yace"dan Allah Hajiya ki bar kudin ki ba sai kin biya ni ba,abincin da ki ka bani ya fi min komai".
Mami ta girgiza kai tace"a'a,abinci ni naga damar baka ai, wannan kuma haƙƙin ka ne dole in ba ka".
Sadauki yace"don Allah Hajiya ki yi hakuri ba zan karɓa ba wallahi,ni saboda Allah na miki aiki".
Mami tayi shiru tana kallon shi jin yace wallahi,ta sauke ajiyar zuciya tace"to nagode Umar Faruq,ka dawo anjima bayan sallar magrib ka karɓi abinci idan makarantar ku babu nisa,zan yi magana da mai gadi idan ya ganka ya buɗe maka ƙofa ka shigo,ka dinga shigowa idan ina da aike ko wani aikin sai ka min".
Kanshi a ƙasa yace"to Hajiya".
Mami tace"sunana Mami ba Hajiya ba,kar in sake ji".
A hankali Sadauki yace"toh".
Ta maida kuɗinta cikin jaka suka fito tana riƙe da hannun Zarah.
Bayan Sadauki ya fita Mami ta karasa wurin mai gadi tace"Iliya, duk lokacin da yaron nan ya zo ka buɗe mishi ƙofa ya shigo dan Allah".
Iliya yace"to Hajiya".
Mata biyu dake tsaye suna hira gaban apartment dake kusa da nata su ka bita da kallo, ɗayar dake sanye da mayafi da alama ita aka rako ta taɓe baki tace"ga likitar gidanku".
Wacce ke sanye da doguwar rigar atampha ta wani bi Mami da harara tace" baƙar munafuka dai".
Kawarta tace"shi kuma wannan da ke biye da ita fa?"
Hajiya Mama ta wani taɓe baki tace"ina zan sa ni tunda tare mu ke tsaye dake anan,kin santa da jaye jayen tsiya ita mutuniyar kirki".
Aminiyarta tace"a haka zata janyowa kanta bala'i ai,wai ina Sudais ne tunda na zo ban gansa ba?"
Mama tace"ina kuwa za ki gansa tunda ba kanwar uwar sa Hafsat ba ce,tun jiya yake fushi dani saboda nace kar in ƙara ganin ƙafar sa a part ɗinta tunda ba ita ta min naƙudar sa ba".
Hajiya Zainab tace"amma Sudais sai yaushe zai san ciwon kansa ya fita hanyar mutanen nan?a ce ƙannen ka mata sun fi ka sanin abinda ya dace da rayuwar su?"
Mama tayi ƙwafa tace"ke dai bari Zainab, wallahi lamarin Sudais ya daina bani mamaki sai dai tsoro,kamar ba ni na haife sa ba bini bini yana wurinta,idan ance ga abinci yace ai naci wurin Mami,abu kamar aikin asiri?"
Hajiya Zainab tace"ai abin ya haɗu biyu ne da asiri da munafurci kin ga kuwa dole abin yayi yawa shege da hauka".
Mama tace"musamman tsakanin sa da wannan yarinyar kamar zabiya,na rasa yadda zan raba tsakanin su wallahi,Allah ya gani na tsani Hafsah da ƴaƴanta musamman ita mai ido a tsakar ka,yarinya sai rashin ta ido kamar goyon kaka".
Hajiya Zainab ta duba wayarta ganin mai kiranta yasa tace"bari in tafi gida,idan na koma zamu cigaba da magana lamarin gidan nan naku babba ne".
Mama tace"to shikenan nagode,a gaida gida".
Ta buɗe motarta ta shiga tace"gida zai ji in sha Allah".




***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol