Free chapter · Read without an account
Chapter 9
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*Bani da Madogara*
(Sai Allah...)
009
Dariya sosai suka tuntsire suna yi, ita Hajiya momma har da riƙe ciki har da baba Uwani sai da ta dara, suna cikin dariyar a banko ƙofar, da sauri suka waiwaya ganin waya ya buɗe ƙofar haka, wata kyakkyawar yarinya ce wacca bazata gaza shekara 15 ba ta shigo da uniform a jikinta, fara ce sosai kana ganinta kaga Hajiya momma, cike da shagwaɓa ta tako har inda iyayanta suke, har ta zauna saman kujera sai ta yi saurin Miƙewa tana kallon Hujayrah ta ce
"Ammie ina muka samu model"
"Aiki aka kawota gidan nan, she is so friendly Razina, you will like her" cewar Hajiya momma tana kallon Hujayrah da murmushi
Buɗar bakin Razina ta ce
"A'a gaskiya Ammie ita ba ƴar aiki bace, kawai ta dawo ɗakina da kwana"
Ba Hujayran ba, Alhaji, Hajiya Momma har da Baba Uwani suka cika da mamakin Razina, musamman Hajiya momma da tasan halin autarta bata son mutane balle ƴan aiki, to amma yanzu fa daga ganin Hujayrah har ta ƙaryata ƴar aiki ce son ma take ta dawo ɗakinta da kwana Ikon Allah. Cike da mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskar Hajiya momma ta dubi autarta ta ce
"Razina are you really serious kina son ta dawo ɗakinki da kwana, ke da baki son mutane balle ƴan aiki"
Murmushi Razina ta yi sai ta riƙo hannun Hajiya momma ta ce
"Ammie ai ita wannan she is special ba kamarsu bace, she is damm beautiful, baki ga idanunta ba irin na mutane bane, zan iya cewa for the whole of our planet da matuƙar wuya a samu masu kalar idanunta guda uku ƙwarara, so she is very special, zan bata baƙin glass ɗina ta dinga sakawa idan zamu fita saboda mutane masu magana"
Shiru ɗakin ya yi ana sauraron Razina wacca tsakaninta da Allah take ƙaunar Hujayrah.Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke sannan ya dubi Razina da murmushi ya ce
"Yanzu kina son ta zama ƴar gida kenan Autana, ta yi miki sosai babu matsala"
Gyaɗa kanta Razina ta yi tana duban Hujayrah da murmushi, ita ma murmushin Hujayrah ta mayar mata. Gyaran murya Alhaji ya yi sannan ya dubi Hujayrah ya ce
"Autata Razina tana son ki kasance kamar ƴar gidan nan, don haka dole ne musan asalinki saboda yanzu duniya ba abin yarda bane, dole ka kasance kana taka-tsantsan da mutane, inaso ki sanar mana garinku da asalin maƙasudin fitowarki neman aiki"
Shiru Hujayrah ta yi yanzu ita me ma za ta ce ya fito da ita,wata idea ne ya zo mata sai ta fara magana cike da sanyin murya
"Abbu kamar yadda na faɗama Mammi ni sunana Hujayrah ɗiyar Abdullahi, mu mazaunan ƙauyan kwanar kwara ƙwai ne a garin Kaduna, mammina ita kaɗai ce wurin Abbuna, mu Huɗu ne mammina ta haifa, ni ce ta biyu a ɗakinmu, yayana Mansur ya dasu ne a sanadiyyar rashin lafiya da ya yi lokacin da aka kai shi almajiranci a birni, Abbuna makaho neeee... "
A nan muryar Hujayrah ta yi rauni wanda idanunta sun ciko da ƙwalla, kowa a ɗakin sai da zuciyarsa ta tsinke saboda tausayi musamman Hajiya momma,sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta ci gaba da cewa
"A sanadiyyar makantar Abbuna mun shiga halin ƙunci da damuwa, yayyin mahaifina basu taimaka mana da komai illa ƙanin Abbuna Baba Musa, shi kuma baba Musa yana da iyali sosai, kaga ba komai zai iya mana ba, Ina aji 3 a secondary na garinmu yayyin mahaifina suka dakatar dani saboda sun ga yaransu ba Karatun suke ba, har ta islamiya sun so na daina zuwa, kakata ce ta yi ruwa ta yi tsaki akan dole na koyi karatun addini, hakan nan suka ƙyaleni, Abbuna yana son muyi karatu mai zurfi a cikin birni amma babu yadda ya iya, haka yana ji yana gani suka hanani zuwa makaranta, ƙanina Salim shima a aji 3 suka dakatar dashi,duk wa'innan abubuwan da suke mana saboda makantar Abbuna ne, da yana gani babu wanda zai yi masa shisshigi a Karatun yaransa ko tarbiyyarsu, to saboda haka ne yasa na fito neman aiki don na samu kuɗin da zai isa mu kai shi asibitin ido ayi mishi magani ko Allah zai sa ya dawo da ganinsa, Sannan da na samu kuɗin yima Abbuna aiki zan koma garinmu, daman saboda aikin idon ne ya kawoni birni"
Shiru ɗakin ya yi baka jin motsin komai sai ƙarar A.C, kowa ya natsu yana sauraron Hujayrah wacca take magana idanunta na zubda ƙwalla, sosai tausayin Hujayrah ya ɗarsu a zukatan Alhaji, Hajiya momma da Razina, daman Baba Uwani tasan komai kasancewar ta sanar mata lokacin suna cikin tasha sai ta sake jin tausayin Hujayrah don tabbas akwai ƙalubale a tattare da rayuwarta.Nauyayyan ajiyar zuciya Alhaji ya sauke sannan ya fara magana
"Hujayrah a labarinki akwai tsantsan tausayi,ke da ahalinki ababan tausayawa ne sosai, a gaskiya mahaifinki bai yi dacan ƴan uwa ba, koda yake ƙaddara ce za ta iya faɗawa kan kowa, suma ba tsallake hukuncin Allah suka yi ba, ba wai baya son sa bane yasa ya makance illa jarabashi ya yi don yaga ya ƙarfin imaninsa da tauhidinsa yake,babu damuwa Hujayrah kisa a ranta nan gidan kamar a gidanku kike, maganar aiki ki ajiye shi a gefe, zan ɗauki nauyin aikin mahaifinki, ƙwararran likitan da yake dubamin ido ya tafi India ƙaro karatu, amma ba zai jima a can ba, course ɗin wata shida zai yi ya dawo Nijeriya, idan ya dawo sai ya duba mahaifinki, sannan ki sha kuruminki indai maganar karatu ce, za ki ci gaba da karatunki da yardar Allah, hakan ba zai gagaremu ba in sha Allah "
Wani irin daɗi da farin ciki Hujayrah ta ji a ranta wanda ya kasa misaltuwa, shin dariyar farin ciki za ta yi ko kuwa kukan farin ciki, Allah kenan mai iko lallai fitowarta daga garinsu ya yi mata rana tunda gashi za ta ci gaba da karatunta sannan za a kai mahaifin asibiti don samun lafiyar idanunsa ya koma yana gani. Matsawa Hujayrah ta yi kusa da Alhaji ta ɗora hannayanta biyu a saman ƙafarsa sai ta saki kuka mai ban tausayi, cikin kukan ta ce
"Abbu ban san da wasu haruffa zan yi amfani dasu wurin haɗa jimlolin da zan gode maka ba,Na gode! na gode! na gode! da wannan alkhairan da ka yi min, in shaa Allah ba za ka taɓa tagayyara ba, maƙiyanka sai dai su ji kunya, mahassadanka su ciza yatsa, Allah ya ɗaukaka,ya kareka da iyalanka daga sharrin masu sharri, ya shirya maka zuri'arka,ya ƙara maka buɗi da wadata, ya kuma ƙara maka lafiya mai amfani, sannnan ya saka maka da mafificiyar aljanarsa wacca take cike da ƙoramai masu kyawun launi, Ina matuƙar godiya a gareka sannan bakina ba zai taɓa daina yi maka addu'ar nasara da ci gaba akodayaushe, tabbas kai fitila ne mai yaye duhu, sannan kai bango ne wanda talakawa za su jingina su yi farin ciki, Ina godiya sosai a gareku bayi ɗaya in shaa Allah ba zu taɓa dana nasanin kasancewata a cikin wannan gidan ba da yardar Allahhh.. "
Kuka ne ya sarƙarfeta yi take sosai, dafata Alhaji ya yi yana ɗagota fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce
" Allah ya amshi addu'o'inki ɗiyata, nima ina godiya da wa'innan addu'o'in naki a gareni "
" Ki ɗauka kamar a gidanku kike Hujayrah, ki ɗauka kamar ni na haifeki Hujayrah" cewar Hajiya momma tana kamo hannayanta, Razina ma riƙo hannayansu ta yi fuskarta shimfiɗe da murmushi ta ce
"Hujayrah ki ɗaukeni a matsayin sister ki"
Cikin sanyin murya Hujayrah ta ce
"Ina godiya sosai Mammi, daman ni tunda na shigo ɗakin nan nake jinku kamar iyayena, Razina nima zan ɗaukeki kamar ƴar uwata ta jini daman banda ƴar uwa mace duk maza ne"
Rungume juna suka yi suna farin ciki, Hajiya momma ta ce
"Yanzu yadda za a yi tunda Razina kina da lesson teacher Sai kawai ya dinga ma Hujayrah karatu a gida, idan muka kai ta makaranta a ƙaramin aji za su sakata tunda bata da background, yara za su iya rainata,ko ya kagani Alhaji"
"All the same ni zan fita ina da meeting da baƙinmu da suka zo daga ƙasar China anjima"
Yana maganar yana miƙewa sai yabar ɗakin. Hajiya momma ta dubi baba Uwani ta ce
"Uwani ku je da Hujayrah ta ɗauko kayanta sai ta dawo nan da zama, amma gaskiya ƴan uwan ubanta basu da kirki"
"Haka suke ai nima tausayi ta bani nace gwara ta zo ta yi aiki ko ta samu kuɗin da za ta kai babanta asibiti a yi masa aiki, sai gashi zuwanta ya yi rana banda ma aikin ido har da karatu za ta ci gaba, muna Godiya sosai Hajiya Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziƙi"cewar baba Uwani tana murmushi don bata san komai akan dagin Hujayrah ba ta dai faɗa hakan ne saboda tun farko ta ce ƴar ɗan uwanta ne. Ajiye jaka Razina ta yi da sauri ta ce
"Ammie tare zamu na rakata ɗauko jakan"
"Ke da kika tsani zuwa sashe ma'aikata yau ke da kanki kike son zuwa" cewar Hajiya momma tana murmushi ita abun autarta har dariya yake bata, Fuska Razina ta kwaɓe cike da shagwaɓa ta ce
"Ammie tare da Hujayrah za mu fa"
"A dawo lafiya"
Miƙewa Hujayrah ta yi sai suka fita su uku, baba Uwani na gaba su Hujayrah da Razina hannunsu sarƙarfe dana junana suna baya suna hira kamar dama can sun san junansu.
Ma'aikata sai kallonsu suke suna mamaki saboda sun san wace ce Razina Masifaffiya ce sosai bata sake musu fuska balle ta yi musu magana, abinda yake haɗata dasu shi ne aiki, uwa-uba ga raini duk girman ƴar aiki za ta iya ɗauketa da mari idan ta kuskure mata, ko kuma tasa mahaifinta ya kori ma'aikincin, don yana matuƙar son autarsa Razina, duk abin ta ce tana so shi yake mata, idan ta ce ya kori mai aikici duk kirkinsa koransa yake. Yanzu haka bakin ma'aikatan gidan da suke waje suna aiki sake yake suna kallon Ikon Allah. Ko a jikinsu Hujayrah da Razina har suka isa sashen ma'aikata baba Uwani na gaba suna biye da ita. Tunda Razina take bata taɓa zuwa sashen ma'aikata sai yau kuma yanzu a sanadiyyar Hujayrah don jinta take kamar ƴar uwata Nazima wacca take wurin Auntynta Hajiya Nafisa ƙanwar Abbansu. Mai ma'aikata za su yi inba gulma ba suna zunɗansu da baki, wata a cikin masu aikin ta kasa haƙuri ta buɗi ƴar uwarta ta ce
"Salame kinga abinda na gani kuwa"
Wacca aka kira da Salame ta ce
"Me kenan Talatu"
"Autar Hajiya momma na gani riƙe da hannun baƙuwar ƴar aikin da baba Uwani ta kawo yau sun shigo cikin sashen nan da murmushi a fuskokinsu"
Wanki Salame take amma tsam! Ta tsame hannunta daga wankin da take cike da mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskarta ta ce
"Dan girman Allah! Yaushe suka shigo cikin sashen nan"
"Yanzu nan baba Uwani ta shigo tana gaba suna biye da ita hannayansu cikin na juna"
Rike baki Salame ta yi tana kallon Talatu sai can ta taɓe bakin tana cewa
"Lallai ma yarinyar nan wato mu ta raina kenan bata sake mana fuska amma daga zuwan baƙuwa har da riƙo hannunta su shigo sashenmu abinda bata taɓa yi ba, Ikon Rabbi sai Rabbani"
"Nima ai mamakin abin ya bani, wai kinsan ita ce ta zuga Alhaji ya kori Hadiza wai saboda da cika mata sugar a shayi, abun ban takaici wallahi"
"ƙyale shegiya dama ce Allah ya bata shiyasa take iskancinta yadda ya kamata, har na ƙosa yayanta ya dawo don shi kaɗai ne yake saitata yadda ya kamata" cewar Salame tana ci gaba da wankin
"Nima haka wallahi, ke kinga wani sabon Ikon Allah" Tana maganar tana nuna mata su Hujayrah sun fito daga ɗakin baba Uwani, Razina riƙe da jakar Hujayrah suna dariya. Da sauri Salame ta yi saurin juyawa don daga abinda Talatu ke nuna mata, ƙara sakin wankin ta yi tana kallonsu ta sake baki sheƙeƙe har suka wuce ta gabansu.
Da sauri Salame ta dubi Talatu ta ce
"Talatu anya baƙuwar nan mutum ce"
Ras ƙirjin Talatu ya bada don akwai ta da shegen tsoro, cikin tsoro wanda ya nuna ƙarara a fuskarta ta ce
"Ban gane anya mutum ce me kika gani ne"
"Koren idanu baƙuwar take dashi gasu manya-manya farare tarr!"
Da sauri Talatu ta ce
"Kin duba ƙafarta ko kofato ne da za ki ce ba mutum bace"
"Sai na duba kinsan zan iya ai"
"mu bar maganar kawai haka" cewar Talatu tana gyara zama
Dariya Salame ta yi tana cewa
"kin cika tsoro wallahi, yanzu in misali aljana ce ya..."
Bata ƙarasa maganar ba Talatu ta yi saurin cewa
"Na roƙeki da girman Allah kibar zancen kar na kasa bacci yau"
"To to na bari shikenan"
Basu ƙara cewa komai ba sai ma Talatu ta tashi tabar wurin zuwa ɗakinsu. Ita kuma Salame ta ci gaba da wankinta tana ƴan waƙe-waƙe.
Koda su Hujayrah suka isa ɓangaren Hajiya momma, sun samu bata falon sai kawai Razina ta yi musu jagora zuwa ɗakinta wanda yake a sama, suna shiga ɗakin Hujayrah ta waro manyan idanunta waje tana cewa
"Aljannar Duniyar , duka nan ɗakinki ne sister"
Da murmushi a fuskar Razina ta ce
"Eh Hujayrah, a nan za mu dinga kwana mu kaɗai abun mu"
Hujayrah na kalle-kalle ta ce
"Maa shaa Allah, Ina ƙara godiya ƴar uwa"
"Babu damuwa, kinga cupboard ɗinki nan na saka miki jakarki ciki, sannan zuwa anjima idan munci abinda driver zai kaimu saloon ayi miki gyaran jiki daga can mu wuce supermarket a siya miki kayan makeup da abayas sai gobe idan na dawo daga School sai mu tafi wurin telan Ammie ya gwadaki idan Ammie ta zaɓo miki kayan sai a kai mishi ya ɗinka miki"
Wata ƙwallar ce ta sake taruwa a idanun Hujayrah murya a raunane ta ce
"Razina ban san da wasu kalmomi zan yi amfani dasu wurin gode muku ba, Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci"
"Ameen ya Rabb, bara na watsa ruwa"
Shiga toilet Razina ta yi, ita kuma Hujayrah ta ci gaba da bin ɗakin da kallo, babba sosai an yi masa fenti kalar pink mai haske, ga manyan teddy bear guda biyu suma kalar pink, gadonta babba ne da pillows guda biyu manya sai ƙananu biyu, ga cupboard ɗin ɗakin ƙofarsa huɗu ne, a taƙaici idan kaga ɗakin dole ya burgeka saboda tsaruwarsa. Wannan kenan...✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A can gidan abinci bayan tafiyar Hujayrah da Rabi da kusan awa huɗu su Black scorpion squad da Habib suka dira a gidan. Zama suka yi a cikin mota sai Habib ya shiga cikin gidan abinci ya zauna a inda aka tanadar ma masu cin abinci kamar ya zo cin abinci, sai kallo matan da suke kawo abinci ga masu buƙata yake yana tantance idanunsu ko zai ga kalar idanun da Ogansa ya suffanta, daman ƙishin-ƙishin aka musu akan anga wata mai koran idanun a gidan abinci tana aiki. Ganin lokaci na iya ƙure mishi sai kawai ya kira wata a cikin matan, Sajida ce ya yi sa'ar kira lokacin ta kaima wani na kusa da taburin da Habib yake zauna.Canja tafiya ta yi tana rangwaɗa ko zai taya har ta kai inda Habib yake. Sassanyan murmushi ta sakar masa har da kashe murya ta ce
"Ganiiii!"
Da wani irin salo ta ja kalmar ƙarshe. Habib ko a jikinsa karairayar da take burinsa kawai ya tabbatar yarinyar tana a gidan abincin daga bisani cikin dare Black scorpion Squad su zo su tafi da ita don a yanzu koda tana nan baza su iya ɗaukarta ba saboda mutane,sannan gangs ɗin Black scorpion squad basayin aiki da rana sai cikin dare, murmushin yaudara ya sakar mata sannan ya ce
"ƴan mata bismillah ga wuri mana za mu ɗan zanta ne, ba za ki ɗaɗe ba za ki wuce"
Wani irin daɗi Sajida ta ji a ranta a tunaninta ƙila ya furta yana sonta kuma zai aureta, babu musu ta zauna a ɗayan kujeran har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallonsa da murmushi kwance a fuskarta. Gyara murya ya yi sannan ya ce
"ƴan mata don Allah ina wata yarinya da take aiki a gidan abincin nan baƙa tana da koran idanun, naga ban ganta bane"
Ai wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tasoma Sajida ya tsaya mata a ƙahon zuciya, a ranta tana Allah ya isa, sai da ta gama sakankancewa akan ita yake so ashe ma tambayarta zai yi akan Hujayrah mtws! A zafafe kamar faɗa ta ce
"Ta tafi garinsu yau ɗin nan, wacca ta rakata tasha bata ɗaɗe da dawowa ba... "
Da sauri Habib ya miƙe ba tare da ya saurari sauran zancen nata ba ya bar gidan abincin da sauri, Sajida bata gama mamakin dalilin fitarsa ba sai ta ji ƙarar jan mota da ƙarfin gaske. Taɓe baki ta yi tare da miƙewa tabar wurin a ranta tana ƙara tsanar Hujayrah, duk ita ce ta ja musu kwantai a gidan abincin da yanzu son samu mazaje ƙila ma har an fara batun aure. (O'o'ohhhh! Su Sajidallare 🤭wanga budget haka kamar wata shugaban ƙasa, to in kinsa Haƙuri Hujayrah ta bar muku gidan abinci sai ki yi yadda kike so da sauran muƙarrabanki ni da My Esteem fans Munyi nan🏃♀️🏃♀️🏃♀️🏃♀️)
Bayan Habib ya bar gidan abincin da saura ya shiga mota sai ya faɗama driver ya wuce tashan garin da sauri kar ta koma garinsu, kamar jira drivan yake ya figa motar a guje suka wurin direct suka nufa tashar garin. Bayan sun sauka shi da driver suka fito nemanta a motocin da suke lodi zuwa Kaduna, gangs ɗin black scorpion squad suna cikin mota basu fita ba, kasa haƙuri na yi akan su waye wa'innan mutanan da basa fita sai cikin dare, leƙa window motar na yi habawa da sauri na dafe ƙirjina saboda lugudan bugun da yake. Tiƙa-tiƙan maza ne su huɗu suna zaune a bayan mota, baƙaƙe ne siɗik! Fuskar nan tasu babu annuri ga ɓaƙin tabarau da kowannansu ya rattafa a idanunsa, baƙin suit suka saka, ga shegen aski akansu sun maƙala Bluetooth a kunnansu na dama,kai in taƙaice muku dole su daina fita da rana saboda ƙirarsu, domin za su sha kallo wurin mutane.
Habib da driver sun yawace tasha baki ɗaya amma basu ganta ba, daga baya suka fara tambayar mutane ko sun ganta kowa sai ce musu yake bai ga mai kalar idon ba,haka suka haƙura suka dawo cikin motar, waya Habib ya ɗauka ya kira Ogansa ya sanar masa akan ta koma garinsu don wata a gidan abincin ta ce musu ta tafi tasha, yanzu haka sun duba ko'ina a tashar amma basu ganta ba, wani ne a cikin ƴan union ya ce wata motar Kaduna bata ɗaɗe da barin tashi ba, ƙila tana cikin motan.A can Alhaji Sambo Dala ya saki wani ƙasaitaccan murmushi sai kawai ya ce su dawo aikinsu ya ƙare na nemanta, yanzu zai kira yaransa na Kaduna su fara nasu aikin, cike da farin ciki Habib ya amsa masa da "To" don ya ƙagara su ga yarinyar ya huta, kar a samu matsala Ogansu yama iyalinsu irin yadda yama ɗiyar Eze wanda sanadiyyar haka cutar Depression ta kama Eze yanzu haka ya koma garinsu ana mishi magani don hauka tuburan yake.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Ƙungiyar Black Pytons Society*
*ƙarfe 1:30am na dare*
Wani irin sauti ne mai kama da kukan mujiya ke tashi sama-sama a ɗakin wanda haske bai wadace shi ba, kamar wancan karon mutane ne sanye da baƙaƙen kaya sun zagaye wani tanƙameman gunki mai suffar maciji hannayansu riƙe da ƙoƙo kamar wancan karon. Lokaci guda suka fara surkulle suna faɗin wasu yarurruka wanda bansan daga ina suka samo yaran ba,har da muryoyin mata a cikin masu surkullan, sosai suke surkullan tun suna yi a hankula har koma yinsa da ƙarfi kuma da sauri-sauri, ga sautin nan mai kama da kukan mujiya sai ƙara tashi yake, babu zato babu tsammani wani abu mai nauyin gaskiya ya sauka ji kake Dammmmmm! Sai da ƙasa ta girgiza babu wanda a cikinsu ya yi gezau sai ni mai ɗaukar rahoto domin na firgita matuƙa-ainun kamar wancan karon,su kuma ko a jikinsu basu tsaya da surkullansu ba.
Bayan Demon King da DODO ƘURNUSSA wanda yake a suffar maciji sun sauka sai suka taka zuwa mazauninsu, lokaci guda mutanan suka tsaya da surkullan. Cikin muryar nan tashi mai cike da hargagi Demon king ya fara magana
"Ya batun yarinyar da muka saka nemanta Linkakuuu!"
Alhaji Sambo Dala wanda yasan kusan zaman nan nasu akan yarinyar ce hankalinsa a ɗan tashe yake a ta wani gefan, amma idan ya tuna yarinyar ta koma gida, yaransa na Kaduna za su har ƙauyan su saceta sai ya yi farin ciki fushi DODO ƘURNUSSA ba zai sauka akan ahalinsa ba. Cike da girmamawa Alhaji Sambo Dala ya ce
"Demon king ina gab da kawota Ƙungiya, nasan inda take yanzu"
Wata iriyar mahaukaciyar dariya Demon king ya tintse dashi sosai yake dariyar har ƙasa na girgiza, sai can ya tsagaita da dariyar kamar ɗaukewar ruwan sama ya duba Alhaji Sambo Dala ya ce
"Ka yi gaggawar nemanta ka kawota Ƙungiya, kar ka bari lokacin da DODO ƘURNUSSA ya ɗibam maka ya wuce, idan ka bari ya wuce kasan sauran, sannan ina ƙara jaddada maka yarinyar ba kanwar lasa bace, akwai hatsabiban jinsin aljanu wa'inda suke bata kariya ta kowani fanni, ka kula! Ka kula! Ina sake jaddada maka ka kula Linkakuuu!!! "
Sosai Alhaji Sambo Dala yake gyaɗa kansa kamar wani ƙadangare,a ranta yana cewa'Dole ya nemota kar a samu matsala ya bani ya lalace' Demon king ya ɗauko wata maganar yana cewa
" Kunsan akwai bikin Ƙungiya da ake a duk shekara, members na kowani ƙasa suna halartar bikin, to tun yanzu za a fara shiri dole ne kowannanku ya tsawaita neman yara kamar yadda kuka sani saboda bikin,Sannan ina mai farin cikin sanar muku mun ƙara kafa wasu rassa a ƙasashe uku a Africa, don haka a bikin da za a ƙaddamar da sababbin ƙungiyoyin ga babbar Ƙungiya kowa yasan ɗan uwansa "
Yana gama maganar wa'innan mutanen da suke fitowa a wata ƙofa ɓangarori biyu suka fito, kamar wancan karon haka suka sha jinin da pepper soup na naman yara,bayan mutanan sun koma a ta ƙofar da suka fito sai lokaci guda Demon king da DODO ƘURNUSSA suka ɓace suma su Alhaji Sambo Dala da sauran members na Ƙungiya suka ɓace, gidan ya nutse cikin ruwa... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Kwanar kwara ƙwai, Kaduna state.Nijeriya*
A ɓangaren Hannatu a washe garin ranar suka nufi ƙauyan Ciri-tawa ita da matar mai unguwa wurin boka mai zamani. Sun iske layi haka suka haƙura layi ya zo kansu, koda suka sameshi da batun aikin ya koma kan ɗanta, dariya ya tintsire dashi, ya ɗaɗe yana dariya sai can ya dubesu muryar irin na mata ya ce
"Ahhayye Chasss sakalubaye!!! Ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya da kyau aikin ya yi kenan"
Da sauri Hannatu ta ce
"A taimaka boka mai zamani asirin ya bar yaron"
Ɗaukar jambaki da madubi ya yi yana shafa jambakin yana kallon madubin,bayan ya sake shafa jambakin sai ya ajiye kayan kwalliyan gefe ya dubi su Hannatu fuska a ɗaure ya fara magana da asalin muryarsa ya ce
"Yi min shiru munafuka ko kin manta kashedin da na yi miki ne akan maganin,ba nace Karki bari a samu matsala ba don banda makarin maganin, mun yi haka dake ko a'a"
Da sauri Hannatu ta gyaɗa kai, sai ya ci gaba da cewa
"Sai ki yi haƙuri don yaranki yanzu ya fara sata, har ya ƙare rayuwarsa akan sata zai ƙareta, ku tashi ku bani wurin akwai mutane a layi, matan banza kawai masu kalle jikin dirarrun mata irin mu masu ƙirar coca cola"
Wani irin matsanancin kuka Hannatu ta fashe dashi, gwiwarta biyu ta zube a ƙasa tana roƙonsa ya yi haƙuri ya karya sihirin tana mutuwar son ɗanta(ƴar banza ai da Salim bawan Allah kika so laƙawa asirin satar ai gashi nan ya koma bisa kan shalelanki 💃😂🤭🏃♀️)
Boka mai zamani bai kulata ba sai ma ɗaukar madubinsa ya yi yana duba gashin dokin da ya saka a kai yana sake gyarawa, bayan ya ajiye madubin ya dakama Hannatu wata uwar tsawa wanda sai hantar cikinta data matar mai unguwa ta kaɗa tsabar firgita da suka yi. Cikin muryarsa ta asali ya fara magana a zafafe yana cewa
"Karki lalatamin jiki da kukanki mana! Abu ɗaye ne zamu iya miki idan kin yarda to tabbas zamu karya asirin ya dawo baya sata!"
Da sauri Hannatu ta gyaɗa kai tana farin ciki ta ce
"Eh eh ina sauraron abinda zan yi"
"Bake za ki yi ba, mu ne zamu yi ba komai bane illa mai dashi ɗan uwanmu, ita kaɗai ce hanyar da zai daina sata ya koma shiga irin tamu, ƙila ya samu Customer namiji mai kuɗin ya yi Wuffff! Dashi, shikenan ɗiyarki ta yi goshi, ahayyeee Chasss sakalubaye "
Ai Hannatu bata san lokacin da ta furta
" Dan daudu Jamilu zai komaaaaa! "
" Sosai ma Kuwa rassss "
Ɗora hannu a kai Hannatu ta yi tana cewa
"Na shiga uku na lalace ni Hannatu babu sauƙi ciwon arne, ɗan daudu Jamilu na zai koma wayyo ni Hannatu"
Sai a yanzu matar mai unguwa ta dubi Hannatu ta ce
"Hannatu idan wannan ce mafitar gwara ki yarda, domin da a ce kin haifa ɓarawo gwanda a ce kin haifa ɗan daudu ko ba komai jama'a uziri za su yi miki akan haka ƙaddararsa ta zo amma fa idan kin ji"
Shiru Hannatu ta yi tana gunki kuka sai can ta dubi boka ta ce
"Shikenan na yarda a mai dashi hakan, ba laifin kowa bane illa na Murja za ta san ta aikata min haka, da sannu za ta gane shayi ruwa ne"
Umurtarsu ya yi da su wuje zai yi musu aikin. Jiki a sanyaye su Hannatu suka kwaso ƙafarsu kwasai-kwasai zuwa inda zasu samu abin hawa, masu mashina biyu suka tara sannan suka hau sai garinsu. Koda Hannatu da iso gida jikinta duk babu ƙwari, haka ta shimfiɗe a bisa gado ta kwanta domin wata masassara ce take niyyar yi mata sallama. Koda Alhaji Zakari cya dawo ya tambayeta bata da lafiya kai kawai ta iya gyaɗa masa... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren Murja bayan yaranta sun zo sai taba kowacce dubu goma ta ja jari, sosai suka shiga farin ciki musamman Hadiza babbar ɗiyarta shikenan za ta ba mijinta ko don ya ƙara sonta akan sauran matanshi, ta ji daɗin yi musu wulaƙanci daman duk ɗan kuɗin da Murja take bata don ta ja jari mijin yake amshewa yana mata daɗin baki akan yafi sonta fiye da sauran matan nashi. Ita kuma Balki kayan mata da ledar ɗaki take da niyyar siya saboda mijinta zai ƙara sabon aure. Gwara-gwaransu ita ce Aliya wacca bata daɗe da auran ba, bata da matsalar komai illa uwar mijinta da ta tasota gaba, ga mijin baya goyan bayanta duk da wani lokacin ita ce keda gaskiya,ga uwar mijinta da shegen kwaɗayi, har kwandon sharar Aliya take dubawa taga abinda suka ci basu bata ba. Idan kuma mijin Aliya ya dawo daga wurin aiki da baƙar leda shikenan hankalin sirikar zai tashi ta dinga safa da marwa a ƙofar ɗakinsu ko kuma ta ajiye tabarmarta a daidai windon ɗakinsu tana jin wace waina suke toyawa a ciki,haka Aliya take haƙuri a gidan ba tare da ta sanar ma mahaifiyarta ba.
Bayan su Hadiza sun yi lafiyayyan girki har da nama wanda Murja ta aiki kasuwa, sai Murja ta dubi babbar ɗiyarta ta ce
"Ta baba wace matsala ce kika sanar min idan kin zo za mu tattauna"
"Ai har na warware matsala ma Inna yanzu bani da matsalar komai" cewar Hadiza wacca daman ƙarya taso ta yi Innarta ta bata kuɗi to tunda yanzu ta bata har dubu goma ai shikenan matsalar ta gyaru. Sun daɗe suna hira wanda sai wurin yamma kowa ya koma gidanshi .
.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangarensu Mammi suna tafiyar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali. Salim ya tafi Zaria shi da baba Musa har baba Musa ya saka shi a wata government School a kusa da inda suke kasuwanci.
Abu ɗaya ne ke matuƙar damun Abbu da Mammi shi ne rashin sanyin idaniyarsu Hujayrah, musamman Abbu kullum da tunaninta yake kwana yake tashi fatan a kullum Allah yasa tana cikin ƙoshin lafiya, sannan duk sallar da zai yi sai ya roƙa mata kariyar Ubangiji a duk inda take. Mammi ma kusan hakane a wurin duk da shirman Hujayrah wani lokacin yana bata haushi amma yanzu har marmarin jin muryarta take, sosai ta yi kewar ɗiyarta kamar Abbu kullum da tunanin halin da Hujayrah take ciki take, daidai da rana ɗaya bata taɓa tsallakewa ba tare da zuciyarta ta ambaci sunan Hujayrah ba. Addu'arta a kullum bai wuce Allah yasa tana cikin ƙoshin lafiya ba.
Haka ma a ɓangaren Kakulle tun lokacin da Hujayrah tabar garin zuciyarta take tunaninta, sosai ta yi kewarta tare da addu'ar kada Allah ya ɗauki ranta ba tare da ta sake haɗa ido da jikarta wacca tafi soyuwa a gareta. Yanzu haka Kakulle ce ke bada maganin, su Attine da sauran yaranta har da jikokin sunyi-sunyi har sun gaji akan taba ɗaya daga cikinsu laƙanin bada maganin tunda Hujayrah bata nan amma ta ƙi ta kafe akan Hujayrah ce ƙarshan wacca za ta iya ba laƙanin bada magani. Wannan kenan... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren Alhaji Zakari abubuwa sun yi masa zafi sosai a kai har ya rasa wanne zai fara ɗaua, ga wani sabon tashin hankalin shi ne matar ƙaninsa Zubairu ta taso shi gaba tabi ta hana shi rawar gaban hantsi kullum cikin zullumi yake da taraddudi akan kar wata rana ta tona masa asiri, ya shiga uku ya lalace mutanan gari suna yi masa kallon na Allah darajarsa ta zube a idanunsu. Kamar duk lokacin da Murja take son ganinsa a can ƙauyan Kwarin ɗan dodo suke haɗuwa da ita, yau ma hakan ta kasance bayan ta kirashi da wata number wanda ya yi saving da Mati saboda Hannatu, sai ya ɗauka ta ce masa su haɗu a inda suka saba haɗuwa. Rai bai so ba haka ya miƙe ya ɗauki mukullin mashin ɗinshi ya ƙara gaba cko sauraron maganar da Hannatu take masa bai yi ba. Direct ya nufi ƙauyan har inda ta ce su haɗu,ya sameta ta saka hijab da niƙaf tana tsaye a wajan wajan bishiyar lemu kusa da wani gida tana kallonsa. Koda ya iso wurin sai ya dubeta cikin ɓacin rai ya ce... ✍️
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***